100% found this document useful (1 vote)
5K views20 pages

Ajiya A Duhu By Billyn Abdull [www.aihausanovels.com.ng]

An interesting new novel by Billy abdul

Uploaded by

seeyamhamad24
Copyright
© © All Rights Reserved
Available Formats
Download as TXT, PDF, TXT or read online on Scribd
Download as txt, pdf, or txt
100% found this document useful (1 vote)
5K views20 pages

Ajiya A Duhu By Billyn Abdull [www.aihausanovels.com.ng]

An interesting new novel by Billy abdul

Uploaded by

seeyamhamad24
Copyright
© © All Rights Reserved
Available Formats
Download as TXT, PDF, TXT or read online on Scribd
Download as txt, pdf, or txt
Download as txt, pdf, or txt
You are on page 1/ 20

********************** ⬇ **************************

********** Ai Hausa Novels ****************


*************************⬆ **********************

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery,
Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from
our blog.

Visit > https://www.aihausanovels.com.ng

Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa
novel ko kuma post.

Email > aihausabooks@gmail.com

******* FOLLOW US ******

Facebook: Ai Hausa Novels

Twitter: Ai Hausa Novels

Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels

Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search
na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu.

********************** ⬇ **************************
*************** Ai Hausa Novels ****************
********************** ⬆ **************************

[10/12, 1:46 pm] Leematu: *_Typing📲_*

*_💞AJIYA A DUHU....💞_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_‫*_ِبْس ِم الَّلِه الَّر ْح َٰمِن الَّر ِحيم‬


_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂_

0101
01
0️⃣
1️⃣

.......Ƙaddarorin rayuwa tamkar TASWIRA ce dake zane a takardar lissafin rayuwar


kowanne ɗan adam, duk yanda ka so gogesu ko san kauce musu ba lallai ne ka samu
makaman yaƙin ba balle GARKUWAR kare kanka daga isowarsu gareka ko mai gajartar
tsahon shekaru ko yawaitarsu. A wasu lokutan mukanyi kuka ne da hawaye, sai dai
kukan ZUCIYA shine mafi ciwo da ɗacin kuka da yafi kassara rayuwarmu da nasarorinmu
a ɓoye ko a zahirance da bama iya mantawa. Dan a wasu lokutan har tambarin tabon da
zamu iya ringa tunawa a lokaci bayan lokacin yake bar mana.
A farkon haihuwar mu iyayenmu sune GARKUWARMU, dan sukan sadaukar da komai nasu
ne domin lulluɓe RAYUWARMU da dukkan fatansu. Sukan rainemu da shauƙi da yaƙini har
zuwa girmanmu. Hakan yake saka SOYAYYAR su bata taɓa iya goguwa a ZUKATANMU, sannan
takan banbanta da irin kowacce soyayya da zata biyo bayanta. Koda hukuntamu sukai
mukaji zafi mukai kuka wannan soyayyar tasu bata taɓa canja kanta a ZUKATANMU
saboda su ɗin sune dai ɗaya tamkar da dubu a dukkan abubuwan dake zagaye damu na
NASARA ko akasinta.
A lokacin da girmanmu ke ƙara yawaita sai TSUFA ya riskesu. Mu kuma ƘURUCIYA
ta baibayemu. Sai dai me daga lokacin daka iya tantance ma'anar FARI da ƁAKI a yau
ɗinka da gobenka littafin ƘADDARARKA kuma ya fara kenan da manyan zanukan layukan
dake bayyana JARABAWOYINKA. Gwagwarmaya ta zama ƙawa ko abokin RAYUWARKA. Yaƙin ba
yana farawa da gwagwarmayar RAYUWAR DUNIYAR kawai bane ba. Harda ta neman LAHIRA da
zaɓama kai makoma ƙyaƙyƙyawa ko akasinta. Domin kuwa fara rayuwar girman na farawa
ne da daidaiton mizanin ayyukan samun LADANKA da kuma ZUNUBI duk a bayyane kuma a
rubuce ga wanda ya HALICCEKA. Iyayenmu kan gama gwagwarmayar ƙuruciyarmu, sannan su
koma ta girmanmu babu gajiyawa saboda su ɗin na dabanne a cikin daban a garemu.
A lissafin fara fahimtar kanka da tabbatar da WANENE kai, da wahala kaga babu
armashin soyayyar ƙuruciya da takanyi kutse a ƙaddararka. Ba soyayyar bace ba kawai
abar kallo ko zama daban a gareka ko wanda ke tare da rayuwarka. A yaya SOYAYYAR ta
FARA? Ko ta ƙare? Ko ta kasance? Ko ta cigaba da wanzuwa? Itace madubin dubawarka
ko masu juriyar bibiyar labarinka.

★ Ƴammata ne uku sanye cikin kayan hidimar ƙasa. Tsaye suke a bakin titi
kowacce hannunta riƙe da hannun trolling alamar abin hawa suke jira. Dan suna ma ta
ƙoƙarin tsaida napep amma mafi yawanci sai kaga akwai wani a ciki ta yanda bazai
isa su ukun duk su shiga ciki ba. Cikin ɗan damuwa da ƙosawa ta tsakkiyarsu da bata
da yawan fara'ar fuska ta ɗaga kai tana kallon sararin samaniya dake haɗa hadari.
Ko kaɗan bata fatan ruwan nan ya taɓa ta. Dan hakan baya zama mai sauƙi a gareta
shiyyasa tafi kowa damuwa da samun abin hawan nasu, daɗin daɗawa tafiyarsu mai nisa
ce. Dan kuwa jihar Kaduna suka nufa.
Fara tasowar iskar hadarin ta sata duban ƴan uwan nata idanunta na cika da
ƙwalla. Sai dai kafin ta samu damar cewa wani abu wata jar mota tai parking a
gabansu. Su duka idanu suka zubama motar, sai dai buɗewa da fitowar matashin
saurayin dake ciki ya saka biyu a cikinsu sakin murmushi da mamaki. Yayinda ta
tsakkiyar sun nan dai ta sake haɗe ƙyaƙyƙyawar fuskarta tana mai kauda kanta gefe.
Shi kam saurayin nan gaba ɗaya hankalinsa na kanta. Ya ƙaraso gabansu dai-dai
saitinta ya tsaya tare da faɗin, “Yanzu duk saurin da nake sai da kika nema guje
min?”.
Fuska ta sake haɗewa tana ɗan matsawa baya. Kansa ya ɗan sosa yana mai sakin
murmushi. Hankalinsa ya maida ga sauran biyu cikin jifansu da harar wasa ya ce,
“Amana batace dai haka ba friends. Kamar ni ina daku amma a so haɗa kai da ku a
gudu min”.
Dariya suka ɗanyi a lokaci ɗaya. Ta gefen damarsa mai ɗan jiki kaɗan ta bashi
amsa da, “Ina ai bazamu taɓa yarda hakan ta kasance ba. Ko an gudu maka mu zamu
kawoka har wajen ɓuyar RK. Amma ai mana afuwa mutuniyar taka ce ta addabemu da
tafiyar sassafen nan. Kasan jiya ko barcin kirki batai ba saboda farin cikin zata
koma gida taga Ammie”.
“Ko dai tana farin cikin zata gudu daga Jos ta bar ɗan nacinta ba?”. Ya
faɗa idonsa a kan budurwar tsakkiyar dai. Da sauri ta gefen haggunta ta amshe da
“Haba RK kaima kasan ba haka bane sam”.
“Humm Aneesa dama ai baƙya son laifinta ke tuni na fahimci haka. Duk ta inda
aka ɓullo sai kin kareta. Ni dai yanzu ku shiga mota muje kunga ruwa na shirin
sakkowa karya jiƙa min sarauniyata”. Kafin wani cikinsu ya bashi amsa a hankali ta
fara jan akwatinta domin barin wajen. Saurin riƙo akwatin yay, hakan ya sata
tsayawa cak batare da ta juyo ba. Zai yi magana Aneesa tai saurin girgiza masa kai
tare da amsar akwatin. Babu musu ya sakar mata yaja da baya.
Akwatin tai ƙoƙarin ƙara ja Aneesa ta sake riƙewa. Hakan ya sata juyowa a
fusace zatai magana a zatonta shine sai taga Aneesa. Idanunta tai wani irin
lumshewa da cizar gefen lips ɗin ta irin na takaicin nan kawai. Hakan ya saka
Aneesa sakin murmushi dan tasan ta gama ƙurewa a fusata. “Kiyi haƙuri dan ALLAH” ta
faɗa da sauri, bata jira amsarta ba ta cigaba da faɗin, “Kiyi haƙuri mu bisa
_Maanal_, kalla garin nan ki gani hadari ne da akoda yaushe za'a iya fara ruwa.
Kinfi kowa sannin illar da hakan yake miki. Kema kin san iyakarsa yace zai kaimu
tasha ne kawai. Daga yau ne fa an rabu shike nan kuma. Dan ALLAH kada ki bari kuyi
irin wannan rabuwar da shi. RK bai cancanci hakan daga gareki ba. Ko bazaki taɓa
amince masa ba kada ki munana masa a yau ɗin nan da zamu rabu. Yanda baki
wulaƙantasa ba a baya yanzu karki aikata. A rabu lafiya daga haka kuma bashi ke nan
ba tunda ko lambarki dai yanzu bai da ita ballema kice zai cigaba da takura miki,
ba kuma sanin gidanku yay ba idan kika cire sunan gari”.
A hankali ta buɗe idanunta da suka gama kaɗawa, ga hawaye sun cika su zubowa
kawai ya rage. Lips ɗinta ta buɗe zatai magana ruwa yay wani irin kecewa lokaci
guda. Gaba ɗaya ta rikice. Har bata ma san Aneesa taja hannunta ta tura cikin motar
ba itama ta shiga. Sai da taji babu saukar ruwan a kanta sai ƙararsa sannan ta
farga ta ɗago kanta data cusa cikin ƙafafunta da sauri. Waigowar da zatai suka haɗa
ido da RK daya wani zuba mata ido kamar zai cinyeta. Nata ta janye da sauri tana
mai juyawa ta kalla ƙawayen nata. Da sauri Zeezah ta nuna Aneesa alamar babu
ruwanta itace. Aneesar ma saita marairaice mata fuska alamar kartace komai dan
ALLAH. Harara ta sakar mata tare da ɗauke kanta, sai kawai ta juya tana goge
fuskarta da ruwa ya fara taɓawa da handkhachief.....

Tunda motar ta fara tafiya babu wanda yay magana. Ga ruwa ana kwararawa kamar
da bakin ƙwarya. Tuni wasu motocin ma sun koma gefen titin sun tsaya. Ganin sunzo
sun wuce tasha yasa Zeezah yinƙurin yin magana. Da sauri RK dake kallonsu ta mirror
yay mata alamar roƙon tai shiru. Haɗiye maganar tayi tana murmushi, sai kuma ta ɗan
dubi Maanal da kanta ke sunkuye novel a hannunta alamar karatu takeyi, shiyyasa
bata san wainar da ake toyawa ba ma.
Shima dai RK ya raba hankalinsa biyu ne. Rabi ga tuƙi rabi a kallonta.
Maanal ƙyaƙyawar yarinya ce kuma nutsatstsiya. Za'a iya kiranta tsaka tsaki a
tsaho, a wani gurin kuwa ma wasu kai tsaye zasu kirata doguwar duk da ba shalleliya
bace, sannan bata da wani jikin kirki. A duk wanda ya santa musamman a tsukun
shekarun nan zai iya sakata a jerin miskilayen mutane. Bata da yawan magana, hakama
bata da fara'a ko yawan walwala sam. Dan da wahala kaga murmushi ma a fuskar Maanal
balle akai ga dariya. Akoda yaushe fuskarta ciɗin-ciɗin take. Hatta da magana ma
sai taso take yinta. In har ba wani abu take mai muhimmanci ba to akoda yaushe zaka
samu novel a hannunta tana karantawa. Hakan na nufin ita ɗin mayyar karance-karance
ce. Dan zamu iya cewa ma yawan karance-karance nata ne yasa koda yaushe zaka samu
idanunta da eyeglasses fari tas da mutane da yawa basa iya ɓoye mata cewar yana
mata matuƙar ƙyau. Itama kanta tasan yana mata ƙyawun, dan takai tun ma tana
sakashi domin karatu, har ya zame mata jiki akoda yaushe zaka ganshi tare da ita in
har ba barci take ba ko wani abinda ba'a buƙatarsa. Sai dai kuma abinda kowa bai
sani ba wani dalili ne daban ya ɗabi'antata da yawan daka gilashin akoda yaushe
bawai dan karance-karance kawai ba, duk da a ɓangaren karatun ma yana bata
gudummawa matuƙa........✍️
✨ZAFAFAN DAI ✨

1 ƘALBIM (Mamu gee)


2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)
3 DUNIYAR MU (Huguma)
4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)

Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000

0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070

Kati MTN:- 09032345899

Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭_*


[10/12, 1:46 pm] Leematu: *_Typing📲_*

*_💞AJIYA A DUHU....💞_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_‫*_ِبْس ِم الَّلِه الَّر ْح َٰمِن الَّر ِحيم‬


_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂_

_________________

Aslm barkanmu da wannan lokaci


Ina Mai farin cikin sanar daku cewa Zuzeam ventures takawo maku ingantattun
magunguna masu inganci cikin Aminci Muna da kaya kamar haka
Mallaka Maganin sanyi
Maganin cire tumbiMaganin farin jini
Maganin matsiMaganin mata
Maganin sa ni’ima da dandano
Dulka Amare Set na gyran jiki
Set na amarya
Tabaje tsumin Gomba
Xuma kiba ta hips and Brest
Magungunan gyran Brest
Magungunan Karin hips
Maganin sliming
Muna da kaya masu inganci cikin sauki da rahusa
Ina wadda keneman mallaka sahihiya quaranty wlh hajiya kixo ga zuzeam ventures
xakiji ddin mallaka duk fadin ran ogah duk fadansa wlh sai yyi sanyi 08144015291
Idan maganin mata kikeso akwai
Idan gyran jiki kikeso gyran fata gyran Brest magungunan sa kiba da hips
DOMIN samunta Kai tsaye kira wannan no 08144015291 DOMIN mgn da ita whatapp
08144015291muna tura kayanmu ko ina cikin iKon allah 🥰👌🏻
Bononza Bononza Tsimin mangoro 1k🥭 Tsimin dabino 1k Gumba ukku balai 700 Gumba aya
da nonon rakumi 700 Garin kafi ciccibi 500
Garin bata gaban kishiya 500
Matsin mallaka tada zaune tsaye 2500
Turaren mallaka ba aba mai kishiya 2500 Total kayan 9500
Za a bakisu akan 3800
Kuma mutun goman farko nadakyautar Abun 2k
ASSALAMU ALAIKUM ALHAMDULILLAH YAN UWA NEW PROMO YA KAMMALA😁😁😁 da 5k dinki ki
kwashi kayan 12k hajiyata 😃🙃Kazar gadali ta mallara Rabi 3500 Tsimin gam gam 1500
Ruwan kara zunzurutun dadı😋800 Garin 7in1 1k Gumba 3 balai 500 Gumba kwakwa da
dabino 500 Infection ruwan tsarki 1k Garin zunzurutun dadi 1200 Matsin ba a fira d
wando 500 Matsin infection mai matse mace gam 500 12k All at 5k
https://wa.link/l1gcz8 kedai dannan link dinnan don samun naki ki maza kiyi bucking
koda kudinki saida Rabonki

_______________

0202
02
0️⃣
2️⃣

.......Ganin tafiyar taƙi ƙarewa yasata kai hannu ta ɗan gyara eyeglasses ɗin tare
da ɗagowa ta kalla titi, har yanzu ruwa ake zulawa, sai dai hakan bai hanata
fahimtar har sun fara barin gari Jos ba. Da mamaki a karo na farko ta dubi RK da
tunda ta ɗago ya kama kansa daga satar kallonta da yake yi. Kamar zatai magana sai
kuma ta kauda kanta. Sake maidawa tayi ga book ɗin, sai dai ba karatun take ba tayi
shiru ne kawai tana juya maganar da take son fitarwa. Sai da ta mula dan kanta
sannan a hankali cikin sassanyar muryarta da take matuƙar zama mafi girman rowa ga
masu son ji irinsu RK ta furta. “Bayan waccan tashar akwai wata ne a gaba naga mun
wuce?”.
Har cikin tsakkiyar kai yaji gajeren zancen nata. Sai da ya wani lumshe
idanunsa ya fuɗe tare da sakin murmushi sannan ya bata amsa da, “Bazan iya saukeki
a ko'ina cikin ruwan nan ba kiyi haƙuri sai a Abuja”.
Ɗagowa tai kamar zata kallesa sai kuma ta fasa. Sake maida kanta tai ga buk
ɗin kawai tana ɗan cizar gefen lips ɗinta. Murmushi ya ɗan saki shima dan ya
fahimci wannan cizar lips ɗin nata takan yisa a duk sanda takai ƙarshen takaicin da
har ta rasa abin cewa.
“Kiyi haƙuri Please”.
Ya sake faɗa a hankali. Bata tanka masa ba, sai ma sake maida kanta tai a karatun
kawai. Shima sai yay gum da bakinsa ya maida hankalinsa gasu Zezaa tunda dai ya
samu da alama ta haƙuran. Tanata karatunta suna hirarsu. Yawan sakkota a hirar tasu
da dariyar da suke ya fara gundurarta, sai kawai ta manna Bluetooth a kunnenta ta
ajiye book ɗin ta lumshe idanunta. A haka barci ya kwasheta tana sauraren karatun
Alkur'ani data sanya daga bakin Gwani Abdullahi Zaria. Har suna gab da shigowa
garin Abuja ruwan akeyi, har kuma lokacin Maanal barci take sosai dan sam batai
isashen barci jiya ba. Addu'a yay tayi da fatan subar Abuja bata farka ba. Dan
yasan zata iya tuburewa akan ya ajiyesu anan ɗin, aiko addu'ar tasa bata amsu ba.
Dan sun wuce zuba kaɗan kuwa ta farka. Agogo ta fara kalla sannan ta juya tana
kallon su Zezaah.
“Muna ina ne yanzu?”..
Ɗan kallon juna sukayi, sai Zezaah tai tsulum tace, “Mun fita a Abuja”.
Da mamaki Maanal dake kallon titi ta ce, “Mun fita fa? Wannan ba hanyar
suleja bace? Ko nan ba madalla bane?”. Yanda ta ƙare maganar tana kallon RK ya
sashi ɗan sosa goshinsa yana furzar da iska. Sai kuma ya jinjina mata kai ganin ta
wani tsaresa da idanunta dake matuƙar firgita masa lissafi. Kanta ta ɗauke tana
faɗin, “To Alhamdullah sai ka sauke mu a dikko kawai ai zamu samu motar Kaduna a
wajen”.
Sosai fuskarsa ta nuna damuwa. A marairaice ya ce, “Haba miya rage Baby,
tunda mukazo nan can ma bazai gagara ba. Kiyi haƙuri mu ƙarasa, ina Abuja ina
Kaduna”.
Yanda yake mata magana kamar zai yi kuka yasa haushi ya sake kamata. Mutumin
nan sam baya ganewa, ta rasa mi kuma zata masa ya gane ɗin. Duk yanda taso hanasa
kaisu kadunar hakan bai yiwu ba. Dole tana ji tana gani ya ɗauki hanya. Hankalinta
ta sake maidawa akan novel ɗinta ta sharesa. Sai su Zeezah ne keta hirarsu da shi.
Yanzun ma ko sun sakkota bata tankawa. Suna isowa Kawo tace ita anan zata sauka. Yi
yay kamar bai jita ba. Cikin ɓacin rai ta juya tana kallon su Neesa. Cikin jin
haushi, duk da muryar tata na fita ne da sanyinta da nutsuwa ta furta, “Malamai
kusa ya saukeni anan tunda naga da sawarku yake komai”.
Kafimma su bata amsa RK yay saurin faɗin, “Sorry Baby babu ruwansu. Ni
dai fatana sai na direki har ƙofar gida dan ALLAH”.
Yanzu kam harara ta zuba masa. Ya wani lumshe idanu da buɗewa a lokaci guda ya
saukesu a kanta. Da tasan ta'asar da harar nan ke masa data tausaya masa ta bari.
Ganin dai zata kife da shi yay ƴar gyaran murya yana wani marairaice fuska. “Please
ki tausaya min hararar nan illa take min”. Ya faɗa a wani irin hankali kamar mai
raɗa har yana ƙoƙarin ɗan matso ta. Janye jikinta tai ta lafe a murfin tana rumtse
ido da ƙarfi. Daga haka bata sake magana ba. Su Neesa ne suka shiga nuna masa hanya
har anguwarsu Maanal ɗin data kasance cikin manyan anguwannin da kadunawa ke ji da
su (Ina da tambaya?, wai Kaduna akwai anguwanni masu ƙyau dan ALLAH ko sai sun zo
Kanon mu suke gani kawai😂. 🏃🏃🏃Bari na ware kafin ƴan Kaduna su maidani awara yau ɗin
😘 Dai-dai ƙofar wani katafaren farin gate da
nan kun san bazazzage ba sauƙi).
akaima ado da golden suka tsaya. Ya wani sauke ajiyar zuciya yana kallon gidan da
ƙyau. Eh lallai ashe itama ƴar masu kuɗi ce. Dan gidan nan kam dai ya kai a kirashi
gida.....
Fitar Maanal a motar ta sashi saurin katsewar tunanin sa. Shima da sauri ya
buɗe ya fita. Dai-dai tana ƙoƙarin buɗe booth. Shine yay saurin sakko mata da
akwatin ta. Ya juya da nufin sauke nasu Neesa taja kayanta. Su Aneesa da suka gama
fahimtar mi take shirin yi duk suka fito. Magana Zezaah tai yunƙurin mata tai mata
wani kallo na babu ruwanki da ni taja akwatinta tai gaba. Sai da tai ɗan taku uku
zuwa huɗu ta juyo ta kalla RK daya zama kamar gunki a tsaye. Idanunta dake cikin
gilashi ta ɗan lumshe ta buɗe a kansa. “Mun gode da ƙoƙarinka. ALLAH yabar zuminci.
Amma zan baka haƙuri dan ALLAH karka cigaba da wahalar da kanka, kamar yanda na
faɗa maka gaskiya tun a farko itace dai har yanzu. ALLAH ya haɗamu da alkairinsa a
yafi juna”..
Kafin yay wani yunƙuri harta shige gida. Ƙoƙarin binta yay da hanzari mai gadi
dake tsaye daga ciki ya babbake ko'ina ya hanashi. Dole ya dakata yana mai kai
hannu ya ɗan dafe goshinsa da furzar da iska mai nauyi...........✍️

✨ZAFAFAN DAI ✨

1 ƘALBIM (Mamu gee)


2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)
3 DUNIYAR MU (Huguma)
4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)

Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000

0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070

Kati MTN:- 09032345899

Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭_*


[10/12, 1:46 pm] Leematu: *_Typing📲_*

*_💞AJIYA A DUHU....💞_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*


*_‫*_ِبْس ِم الَّلِه الَّر ْح َٰمِن الَّر ِحيم‬
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?


id=675067e55c3130f457527f30

_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂_

0303
03
0️⃣
3️⃣

______________

Aslm barkanmu da wannan lokaci


Ina Mai farin cikin sanar daku cewa Zuzeam ventures takawo maku ingantattun
magunguna masu inganci cikin Aminci Muna da kaya kamar haka
Mallaka Maganin sanyi
Maganin cire tumbiMaganin farin jini
Maganin matsiMaganin mata
Maganin sa ni’ima da dandano
Dulka Amare Set na gyran jiki
Set na amarya
Tabaje tsumin Gomba
Xuma kiba ta hips and Brest
Magungunan gyran Brest
Magungunan Karin hips
Maganin sliming
Muna da kaya masu inganci cikin sauki da rahusa
Ina wadda keneman mallaka sahihiya quaranty wlh hajiya kixo ga zuzeam ventures
xakiji ddin mallaka duk fadin ran ogah duk fadansa wlh sai yyi sanyi 08144015291
Idan maganin mata kikeso akwai
Idan gyran jiki kikeso gyran fata gyran Brest magungunan sa kiba da hips
DOMIN samunta Kai tsaye kira wannan no 08144015291 DOMIN mgn da ita whatapp
08144015291muna tura kayanmu ko ina cikin iKon allah 🥰👌🏻
Bononza Bononza Tsimin mangoro 1k🥭 Tsimin dabino 1k Gumba ukku balai 700 Gumba aya
da nonon rakumi 700 Garin kafi ciccibi 500
Garin bata gaban kishiya 500
Matsin mallaka tada zaune tsaye 2500
Turaren mallaka ba aba mai kishiya 2500 Total kayan 9500
Za a bakisu akan 3800
Kuma mutun goman farko nadakyautar Abun 2k
ASSALAMU ALAIKUM ALHAMDULILLAH YAN UWA NEW PROMO YA KAMMALA😁😁😁 da 5k dinki ki
kwashi kayan 12k hajiyata 😃🙃Kazar gadali ta mallara Rabi 3500 Tsimin gam gam 1500
Ruwan kara zunzurutun dadı😋800 Garin 7in1 1k Gumba 3 balai 500 Gumba kwakwa da
dabino 500 Infection ruwan tsarki 1k Garin zunzurutun dadi 1200 Matsin ba a fira d
wando 500 Matsin infection mai matse mace gam 500 12k All at 5k
https://wa.link/l1gcz8 kedai dannan link dinnan don samun naki ki maza kiyi bucking
koda kudinki saida Rabonki

_______________

........“Kayi haƙuri dan ALLAH RK”. Aneesa ta dawo da RK dake bin maigadi da kallo
idanunsa sun kaɗa sosai. Iska ya ɗan sake furzarwa batare daya daina kallon maigadi
ɗin ba. Sai kuma yay murmushi da gyara tsaiwarsa hannayensa duka biyu a cikin
aljihu. Kansa ya ɗan girgiza tare da juyo da dubansa yana kallon Aneesar fuskarsa
da murmushin dake bayyana damuwarsa. “Baku min laifin komai ba Aneesa. Haka itama
banji haushinta ba sam. Sai dai bazan iya rabuwa da ita ba kamar yanda take buƙata.
Da gaske ina son ƙawarku matuƙar so da ban taɓama wata mace ba da sunan soyayya ta
aure. In dai zan jure waccan shekara gudar data shuɗe mizai hana na iya jure wannan
balle yau dana san gidansu. Zan cigaba da farauta nasan watarana zan dace in sha
ALLAH”
Zezaah da ranta yakai ƙololuwar ɓaci ta ce, “Humm amma RK kasan dai Maanal da
kafiya. Wlhy duk abinda tace bazatai ba bafa zatayin ba. Ya kamata kaima ka gane
hakan tunda dai kagani. Shekara ɗaya cur ana abu ɗaya amma komai bai canja ba. Taya
yanzu kake tunanin zata canja da kuke nesa da juna?”.
“Nabar komai a hannun UBANGIJI, shine mai sarrafa zuciyoyi a yanda yaso ai
Zulfah, ina ji a raina zata canja”. RK ya bata amsa yana haɗiye damuwarsa. Aneesa
ce tai ɗan murmushi, har cikin ranta tausayinsa take ji. Murya ta kwantar cike da
son kwantar masa da hankali ta ce, “In sha ALLAHU kam tunda ka dogara da ALLAH
zakaci riba. In dai Maanal matarka ce kuwa sai ka aura, itama nasan ba tana yin
komai danta wulaƙantaka bane, akwai dai wani dalili, saboda duk wanda yasan Maanal
sani na gaskiya yasan bata da wulaƙanci, na nesa da itane kawai ke mata kallon
girman kai amma sam ba haka bane ba wlhy”.
“Nima shaida ne Aneesa, shiyyasa nake mata uziri”.
“Nagode sosai daka fahimci haka RK. Bari muje mu ƙarasa gida muma, mun gode
sosai da ƙoƙarin ka, ALLAH yabar zuminci ya saka da alkairi. Mun tasoka tun daga
Jos”.
Murmushi ya saki mai sanyi. Sai kuma ya girgiza kansa tare da shafa
kwantaccen sajensa ya ce, “Babu damuwa. Dama Abuja zanzo ai. Ku ba nan anguwar kuke
ba kenan?.”
“Eh anguwannin duk daban-dabanne”. Zeezah ta bashi amsa.
“Oh to ku muje na kaiku ai har gida kuma. Kunga idan na tashi dawowa saina
tattaroku dan ƴar darun nan tawa al'amarin ta sai da ku a kusa”.
Dariya sukayi gaba ɗaya. Babu musu suka koma motar yaja suka bar anguwar. A
gidan su Zezaah duk suka ce ya saukesu. Dan basu da nisa da Aneesa da ƙafa ma zata
ƙarasa. Su Zeezah dai ba masu kuɗi bane ba. Amma akwai rufin asirin ALLAH. Da alama
ƴar darun tasa ta fisu komai dai kam. Godiya suka masa da sake bashi haƙuri. Ya
tabbatar musu babu komai sai ya dawo dubasu zuwa weekend. Zai kuma kirasu a waya in
sha ALLAH. Daga haka yaja motarsa ya wuce...

★★★★★

A hankali ta jingina da jikin gate ɗin ƙwalla na cika mata ido. Dauriya kawai
takeyi, amma tausayi RK ke bata matuƙa. Ta jima da fahimtar irin ɗunbin soyayyar da
yake mata a cikin idanunsa. Sai dai tasan bazata iya bashi abinda yake buƙatar ba.
Kota bashi ma zata cutar da shi ne kawai dan bazai taɓa samunta yanda yake huƙata
ba. Dan zuciyarta ta jima da mutuwa. Mutuwa irin wadda mushenta ma baida daɗin
kallo. A zahiri take Maanal, amma a zuciya tuni ta mutu, ta mutu babu ita a wannan
rayuwar... RK na tuna mata abubuwa da yawa a rayuwarta da sam bata son tunawa,
shiyyasa akoda yaushe take yakicesa a jikinta ta ƙarfin tsiya. Amma shi ya kasa
fahimtar akwai wani ciwo ne a zuciyarta da ya jima da raunata ta ta yanda babu wani
ɗa namiji da zai sake morarta.....
Raff-raff!! Sautin tafi da dariya ya sata dawowa hayyacinta. Hannu ta kai ta
share guntun hawayenta kafin ta kai dubanta ga mai dariyar da basai an mata ƙarin
bayani ba tasan Huznah ce. Ita ɗince kuwa. Ƙyaƙyƙyawar budurwa fara doguwa san kowa
ƙin wanda bai samu ba. Zata girmeta a shekaru, girma ma bana wasa ba dan Huznah
zata iya zama kusan sa'ar babbar yayarsu duk da dai ita yayar tasu zata iya
girmarta....
“Agola kafi ɗan masu gida. Wato iskanci yayi lagwada har ba'a so dawowa
gida ba kenan?”. Huznah ta faɗa tana watsa mata kallon wulaƙanci.
Idan gate ɗin da ke kusa da su ta motsa to Maanal ta tanka. Dan kuwa daga
kallo ɗayan nan bata sake dubar ko sashen da Huznah take ba taja akwatinta tai gaba
cikin tafiyarta mai sanyi da tarin nutsuwar da kowa ke ɗauka iyayi da yanga ce. Sai
dai kuma hakan a gareta normal ne. Dan tun ma tana tashen rashin jinta tafiyarta
mai sanyi ce.
Ba ƙaramin takaici rashin tankawar ya saka Huznah ba. Cikin haushi ta lailayo
ashariya ta maka ma Maanal. Sai dai yanzun ma bata samu amsa ba, Maanal ɗin kuma
bata waiwayo ta dubeta ba harta shige ɗaya daga cikin ɓangarorin gidan. Domin
ɓangare har biyar ne a gidan ciff kasancewar matan mai gidan uku ne. Sai sashensa,
sai kuma na samarin yaransa. Ƴammatan dai kowacce tana sashen uwarta ne....

Shigowarta sashen nasu da abinda ta taras ya wanke mata gaba ɗaya damuwarta.
Dan kuwa taci karo da ƴan uwanta biyu da yaransu duka sunzo gidan domin dawowar
tata kawai. Ai tuni ta watsar da damuwar RK data Huznah suka rungume juna. Sosai
suke matuƙar ƙaunar junansu ta yanda idan ka gansu kai kanka sai sun matuƙar
burgeka.
“Amma Didi kikace min ke bazaki wani zo tarbata ba”.
Dariya wadda ta kira da Didin tayi tana mai dungure mata kai da faɗin, “Naƙi
zuwa babarki ta ƙulaceni Auta”.
A tare suka kwashe da dariya, dai-dai nan wata dattijuwar mata cikin kwalliya
ta fito daga wani lungu mai nuni da hanyar kitchen ne dan hannunta riƙe yake da
wani ɗan bowl. Tuni Maanal ta saki yayunta ta nufi matar da sauri ta wani daka
tsalle ta rungumeta. Dariya yayunta da yaransu suka sanya. Yayinda matar ke faɗin,
“Oh ya ALLAHU jama'a sai yaushe Maanal zata girma ne? Yanzu idan kika karyani fa?”.
Cike da shagwaɓa, tare da sake shigewa jikin matar ta ce, “Ni dai bazan taɓa
girma ba Ammie. Nayi kewarki fiye da kowa da komai. I really miss you Ammie na”.
Ƙaramar dariya Ammien ta saki mai ƙayatarwa, tare da sake rungume ɗiyar
tata a jikinta tana mai sumbatar kanta da faɗin, “Nima nayi kewarki sosai Maanal.
Congratulations my Auta, yau dai finally an gama boko.”
“Kai Ammie dama ana gama boko?”. Ta faɗa cikin dariya mai ƙayatarwa da mutane
da yawa basu san tana yi ba. Itama Ammien dai dariyar ta sake yi, sai kuma ta
ɗagota tana mai ƙare mata kallo da ƙyau. “Auta duk kin sake rame min, kina lafiya
kuwa?”.
Kanta ta kwantar a jikin hannun Ammien data riƙe, sai kuma ta amsa da,
“Lafiya Lau nake Ammie. Kewarki ce kawai ta hanani sukuni”.
“Oh wai kin damu mutane da kewar Ammie kawai. Kina nufin mu bakiyi kewarmu ba
ne Auta?”.
“To Sarkin kishi, ALLAH Ammie ban taɓa ganin mai kishinki sama da Didi
Amal ba. Kijifa dan ALLAH, nayi kewarki itama dole sai nayi kewarta?”.
Jefota da filo Amal tayi, da sauri ta kauce tana murmushi. Yayinda Didi Shahidah
da Ammie da yaransu ke musu dariya..........✍️

✨ZAFAFAN DAI ✨

1 ƘALBIM (Mamu gee)


2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)
3 DUNIYAR MU (Huguma)
4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)

Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000
0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070

Kati MTN:- 09032345899

Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭_*


********************** ⬇ **************************
********** Ai Hausa Novels ****************
*************************⬆ **********************

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery,
Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from
our blog.

Visit > https://www.aihausanovels.com.ng

Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa
novel ko kuma post.

Email > aihausabooks@gmail.com

******* FOLLOW US ******

Facebook: Ai Hausa Novels

Twitter: Ai Hausa Novels

Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels

Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search
na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu.

********************** ⬇ **************************
*************** Ai Hausa Novels ****************
********************** ⬆ **************************

[10/12, 1:46 pm] Leematu: *_Typing📲_*


*_💞AJIYA A DUHU....💞_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_‫*_ِبْس ِم الَّلِه الَّر ْح َٰمِن الَّر ِحيم‬


_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?


id=675067e55c3130f457527f30

_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂_

0404
04
0️⃣
4️⃣

______________

Aslm barkanmu da wannan lokaci


Ina Mai farin cikin sanar daku cewa Zuzeam ventures takawo maku ingantattun
magunguna masu inganci cikin Aminci Muna da kaya kamar haka
Mallaka Maganin sanyi
Maganin cire tumbiMaganin farin jini
Maganin matsiMaganin mata
Maganin sa ni’ima da dandano
Dulka Amare Set na gyran jiki
Set na amarya
Tabaje tsumin Gomba
Xuma kiba ta hips and Brest
Magungunan gyran Brest
Magungunan Karin hips
Maganin sliming
Muna da kaya masu inganci cikin sauki da rahusa
Ina wadda keneman mallaka sahihiya quaranty wlh hajiya kixo ga zuzeam ventures
xakiji ddin mallaka duk fadin ran ogah duk fadansa wlh sai yyi sanyi 08144015291
Idan maganin mata kikeso akwai
Idan gyran jiki kikeso gyran fata gyran Brest magungunan sa kiba da hips
DOMIN samunta Kai tsaye kira wannan no 08144015291 DOMIN mgn da ita whatapp
08144015291muna tura kayanmu ko ina cikin iKon allah 🥰👌🏻
Bononza Bononza Tsimin mangoro 1k🥭 Tsimin dabino 1k Gumba ukku balai 700 Gumba aya
da nonon rakumi 700 Garin kafi ciccibi 500
Garin bata gaban kishiya 500
Matsin mallaka tada zaune tsaye 2500
Turaren mallaka ba aba mai kishiya 2500 Total kayan 9500
Za a bakisu akan 3800
Kuma mutun goman farko nadakyautar Abun 2k
ASSALAMU ALAIKUM ALHAMDULILLAH YAN UWA NEW PROMO YA KAMMALA😁😁😁 da 5k dinki ki
kwashi kayan 12k hajiyata 😃🙃Kazar gadali ta mallara Rabi 3500 Tsimin gam gam 1500
Ruwan kara zunzurutun dadı😋800 Garin 7in1 1k Gumba 3 balai 500 Gumba kwakwa da
dabino 500 Infection ruwan tsarki 1k Garin zunzurutun dadi 1200 Matsin ba a fira d
wando 500 Matsin infection mai matse mace gam 500 12k All at 5k
https://wa.link/l1gcz8 kedai dannan link dinnan don samun naki ki maza kiyi bucking
koda kudinki saida Rabonki

________________

.......Bayan an natsa da murnar dawowar tata da gaishe-gaishe Ammie tace ta wuce ta


gaida mutanen gidan. Fuska ta ɓata kamar zatai kuka, sai kuma ta shiga roƙon Ammien
akan dan ALLAH ta barta taje tai wanka ta canja kayanta tukunna. Ammie zata ƙi su
Amal suka tayata roƙonta. Dole ta barta taje ta fara wankan sannan, yayinda su kuma
suka cigaba da aikin shirya abinci dan dama girki suke sanda ta shigo.
Ɗakin da yake mallakinta ta shiga, an gyarashi tsaf ga ƙamshi mai daɗi na
turaren da take matuƙar so na tashi a cikinsa. Sosai ɗakin ya haɗu, sai dai haɗuwar
tasa baisa ta taɓa jin daɗin zaman gidan ba. Kawai dai tana zaune ne saboda
mahaifiyarta na'a cikin gidan ne. Duk kuma inda Ammie take rayuwa koda a dokar daji
ne itama zata zauna ta rayu saboda a duniya bata haɗa komai da soyayyar da takema
mahaifiyarta ba. Ita ɗin dabance a zuciyarta. Idan tace daban tana nufin daban a
cikin dukan daban. (ALLAH ka gafartama iyayenmu, wanda suke raye ka bamu ikon
ƙyautata musu😭).
Jacket ɗinta ta fara cirewa, tare da ƙurama rigar ido tana mai sakin murmushi.
Finally yau ta gama sarvese, duk da Ammie tace boko ta ƙare, itafa a gareta yanzu
ne aka saka ɗanba, sai dai Ammie tayi haƙuri amma sai taga ƙarshen biro in har ana
ganinsa. Sanin yaran can zasu iya shigowa su fara addabarta yasa taƙarasa zame
kayan nata da sauri-sauri ta ciri towol daga Waldrop ɗinta fari tas ta ɗaura. Bayin
ta nufa dan tasan duk abinda zata iya buƙata Ammie ta saka mata shi kasancewar ta
jima bata gida. Dan watanni biyar kenan bata zo ko weekend ba. Tunma data wuce
sarvese sau ɗaya tazo gida, ɓacin ran data gumtsa a zuwan yasa tai alƙawarin ƙin
sake zuwa har sai ta kammala. Alhamdullah kuma gashi sai da ta kammala ɗin.
Wanka tayi na gaske. Dan sai da ta tabbatar ko'ina na jikinta ya mata
yanda take so sannan ta fito tana raɓar ruwa da ƙamshin shower gel ɗin ta mai
shegen daɗi daya gauraya da na sabulunta da turaren wanka. Maanal tasan sirrin
gyaran jiki da kula da jikin ma. Dan yarinya ce ƴar ƙwalisa akwai son gayu. Damma
ba Maanal ɗin da bace data taso da shegen son kwalliya kamar ƴar aljanun. Tana
tsaka da shafa mai Amal ta shigo. Cike da tsokana ta ƙaraso gareta tana faɗin, “Uhm
kaga ƴar ƙwalisar gidanmu Autar Ammie. Irin wannan ƙamshi haka kamar zaki tashi
gari”.
Murmushi mai sanyi Maanal ta saki da ɗan girgiza kanta tana ajiye man
hannunta data matsa. Wanda ta matsa ɗin ta fara shafawa a fuska tana faɗin, “ALLAH
Didi sai kisa a rataye mutum a tsakiyar kasuwa. Daddyn su Safnah na haƙuri dake
gaskiya. Yanzu mine abin wani ƙwalisa anan daga shafa mai dai sai wanka. Ni ko
fauda bazan shafaba ma”.
“A'a wlhy dole ki shafa. Zakije gaida waɗan can ƴan tsirkun ai sai kin
cakare. Dama ga ɗan mutuminki yazo garin, dan muna shigowa da shi na fara cin karo
a harabar gidan nan ɗazun”.
Cak Manaal ta dakata daga shafa man da take zuciyarta na wani irin motsawa da
ƙarfi, a take fara'ar fuskarta ta ɓace ɓat. Sai kuma ta fara haɗiyar numfashi da
sauri-sauri. Fahimtar hakan ya saka Amal wayancewa da faɗin, “Amma ban sani ba ko
shirin komawa yake a lokacin dan da akwati na gansa ma fa. Fitinanniyar uwarsa a
tare da shi ko rakkiya tai masa oho musu”.
A hankali Manaal ta saki numfashin data ɗan riƙe a maƙoshinta. Sai kuma
ta cigaba da shafa manta da kauda zancen ta hanyar faɗin, “Ina dai fatan kin soyo
min fara ta Didi?”.
“Harma da su Alewar madara Munaya ta matsa nai miki”.
“Oh my sweet daughter ɗina, Shiyasa nake son yarinyar nan. She is my
bestie”.
“Uhm kudai kuka sani. Ni tashi ki shirya ke ake jira aci abinci. Kin san yau
akwai hira duk an haɗu”.
Murmushi tayi cike da jin daɗi, dan tafi kowa son irin wannan haɗuwar tasu.
Takanji kamar su dawwama a haka tare gaba ɗaya kamar yanda suke da can. A gurguje
ta shirya cikin doguwar rigar Abaya milk color da ɗan kwalliyar coffee kaɗan a
jiki. Ta saka turarrukanta masu sauƙin ƙarfi. Suna ƙoƙarin fitowa Shahidah ta shigo
ɗakin, dariya suka sanya mata dan sun tuna baya. In dai kaga Shahidah tai irin
wannan shigowar fuska a ƙwaɓe to abinci aka ajiye zasu fara ci sukuma suka maƙale a
ɗaki hira, ita kuma sam bata da jimirin yunwa musamman idan ta dawo daga makaranta
ta kwaso rana. Sai ta shigo cikin haushi tana faɗin (“ALLAH idan baku fitoba zanci
nawa ne”).
Baki suka haɗa wajen furta (“ALLAH idan baku fitoba zanci nawa ne”). Ai ba
shiri Shahidah ta sanya dariya da musu daƙƙuwa. Daga haka suka rankaya suka fito
inda Ammie ke zaune a tsakkiyar falon da ƴan jikokinta zagaye da ita. Dan a anan
aka shirya abincin yanda za'aji daɗin ci fiye da saman table.
Manaal na zama yaran duk suka matso kusa da ita kowa na faɗin tare da ita shi
dai zai ci. Ganin abin zai zama rigima ta miƙe tana faɗin, “Kunga ku jira ku gani”.
Kitchen ta shiga sai gata da babban faranti ta ɗakko, ganin haka Ammie tace, “To ai
kawai zuba gaba ɗaya anan Auta sai muci duka baki ɗaya”..

Cike da farin ciki suka ci suka ƙoshi, damma Ammie ta hana surutu. Bayan sun
kammala babbar yarinyar Didi Shahidah mai suna Barru ta gyara wajen tsaf sauran
yaran na tayata. Maanal ya gyara zama da tunanin Ammie ta manta da batun zuwa gaida
mutanen gida sai Ammien ta harareta da faɗin, “Oya tashi kije gaida mutane”.
Fuska Maanal ta ƙwaɓe sai dai babu yanda zatai dole ta miƙe. Hannun ƴar
gaban goshinta Munaya ta kama suka wuce tare. ALLAH badan Ammie ba babu inda
zataje. Da sashen Hajiya Yaya ta fara. Hajiya Yaya itace uwargida a wannan gida na
Alhaji Usman Chalawa. Tanada yara bakwai tare dashi. Babban shine kaɗai namiji
sauran duk mata ne. Macece mai son mulki da ƙyamar talaka. Dan mahaifinta kamar ma
shine silar arziƙin mijin nasu shiyyasa take jin komai na gidan ta isa da shi kuma
dole a bita har shi kansa mai gidan ma. Sai dai kasancewar shi ɗin tsayayyen namiji
ne a gidansa yasa wani abun bata da power a kansa, dan in ma ta nuna ƙarfa-ƙarfar
yakan saurin taka mata birki. Kasancewar ta mace ta farko a gidan part ɗinta yafi
na kowa girma da tsaruwa, sai dai hakan ba yana nufin na sauran matan ma bai haɗu
bane. A'a a komai dai natan yana sama dana kowa kasancewar ita ta fara tarewa a
cikinsa.
Sai da Maanal ta dana door bell har sau biyu kafin ta tura ƙofar falon da
sallama duk da tasan ba sallai a jita ba kasancewarsa ƙaton gaske ne. Ilai kuwa
babu wanda ya amsa mata sallamar duk da kuwa kusan duk yaran na falon harma da ita
kanta Hajiya Yayan. Sai dai kasancewar ta danna door bell kafin shigowar yasa duk
suka maido hankalinsu ga ƙofar dan son ganin mai shigowar. Suna yin tozali da
Maanal wasu a cikinsu suka kauda kawunansu cikin jan tsaki. Yayinda Hajiya yaya ta
zubama Manaal ɗin idanu tamkar zata cinyeta da su. Sai Autar Hajiya Yayan da zata
iya zama sa'ar Manaal ɗin mai suna Amrah ce tai murmushi tare da miƙewa cike da
farin ciki tana faɗin, “Oyoyo mutanen Jos sauka haka babu notis”.
Murmushi Manaal ɗin tai mata, yayinda ita kuma ta rungumeta. A dai-dai nan idon
Manaal ɗin ya kai ga ƙaton dining table dake gefensu kaɗan. Sosai zuciyarta ta
motsa sakamakon saukar ƙwayoyin idanunta akan wanda ke zaune a wajen shima ya zubo
ma inda take idanunsa masu kaifi.........✍️

✨ZAFAFAN DAI ✨

1 ƘALBIM (Mamu gee)


2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)
3 DUNIYAR MU (Huguma)
4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)

Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000

0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070

Kati MTN:- 09032345899

Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭_*


[10/12, 1:46 pm] Leematu: *_Typing📲_*

*_💞AJIYA A DUHU....💞_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_‫*_ِبْس ِم الَّلِه الَّر ْح َٰمِن الَّر ِحيم‬


_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?


id=675067e55c3130f457527f30

_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂_
0505
05
0️⃣
5️⃣

______________

Aslm barkanmu da wannan lokaci


Ina Mai farin cikin sanar daku cewa Zuzeam ventures takawo maku ingantattun
magunguna masu inganci cikin Aminci Muna da kaya kamar haka
Mallaka Maganin sanyi
Maganin cire tumbiMaganin farin jini
Maganin matsiMaganin mata
Maganin sa ni’ima da dandano
Dulka Amare Set na gyran jiki
Set na amarya
Tabaje tsumin Gomba
Xuma kiba ta hips and Brest
Magungunan gyran Brest
Magungunan Karin hips
Maganin sliming
Muna da kaya masu inganci cikin sauki da rahusa
Ina wadda keneman mallaka sahihiya quaranty wlh hajiya kixo ga zuzeam ventures
xakiji ddin mallaka duk fadin ran ogah duk fadansa wlh sai yyi sanyi 08144015291
Idan maganin mata kikeso akwai
Idan gyran jiki kikeso gyran fata gyran Brest magungunan sa kiba da hips
DOMIN samunta Kai tsaye kira wannan no 08144015291 DOMIN mgn da ita whatapp
08144015291muna tura kayanmu ko ina cikin iKon allah 🥰👌🏻
Bononza Bononza Tsimin mangoro 1k🥭 Tsimin dabino 1k Gumba ukku balai 700 Gumba aya
da nonon rakumi 700 Garin kafi ciccibi 500
Garin bata gaban kishiya 500
Matsin mallaka tada zaune tsaye 2500
Turaren mallaka ba aba mai kishiya 2500 Total kayan 9500
Za a bakisu akan 3800
Kuma mutun goman farko nadakyautar Abun 2k
ASSALAMU ALAIKUM ALHAMDULILLAH YAN UWA NEW PROMO YA KAMMALA😁😁😁 da 5k dinki ki
kwashi kayan 12k hajiyata 😃🙃Kazar gadali ta mallara Rabi 3500 Tsimin gam gam 1500
Ruwan kara zunzurutun dadı😋800 Garin 7in1 1k Gumba 3 balai 500 Gumba kwakwa da
dabino 500 Infection ruwan tsarki 1k Garin zunzurutun dadi 1200 Matsin ba a fira d
wando 500 Matsin infection mai matse mace gam 500 12k All at 5k
https://wa.link/l1gcz8 kedai dannan link dinnan don samun naki ki maza kiyi bucking
koda kudinki saida Rabonki

________________

......Da sauri ta kauda idanun nata tamkar bata ganshi ba. Sai ma cikin wayancewa
ta ɗago Amrah tana faɗin, “Wai haka kika ƙara lukucewa matar nan?”.
Dariya Amarhn tayi da kai mata mintsini a gefen hannunta itama tana faɗin, “Ke
dai zauna nan kamar za'a hureki. Ni kin san bana wasa da cikina”.
Murmushi kawai Manaal ɗin tayi batare data bata amsa ba. Hakan yasa Amrah jan
hannun Munaya tana mata wasa. Da wannan damar Maanal ta ƙarasa cikin falon sosai.
Cike da girmamawa ta kai duƙe duk da kallon wulaƙancin da Hajiya Yaya ke mata da
sauran yaran ta shiga gaidata a mutunce. A yatsine ta amsa mata sau ɗaya ta ɗauke
kanta. Hakan ya ƙona ran Maanal matuƙa amma sai ta daure, fuskarta da ɗan murmushi
ta maida ga sauran yaran ta shiga gaishesu dan duk sun girmeta. Babu wanda ya amsa
mata sai ma tsoki da wasu suka ja mata. Dai-dai nan saurayin nan dake zaune a
dining ya miƙe zai fita a falon yana kai waya kunnensa alamar zaiyi magana.
“Ina kuma zakaje Yazeed?”.
Uwar ta ƙatse masa hanzari da ƴar tsawa-tsawa. Cikin dakiyarsa ya juyo da hannu
yay mata nuni da waya zaiyi, batare da ya jira sake cewarta ba ya fice abinsa.
“Hummm! Wai shi mai wayo fa Mamma”.
Ɗaya daga cikin ƴammatan ta faɗa fuska a kumbure. Kafin wani ya bata amsa
Maanal taja hannun Munaya suka fice suma. Duk rakata sukai da harara, sai kuma
wadda tai maganar ta miƙe zumbur tana faɗin, “Ina zuwa bari na muku leƙen asiri.
Dan nasan ko rantsuwa zanyi babu kaffara dan ita Yaya ya fita a falon nan babu wata
waya da zai amsa”.
“ALLAH nima na fahimci haka Nanah, dan tunda ta shigo ya dakata da cin
abincin ma sai wani binta da kallo yake. Kinga muje”.
A hasale Hajiya Yaya ta furta, “Aiko da naci ubansa a gidan nan yau. Tunda na
rabashi da yarinyar nan na kuma haramta masa alaƙa da koda inuwarta ma balle ita.
Amma kuje ku ganar min yana ina”.
Ai kafin ma uwar ta rufe baki sun fice da sauri har su uku. A dai-dai fitowar
tasu kuma Manaal ke shigewa sashen Hajiya Basariyya. Hajiya Basariyya itace mace ta
biyu a gidan. Itama dai ɗin ba kanwar lasa bace ba. Dan ba mutuncin ne da ita ba.
Sai dai ita akwai banbanci tsakaninta da Hajiya Yaya. Dan a zahiri baka isa
fahimtar ita ɗin wacece ba saboda macece mai fuska biyu. A zahiri akwai faran-faran
da jama'a da son nuna ita ɗin ta ALLAH ce. Shiyyasa mutane da yawa sai ta gama musu
illa suke farga da ita ɗin wacece. Macijin sari ka noƙe ce ita ta bugawa a jarida.
Yaranta biyar itama a gidan kuma duk mata, dan ita bata da namiji ko ɗaya. Huznah
da Maanal ta fara haɗuwa sanda ta dawo itace ƴarta ta farko. Itama ɗin dai family
nata akwai kuɗi, dan Yayanta daya riƙeta hamshaƙin mai arziƙi ne. Kuma babban
aminin Alhaji Usman Chalawa ne, suna huɗɗar kasuwanci sosai da har wasu ma ke ganin
dukiyarsu a cuɗe take da juna. Shiyyasa itama bata yarda Hajiya Yaya ta ɗaga mata
hanci ta ɓangaren dukiya dan kar ce tasan kar. Kowa najinsa a wani shege. Komawa su
Nanah sukai nasu sashen cikin taɓe bakuna. Dan Manaal na ƙoƙarin shiga sashen
Hajiya Basariyya shi kuma yayansu nama ficewa a gidan da motarsa.
Tun ma kafin su ƙaraso Hajiya Yaya data cika tai tab ta fara jeho musu
tambaya cikin huci dan macece mai ƙiba sosai. Irin ƙibar nan bata wasa ba. Dan ko
daga nesa ka hango ta kasan ALLAH yayi manyan mata a wajen nan. Zaune duk suka zube
cikin takaicin rashin samo abinda za'aci mutuncin Maanal da uwarta yau a gidan.
Nanah tace, “Mamma yama fita a mota. Ita kuma ta wuce sashen Momyn Suhana”.
Cikin ƙwafa da takaicin itama bata samu yanda take so ɗin ba ta ce, “Ya taimaki
kansa. Dan wlhy da yau har shegiyar uwartata sai sun bar gidan nan. Kai na tsani
mutanen nan a rayuwata”.
“Ai bake kaɗai ba Mamma”. Cewar ƴarta ta biyu mai tana huci. Auren nata ne ya
mutu kusan shekara uku kenan tana gidan. Dama ita kawai ta aurar, rana ɗaya akai
bikinsu da su Shahidah yayun Maanal. Sauran kuma ALLAH bai kawo ba, ko muce ruwan
ido da jiran ƴaƴan masu hannu da manda irinsu ya hanasu auruwa. Burin kowannensu da
ma uwarsu shine suyi auren ƙwarya tabi ƙwarya.. Buɗe shafin zagin su Manaal sukai a
falon kamar sun tare musu numfashi, sai Amrah ce keta ɓata fuska dan ita bata son
hakan. Ita birgeta ma Ammien take a rayuwarta mace mai dattako da sanin ya kamata.
Babu ruwanta da duk abinda iyayen nasu keyi a gidan sabgar gabanta takeyi kawai da
ƴaƴanta. Ko su duk abinsu bazasu taɓa cewa ga randa Ammien taima wani abu mara daɗi
ba, amma tasa miyasa basa sonta da yaranta?...

A ɓangaren Maanal can ma door bell ta fara dannawa kafin ta shiga. Shima dai
sashen Hajiya Basariyya da suke kira da Momyn Suhana ya matuƙar haɗuwa. Girmansa
kuma ɗaya dana Ammie. Ita dai bata falon sai su Huznah da ƙannenta dake cin
dafaffen gyaɗa suna hira. Duk sun zubar da kohon a saman lallausan carpet ɗin
tsakkiya ko'a jikinsu. Dan sun san mai-aiki ce zata gyara basu ba. Har zata juya
batare data musu magana ba sai ga Hajiya Basariyya ɗin ta fito daga kitchen riƙe da
kofi tana waya fuskarta da murmushi.
“A'a ƴan Jos an dawo kenan?”.
Ta faɗa cikin katse hanzarin Maanal kamar tuni ƴarta Huznah bata kawo mata labarin
dawowar Maanal ɗin ba tun ɗazun. Juyowa Maanal ɗin tayi fuskarta kadaran kadahan ta
ɗan kalla Hajiya Basariyya ɗin da nata fuskan ke ɗauke da murmushi mai ƙayatarwa,
sai dai acan ƙasan zuciyarta wani irin maƙoƙon tsanar Maanal ɗin ne ke mata
kaikawo. Risinawa Manaal tai tana gaisheta. Nan ma ta amsa cike da fara'a tana nuna
ma Maanal ɗin kujera da faɗin, “Haba sai kace wata baƙuwa zauna mana Maanal ga ƴan
uwanki nan na bikin cin gyaɗa ka kuci. Da fatan dai kun dawo lafiya? Kuma komai ya
kammala?”.
Kai kawai Maanal ɗin ta jinjina mata kanta a ƙasa, sai dai yanzu da ɗan
gajeren murmushi a fuskarta. Ganin bata zauna ɗin ba Hajiya Basariyyar ta sake nuna
mata kujera. Kai ta girgiza mata da kama hannun Munaya ta ce, “A'a Momy mun gode
dama munzo gaisheki ne kawai”.
“Masha ALLAH aiko ina godiya. Sai dai ni bana cin miƙe gaskiya azo mini
hira dai. Suma su Shahidah ki faɗa musu ina godiya sun barni da jira. Tun ɗazun har
abinci nasa akayi dasu ga gyaɗa da aka dafa amma shiru kake ji”.
“Zan faɗa musu in sha ALLAH Momy”. Maanal ta faɗa cikin muryarta mai zurfi da
nutsuwa. Daga haka ta kama hannun Munaya tana mata sallama. Da harara duk suka bita
har Hajiya Basariyyar. Sai da ta gama ficewar harda turo ƙofar Huznah taja tsoki da
faɗin, “Ni wlhy Momy ina mamakinki, kiyita wani musu magana mai daɗi. Shegu sunzo
sun gaje mana gida baka isa kai magana ba Daddy ya kama faɗin yayansa ne suma na
halak. Ko ina suka zama ƴaƴan nasa agololi. Ni ko wanda ma yakema kallon ƴaƴan nasa
ƙilama da cikinsu tazo.”
“Hummm”.
Kawai Hajiya Basariyya ta faɗa tana kaiwa zaune batare data kula maganar Huznah
ɗin ba. Hakan ya sake bama yaran haushi suka cigaba da zagin Maanal dan kamar ma
sunfi tsanarta fiye da sauran ƴaƴan Ammien. Duk da kuwa sunƙi jinin Hameed ma da
Waleed da Ammien ta haifa a gidan suke matsayin uba ɗaya dasu. Balle da Daddyn ke
tsananin nuna musu soyayya. Dan yanzu haka ma yana tare dasu ƙasar Amurika yin
hutu. Duk da dai yace taro zaije ya tafi da su. Amma babu wani taro kawai yaje dasu
ne dan hutawa na sati har biyu...

Rai ɓace Manaal ta koma sashensu. Sai dai yanda bata gayama kowa abinda ya
faru ba babu wanda ya tambayeta. Sai ma zama tai suka fara hirarsu. Babu jimawa
kuma Daddy ya kira Ammie ta video call. Daga nan suka gaisa da shi ya bama Hameed
da Waleed da Ammien ta haifa a gidan. Ƙanensu kenan guda biyu. Yarane matasa da
zasu iya kai shekara sha biyar da sha uku. Suma duk kamanin Ammie suka biyo kamar
su Maanal ɗin. Sai dai su farare ne sun kwaso hasken fatar Alhaji Usman Chalawa
sosai kasancewarsa farin mutum tas..
Suna cikin hira da ƙannen nasu ne babu zato akai knocking ƙofar falon. Kafin
wani yay magana a cikinsu mai knocking ɗin har ya shigo. A take Maanal ta shanye
fara'ar fuskarta da maganar da take da Waleed ko nace faɗa irin na sako duk da kuwa
ta girmesa sosai. Kauda kanta tai da jan mayafin abayarta daya zame ta rufe
gashinta da ƙyau, yayinda su Amaal ke masa barka da shigowa. Shiko yana amsawa da
ɗan murmushi hankalinsa akan yaransu dake gaishesa duk da sai da ya gama ƙarema
Maanal kallo a kai-akaice.
Gaban Ammie da hankalinta itama ke kansa tana ɗan murmushi ya ƙaraso. Cike da
girmamawar da yake bata ya rissina yana gaisheta. Da kulawa take amsawa itama,
kafin ta ɗora da faɗin, “Baka wuce Abujan ba kenan?”.
“Eh Ammie fasawa nai saboda wanda zanje wajensa yace yana Lagos sai gobe
zai dawo. Nima kawai sai na bari sai goben na tafi dan bana son naje naita zaman
jiransa ina kuma da abinda zan ɗanyi anan ɗin”.
“To ALLAH yayi jagora. Yay muku albarka, ya kuma saka muku hannu a dukan
al'amuranku”.
“Amin ya rabbi Ammie Nagode sosai”. Ya faɗa cike da jin daɗi yana maida
hankalinsa kan Maanal dake ƙoƙarin tashi tabar falon. Kansa tsaye ya furta, “Ke ƴar
hidimar ƙasa yaushe kika dawo?”........✍️

Hummm yanzu fa aka fara shimfiɗar bama wasan ba. Mi kuke tsammani. Yazeed, ga
kuma RK. Ga Maanal da bama musan alƙiblarta ba. Shin wai mi aka AJIYE A DUHUN nan
ne? Ya dai kamata a haska mana mu gani ko zamu tayasu lalube🏃🏃🏃🏃🏃.

Maza garzayo cikin tawagar littafan zafafa biyar da zasu zo muku da sabon salo na
musamman in sha ALLAHU. Kowanne da salonsa da kuma takunsa. Mi kuke jira, ai sai
kawai kuzo ayi tafiyar nan daku karku bari sai wasu sun baku labari.😘😘😘

A fa dun inda ZAFAFAN suke ZAFAFAN ne😘😘

✨ZAFAFAN DAI ✨

1 ƘALBIM (Mamu gee)


2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)
3 DUNIYAR MU (Huguma)
4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)

Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000

0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070

Kati MTN:- 09032345899

Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭_*


********************** ⬇ **************************
********** Ai Hausa Novels ****************
*************************⬆ **********************

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery,
Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from
our blog.

Visit > https://www.aihausanovels.com.ng

Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa
novel ko kuma post.

Email > aihausabooks@gmail.com

******* FOLLOW US ******

Facebook: Ai Hausa Novels

Twitter: Ai Hausa Novels


Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels

Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search
na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu.

********************** ⬇ **************************
*************** Ai Hausa Novels ****************
********************** ⬆ **************************

You might also like