Auren Dole Book 2..Complete
Auren Dole Book 2..Complete
😰😰😰😰😰😰
AUREN DOLE
😰😰😰😰😰😰
*T.W.F*
BOOK 2
Page 1 - 5
Story nd written
By
Mufeeda Muazu
Classic feedoh
Feedohm
Sunera
Basma er lele
Halima Ameen
Jin kara yasa su jidda juyowa Dalhat suka gani rike da Hudah tana kokarin kwacewa
amma ta kasa saboda irin rikon da yayi mata sai kuka take tana kiran hajiya ganin
zata tara masa mutane yasa ya dauketa cak ya shige da ita part dinsu Sumayya ta
tintsire da dariya tace Allah ya kara Jidda tace kai keko baki da tausayi Sumayya
ta harareta tace tunda ke kinada tausayi ai sai kije ki kwatota mata da mijinta
jidda ta kai mata duka da gudu Sumyya ta shige part din su Jiddan tana yi mata
gwalo dakin kasa suka shige dukkansu sukayi kwanciyarsu a gado Jidda kuwa falo ta
wuce anan taga Radiya tana zaune tana kallo amma kwata kwata hankalinta baa tv yake
ba Jidda ta zauna a one seater Radiya ta harareta ta tsuka tsaki Jidda dai ko
kallonta batayi ba
Wacece Radiya
Radiya Ahmad tijjani yar kanwar Ummi ce wato Aunty Ramlat babanta yana da kudi
sosai Radiya irin shagwababbun yaran nan ne wanda baa musu fada duk abinda sukayi
dai dai ne tana son Dalhat sosai shi kuma sam batayi masa saboda shi a tsarinsa
yafi son mace mai kunya da kawaici saboda hakene yasa basa shiri da Jidda ita gani
take bata so dan uwanta ya aureta tafi son ya auri Hudah saboda kawarta ce Allah
sarki Jidda baiwar Allah ba ruwanta
Cigaban labari
Jidda bata so taga Radiya a falo.ba saboda kada ta bata musu shirinsu don tasan
halinta sarai ba mutunci ne da ita ba Jidda ta dauki remote ta kashe tv Radiya tazo
ta fizge remote din ta hau mata masifa wai don mene tana kallo zata kashe mata don
wulakanci Jidda tace bakiga dare yayi bane Radiya tace ina ruwanki koke kika kunna
kuma wlh daga ke har Hudan sai nayi maganinku sai kun raina kanku nice na dace dana
auri yaya Dalhat ba wata banza ba Jidda tace haba Radiya wai me kike nufi ne ka
baki yarda da kaddara bane iyayen mu su suka hada auren itama baso takeyi ba Radiya
tace dallah rufe mana baki Jidda tashi tayi ta shiga kitchen ta barta tana zage
zage ita kadai
A bangarensu Dalhat kuwa tunda ya dauketa bai direta ko ina ba sai kan gado sai
ihu take tana birgima kamar karamar yarinya kallonta yayi fuska a murtike kiyiwa
mutane shiru kafin inyi kasa kasa dake ganin ba wasa a fuskarsa yasa tasa hannu ta
toshe bakinta toilet ya shige yana shiga ta diro daga kan gadon ta nufi kofa ta
murda tajita a rufe waige waige ta fara tana neman makulli bata ganiba can kamar
ance ta kalli sama sai ga key din a saman wardrob da sauri taje ta dauka ta bude
kofar a hankali yadda bazaiji ba ta fita
Tana xuwa main kofa ta fita aguje sai part dinsu Jidda ta baya dama tunda ta fito
jidda ta hangota ta kitchen don haka ta bude kofar kafin ta iso Hudah na zuwa ta
kama kofar zata kwankwasa Jiddah tace shigo da sauri Hudah ga yaya Dalhat can yana
waige waige kuma na tabbar dake yake nema Hudah ta shigo da sauri da rufu kofar da
karfi jin kara yasa shi juyoya da sauri tasa ma kofar key tana ajiyar zuciya Hudah
ta kalli Jiddah,Jidda ka kalli Hudah ba wanda dai yayi ma wani magana suna tsaye
basu bar kitchen din ba har ya kariso Hudah tana wurin windo tace gara ma ka koma
ka kwanta dan wlh ba mai bude kofar nan inma ummi zaka kira tayi bacci tana sama
Dalhat yayi kwafa yace zanyi maganinki daga ke har Jiddan wayarsa ya ciro daga
aljihu yayi dialing numbern Ummi ya kara sau uku har ya gama riging bata daga
ba.............
🌱🌱🌱🌱
Muffy
🌱🌱🌱🌱
😰😰😰😰😰😰
AUREN DOLE
😰😰😰😰😰😰
*TWF*
BOOK 2
Page 6 - 10
*Story nd Written*
*by*
*Mufeeda Muazu*
Kwafa yayi ya juya Jiddah tace Hudah nidai gsky babu ruwana kada ki kuskura kisa
sunana a ciki wlh ba ruwana Hudah ta harareta batace komi ba barin kitchen din
sukayi a kofar kitchen din sukaci karo da Radiya tana musu labe Hudah ta zabga mata
harara tare da tsaki tayi gaba abinta Jidda ne tace kedai wlh Radiya halinki baida
kyau Radiya tace duk munafuncin da kuka kulla duk a kunnina kuma sai na fadawa Ummi
Jidda tace ki fada mata mana sai me itama ta wuce ta barta anan tanata maganganu
falo suka kwanta Jidda a 2seater Hudah ya 3seater Radiya tazo ta wuce su ta haura
sama a nan dai bacci ya kwashe su
Dalhat kuwa tunda ya tafi daki yake tufka da warwarar yadda zai wulakanta Hudah
shima daya gaji kwanciya yayi nan da nan bacci ya kwashe shi saboda dama a gajiye
yake lokacin daya kira Ummi idonta biyu amma wayar tana silent ne asuba nayi kamar
a kunnen Hudah aka kira sallah a hankali ta tashi jidda tayi sallah saboda ita
tana fashin sallah Jidda da kyar ta tashi saboda gajiya daki ta shiga ta tarar
dasu sumayya sai baccinsu sukeyi tashinsu tayi sannan ta shige toilet tayo alola
sannan ta dauki sallaya tafito falo anan ta tarar da Hudah zaune tayi zubga tagumi
Jiddah tace lpy Hudah kikayi tagumi haka Hudah tace bkm Jiddah bari in tafi kafin
ya dawo ya tara mun mutane Jidda tace to amaryan yaya sai mun shigo Hudah ta fita
tana harararta da sauri ta fita lokacin gari bai gama wayewa ba a bude ta tarar da
kofar tayi sauri ta shige dakinta ta shige ta shiga toilet ta gyara kanta sannan ta
fito ta kwanta can karshen gado ta rufa da bargo tana jin lokacin daya shigo
dakinsa ya shiga bai dade da shigowa ba taji fitar sa dada lafewa tayi side dinsu
ya tafi baiga kowa a falo sai motsi dayaji a kitchen ya leka Ummi ne da Jiddah sai
Radiya shiga yayi ya duka har kasa ya gaisheta da faraarta ta amsa har take
tambayar ya Hudah shiru yayi bai ce komi ba Radiya da Jidda suka gaishe shi a tare
fuska a daure ya amsa yace Ummi Hudah bata kwana a side dinmu ba Ummi ta ta juyo a
firgice tace to a ina ta kwana Dalhat yace a tambayi Jidda Ummi tace jidda kuma
Jidda dake fere dankali ta tsaya duk ta rude batasan wani irin mataki Ummi zata
dauka ba Radiya tace eh Ummi jiya bayan sun dawo dasu Sumayya duk suka shige daki
Jidda ta dawo falo ta zauna nima a lokacin ina zaune a falon ina kallo baa dade ba
sai tashiga kitchen can naji ta bude kofar baya suka shigo nidai sama na haye
bansan abinda ya faru ba Ummi ranta yayi matukar baci ta janyo Jiddah da karfi
kyawawan mari ta zabga mata duka kuncin sai da taga wuta dafe wurin tayi tana kuka
tace Ummi ni ba ruwana karyar Radiya ne Ummi tace in ita Radiya tayi miki karya
Dalhat zaiyi miki karya ne yanzu ina Hudan take Jidda murya na rawa tace tana side
dinta kuma ba anan ta kwana ba Dalhat yace zakiyi wa mutane shiru ko kuwa sai na
babbala ki Ummi tace Dalhat muje side din mugani ba musu suka tafi side din har da
Radiya
A daki suka sameta kwance idonta a rufe kamar mai bacci jin maganar Ummi yasa tayi
sauri ta tashi ta zauna ta gaisheta da kyar Ummi ta amsa ganin Jiddah na kuka yasa
ta dukar da kai tana hawaye Ummi tace ina kika kwana jiya Hudah tayi shiru batace
kom Ummi ta daga murya tayi bada ke nake magana ba murya na rawa tace anan na kwana
Ummi Radiya tace karya ne wlh Ummi tace wayasa bakinki ciki shiru tayi Ummi tace
tunda bazaku fadi gsky ba to zan fadawa Abbu yasan halin da kuke ciki Hudah tace
Allah zamu fada a baa nan na kwana ba a side dinsu jidda na kwana amma ba ruwan
Jiddah Ummi kiyi hakuri haka bazai kara faruwa ba Ummi tace to shikenan ya wuce nan
dai tayi musu nasiha sosai sannan ta tafi Dalhat ma yabi bayanta dakin ya rage daga
ita sai Jiddah da Radiya Hudah ta tashi tsaye ta isa inda Radiya ke zaune ta
fincikota tace malama a fita mun a daki banda munafunci ina ruwanki damu harda sawa
a mari Jiddah na wlh ki kiyayeni.............
🌱🌱🌱
Muffy
🌱🌱🌱
😰😰😰😰😰😰
AUREN DOLE
😰😰😰😰😰😰
*TWF*
BOOK 2
Page 11 - 15
*Story nd Written*
*by*
*Mufeeda Muazu*
Radiya tace idan baa fita ba fah Hudah tace jikin mutum yanxu yayi tsami Radiya
tace bazan fita ba inada ikon shiga ko'ina a gidan nan don ba gidan ubanki bane
Hudah tace aike gidan ubanki ne ni gidan mijina ne inada iko ke kuma fah ashe
maganar tayiwa Radiya ciwo daga hannu tayi zata mareta sai a lokacin Jidda tayi
magana tace ke Radiya baki da hankali ko rike hannun Hudah tayi ta zabga mata mari
ji kake tasssss!!! dai dai lokacin Dalhat ya shigo Radiya tana ganinsa ta kara
narkewa ta dada rushewa da kuka bai tambayi meya faru ba kawai ya hau Hudah da duka
saida yayi mai isar sa sannan ya kyaleta Radiya tana gefe tana mata gwalo fuska ba
annuri yace su tafi side dinsu Jidda jiki ba karfi ta fita tana mai tausayawa Hudah
Radiya kuwa ranta fes kamar ranar sallah
Suna fita ya matso kusa da ita dama da kula guda biyu ya shigo idonta rufe
tana share hawaye yace tashi kije kitchen ki dauko mana plate da flask akwai ruwan
zafi a ciki ba musu ta tashi taje ta dauko ta aje masa a gabansa ta koma can nesa
dashi ta zauna hararanta yayi yace waye kika aje wanda zai zuba mun ko kina nufin
da kaina zan zuba jikinta a sanyaye ta tashi ta zauna a kasa kusa da shi kamshin
turarenta ya daki hancinsa saida ya lumshe ido ruwan zafi ta zuba ta kalleshi
idonta duk ya kumbura shi kanshi ta bashi tausayi kawar da kai yayi yace lpy kika
tsareni da ido kaman na mujiya sunkuyar da kai tayi tace kana son sugar dayawa
hararanta yayi yace ni ni sha zumami ne bata kara cewa komi ba ta hada masa ta tura
masa gabansa sannan ta dauko plate ta zuba masa wainar fulawar ta koma gefe daya ta
takure tsawa ya daka mata yace bani son munafurci kin wanije kin takure me kike
nufi come on zokici abinci jiki na rawa ta taso ta zuba kadan ta hada tea din ta
koma zata zauna yace dole sai dai ta zauna a gabansa bayadda ta iya haka nan ta
zauna da kyar ta tuttura abincin bayan sun gama ta kwashe komai takai kitchen a
falo tayi xamanta tana kallo
Shiko yana daki yana jiranta dayaji shirun yayi yawa ne ya fito ya gani kota
Kara guduwa ne sai ya ganta a falo daure fuska yayi yace ke wa kika aje dazai gyara
miki daki kin wani dawo nan tashi tayi tana matsar kwallah ta rabe ta wuce ta
gabansa sai da ya lumshe ido saboda daddan kamshinta tana shiga daki ita bataga
wani datti ba gado ne kawai ya dan bacci tsaki tayi bata sani ba Ashe yana
bayanta sai ji kawai taji yace wa kikewa tsaki matsawa tayi da baya tace Ina
ruwanka dani duk kabi ka takurawa rayuwata matsowa yayi ta kara matsawa a haka a
haka har saida ya kaita bango suna shakar numfashin juna yace ke ni zakiwa rashin
kunya kasa tayi da kanta batace komi ba kugunta ya rike yace bada ke nike ba
jitayi yarrr!! tace to shine don iskanci bazakai wa mutum magana ba sai ka taba shi
girgiza kai yayi yace nine dan iska ko to yau kuma yanzu xan nuna miki ni dan
iskane na gaske nan da nan gabanta ya shiga faduwa amma ta dake saboda kada ya
rainata zip din rigarta ya zage ta rike rigar iya karfinta nan suka fara kokowa nan
dai yafi karfinta ya cire rigar kuka ta farayi ya jefata kan gado daga ita sai bra
hau gadon yayi da karfin tsiya ya ciremata kuka take kaman ranta zai fita.....
🌱🌱🌱🌱
Muddy
🌱🌱🌱🌱
😰😰😰😰😰😰
AUREN DOLE
😰😰😰😰😰😰
*TWF*
BOOK 2
Page 16 - 20
*Story nd Written*
*by*
*Mufeeda Muazu*
Rufaida ce ta shigo bako sallama su sumayya na bayanta da sauri suka juya shi kuma
tashi yayi ya gyara rigarsa ya kalleta yace ki shirya zamu hadu anji zaki gane
kurenki ita dai bata ce komai ta dauko rigarta ta saka fita yayi Daga dakin a falo
ya wuce suna zaune yana fita sumayya ta shigo tana dariya harda tintsirawa Hudah
dai tana kallonta ta takure tana hawaya su jidda suma duka shigo!
Rufaida kuwa sai cika take tana batsewa kaman ance ta shigo dole
Sumayya da JIdda ne suka zauna kusa da Hudah sumayya tace Amarya yaya jiki Hudah
tai banza da ita kaman bata jiba ta Kara matsawa kusa da ita tace nace yaya jiki
Hudah tai tsaki tace dallah malama ki kyaleni an gaya miki ciwo nikeyi Jidda tace
kyaleta Hudah neman magana take
Rufaida ce ta tsuka tsaki mtsw....... tace aikin banza munafukai kawai wlh sai
kin bar gidan nan nice na dace da yaya bake ba yar qauye kawai Hudah zatayi magana
su sumayya suka hanata
Tashi sukayi suka koma falo suka barta anan tanata zage zage a falo ne Hudah take
basu lbrn abinda ya faru tsakaninta Dalhat sumayya tace da zan baki shawara kiji
da sai ince kiyi hakuri da kaddara ki rungumi mijinki kinga wata so take ta kwace
Kuna ki daina fada masa irin maganganun da kike fada masa
Jidda tace yawwa sumayya fada mata kila ke zataji naki Hudah ta goge kwallar daya
zubo mata tace shima fah ba sona yake ba nidai mafita kawai nake nema yanzu
Sumayya tace baki da wani mafita illa kawai kiyi hakuri idan Kuma kinki ke zaki
sha wuya wlh
Hudah tace jidda ki taimaka mun jiddah ta bude ido tace rufa mun asiri kiyi hkr
kawai in ba so kike yaya ya karkaryani bane
Bangaren Dalhat kuwa yana fita side din Abbu ya tafi a falo ya tarar dashi yana
zaune yana karyawa cikin ladabi ya gaishe shi Abbu ya amsa cikin sakin fuska
Dalhat yace Abbu na kawo karar Jidda ne saboda kada in dauki hukunci a hannuna
kace nayi ba dai dai ba
Abbu yace hakane me kuma autar tawa tayi Dalhat ya zayyane masa duk abinda ya
faru
Ran Abbu ya baci matuka yace kayi hkr Dalhat insha Allah zan dauki mataki Dalhat
yayi godiya ya tashi ya tafi
Gidansu Hudah kuwa hajiyace ta hana a shiga wurin Hudah wai sai dai in zasu tafi
sai su shiga suyi mata sallama
Aunty binta ce tace ita dai sai ta shiga ta duba lpyr yarta
Suna zaune a falo Hudah sai kuka take sun sata a tsakiya sun rasaj yadda zasuyi
da ita sai ga Aunty binta ta shigo tace lpy take kuka ku kuma kun tasata gaba kaman
masu zaman makoki jiddah tace Aunty wlh tun daxu muke lallashinta amma taki yin
shiru
Hudah ta tashi da gudu ta rungume Aunty binta tana kuka tace Aunty don Allah ki
tafi dani wlh yaya Dalhat kasheni zaiyi yace baya sona
Aunty binta tace ki natsu Hudah Dalhat yana sonki kinji kiyi hkr nan dai taita
lallashinta har tayi shiru
Hudah tace Aunty binta muje daki kiji wata magana suka shiga daki zauna suka
tarar da Rufaida.....
🌱🌱🌱🌱
Muffy
🌱🌱🌱🌱
😰😰😰😰😰😰
AUREN DOLE
😰😰😰😰😰😰
*T W. F*
Www.Mufeedamuazu.blogspots.com
BOOK 2
Page 21 - 25
*MUFEEDA💦 MUAZU*💦
Zaune suka a bakin gado suka tarar da Radiya ta daura kafa daya kan daya tana
chatting abinda hankali kwance kaman tana dakinta
Jin karar bude kofa yasa ta dago da kanta Hudah ta kalleta ta watsar tace malam
sai ki fita ki bamu wuri zamuyi magana nida uwata tunda dai ba dakinki bane
Radiya tace idan baa fita bafa Aunty Binta tace yi hakuri baiwar Allah Radiya tace
ina ruwanki haushi ya Kama Hudah da karfin ta figi hannun Radiya ta ingizata waje
ta rufe kofar da key.
Aunty binta tace Hudah sai kinyi hkr ba kowani Abu bane zaki ringa kulawa ba
Hudah tace Aunty kinga wannan yarinya bata da mutunci bata ganin kowa da gashi
wai ita dole son yaya Dalhat takeyi
Ni wlh dama ita aka aura miki Aunty binta tace lallai baki da hankali wace magana
zaki fadamun tafiya zamuyi Hudah idanunta suka cika da kwallah tace Aunty don Allah
ki gudu dani wlh yaya Dalhat mugu ne wlh ban san wani abu kuma zaiyi mun ba idan ya
dawo Aunty ta tausasa murya tace Hudah kiyi hkr ki kwantar da hankalinki kinji kiyi
masa biyayya kinsan dai iyayenki baza su cutar dake ba kiyi hkr ki cigaba da addua
kuma kiyi taka tsantsan da yarinyar nan
Don na kula batada da tarbiyya zata iya yin komi akan mijinki don haka ki dage da
addua muma iyayenki zamu tayaki
Hudah cikin sanyin murya tace to Aunty ngd sosai tashi tayi ta bude kofar bata ga
kowa a falon ba
Sukayi sallama da Aunty har gate ta rakota tana kuka tana ganin gidansu kaman ta
shiga Amma ba dama tana kuka suka rabu da aunty
Side dinta ta koma ita kadai ta zabga tagumi tana tunanin Irin rayuwar da zatayi
a gidan
Radiya tana fitowa su sumayya ba Wanda ya ko kalleta cikin jin kunya ta tashi ta
bar dakin!
Bata dade da fita ba sumayya tace su zo su rakata ta hada kayanta anjima zasu
tafi
Hudah na zaune shiru ita kadai a daki wurin karfe 4pm ta jiyo muryar yan uwan
mamanta Harda su sumayya sunzo yin mata sallama zasu tafi
Nasiha suka dada yi mata sannan suka wuce rungume juna sukayi da sumayya Suna kuka
da kyar suka rabu Jidda ta rakasu har mota sannan ta dawo
Side din Hudah ta dawo gida duk an warwatse saura Radiya dataki tafiya wai sai ta
Kara sati daya
Hudah tace jidda gobe zakije skull ne Jidda tace eh zani insha Allah
Hudah tace nima Inaso inje idan kin shirya ki biyo mun Jidda tace nidai ba ruwana
kiyi hkr a dan kwana2 kin san yaya Dalhat bazai bari Idan an kwana2 sai kiyiwa ummi
magana Hudah tace to shikenan bkm Suna zaune Suna hira har magriba Jiddah tayi
sallah aka kawo abinci sukaci suka ajewa Dalhat nashi sai issha tayi mata sai da
safe ta tafi
Tashi tayi ta shiga wanka tai wanka ta gyara kanta ta sauya kaya ta fesa turare
kayan bacci tasa mai kauri tayi kwanciyarta
Bai shigo ba sai wurin karfe 9pm ya shigo yaji gidan Yayi shiru kaman ba kowa
dakinsa ya wuce Yayi wanka yasa kayan bacci
Sannan ya wuce dakin Hudah ya murda yajita a rufe dakinsa ya koma ya dauko extra
key ba bude kallonta Yayi yanda take barcinta cikin nutsuwa saita burge shi
Side bed din ya bubbuga a hankali ta fara bude idonta ganin ta bude ido yasa ya
daure fuskarsa Yayi kaman bai taba dariya ba
Tashi tayi ta zaune idonta ya cika da kwallah kallonta yayi ya watsar sannan yace
ke ina abinci na a hankali tace yana dinning tsawa ya daka mata yace a nan zanci
kije ki kawo ina jira saura ki dade.......
🌱🌱🌱🌱
*Muffy*
🌱🌱🌱🌱
😰😰😰😰😰😰
AUREN DOLE
😰😰😰😰😰😰
*T W. F*💦💦
Www.Mufeedamuazu.blogspots.com
BOOK 2
Page 26 - 30
*MUFEEDA💦 MUAZU*💦
Ba musu ta mike ta fita tana share kwallar daya zubo mata bata dade da fita ba ta
dawo da tray a hannunta ta aje a gabansa
Komawa tayi ta dauko lemu da cup shima ta aje a gabansa ta koma zata xauna yace
wa kika aje da zaiyi serving dina
Haka nan ta juyo ta duka a gaban ta dauko kusa dashi sai kamshin humra takayi
gogan kuwa sai lumshe ido yake yaji kamshi mai sanyi
Tuwon shinkafa ne miyar agushi ta zuba masa ta tsiyaya masa lemun a zuciyarsa
addua yakeyi Allah yasa tayi zamanta kada ta tashi saboda bai gaji da jin kamshin
ba
Tana gama zuba masa kuwa ta miki ta koma gado tayi kwanciyarta ta dauki wayarta a
bed side ta hau online jidda ta gani
Jidda tace Amarya kin sha kamshi ina angon ya barki kina chatting Hudah tace
gashi nan abinci yake ci Jidda tace to dan Allah ki aje wayar ki kular mun da
yayana
Hudah tace goya shi kikeso inyi ko mene Jiddah tace rufa mun asiri ni bance ba
Abinda Hudah bata sani shine Dalhat yana tsaye a kanta yana kallonta yana tana
danna waya tana smiling
Ji kawai tayi an fisge wayar batayi wani yunkuri ba sbd tasan Dalhat ne yace ke
dawa kike chating kike wani smiling dukar kanta kasa tayi batace komi ba
Duba wayar yayi yaga swt sis budewa yayi ya krnta chat dinda sukayi murmushi yayi a
zuciyarsa
A fili kuwa daure fuska yayi yace ki kwashe tray dinnan ki kai kitchen ki dawo
xamuyi mgn minti biyar na baki Idan kuma kika kara koda sec ne nida kene a cikin
gidan nan
Kwashe komi tayi ta gyara wurin tsaf yana kallonta yana kallon agogo 5mns dai dai
ta gama ta dawo ta zauna
Har yanxu fuskarsa a daure take yace kije ki alola kizo muyi sallah tana zaune ko
motsawa batayi ba balle tai yunkurin tashi
Tsawa ya daka mata har saida yan hanjin cikinta suka kada yace bakiji abinda nace
ba kenan
Duk ta daburce cikin rawar murya tace ba... ba... bana sallah kusa da ita ya
matso yace karya kikeyi wannan shine dabaran da kuka shirya kenan zaki tashi ko sai
na bata miki rai
Hawaye ke zubo mata kamar an bude famfo tace Allah yaya ba karya nake da gske
nake
Girgiza kai yayi yace naji kwana nawa kikeyi kanta a kasa tace 5days to yaushe kika
fara tace jiya yace to shikenan
Ba damuwa Amma duk da haka sai na nuna miki Niba yaro bane Hudah tace dan Allah
kayi hkr wlh wasa nake maka Dalhat yace ni abokin wasanki ne dama oya taso kixo nan
ya nuna kusa dashi tayi kamar bataji ba tashi yayi yace tunda baxaki zoba ni sai
inxo kuma xuwana wani karin hukunci ne a wurinki
Mikewa tsaye tayi ta fara ja da baya yana binta harta kai bango tsugunnawa tayi
ta fashe da kuka daukar ta yayi cak ya kaita gado nan ya dinga romancing dinta na
hauka tun tana kokowa harta gaji ta kyaleshi sai hawaye da takeyi wani na bin wani
Bai bari ta huta ba har asuba sannan ya tashi yayi wanka ya tafi masallaci ya
barta a kwance da kyar ta iya tashi duk jikinta yayi tsami....
🌱🌱🌱🌱
*Muffy*
🌱🌱🌱🌱
😰😰😰😰😰😰
AUREN DOLE
😰😰😰😰😰😰
*T W. F*💦💦
Www.Mufeedamuazu.blogspots.com
BOOK 2
Page 31 - 35
*MUFEEDA💦 MUAZU*💦
Toilet ta shiga dama yau zata gama period dinta but tayi masa karya wanka tayi
sannan tayo alola ta fito ta zauna gaban mirror ta goge kanta da karamin towel
sannan tadan shafa mai ko powder bata shafa ba sai humra data goga wani gown ta
dauko red mai ratsin baki ta saka kayan sunyi mata kyau sosai duk da ba wata
kwalliya tayi ba saida tayi sallah sannan
ta gyara dakin tsaf sannan ta kunna burner tasa turaren wuta dakin ya dauki
kamshi da kyar ta fita falo duk ta gaji dakin Dalhat ta shiga ta wanke toilet
sannan ta gyara dakin ta gyara koina a gidan, gida ya dauki kamshi
Daki ta koma ta kwanta nan da nan bacci mai nauyi ya dauketa shiko Dalhat tunda ya
tafi masallaci bai dawo ba sai 7am koda ya dawo ma side dinsu ya tafi a kitchen ya
samu Ummi gasheta yayi ta amsa cikin kulawa
Tambayarsa tayi ya Hudah ta kwana lpy klu yace mata Ummi ina Jidda me takeyi har
yanxu bata tashi ba ta barki ke kadai a kitchen Ummi tace suna can daki ita da
Rufaida bata dade da komawa ba zata fara shirin skull Kasan yau Monday
Baice komi ba ya koma falo ya zauna yace Ummi wai me Rufaida takeyi bata tafi ba
Ummi tace ina ruwanka komi ta tsare maka yata ce don haka babu ruwanka Dalhat yace
Allah ya baki hakuri Ummi ina Abbu? Ummi tace ban saniba ka tashi ka tafi can wurin
matarka kaxo nan da sassafe zaka dame mu Dalhat yace au korata ma akey Ummi tace eh
ka girma murmushi yayi yace bari in tafi tunda korata akeyi tashi tayi
Ummi tace ka gaisar mun da diyata murmushi yayi ya fita bai ce komi ba yana zuwa
kofar side dinsu yaji kamshi ya daki hancinsa.
Wani irin dadi yaji acikin ransa yana shiga yaga koina tsaf sai kamshi ke tashi
dakinsa wow ya fada toilet ya shiga yayi wanka yayi brush
Shiryawa yayi cikin white boyel ya fesa turarensa mai dadin kamshi wurin 8:30pm
ya fito dakin Hudah ya shiga a kwance ya tarar da ita tana baccinta cikin nutsuwa
Zama yayi kusa da ita ya kura mata ido a zuciyarsa yace to meye aibun Hudah
tanada duk abinda yake bukata a wurin mace uwa uba ga tsafta saurin kawar da sannan
tunani motsawa tayi saurin tashi yaya ya bubbuga gefen gado tashi tayi tana
murmurxa ido a hankali ta bude idonta tsaf
Daure fuska tayi a tsiwace tace malam lpy mutum na bacci dan wulakanci zaka
tasheni bayan kai ka hanani baccin don zalunci
Tsayawa kawai yayi yana kallonta yace lallai yarinya baki hankali ba Amma nan da
3days idan ance ki daga kai ki kalleni koda kudi bazaki iyaba balle har ki iya fada
mun magana Irin wannan
Ina breakfast dina Hudah tace ban girka ba kuma bazan girka ba don ba yar aiki aka
kawo maka ba
Daure fuska yayi yace kafin in dawo ki tabbatar kin gama breakfast in ba haka ba
wlh ranki sai ya baci ya fita fuu......
Yana fita tace wlh bazanyi ba sai dai idan ka dawo ka kasheni komawa tayi ta kwanta
abinda
Bangaren su Jidda kuwa karfe 9:45am ta sauko kasa domin karyawa anan ta tarar da
kowa Harda Rufaida
Dama sun gaisa da Ummi ta gaisar da daddy taja kujera ta zauna nan daddy yayi
mata fadan abinda sukayi hkr ta bashi Rufaida sai hararanta takeyi ko kallonta
jidda batayi ba
10am suke da lecture ta makara sallama tayiwa su Ummi ta dauki key din motarta da
tafi bata shiga side din Hudah ba sai ta dawo don tasan halin Hudah yanxu sai ta
dama musu lissafi
10:30am Dalhat ya shigo gidan yaji shiru dakinsa ya shiga direct ya dauko belt
sannan ya tafi dakin Hudah cikin bacin rai
Bacci ya tarar tanayi iya karfinsa ya zabga mata a firgice ta tashi tana kuka
tambayarta ina breakfast din tace ban girka ba
🌱🌱🌱🌱
*Muffy*
🌱🌱🌱🌱
😰😰😰😰😰😰
AUREN DOLE
😰😰😰😰😰😰
*T W. F*💦💦
Www.Mufeedamuazu.blogspots.com
BOOK 2
Page 36 - 40
*MUFEEDA💦 MUAZU*💦
Tashi tayi a guje zata fita sauri yayi ya rufe kofar tsayawa tayi tana kuka sai da
Dalhat ya daketa san ransa sannan ya bude kofa ya tasata har kitchen ya tsaya a
bakin kofa yace 15mns ya bata ta gama gas ta kunna ta daura ruwan zafi hade da
kayan kamshi
Sannan ta soya masa kwai ruwan na tausa ta juye a flask dinning ta kai masa dama
jiya Jiddah ta kawo bread da daddare
Ta kai masa yana zaune zata wuce ya riko hannunta yace zauna ki karya kema hawaye
na bin fuskarta tace na koshi ko an gaya maka yunwa nakeji
Da karfi ta saki hannunta tace malam sakar mun hannu belt dinsa ya dauko yace zaki
zauna ko sai na fasa miki jiki share hawayen daya zubo mata tayi ta zauna
Tea ta hada rabin cup da kyar ta iya shanyewa ta tashi ta shige dakinta ta kwanta
taja bargo ta rufa tunani take kala kala a cikin ranta
Husnah ke rokon Hajiya don Allah ta barta ta shiga wurin Hudah da kyar Hajiya ta
barta Amma tace karta dade tace to da saurinta ta dauko gyalenta ta fito
Saida ta shiga ta gaida Ummi sannan ta wuce side din Hudah a falo ta tarar da
yaya Dalhat yana kallo gaishe shi tayi ya amsa cikin sakin fuska ya tambayi su
hajiya tace duk lpy klu
Dakin Hudah tashiga a kwance ta ganta Hudah najin motsi tai Sauri ta goge hawayen
fuskarka husna tace Aunty lpy na ganki haka ko baki da lpy ne Hudah tace Haba Irin
wannan tambaya sai kace yar jarida kuma sai yau kika daman zuwa ga baki ga hanci
husna tace don Allah kiyi hkr wlh hajiya ce hanani shigowa wai zanzo in takura miki
yanxu ma da kyar ta barni kuma tace kada in dade
Hudah tace lallai aiko zaki dade don sai kinyi mun girki zaki tafi don bana jin
dadi husna tace toh ki kirata ki fada mata kada tayi fada Hudah tace bazata yi ba
husna tace to meza a dafa Hudah tace coconut rice sai Kuma sakwara da miyar agushi
amma idan kin gama sakwarar kisa a babbar food flask ki barshi a kitchen din
Sai kuma kunun aya don Allah kiyi mai dadi komi na nan a kitchen husna tace to
naga yaya Dalhat a falo Hudah tace to ina ruwana kije kiyi abinda nasaki
Husna tace to mayafin ta cire ta wuce kitchen bata ganshi ba Hudah kuwa komawa
tayi ta kwanta nan da nan bacci ya dauketa husna ko tana kitchen sai aikinta takeyi
Dalhat tunda husna tazo ya dauki key din motarsa ya fice karfe 1:30pm husna ta
gama komi gidan sai kamshi yakeyi ta jera komi a dinning ta gyara kitchen din tsaf
sannan tazo tayi alola ta tashi hudah
Hudah tace wow har kin gama kenan husna tace eh na gama har nayi alola Hudah tace
ngd nima bari inyo alolar toilet ta shiga tayo alolar itama taxo tayi sallah Hudah
kinci abinci ne husna tace aa hudah tace ina yaya Dalhat din Husna tace baya nan
Hudah tace yawwa zubo mana abincin kika kawo mana nan da kunun ayar
Anan sukaci abincin su Hudah dai taki cire hijjabi saboda kada husna ta taga
shedan bulala tayita mata tambayoyi
Karfe 2:15pm Dalhat ya shigo gidan kamshine ya Daki hancin sa saida ya lumshe ido
saboda dadin kamshin......
🌱🌱🌱🌱
*Muffy*
🌱🌱🌱🌱
[3/11, 9:23 AM] Naja: 😰😰😰😰😰
AUREN DOLE
😰😰😰😰😰
*T. W. F*
BOOK 2
Page 46 - 50
mufeedamuazu.blogspot.com
*Mufeeda Muazu*
Shima wuri ya samu kusa da ita ya zauna matsawa tayi ya matso da taga ya kure
wurin ta mike zata canxa kujera fixgota yayi ta fado jikinsa ya matseta mutsu mutsu
take tana kokarin kwacewa ta kasa kwalla ne ya zubo mata tace malam ka sakeni mugu
kawai
Murmushi yayi yace lallai yarinya kin raina ni ammah zanyi maganin rashin
kunyarki yace abinci nafa Hudah ta turo baki tace gashi can a dinning yace baa anan
zanci ba kowo mun
Tashi tayi ta dauko masa sai kallonta yakeyi duk da ta sanya hijabi duk sai ta
tsargu sakwara ne miyar agusi ta kawo ta aje masa zata tafi yace ina zaki dawo ki
zauna ya nuna mata kusa dashi ba yadda ta iya hakanan ta zauna tana kumbura baki
Yace wannan hijab dinfa na menene common cire shi banza dashi tayi kamar bata
jiba kyaleta yayi ya bude abinci aroma din abincin yasa shi ya lumshe ido yaci
abincin sa ya koshi tana nan zaune ya hanata tashi saida ya gama Sannan yace ta
kwashe
Ta kwashe ta gyara wurin tsaf ta dawo ta zauna shiru ne ya biyo baya na yan mintuna
Dalhat ne ya katse shirun da cewa yau kwana nawa da fara period dinki shiru tayi
kamar bataji ba a tsawace yace bada ke nikeyi ba tace yau kwana 3 baice komi ba ya
girgiza kai yace cire hijabin jikinki nace yanxu ko ranki ya baci turo baki tayi
tace dan Allah ka kyaleni kananan kaya ne a jikina hararanta yayi yace me zan gani
a jikinki zaki cire ko saina bata miki rai
Tsaki tayi a hankali sannan ta cire Ashe yaji tsakin tasowa yayi yazo kusa da ita
yace ni kikewa tsaki
Tace ni bada kai nikeyi Dalhat yace dawa kike mara kunya janyota yayi jikinsa ya
matseta bakinsa ya hada nata ya fara kissing dinta tun tana kokarin kwacewa ta
daina jikinta yayi sanyi sai da yayi mai isar sa Sannan ya kyaleta
Yace kada kiga haka ba wai na fara sonki bane kawai dai ina baki hakkinki ne kada
ki kaini kara don na kula ke jarababbiya ne
Tana jinsa batace komi ba suna zaune a haka yana rungume da ita dataga xaman bana
kare bana kuma bacci takeji
Ta dago Ashe ita yake kallo hada ido sukayi tayi sauri ta dauke kai tace don Allah
ka kyaleni inje in kwanta
Dalhat yace towa ya hanaki tace to ka sakeni inje daki in kwanta yace Ashe baki
shirya yin bacci ba tundaga nan bata kara cewa komi ba nan dai tayi bacci a jikin
shi sai da yaga baccin yayi nisa sannan ya kaita daki ya kwantar da ita sannan ya
kula da shedar dukan da yayi ya tausaya mata Ashe haka jikinta yake baya son duka
Shi yayi dukan amma sai baiji dadi ba ya dade a tsaye kafin Shima yaje dakinsa ya
kwanta tunani yake Kala kala daga karshe yaga tunanin ba zai fisshe shi ba ya
watsar da komi yayi kwanciyarsa
Asuba karfe biyar na 5am Dalhat ya tashi ya tafi masallaci ba tasheta ba saboda a
yadda ta fada masa bata sallah ita kuwa Hudah sai bacci take bata tashi ba sai
wurin 5:45am
Da sauri ta sauko daga gado ta shiga toilet tayo alola tazo ta shimfida
sallayarta ta fara sallah abinda bata sani ba shine tana tayar da sallar Dalhat ya
shigo yana tsaye a bakin kofa ya harde hannayensa yana tsaye harta idar
Tayi adduarta juyowan da zatayi suka hada ido gabanta ne yace ras duk ta tsorata
jikinta ya fara rawa
Takowa ya farayi tana jada baya yace cool down tambayarki kawai zanyi hawaye na bin
fuskarta tana girgiza kai tace to ina ruwanka dani da zaka shigo mun daki babu ko
sallama
Tsawa ya daka mata yace nace kizo ko Hudah tace wlh bazan zoba ni dai kawai ka
fitar mun a daki kofar yayi da key ya koma ya zauna yace zo nan ki zauna ya nuna
kusa dashi a hankali take takowa ta zauna hawaye duk ya wanke mata fuska.......
🌱🌱🌱🌱
Muffy
🌱🌱🌱🌱
[3/11, 9:23 AM] Naja: 😰😰😰😰😰
AUREN DOLE
😰😰😰😰😰
*T. W. F*
BOOK 2
Page 51 - 55
mufeedamuazu.blogspot.com
*Mufeeda Muazu*
Daure fuska yayi yace zakiyi mun shiru ko kuwa me akai miki shanye kukan tayi
saboda yadda taga ya murtuke fuska yace ni zaki rainawa wayo kiyi mun karya ko
girgiza kai tayi tace aa don Allah kayi hkr bazan sake ba
Hijabin ya cire mata ya aje gefe guda jikinta sai rawa yake duk ta tsorata yace
yau zan banbance miki tsakanin yaro da babba zumbur ta mike tsaye ta fara ja da
baya yana binta harta kai karshen gado yazo daf da ita numfashin su na haduwa
fizgota ta fado jikin sa hada bakinsa yayi da nata ya fara kissing dinta sai mutsu
mutsu takeyi tana kokarin kwacewa amma ta kasa
Saida yayi son ransa sannan ya kyaleta yace muje muyi alola ba musu ta miki don
ta riga ta tsorata dashi a tare suka yo alola yaja su sallah bayan sun idar ne ya
Kama kanta yayi addua kamar yaya addinin musulunci yace
Ita ta fara tashi kan sofa taje ta zauna duk ta takure guri guda sai kwallah take
sharewa ya dade yana addua sannan ya tashi har gurinta yazo ya tsugunna dai dai
saitin fuskarta yace wannan hawayen na menene bayan ba ai komi ba
Hudah tace don Allah yaya Dalhat kayi hkr wlh bana so Dalhat yace ni inason
hakkina daukanta yayi cak bai direta ko ina ba sai a tsakiyan gado sata yayi ta
cire hijabin ta aje a gefe rungumota yayi ta kwanta a kirjinsa gashin kanta data
tufke ya warware
Hannunsa yasa Yana ya mutsawa Yana jin kamshinta ita kuwa jikinta ba abinda yake
sai rawa doguwar riga ne a jikinta jan rigar ya farayi ta rike tana kuka tace dan
Allah yaya kayi hkr wlh bana so ko kulata baiyi ba ya cigaba da abinda yake
Cire rigar yayi gaba daya kuka take kamar ranta zai fita babu mai taimako cire
jallabiyar yayi ya rage daga shi sai boxers rumfa yayi mata da faffadan kirjinsa ni
Mufeeda da naga haka sai nayi sauri na fita na rufo kofar na koma falo
Can najiyo kukan Hudah kamar ana yankata anan dai na kwanta ban koma ba sai
9:45am dan gane ma idona abinda ya faru koda na shiga Hudah na gani kwance ita ba
bacci take ba idonta a lumshe sai hawaye da yake zuba kamar an bude famfo
Dalhat kuwa tunda ya samu nutsuwa kota kanta bai bi ba dakinsa ya wuce yaje yayi
wankansa cike da farin ciki Hudah na kwance har 10:am ta kasa tashi data yunkura
zata tashi sai ta kasa tashi duk jikinta yayi tsami sai kuka take ta rasa mai
taimakonta
Da taga dai ba wani sarki sai Allah yasa tayi kokari ta mike a hankali tana bin
bango harta shiga toilet ruwan zafi tasa ta gasa jikinta sannan tayi wanka tazo
tasa kaya doguwar riga ta gyara gadon ta koma ta kwanta ga yunwa datake ji kuka
take mara sauti
A haka Jidda tazo ta sameta jidda tace lpy Hudah meyafaru na ganki a haka Hudah
ta runtse ido batace komi ba jidda tace Hudah magana nake amma kinyi banza dani don
Allah ki fada mun abinda ke damunki ko sai na fadawa Ummi Hudah tace bkm yunwa
nikeji dan Allah ki kawo mun abinci jidda tace tunda bazaka fadamun ba bari inje in
fadawa Ummi Jiddah ta mike zata fita Hudah ta janyota tace dan Allah kiyi kada ki
fada mata
Jiddah tace to fada mun menene mayafaru Hudah ta runtse idanunta hawaye masu zafi
suka zubo tace yaya Dalhat ne sai kuma tayi shiru jidda tace kiyi magana
mana.......
🌱🌱🌱🌱
Muffy
🌱🌱🌱🌱
[3/11, 9:27 AM] Naja: 😰😰😰😰😰
AUREN DOLE
😰😰😰😰😰
BOOK 2
Page 56 - 60
mufeedamuazu.blogspot.com
*Mufeeda Muazu*
Hudah tace yaya Dalhat ne yayi mun fyade tana fadin haka ta fashe da kuka Jiddah
tace haba Hudah ki daina fadin haka mijinki ne fah don Allah kiyi hkr ki share
hawayenki Hudah tace dole inyi kuka Jiddah yaya Dalhat bashi da tsusayi karfinsa ya
gwada akaina sannan ba wani nuna kulawa sai da ya samu abinda yake so yayi
tafiyarsa
Ban kara ganinsa ba da kyar na iya tashi nayi wanka na gyara gadon nan ga yunwa
inaji ga bacci bai isheni ba jidda tace kiyi hkr Hudah Allah zai baki ladan hkrn da
kikayi bari in fadawa Ummi ko akwai taimakon da zatayi miki wuyanta ta taba tace
kinga jikinki ma yayi zafi
Hudah tace nidai kada ki fadawa Ummi da wani ido zan kalleta ki barni kawai Jidda
tace wlh bazan barki ba da gudu ta fita tana kwala Kiran Ummi Ummi.........
Ummi....
Ummi dake kwance a falo ita da Rufaida suna hira taji kira ba kakkautawa tashi
tayi zata fita sai ga jidda ta shigo da gudu Ummi tace lpynki kuwa Irin kwala kira
haka
Jiddah tace Hudah ce bata da lpy shine tace wai kar a fada miki Ummi tace ina
Hudahn take Jiddah tace tana can daki a kwance Ummi tace muje tafiya sukayi Harda
Rufaida a kwance suka sameta idonta biyu amma ta rufesu sbd kunyar Ummi
Ummi ta tabi jikinta taji zafi rau kamar garwashin wuta tace meke damunki Hudah
tace bkm zazzabi ne kawai Ummi ta kalleta tsaf ta girgiza kai alamar tausayi don
ta gano ko meyafaru
Tace Jiddah kije ki hado mata tea mai kauri da farfesun kaji sannan kije dakina a
first aid box xakiga PCM ki dauko kiyi sauri
Rufaida na tsaye sai tabe baki take Ummi tace rufaida ki kula da ita ina zuwa
toilet ta shiga ta hada mata mai zafi sannan ta fito tace zaki iya tashi ko sai an
kamaki Hudah ta cije baki sbd yadda take jin zafi tace zan iya
Da kyar ta iya tashi Ummi ta kamata ta kaita har toilet din tace ta shiga ruwan
ta gasa jikinta sannan ta fito dai dai tym din jidda ta dawo hannunta rike da
basket a ciki ta hado kayan Ummi ta hada mata tea sannan ta zuba mata farfesun a
plata
Rufaida tace Ummi wlh yarinyar nan bata da kunya ta cika raki Ummi tace Waye
Yarinyar saankice ita to wlh ki kuyayeni
Hudah bata fito ba saida ruwan ya huce ta gargasa jikin kamar yadda Ummi tace a
toilet din tasa kayanta sai kuma taji dadin jikinta sai dai tafiyarta daya canxa
ta kasa hada kafa haka nan ta fito tana bin bango tana dingisa ka cike da kunya
tazo ta zauna a sofa
Ummi tace sannu kasa amsawa tayi Jiddah ce ta dauki plate din da tea ta aje mata
a gaba tace gashi ki daure ki tuttura ko bakya jin dadi
Hakanan taita turawa harta cinye Ummi ta ballo mata maganin ta bata da kyar ta
hadiye kamar zatayi amai sbd ita ba gwanar shan magani bane
Ummi tace ki kwanta ki huta Kada kice zakiyi girki zaa kawo miki Allah ya sawwake
Da kyar ta karisa gado ta kwanta Jiddah ta gyara mata rufa Ummi na fita Rufaida
ta tsuka tsaki mtsw..... aikin banza sai nayi maganinki sannan tabi bayan Ummi
A kofar falo suka ci karo da Dalhat keya ya sosa yace inakwana hararanshi tayi ta
amsa a dakile Rufaida dake bayan Ummi tace yaya ina kwana ya amsa mata ba yabo ba
fallasa
Wucewa sukayi shi kuma ya shige ciki direct dakin Hudah yaje ya tarar da ita a
kwance Jiddah kuma a sofa tana zaune Hudah na ganinsa ta juya baya Jiddah ce ta
gaishe shi ya amsa da kyar yace nasan kece kika kira Ummi wlh ki kiyayeni kuma fito
da miji zakiyi zan sami Abbu zaman naki ya isa banga abinda kike ba sai
gulma........
🌱🌱🌱🌱
Muffy
🌱🌱🌱🌱
[3/11, 9:27 AM] Naja: 😰😰😰😰😰
AUREN DOLE
😰😰😰😰😰
*T. W. F*
BOOK 2
Page 61 - 65
mufeedamuazu.blogspot.com
*Mufeeda Muazu*
Haka nan ya karaci fadansa ba Wanda ya kula shi Jidda kuwa tashi tayi abinta tace
na tafi skull sai anjima Hudah kuwa juya masa baya tayi a cikin ranshi yana jin
gsky bai kyauta ba amma dole ya tsare girmansa kada yarinya ta raina shi tsaki yayi
ya fita tana jinsa bata dai tanka ba yana fita bacci mai nauyi yayi gaba ita.
Hudah ta koma mkrnt abinta Dalhat shima ya koma wurin aikinsa sai in yazo wkend
haka dai zaman yake bai canxa ba amma dai ya rage wasu abubuwa tafi sakewa idan
baya nan idan yazo ko duk ya takura mata da bukatarsa wani lokaci har mamaki yake
bata idan yana tarairayarta ita kuma sai tayi kam bata san yanayi ba
Wata rana yaxo wkend wani abokinsa yai masa waya yace zaizo shida family dinsa bai
soba don yasan halin Hudah sarai zata iya jisgashi agaban kowaye tana zaune tana
kallo yace abokina na kan hanya shida matarsa zasu kawo mun ziyara Hudah ta miki
cike da masifa tace toni ina ruwana da wasu abokananka ba abinda zanyi musu ko ruwa
wlh ranshi ya baci sosai yace ni zanje taro su wlh naga ba dai dai ba sai nayi
maganinki Hudah tace maganina yafi karfin naka nufota yayi aguje ta shige daki ta
turo kofa kwafa yayi ya wuce
Tana shiga daki ta fada gado tana haki tanata tunanin abinda zatayi musu don tasan
Dalhat zai iya dukanta wannan ba wani abu bane a gurinsa
Wani tunani tayi murmushi tayi ta miki ta fito kitchen ta shiga jollof din indomie
tayi sannan ta dafa kwai ta jera a sama batayi wani abin sha ba sbd sunada lemu a
fridge gida sai kamshi yake a sha wani delicious food aka dafa suna shigowa yaji
kamshi yaji dadi a ransa bai san tsiyar data shirya masa ba wuri ya nuna musu suka
zazzauna yace ina zuwa dakin Hudah ya shiga ya tarar da ita zaune tana danna waya
yace ga bakin namu can a falo ki fito ku gaisa ko dagowa batayi ba balle ta amsa
yaji haushi amma ya danne yace bada ke nikeyi ba Hudah tace niba bakina bane bakin
Kane don haka ka fitar mun a daki abinci na kitchen da kyar ya lallasheta sannan ta
aje wayar ta sauki mayafi tare suka fito ba yabo ba fallasa suka gaisa daga nan ta
wuce kitchen ta dauko tray din data jera abincin sannan ta bude fridge ta dauko
musu ruwa da lemu ta aje musu ta koma ta zauna
Matar ta taso zata zuba abinci tana bude kular taga indomie ita bata damuba saboda
tana ci ita da danta mijinta ne baya ci kallon shi tayi shima ya kalleta Dalhat
yace lpy murmushi yayi yace ah bkm matar ta zuba a plate ta mikawa dansu mai suna
Ahmad ta zuba nata Dalhat yana gani yace meye haka nike gani indomie sbd yasan
abokin nasa baya cin indomie tun suna skull ranshi yayi matukar baci zai fara fada
abokin ya hanashi(Farook) hudah tace ai ina ce bakin naka turawa ne ta ya mutsa
fuska ta tashi ta shige daki abinta Dalhat abin duniya duk ya ishe shi tashi yayi
ya fita waje Jiddah ya kira yace don Allah idan da abinci ta kawo masa yayi baki ne
batayi mamaki ba saboda tasan halin Hudah sarai bata jin magana dawowa yayi yana ba
farook hkr ace mutum yazo tundaga nesa a rasa abinda zaa bashi sai indomie ai
wannan wulakanci ne farook yace kasan mata sai hkr bilkisu(matar farook) tace kada
ku daura mata laifi dayawa fah may be ko bata jin dadi ne yasa tayi indomie sbd shi
zai zaifi mata sauki
Baa dau lokaci ba Jiddah tashigo da sallama hannunta rike da tray gaishe su tayi ta
aje tray din ta juya zata shiga dakin Hudah Dalhat yace ina zaki gulma ko to wuce
ki tafi ngd kirikiri ya hanata shiga haka nan ta hakura ta juya cike da kunya a
gaban mutane ya jisgata
Farook yace ya zaayi ka hanata shiga Dalhat yace kyaleta ai duk halinsu daya
bilkisu ta bude kular da Jiddah ta kawo rice nd stew with salad ne ta zuba masa
Dalhat yace madam ke bazaki ci bane bilkisu tayi murmushi tace Alhmdllh tashi tayi
tace bari in shiga gurin gimbiyar Dalhat ya kirkiro da murmushin karfin hali yace
shikenan zaaje ayi kuskus ko
Dakin Hudah ta shiga da sallama Hudah ta dago ba yabo ba fallasa tace sannu bilkisu
tace yawwa dan Allah zanyi sallah Hudah ta nuna mata toilet kifin ta fito ta
shimfida mata sallaya
Dalhat da farook kuwa tare sukaci abincin suka kara sannan suka wuce masallaci
harda Ahmad a hanyarsu ta dawowa ne Dalhat yake bashi labarin yadda aurensu ya
kasance shida Hudah dayake anyi auren basa Nigeria Dalhat ya kara da cewa yanxu
Allah ya jarrabeni da sonta amma ban san yadda zanyi in fada mata ba kona fada mata
ma ba dole bane zata iya cewa karya nike yaudaranta zanyi farook ya numfasa yace
abokina gsky kayi kuskure tun farko ya zaayi ka biye mata kuyita shirme kaifah
namijine Dalhat yace kuskure dai anriga anyi yanxu meye shawara
Farook yace shawara dayace ka rika nuna mata kulawarka sannan ka rika kawar da
kanka a wasu abubuwan daga nan har akai mataki na biyu Wato lokacin daxaka furta
mata kalmar so farook ya kara da cewa kaga kaman yanxu kada kayi mata magana akan
abinda tayi dama tayi ne don ta bata ma rai Dalhat yace shikenan ba abokina ngd
nidai fatana Allah yasa kada tayiwa madam wulakanci farook yace insha Allah bazata
yiba da haka suka shigo gida
Bilkisu kuwa tana fitowa daga toilet din taga har ta shimfida mata sallaya sallah
tayi Hudah tace ga kayan kwalliya nan a dress mirror powder kawai ta shafa ta dawo
kusa da ita ta zauna tace ni sunana bilkisu kefa tace sunana Hudah bilkisu tace
nice name Hudah tace tnx bilkisu naso suyi hira Ammah Hudah taki sakin jiki sai cin
magani take Hudah tace ya sunan yaron nawa bilkisu taji dadin karan datayi mata
tace sunan sa Ahmad tashi tayi ta bude drower ta kwaso turaren wuta da humra masu
kyau da tsada tun na aurenta ne tasa a leda tace gashi ba yawa bilkisu ta amsa tayi
godiya sunyi shiru ba mai magana bilkisu tana tunanin hali Irin na Hudah kamar mai
aljannu Dalhat ne ya shigo yace madam ki fito zaku tafi juyawa yayi bilkisu ta
dauki mayafinta tace to Hudah sai anjima itama mikewa tayi sukayi exchanging no a
tare suka fito a tsaye suka tarar dasu Hudah tace Ahmad zo mana mu gaisa da yake
yana da wayau baiyi quyaba yaje 2k ta bashi tace gashi ka sha sweet Ahmad yace ngd
Aunty farook yayi gdy har waje ta rakasu tana harar Dalhat duk suna kallonta
murmushi farook yayi yace wannan madam din taka yar daru ce Ammah fah tanada
taushin zuciya duk da haka kayita lallashinta haka sukayi sallama cike da begen
juna saida yaga tafiyar su sannan ya dawo gida ya tarar ta kwashe kayan da sukaci
abinci ta gyara wurin kusa da ita ya zauna yace my wife ngd sosai sunanda ya kirata
dashi ya bata mamaki bata gama mamaki ba taji yace ki shirya anjima zamu fita
shopping batayi musu ba saboda itama tana son fita
Tace to don Allah inaso in shiga wurin hajiya yanxu yace to ba damuwa zuciyanta
fari kal da gudu ta shiga daki ta dauko hijab dinta ta fito yana zaune tace sai na
dawo
Da gudu ta shiga tana kwada Kiran hajiya, hajiya tace ke wai yaushe ne zakiyi
hankaili turo baki tayi tace nine banida hankali ko hajiya tace ya Dalhat din
Hudahh tace yana gida yau bazan koma gida ba sai dare suna cikin hira shahid ya
shigo ya kalli Hudah yace ke bakida mutunci ko Hudah tace me kuma nayi yace bansani
ba zakiyi shiru ko saina fasa bakinki anan wurin hajiya tace lpy shahid yace daxu
ina gidan Dalhat ya kira Jiddah wai insu nada ta kawo masa yayi bakine yanxu hajiya
abinda takeyi ya dace kenan hajiya ranta yayi matukar baci Hudah batayi aune ba
taji saukan mari rike wurin tayi don azaba ta bude baki zatayi magana shahid ya
bige bakin zai daketa hjy ta hana tace baa asan kotana da juna biyu......
🌱🌱🌱🌱
Muffy
🌱🌱🌱🌱
[3/11, 9:27 AM] Naja: 😰😰😰😰😰
AUREN DOLE
😰😰😰😰😰
*T. W. F*
Book 2
Page 66 - 70
Mufeedamuazuu.blogspot.com
STORY
And
WRITTEN
BY
*Mufeeda Muazu*
*Rahmat Nalele*
*Husnah mb*
Hudah ta turo baki tace hajiya ki daina Irin wannan maganan Nifa banida komi kuma
ma Allah ya kyauta in tsaya yayi mun ciki bana sonsa bana kaunarsa Shahid yace
hajiya kinji abinda take fadi ko sbd taga kince a kyaleta mikewa tsaye yayi ya nuna
kofan fita yace fita a gidan kafin in karkaryaki mara kunyar banza kawai hajiya
kasa magana tayi lallai haryanxu Hudah batayi hankali ba
Hudah tayi kaman bada ita yake ba saida taga ya zaro belt zai daketa sannan ta daka
tsalle ta koma bayan hajiya tana kuka tace ya zaayi mutum da gidansu a rika korarsa
hajiya kice ya kyaleni hajiya tace aini Kinfi Karfina duk abinda zaiyi miki bazan
sake magana ba tana gama fadar haka ta tashi ta haye sama abinda ganin haka yasa
Hudah ta mike tana goge hawayenta jikinta duk ya mutu ta kalli Shahid dake nuna
mata kofar fita tace Allah ya isa mugu kawai ta fita a guje koda ta shiga gida side
din su Jiddah ta wuce a falo ta tarar da Jiddah da Radiya kusa da Jiddah taje ta
zauna tana haki Jiddah tace ke lpynki sai kace an biyoki Hudah tace yaya Shahid ne
don wulakanci wai zai dakeni da aurena mtsw.....tsaki sukaji a tare suka dago don
gane ma idonsu Waye mai tsakin Rufaida ce ba Wanda ya kulata ta taso tazo har gaban
Hudah tace ke banza baki ganin mutanene da bazakiyi musu sallama ba Hudah ta mike
tsaye cike da masifa ta kalleta sama da kasa tace ina mutanen suke waike wace Irin
karya ce mara zuciya ance baayi dake amma kin nace Rufaida tace ai naga dai kema
din ba sonki yake ba kuma ai kece karyar Hudah ta kai mata magigicin mari kikake
tas!
Rike wurin tayi tace ni kika mara Hudah tace an mareki din ke din banza ta
murmushin mugunta tayi tace yanzu kam duk abinda zakiyi kiyi lokacinki ne nan da
kwana kadan ba kya gidan nan wlh sai kin barshi Jiddah tace ke Rufaida mekike fada
haka Hudah tace kyaleta ai ni nafison haka sbd nima dole akaimun kare yayar da
zuciyarsa an dauka kullum ana gidansu saurayi don nasan ba don zumunci kike zuwa ba
ai sai ki zauna a gidan ubanki yazo ya sameki sakarya kawai wadda bata da aji tana
gama fadar haka taja hannun Jiddah suka haye sama suka barta a nan sororo
A dakine Jiddah take fadawa Hudah ankawo goron sa rana da nata dana Husnah 6mnth
zaa sa Hudah tace lallai ne shine ba wanda ya fadamun yanzu da ba danke da kika
fadamun ba bazan sani ba koda yake yanzu na zama bare kwallah ne ya cika idonta
Jiddah tace ba haka bane kene kinki ki kwantar da hankalinki ki natsu ki rungumi
kaddara ba wanda bai sonki so ake kiyi hkr ki gyara komi mai wucewa ne watarana sai
labari
Hudah tace bazaki gane bane amma kinsan wani abu kuwa? Jiddah ta girgiza tace aa
sai kin fada Hudah tace naga kwana biyu ya chanza sai wani kula dani yake yana
tattalina kinga dazu da yayi baki ban dafa abinci ba da ace da ne da wlh raina sai
ya baci Jiddah tace ni dama nasan yaya Dalhat yana sonki kene dai kike shirmenki
Hudah tace rufe mun bakinki anan bani yake soba jikina yake so Jiddah tace kwaji da
shi dai ku kuka sani Hudah ta mike tace ni kinga tafiyata magriba tayi Jiddah tace
to muje in rakaki koda suka sauko ba kowa a falon
Side dinta suka tafi anan sukayi magriba sukai issha sannan suka ci abinci suna
zaune wayar Jiddah ta fara ringing dubawa yayi taga mai Kiran mikewa tayi tace
matan yaya swtyna yaxo yana jirana gud nyt bata jira jin me zata ce ba ta fita da
sauri kwallah ne ya kawo mata tace Allah sarki soyayya ni ban samu wannan daman ba
Jiddah na fita ba dadewa Dalhat ya shigo sannu da zuwa kawai tace shi kuma gogan
dadi yaji yau ta kulashi bai san sbd yace zasu fita bane yace yawwa ki shirya ko da
sauri tace to ta tashi ta tafi dakinta shima dakinsa ya wuce tana shiga ta bude
wardrop dinta taga kayanta ba yanda yake ba
Dalhat harya shirya ya fito falo yaga bata fito ba dakinta ya shiga ya ganta tsaye
tana fitowa da kaya yace ya dai madam juyowa tayi tace yaya bayan na fita waye ya
shigo min daki Dalhat yace ba wanda ya shigo nima fita nayi lpy tace lpy bkm yace
ko inzo in tayakine tace Aa ka barshi kawai nakusa gamawa ta janyo wani kaya kenan
wani magani ya fado kallonsa tayi ta kalli maganin shima kallon maganin yayi ya
kalleta ya duka ya dauka har an sha rabi karantawa yayi maganin family planning ne
tsareta yayi da ido jikinta ya fara rawa ta bude baki zatayi magana ya bige bakin
cikin zafin rai ya kaita bango ya matseta yace waya baki wannan maganin a ina kika
samu bakinta na rawa tace Allah yaya bani na sha ba ni ban san wanda ya kawo mun ba
ranshi ya dada baci wato shi zata rainawa hankali ga abu ya gani da idonsa......
🌱🌱🌱🌱
Muffy
🌱🌱🌱🌱
[3/11, 9:27 AM] Naja: 😰😰😰😰😰
AUREN DOLE
😰😰😰😰😰
*T. W. F*
Book 2
Page 71 - 75
Mufeedamuazuu.blogspot.com
STORY
And
WRITTEN
BY
*Mufeeda Muazu*
*Masoya littafin Auren dole ina mai baku hakuri na rashin jina da mukayi kwana2
fatan zamu kasance tare dani ngd Allah ya bar kauna*
Hudah da tuni hawaye ya wanke mata fuska tace don Allah yaya kayi hkr wlh bazan
kara ba ammah don Allah kada ka fadawa su hajiya Dalhat ya koma gefe ya xauna cikin
damuwa yace yanxu kin da kike mun har ya kai haka Hudah dai batace komi ba don ta
san ita dai bata taba shan maganin family planning ba to waye ya kawo mata har
cikin drawer koma waye Allah ya saka mun Dalhat ya daka mata tsawa yace ba magana
nike miki ba Hudah tace Allah yaya ni ban san da shiba ba nawa bane hannu ya daga
ya sharara mata mari yace ni zaki rainawa wayo banaki bane nawa ne ko
Tashi yayi ya kwashe maganin ya fita a dakin don idan ya zauna zai iya zaneta
sbd yanda zuciyarsa ke kuna yana fita ta dauko wayarta numbern Jiddah tayi dialing
ring biyu aka daga tace jiddah don Allah idan bakya komi ina son ganinki jiddah
tace lpy ba yanzu muka rabu ba Hudah tace don Allah ke dai kizo Jiddah tace to
ganinan zuwa baa sauki wani lokaci ba Jiddah ta shigo Hudah ta rungumeta tana kuka
ta kasa magana Jiddah ta dagota fuskarta cike da damuwa tace kince inzo gani kuma
nazo kin tasani a gaba sai faman kuka kike ko in kira su Ummi ne
Hudah dai ta kasa magana sai ajiyar zuciya takeyi da kyar tayi shiru tace jiddah
don Allah ki taimaka kicewa Ummi tasa yaya Dalhat ya sakeni ni gsky nagaji da
wannan auren Jiddah tace waike Hudah meke damunki ne yanzu me kuma akayi
Abinda basu sani ba shine duk maganar da sukeyi Dalhat yana jinsu yazo wucewa
yaji ana magana shine ya tsaya ji kawai sukai an bugo kofa da karfi cikin hargagi
ya fara magana yace ke meya hana kije kice kin gaji tace in sakeki mara kunyar
karya to bazaa sakeki ba sai dai ki mutu Jiddah duk ta tsorata ta tashi zata fita
ya daka mata tsawa yace ina zaki munafuka kawai kashedi daga yau kada in kara ganin
kafanki anan side in bada wani kwakkwaran dalili ba in ba haka ba yayi kwafa ganin
ta fita a dakin Hudah ta tashi da gudu zata bita Dalhat yasa kafansa ta fadi
dukawa tayi anan tana kuka mai tsuma zuciya shi kansa daurewa kawai yakeyi saboda
kukanta har cikin zuciyarsa yake ji dukowa yayi inda take ya dagota ya zaunar da
ita a sofa yana goge mata hawaye yace kiyi shiru kinji don Allah ina rokonki kada
ki ra shan irin wadannan maganin kinji ba kya tunani zai iya cutar dake daga kai
tayi alamar taji Dalhat yace to dan yi murmushi mana smiling tayi yace koke fah
Tunani take anya wannan yaya Dalhat ne kuwa? ya kula da hankalinta baya wurin iska
ya hura mata firgigit tayi kaman ta tashi daga bacci yace tunanin me kikeyi haka
tace bakomi yace Anya kuwa tace bacci nikeji yaya yace kinyi wanka ne tace yanzu
dai zanyi
Dalhat yace muje in tayaki ba musu tace to sbd tana neman shiri kada yaje ya
fadawasu hajiya abinda bataji ba bata ganiba tare sukai wankansu suka shirya tare
ranar dai sun farantawa junan su kaman ba auren dole akayi ba
Da asuba shiya rigata tashi saida yaje yayi alola sannan yaxo ya tasheta ya wuce
masallaci ita kuma tunda tai sallah bata koma ba ta gyara gidan tsaf sannan ta
shiga kitchen ta hada musu breakfast daki ta koma daki ta shiga wanka
Bai dawo masallaci sai karfe bakwai na safe da kamshi ne ya daki hancinsa wani
dadine ya ziyarci zuciyarsa yana jinjinawa lallai yayi saar mata mai tsafta da iya
girki sai dai kash bata sonsa amma zan koya mata sona insha Allah ya fada a
fili..........
🌱🌱🌱🌱
Muffy
🌱🌱🌱🌱
[3/11, 9:27 AM] Naja: 😰😰😰😰😰
AUREN DOLE
😰😰😰😰😰
*T. W. F*
Book 2
Page 75 - 80
Mufeedamuazuu.blogspot.com
STORY
And
WRITTEN
BY
*Mufeeda Muazu*
*Masoya littafin Auren dole ina mai baku hakuri na rashin jina da mukayi kwana2
fatan zamu kasance tare dani ngd Allah ya bar kauna*
Yana shigowa dakinsa ya shige anan yayi wanka ya shirya cikin shadda light blue
sunyi masa kyau sosai kaman sun hada baki itama less tasa light blue tayi kyau
sosai a dinning ya sameta tana hada tea cikin sakin fuska ya kariso kujeran dake
kallon nata yaja ya zauna yace amarya kin sha kamshi murmushi tayi tace ina kwana
yaya amsawa yayi yace fatan kin tashi cikin koshin lpy murmushi kawai tayi batace
komi ba
Tagama hada tea dinta ta fara sha yana kallonta yace madam kinta shan abinki ke
daya bako tayi hudah tace ai gashinan ni ba hanaka nayi ba Dalhat yace to a hada
mun mana tashi tayi da kofinta a hannu ta harare shi tace ai kanada hannu tayi gaba
abinta kallonta yakeyi har ta shige daki yana mamakin hali irin na Hudah ga taurin
kai ga kafiya
Sauri yayi ya hada tea ya karya abinsa dakinsa ya koma ya dauko jakarsa don yau
Monday zai koma wurin aikinsa dakinta ya shiga yayi mata sallama ba yabo ba
fallasa tace masa a dawo lpy Allah ya tsare Dalhat yaji dadin adduar datayi masa
yace ngd ko kinada bukar wani abu ne girgirza kai tayi tace babu komi bakin kofa ta
rakoshi
Bayan fitarsa ba dadewa ta kira jidda a waya tace idan ta shirya ta sameta a waje
ba a dau mintoci ba Jiddah ta fito cikin shirinta daga nan suka dauki hanya sai
mkrnta
Da rana Rufaida tafi gidansu dama sbd Dalhat take zuwa kamar yadda Hudah ta fada
Ansa ranar jiddah da Shahid Husnah da sir Haidar wata shida aka sa a skull su
jiddah suka hadu da sir Haidar bayan su gaisa sai gdy yakewa Hudah sannan yayiwa
jiddah fatan alkhairi
Friday ranar ne kuma Dalhat zai dawo Hudah sai aikace2 takeyi jidda ta shigo tace
matan yaya ki saurareni da kyau wlh gara ki cire taurin kan nan naki kinsan yau
yaya zai dawo ko to gashi har Rufaida taxo tace wlh sai ta auri yaya kota halin
kakane Hudah ta mike tsaye tace wlh bata isa ba kuma tayi kadan
Jiddah tace abinda zaisa tayi kadan shine kawai ki rike mijinki da kyau kin san shi
namiji yana son kulawa kisawa zuciyarki salama sannan ki yawaita addua
Hudah da hawaye ya cika mata ido tace jiddah nasan duk abinda kike fadamun gsky ne
kuma nasan ke mai kaunata ce da gsky kada ki manta yaya Dalhat ba sona yakeyi ba
tayaya kike gani xaman mu zai dai daita tana kaiwa nan ta fashe da kuka Jidda sai
lallashinta take tana bata hkr tare da shawarwari har dai ta samu ta shawo kanta da
kyar
Jiddah tace yanzu me zakiyi in tayaki Hudah tace nagama komi wanka kawai zanyi
yanzu jidda tace to muje in zabo miki kayan da zaki sa Hudah dai bata ce komi ba
suka shiga daki Hudah ta shiga wanka Jiddah ta dauko akwatin kana nan kaya a ranta
tace lallai Hudah akwai wauta Wato ko jerawa ma batayi ba ta barshi a cikin akwati
wani riga red da mini skirt black sai band black shima ta aje a gefen gado ta mayar
da akwatin
Hudah na fitowa jiddah tace iyyeh amaryarmu kinji kamshi yanda yake tashi tun
kafin ma ki fito lallai yau yayana zai more Hudah ta kai mata dukan wasa tace
dallah bani wuri in shirya kinzo kin cikani da surutu wlh yaya shahid zai sha fama
dake Jiddah tace shikenan na daiji ga kaya nan don nasan yanzu yaya ya kusa
isowa............
🌱🌱🌱🌱
Muffy
🌱🌱🌱🌱
[3/11, 9:30 AM] Naja: 😰😰😰😰😰
AUREN DOLE
😰😰😰😰😰
*T. W. F*
Book 2
Page 81 - 85
Mufeedamuazuu.blogspot.com
STORY
And
WRITTEN
BY
*Mufeeda Muazu*
Hudah tace uhmm ni kinxo duk kin dameni da surutunki kinsan dai ba auren soyayya
mukayi ba Jiddah tace wai meyasa kike dawo da hannun agogo baya ne kuma nina san
yaya Dalhat yana sonki kece dai baki bashi damar ya nuna miki ba
Uhmmm kawai Hudah tace ta zauna a gaban mirror ta fara kwalliya ta shafa wancan ta
goga wancan tayi kwalliyarta kaman ba ita ba gasu humra data shasshafa Jiddah ta
miko mata kayan Hudah ta daga kayan ta kallah tace gsky bazan iya saka wannan kayan
ba sai kace yar iska
Jiddah tace wani irin iskanci ba mijinki bane wani dare ne jemage bai ganiba
Hudah ta bata rai tace kinga kada ki bata mun rai yayi ta gani mana Jiddah tace
maida wukar gyara kayanka ai bai zama sauke mu raba ba kuma ni bana son yaya ya
kawo miki watane musamman ma Rufaida data nace ta like masa kamar cingum Hudah tace
hakane kuma ya na iya kayan ta dauka ta saka Jiddah tace wow gsky ba karamin kyau
kikayi ba anya yaya zai iya ganeki kuwa gsky kinyi kyau sosai Hudah tace uhmm
kalli fah skirt din iyaka gwiwa fah kaman wata karuwa Jiddah tace shine fashion
tashi tayi tace na barki lpy a sha soyayya lpy Hudah tace ina kuma zakije muna
hirar mu Jiddah tace zan dawo ai tashi tayi ta fita Hudah ta bita a guje
A bakin kofa sukai karo da Dalhat dago kai tayi suka hada ido taga ya kura mata ido
kallon jikinta tayi taga ashe kananan kayane a jikinta juyawa tayi zata bar falon
sauri yayi ya rikota ta fado jikinsa rungumeta yayi tsam a jikinsa dada lafewa
tayi a fadadden kirjinsa sun dauki lokaci a haka kafin ya saketa tare da cewa kinyi
kyau da gudu ta shige daki tana haki
Murmushi yayi yaji dadi a ransa kuma yana fatan Allah yasa itama ta fara sonsa ne
kamar yadda yake sonta dakinsa ya shige yayi wanka ya sauya kayansa kananan kaya ya
saka koda ya fito falo bai ganta ba dinning area ya kalla yaga kuloli an jajera
zama yayi a 3seater kiranta ya shiga saida ya kira sunanta sau biyu sannan ta amsa
zunbulelen hijab ta saka tana tafe a hankali harta fito falon kallonta kawai yake
nesa dashi ta zauna daure fuska yayi yace meye haka kuma mijinki ya dawo ai kamata
yayi kizo kiyi masa sannu da zuwa ba
Turo baki tayi cikin shagwaba kaman zatayi kuka tace sannu da zuwa yaya dariya ta
bashi ma boye dariyar yayi sbd kada tayi fushi murmushi kawai yayi yace gimbiyata
me kuma akai miki na kuka ke kullum kuka tasowa yayi yazo kusa da ita yace fada mun
mai akayi miki goge mata fuska hijab din ya fara kokarin cire mata rikewa tayi
kallonta ya tsaya yi ido cikin ido data ga kallon ya isheta dukar da kanta tayi
Kokarin tashi takeyi ta kasa sbd yadda ya rungumeta da kyau Dalhat ya kalleta yace
ina zaki bayan baki nuna min kwalliyar ba nasan kuma sbd ni aka yishi wani haushi
ne ya kamata wai sbd shi tayi kwalliya
Jikinta duk ya mutu ta kasa komi haka nan tana gani ya cire mata hijabin kissing
dinta ya farayi kota ina kuka ta saka masa saurin dagowa yayi da idonsa da suka
canxa kala yace mene ya saki kuka kasa cewa komi tayi sakinta yayi yace nasan baki
sona kiyi hkr muje ki bani abinci ko kunyar tashi take sbd kayan dake
jikinta..........
🌱🌱🌱🌱
Muffy
🌱🌱🌱🌱
[3/11, 9:30 AM] Naja: 😰😰😰😰😰
AUREN DOLE
😰😰😰😰😰
Book 2
Page 86 - 90
Mufeedamuazuu.blogspot.com
STORY
And
WRITTEN
BY
*Mufeeda Muazu*
Ya kula da haka dukowa yayi kusa da ita yace ko in daukeki ne bazaki iya tafiya ba
me kike boye mun a jikin naki wani dare ne jemage bai gani ba pillow din kujera ta
jefa masa ta tashi a guje rufa mata baya yayi
Kujera yaja ya zauna yana kallonta yakeyi cikin kauna inama da tun farko bai nuna
mata baya sonta ba gsky tana da saukin kai ammah sai ka fahimceta wannan zancen duk
a zuci yake yi ta zuba masa abincin tana ta magana bai san tanayi ba sai data hura
masa iska yayi firgigit kaman ya farka daga bacci murmushi tayi taja kujeran dake
kallon nasa ta zauna tayi tagumi Dalhat yana cin abinci yana lumshe ido sbd dadi
cikin kuluwa yace lpy kike tagumi bayan gani kusa dake hararansa tayi tace sai me
don kana kusa dani mutum da baya sonka don kana kusa dashi meye amfaninsa tsaki
tayi ta ja kujera zata tafi rike hannunta yayi yace ina zaki bayan muna hiran mu
mai dadi
Kwallah ne ya cika mata ido aje abincin yayi ya rike mata hannu yace muje inji
waya taba mun Mrs Dalhat ne falo suka koma suka zauna ya rungumeta yace fada mun
meyake damunki shiru tayi batace komi idonta a rufe Dalhat yace bude idonki ki
kalleni da kyau ki kalli kwayar idona wlh ina sonki ina matukar kaunarki da sauri
ta bude idonta fuskanta cike da mamaki hawaye wani na bin wani tace yaya wlh karya
kakeyi ni nasan baka sona kai ka fada da bakinka tayaya kakeso in gaskata ka
yunkurawa tayi zata tashi ta kasa sbd irin rikon da yayi mata
Dalhat yace haba Hudah wlh ina sonki don Allah kiyi hkr da duk abubuwan da suka
faru ki daukeshi a matsayin kaddara kin san kuma ba wanda ya isa ya ketara abinda
Allah ya rubuta masa girgiza kai tayi tace ni dai gsky bazan yarda ba yaudarata
kawai kakeso kayi nidai kawai abinda na sani shine baka sona nima kuma bana sonka
Dalhat yayi sauri ya rufe mata baki yace kada ki fadi haka my swt hrt wlh ina sonki
ki yarda dani wlh bazan cutar dake ba ki daure ki soni koda rabin sonda nike miki
ne ki bani dama in nuna miki irin sonda nike miki
Tureshi tayi iya karfinta ta tafi daki aguje tana kuka baiyi yunkurin binta ba sbd
kada ya matsa mata tashi yayi ya tafi side din su mama don ya gaishesu
Hudah najin fitansa ta tashi ta zauna tana share hawayen da yaketa ambaliya a
fuskarta ta dauki wayarta numbern Jiddah tayi dialing ringing daya ta dauka Hudah
tace kina ina don Allah kizo yanzu Jiddah tace lpy yayan fah Hudah tace ya fita ita
a tunaninta waje ya fita batasan ciki ya shiga ba Jiddah itama batasan ya shigo ba
tana dakinta
Jiddah tace to ganinan zuwa suna gama wayar ta sauko kasa ganinshi tayi shida Ummi
suna hira a hankali ta kariso tace gaishe shi tashi tayi zata fita Dalhat yace ke
ina zaki Jiddah tace gurin Hudah zani Dalhat ya sha mur yace inace yanzu kika dawo
to bazaki jeba Ummi tace sbd me zaka hanata zuwa gurin yar uwanta Dalhat yace Ummi
ita ke zugata yanzu tana zuwa zan rasa gane kanta Jiddah tace Allah Ummi ni ba
ruwana Dalhat yace rufemun baki zaki koma ko kuwa bayadda ta iya haka nan ta hkr ta
koma tana shiga daki Rufaida ta kwashe da dariya tace Allah ya kara uwar gulma ai
sai Hudah ta bar gidan nan Jiddah tace tunda gidan ubanki ne ba Rufaida taji zafin
maganar ta mike a fusace tace ni kike fadawa haka Jiddah tace ke din banza daga
hannu tayi zata mareta Jiddah ta rike hannun ta zabga mata mari ta daga hannu kenan
zata kai mata a daya kuncin taji an rike hannun Ashe Ummi ce Marinta tayi tace ashe
ke wawiyace Jiddah ta bude baki zatayi magana Ummi tace yi mun shiru mara kunya
kawai Ummi ta rike hannun Rufaida suka bar dakin
Jiddah ta dauki wayarta takira Hudah ta fada mata Dalhat ya hanata shigowa Hudah
tace to shikenan ina nan shigowa sukai sallama
Dalhat kuwa suna gama gaisawa da hajiya Dalhat ya fita daga gidan
Hudah kuwa suna gama waya da Jiddah ta dauki mayafinta ta rufe side dinta ta tafi
side dinsu Jiddah bata tarar da kowa ba a falon kasa sama ta hau Ummi ta gani zaune
ita day Rufaida kusa da Ummi taje ta zauna a kasa ta gaisheta mikewa tayi zata
shiga dakin Jiddah Ummi tace ina fatan dai lpy Hudah tace lpy klu Ummi tace to
shikenan
A zaune ta tarar da Jiddah ta zabga tagumi Hudah tace lpy na ganki haka meyake
faruwa Jiddah tace uhmmm wancan yarinyar mana yanzu tasa Ummi ta mareni Hudah tace
kyaleta zamuyi maganinta......
🌱🌱🌱🌱
Muffy
🌱🌱🌱🌱
[3/11, 9:30 AM] Naja: 😰😰😰😰😰
AUREN DOLE
😰😰😰😰😰
Book 2
Page 96 - 100
Mufeedamuazuu.blogspot.com
STORY
And
WRITTEN
BY
*Mufeeda Muazu*
Ki jirani ina dawowa wlh sai nayi maganinki Dalhat ya fada tare da fita tunda ya
fita tana zaune a inda ya barta ta kasa motsawa sbd bakin ciki gashi bata gane mai
yake nufi ba
Gidansu Hudah ya shiga a falo ya tarar dasu Hajiya da Alhaji kusa da Alhaji ya
zauna a kasa ya kasa magana Hajiya ce tace lpy na ganka haka
Dalhat ya dukar da kai yace Hajiya Hudah ce kasa magana yayi ya ciro maganin ya
mikawa hajiya
Alhaji yace wannan maganin fah na menene karantawa Hajiya tayi ta mikawa Alhaji
tana salati
Alhaji na gani ya tashi cikin bacin rai ya shiga daki ya dauko bulala ya boye a
aljihu sannan ya fito
Da karfi Alhaji ya bude kofar Hudah na ganinsa ta tashi zata gudu daki tsawa ya
daka mata yace ina zaki marajin magana
Babu abinda take sai kuka tace Alhaji wlh ba nawa bane ni ban san wanda ya kawo ya
aje mata ranshi ya dada baci
Bulalarsa ya ciro daga aljihu tana ganin bulala kukanta ne ya dada karuwa zata gudu
alhaji yace idan kika motsa daga nan zaki gane kurenki
Dukanta yake baya ji baya gani kuka take tana ihu tare da bashi hakuri amma ina
Dalhat ne daya ga dukan yayi yawa yaxo ya Kama bulalan ya rike yana bashi hakuri
Ummi ce ta shigo sbd tun daxu take ta jin kuka bata san daga inda yake fitowa ba
sai yanzu ta tabbatar da inda kukan yake
Ummi tace lpy meya faru haka Alhaji don Allah kayi hakuri
Yarda bulalan yayi ya fita batare da cewa komi ba
Ummi ce ta karisa kusa da Hudah ta rikota tana lallashinta kallon Dalhat tayi tace
me tayi maka kaje ka hadota da mahaifinta
Hudah dake kuka tace Ummi Allah ni ban taba shan wani magani ba domin hana daukan
ciki Allah shine shaidata ta karisa magana tana kuka
Bayan Ummi ta tafi Dalhat ya shige daki abinsa ya barta anan sai kuka take gashi
zazzabi ya fara kamata da kyar ta iya tashi ta shiga daki ta kwanta ta lulluba da
bargo ranar dai batai bacci ba da Asuba ma da kyar ta iya tashi tayi sallga
Dalhat kuwa ya dauki fushi da ita don koda safe daya tashi baibi ta kanta ba
wankansa yayi ya fita
Allah sarki Hudah baiwar Allah tana kwance sai rawar sanyi takeyi gashi kowa ya
juya mata baya akan laifin da bataji ba bata gani ba
Cikin daki ta shiga can karshen gado ta hangota rufe da bargo sai rawan sanyi
takeyi da sauri ta karisa gurinta ta tabi jikinta taji zafi rau kamar garwashi
Da yake Ummi ta fada musu duk abinda ya faru jiya Rufaida sai murna take
Hijab ta dauko da takalmi ta saka mata ta rungumeta ta dauki key din motarta
Asibiti suka tafi suna zuwa aka karbeta aka basu gado likita ya dubata sannan wasu
nurses sukazo suka daura mata drip
Ana gama sa mata tayi bacci Jiddah na zaune ta kura mata ido duk tayi wani fari ta
rame ita tausayi ma take bata
Doctor ne ya shigo ya tambayi Jiddah ina mijinta ko mamanta lallai yana son ganin
wani a cikinsu Jiddah tace doctor ka fadamun meke damun yar uwata
Doctor yace aa sai ta kira musa wanda yace yana son gani
Wayarta ta dauko numbern Ummi ta kira bugu daya ta dauka muryarta na rawa tace Ummi
Hudah bata da lpy muna asibiti yanzu haka doctor yace yana bukatar ganin daya daga
cikin ku koke ko yaya Dalhat
Cikin firgice Ummi tace meke damunta Jiddah tace nima ban sani ba doctor yace sai
kunzo nan dai Jiddah tayi mata kwatancen asibitin
Ummi cikin sauri ta shirya ta sami Abbu ta fada masa sannan ta kira Dalhat ta fada
masa ya yanuna rashin damuwarsa sbd cewa ma yayi yanada uziri bazai samu damar zuwa
ba sai da Ummi tayi masa tatas sannan ta kashe wayarta Dalhat fushi yake da ita
haryanzu bai huce ba
A kwance suka sameta tana bacci office din likita suka tafi suna zuwa saiga Dalhat
shima a tare suka shiga
Sun gaisa da likita sannan ya fara musu bayani kamar haka:bincike ya nuna tana
dauke da ciki wata uku da sati biyu dukan da akayi mata shine ya kara mata ciwon
jiki Allah ya tsare bai tabi cikin dake jikinta ba ammah gsky ya kamata a kiyaye
nan dai ya basu shawarwari ya rubuta musu maganin daya kamata
Ummi ce tace toh don Allah doctor a binciken da kayi bai nuna maka tana shan wani
magani ba
Godiya sukayi masa dakin da Hudah take suka shiga Abbu kuwa tafiya yayi
Ummi da Dalhat kuwa mamaki ne ya cikasu Jiddah tace Ummi meyake damunta tun daxu
bacci take haryanzu bata tashi ba
Ummi tace kada ki damu zazzabi ne kawai insha Allah zata samu sauki
Daga nan ta fita a dakin wayar hajiya ta kira ta fada mata wannan abin mamakin
Abin ya bata mamaki lallai akwai alamun tambaya koma dai menene in sun dawo gida
dole zaayi bincike daga nan sukai sallama.....
🌱🌱🌱🌱
Muffy
🌱🌱🌱🌱
[3/11, 9:30 AM] Naja: 😰😰😰😰😰
AUREN DOLE
😰😰😰😰😰
Book 2
Page 91 - 95
Mufeedamuazuu.blogspot.com
STORY
And
WRITTEN
BY
*Mufeeda Muazu*
Jiddah tace yar uwa meya faru kike ta nemana haka Hudah ta numfasa ta fada mata duk
abinda ya faru yau tsakaninta da Dalhat Jiddah tayi shewa tace dama ai na fada miki
yaya Dalhat yana sonki kinki sakin jikinki da shine shiyasa ya kasa fada miki Hudah
tace uhmm ni ba wannan ba yanzu meye shawara Jiddah tace shawara daya ce ki bada
kai kawai bori ya hau Hudah tace haba ya zaayi kice haka bayan irin wahalar daya
bani gsky nima sai na rama sannan kuma inja ajina
Jiddah tace nidai na baki shawara ta gsky kyaje garin jan aji yaje ya tsinke
Hudah taja dogon numfashi tace naji zanyi shawara ni zan tafi sai nashigo anjima
Jiddah tace ba sai kin shigo ba ki zauna Kusha soyayyarku Hudah ta harareta tace
kyaji da shi ta bude kofa ita kuma Rufaida tazo kenan zata shigo bangajeta tayi
zata wuce Hudah ta janyota tace wai ke wace irin karya ce ance ba ayi kin nace
murmushin mugunta Rufaida tayi tace kin kusa barin gidan don dama yaya Dalhat ba
saan aurenki bane nice na dace dashi bake ba tsaki Hudah tayi ta wuce abinta
Dalhat yana fita gidansu Hudah ya shiga ya gaishe dasu hajiya sun dan taba hira
kadan ya dawo gida ya tarar da side din a rufe baiji mamaki ba don yasan tunda ya
hana Jiddah zuwa ita sai taje mamakin kawancen su yake jininsu ya hadu sosai basa
boyewa juna sirrinsu
A bude ta tarar da kofan tana shiga ta tarar dashi zaune a falo yana latse2 a
wayarsa wuce shi tayi zata shiga daki Kiran sunanta ya kira bata amsa ba tsayawa
tayi inda take yace ina kikaje ba izini banza tayi dashi saida ya sake maimaitawa
sannan tace wurin Jiddah na shiga tunda kai ka hanata ta shigo wurina sbd wani
tunani irin naka tana gama fadin haka ta shige daki abinta
Ajiyar zuciya yayi tunanin yanda zai shawo kanta yake don gsky Allah ya jarrabeshi
da sonta gashi ita kuma bata sonsa abinda bai saniba shine itama tana shiga daki
tunaninsa ne fal a cikin ranta sai dai gsky tana kokonton son da ya fada mata
yanayi mata don haka bazata yi saurin amincewa shiba koma zata amince masa to gsky
ba yanzu ba sai taja ajinta yadda ya kamata
Abinda basu sani ba shine Rufaida na biye da Hudah a baya saida ta tabbatar da
babu kowa a falon sannan ta shiga ta boye bayan labule Dalhat yana shiga daki alola
ya yo don an fara Kiran sallar magriba tunda ya tafi masallaci bai dawo ba saida
akayi sallar issha
Sanda ya dawo a falo ya tarar da ita tana sallah wuri ya samu ya zauna har sai da
ta idar tayi addua suka shafa a tare kallonta yayi cike da kulawa yace baby ki
shirya mu dan fita cikin jindadi tace toh tare da nade abin sallar daki ta shiga
cikin yan mintoci ta fito sanye da zumbulelen hijabinta sai kamshi take zubawa yaji
dadin shigar da tayi
Murmushi yayi yace kinyi kyau taji dadi a ranta amma batace komi a tare suka fita
saida sukayi nisa sannan ta kalleshi tace yaya ina zamuje dan kallonta yayi kadan
sannan ya maida hankali ga tukinsa yace kisa ido zaki gani ba wanda ya kara magana
cikinsu har yayi parking a gaban wani katon mall fita yayi yaga bata fito ba ta
window ya leko yace madam ki fito mana ba musu ta fito yace muje ki zabi abinda
kikeso siyayya sukayi sosai kananan kaya kuwa shiya zabar mata da kansa
Daga nan restaurant sukaje a can sukaci abinci sannan suka Kama hanyar gida
zuciyarta cike da farin ciki dama tana son fita irin haka
Rufaida najin dawowar su tayi sauri ta koma bayan labule Dalhat ne ya shigo da
kayan da suka siyo dakinsa ya wuce da shi itama daki ta shiga don yin shirin bacci
Rufaida na ganin haka tayi sauri ta dauko ruwa da kofi ta tsiyaya ruwan a kofi ta
aje tabs din FP a gefe tayi sauri ta fita a side din a kofar kitchen suka ci karo
da Jiddah bata ce mata komi ba ta wuce zuciyarta cike da farin ciki
Fitan ta ba dadewa Dalhat ya fito daga daki kaman ance ya kalli gurin hango magani
yayi a center table zuwa gurin yayi ya dauki maganin iri daya dana rannan ransa
yayi matukar baci Wato har yanzu bata daina sha ba kenan sai tayi kamar ta bari
kiranta ya farayi bataji ba sbd ta fara bacci saida ya kira sau 3 sannan taji da
sauri ta sauko daga gado ta fito tana mitsike ido almamun mai bacci yana yin data
ganshi ya bata tsoro tace lpy meya faru
Bata ankara ba sai jin Mari tayi dafe gurin tayi tana hawaye magana ya fara da
kakkausar murya yace wato kin maidani banza kike tambayata abinda ya faru nuna mata
maganin yayi yace Allah ya Kama ki kin dauko ruwanki zaki sha sai kika manta kuka
take sosai tace Allah bani na ajeba ban san dashiba wani magigicin tsawa ya daka
mata yace yi mun shiru daga ni sai ke a gidan nan kada ki raina mun hankali......
🌱🌱🌱🌱
Muffy
🌱🌱🌱🌱
[3/11, 9:34 AM] Naja: 😰😰😰😰😰
AUREN DOLE
😰😰😰😰😰
Book 2
Page 101
Mufeedamuazuu.blogspot.com
STORY
And
WRITTEN
BY
*Mufeeda Muazu*
A hankali Hudah ta fara motsi da idonta tana budesu a hankali har ta bude su gaba
daya Jiddah na ganin ta bude ido ta matso kusa da ita tace sannu ya jikin dai Hudah
bata iya cewa komi ba sai hawaye dake bin fuskarta
Dalhat da Ummi suna waje suka ga Jiddah ta fito a rude Ummi ta tareta tace lpy
Jiddah tace ta farka ta kasa magana sai kuka take shine zanje in kira doctor
Da sauri suka shiga dakin Jiddah kuma taje Kiran doctor Ummi ta zauna kusa da ita
ta riko hannunta tana lallashinta yunkurawa tayi zata tashi Ummi tai sauri ta komar
da ita tace kiyi hakuri kinga ruwa ake kara miki Dalhat na tsaye a gefe yana
kallonta cike da kauna suna hada ido tai sauri ta runtse idonta ta mai jin zafin
abinda yayi mata ya bude baki zaiyi magana kenan sai ga doctor ya shigo Jiddah na
biye dashi a bayanta
Likita ya duddubata sannan yayi mata wasu yan tambayoyi da yadda takeji a jikinta
ta bashi amsa yayi rubuce-rubucensa yaba Dalhat yace yaje pharmacy ya siyo
Jiddah tace sannu yar uwa tare da goge kwallar dake zubo mata tace yawwa ngd
Hudah tace Ummi wai me likita yace ke damuna zazzabin yayi mun sauki yanzu zuciyata
ke tashi ga matsanancin ciwon cikin dake damuna
Ummi tace kiyi hakuri Hudah insha Allah zaki samu sauki yanzu zai kawo miki
magani kinji
Tun daga nan Hudah bata kara cewa komi ba lumshe idonta tayi kamar mai bacci har
Dalhat ya dawo tare da magunguna a hannunsa
Ya mikawa Ummi sannan yace bari yaje ya dawo Ummi tasa Jiddah ta hada tea mai
kauri
Sannan tasa ta kawo mata babban roba ta kuskure baki rungumeta tayi tana bata a
baki da kyar ta iya shan rabin kofi sannan ta sha maganin nan da nan bacci ya
dauketa
Ummi tace jiddah ta kula da ita zataje gida ta dafa musu abinci zata turo Rufaida
Jiddah ta bata rai jin an ambaci sunan Rufaida tace Ummi da kin kyaleta kawai ni
zan iya kula da ita
Ummi tace aa hakan bazai yiwu ba sai na dau Allah ya kara sauki
Tafiyan Ummi ba dadewa Dalhat ya dawo hannunsa rike da leda kayan marmari ya siyo
ajewa yayi akan drawer bude Jiddah ya tambaya ina Ummi tace masa ta tafi gida ta
dawo
Ya kalli Hudah dake kwance idonta a lumshe kamar mai bacci Dalhat yana kula da
ita ba baccin take ba kallon Jiddah yayi yace dan bamu guri
Tayi kamar bataji ba saida ya kara maimaitawa sannan tace yaya ai tana bacci yace
ina ruwanki batace komi ba ta fita
Tana fita yasa ma kofar key ya dawo kusa da ita ya riko hannunta yana murzawa har
lokacin taki bude ido murmushi yayi yace nasan idonki biyu nine dai bakya son gani
sbd laifin dana aikata a gareki ba tare da nayi bincike akai ba ina mai baki hkr
akan abinda ya faru don Allah kada kiga laifina idona ne ya rufe kiyi hkr kinji ita
dai jinsa kawai take bata gane inda maganarta ya dosa ba
Hawayene ke zuba a idanunta ba tsayawa goge mata yakeyi yace Hudah bakice komi ba
don Allah ki bude idonki kiyi mun magana kona samu sassauci a cikin zuciyata nan ma
shiru
Sakin hannunta yayi tare da mikewa yace shikenan tunda bazakiyi hakuri ki yafe mun
laifukana ba shikenan bkm ammah ina rokon alfarma a gurinki don Allah ki kula da
kanki da kuma cikin dake jikinki jin ya ambaci tanada ciki tayi sauri ta bude ido
tayi farin ciki da Allah ya fitar da ita da zargi a daya bangaren kuma tana tunani
bazata iya barin cikin ba sbd ta gaji da wannan auren na yaya Dalhat
Kusa da ita ya dawo ya zauna yace banga kina farin ciki ba hararasa tayi ta
kalleshi ido cikin ido tace bana farin ciki kuma ka daina wani rawar kafa don sai
na zubar da cikin nan na fada maka bana sonka bana kaunarka ni ka kyaleni inyi
rayuwata cikin farin ciki ka bani takardata ni bazan koma gidanka ba
Maganganunta sunyi masa zafi matuka ammah ya danne don ya san yanzu tana cikin
bacin raine kuma ga ciki lallabata zai tayi har Allah yasa ta sauko ta
fahimceshi........
🌱🌱🌱🌱
Muffy
🌱🌱🌱🌱
[3/11, 9:34 AM] Naja: 😰😰😰😰😰
AUREN DOLE
😰😰😰😰😰
Book 2
Page 102
Mufeedamuazuu.blogspot.com
STORY
And
WRITTEN
BY
*Mufeeda Muazu*
Su jiddah ne suka shigo su uku da Husnah da Rufaida ganin Haka yayi sauri ya
fita suna gaishe shi bai tsaya amsawa ba yayi gaba abinsa
Hudah sai kuka take Mara sauti ganin haka ya sanya Rufaida jin dadi a ciki
ranta ita bata San abubuwan da suke faruwa ba da batai farin ciki ba
Husnah da Jidda suka matso kusa da gadon da hudah ke kwance Husnah ta riko hannun
yayarta tana mata sannu tare da share mata hawaye da yake duk ta San abubuwan da
Duke faruwa tanata bata hkr Allah sarki Dan uwa rabin jiki
Rufaida kuwa sai kallon banza take mata ko ya jiki ta kasa ce mata Jiddah tace
Hajiya tace a gaisheki daga kai kawai tayi alamar taji ba wai don bazata iya
amsawa ba aa maganar ce kawai bata so tayi sbd yanda takejin zuciyarta kamar
ta fito ta fashe sbd bakin ciki da damuwa ta san idan harta bude baki to ba Abu
mai dadi zai fito ba
Dalhat tunda ya fita bai dawo yan uwa da abokan arxiki sai zuwa ake ana
gaisheta da yamma da likita yaga jikin nata da sauki sosai ya rubuta musu sallama
Jiddah da Husnah suka har hada kaya suka kai mota Rufaida na zaune tana kallon su
saida suka gama kwashe kayan kaf sannan Jiddah ta kira Dalhat ta sanar masa
likita ya sallamesu da har yace ta tsaya gashinan zuwa sai ce masa tayi gasu
har sun fito bakin asibitin zasu taho gida Dalhat yace to shikenan su hadu a gida
Husnah da Jiddah ne suka taimaka mata sbd jikinta ba karfi sosai Jiddah ta kalli
Rufaida tace idan kinga dama ki fito mu tafi sukai gaba abinsu
Sunxo gate zasu shiga gida Hudah tace Jiddah don Allah danyi parking a nan
Jiddah tace me kuma zakiyi a nan gaskiya bazan tsaya ba baba maigadi yaxo ya bude
gate suna tsayawa ta bude kofa ta fito da sauri ta fito Jiddah na magana tai
banza da ita tana tafiya kamar zata fadi sbd jikinta ba kwari ta bude gate zata
fita shi kuma Dalhat yana dawowa yana ganinta yayi sauri yayi parking motarsa ko
kafin ya zo inada take ta bude gate din gidansu
Biyota yayi da sauri tana ganin ya shi ya shigo ta kara da sauri ta shiga falo
tana shiga ta fada a kujera tana maida numfashi kaman tayi gudu ita bata ma kula
akwai mutum ba Dalhat shima shigowa yayi ta tashi zata shige daki jiri ya debeta ta
koma ta zauna Shahid yace lpy kuwa yaya Dalhat meya faru ba ance tana asibiti
bane
Dalhat yace nima ban sani ba Jidda dai ta kirani tace an sallamesu nima yanzu
dawowata kenan na ganta zata shigo nan
Hudah dai tana kwance tana jinsu Shahid ya dauko wayarsa ya kira Jiddah ya
tambayeta lpy kuwa ta fada masa duk yadda sukayi
Hade rai yayi ya fadawa Dalhat yadda Jiddah ta fada masa Shahid ya daka mata
tsawa yace ke......... tashi kibi mijinki kafin in bata miki rai
Tashi tayi ta zauna tace wlh yaya bazan koma ba saidai a kasheni Hajiya ce ta
fito jin hayaniya
Tambaya tayi meke faruwa Shahid ne yayi mata bayanin abinda ya faru
Hajiya tace Hudah kefa bakida kunya ko tashi kibi mijinki hawayene yake bin
fuskarta zatayi magana amai yazo mata da gudu ta shiga toilet tayi ta wanko
bakinta ta fito jiki ba kwari tana hawaye ta zauna kusa da hajiya tace wayyo
cikina zan mutu
Hajiya tace kiyi hkr bazaki mutu ba kinji hakuri ake kina shan magani zaki samu
sauki
Hudah tace hajiya bacci nakeji alhat yace hajiya ki barta tayi baccin anjima
zanzo mu tafi hararansa tayi sallama yayiwa hajiya tare suka fita da Shahid.....
🌱🌱🌱🌱
Muffy
🌱🌱🌱🌱
[3/11, 9:34 AM] Naja: 😰😰😰😰😰
AUREN DOLE
😰😰😰😰😰
Book 2
Page 103
Mufeedamuazuu.blogspot.com
STORY
And
WRITTEN
BY
*Mufeeda Muazu*
Suna tafiya Hajiya ta taimaka mata ta kaita daki ta kwanta ta lullubeta da bargo
sannan ta rufe mata kofa tana fitowa Alhaji na shigowa tayi masa sannu da zuwa ya
wuce daki saida ya huta sannan tayi masa bayanin abinda ke faruwa Alhaji addua
yayi Allah ya sawwake
Hajiya tace tana daki tana bacci Alhaji yace wani dakin tace dakin Husnah Alhaji
yace don me zatazo nan bayan ga gidanta can kira mun ita hajiya tace tana bacci
Alhaji yace tasota taxo ta wuce gidanta tun wuri wannan ai sakarci ne sai fada
yakeyi Hajiya dai hkr taketa bashi
Alhaji ya rufe idonsa yace wlh sai an tasota ta tafi gidanta hakanan hajiya
taje ta tasota da kyar ta tashi tana goge ido alamar bacci bai isheta ba tace
hajiya don Allah ki kyaleni inyi bacci hajiya tace Alhaji ne yace a kiraki idan
kuma baza kije bane to tashi tayi tana ya mutsa fuska tace ganinan zuwa wai meyasa
akace masa ina gidan nan ne hajiya tace ke dai kika sani tana gama fadar haka
ta fita a dakin
Hajiya na fita Hudah ta shiga toilet ta wanke fuskarta sannan ta fito tana tafiya
a hankali har ta isa falo a kasa kusa da hajiya ta zauna kanta a kasa tace gani
Alhaji yace me kikaxo yi gidan nan bakinta na rawa tace banida lpy ne shine nazo
idan naji sauki sai in koma
Alhaji yace to baki isa ba da izin wa Hudah tayi shiru yace to maxa ki tashi ki
dauko mayafinki ki koma gidan mijinki turo baki tayi tace Alhaji don Allah kayi
hakuri inci abinci idan anyi sallar issha sai in koma alhaji yace idan an gama
abinci zaa kawo miki tana kuka ta tashi dama anan falo aje gyalenta ta dauka
zata tafi hajiya ta tsayar da ita ta kira Husnah tace ta rakata tare da Husnah
suka tafi
Suna fita Alhaji yace wa hajiya kada kiga nayiwa Hudah haka ki dauka ko bana
sonta ne aa ko daya ba haka bane ina sonta sosai inayi mata hakene sbd ta
rungumi kaddara ta gane cewa ba komai bane mutum ke nema ya samu ba
Hajiya tace hakane na fahimceka Allah dai ya basu zaman lpy Alhaji ya Amsa da
Ameen
Suna fita Hudah tacewa Husnah kinga ni ko su Alhaji basa sona kina ganin
yadda ya koreni bayan kuma banida lpy
Husnah tace ba haka bane Aunty suna sonki kuma suna matukar kaunarki so suke suga
kin saki jiki da mijinki kun zauna lpy
Suna tafe a hankali suna hira gunin ban shaawa har suka shiga gidan a falo suka
tarar da Dalhat yana zaune yana kallo Hudah na ganinshi tai tsaki ta shige
dakinta Husnah ce ta gaisheshi itama tabi bayan yayarta
Murmushi Dalhat yayi ya cigaba da kallonsa amma acikin zuciyarsa tunanin Hudah ne
kawai yana mamakin irin sonda yake mata gashi tana so ta bashi wahala yana cikin
tunanin ne yaji kiran sallah ya tafi masallaci
Side dinsu Jiddah kuwa Ummi ce take ta aikin girki tana dafa abincin marmari sbd
Hudah
Saida ta gama hada abincin ta kira Jiddah tace taje ta kaiwa Hudah
Koda ta shiga bataga kowa a falon ba sai ta aje basket din abincin a falo ta shiga
daki a kwance ta tarar da Hudah Husnah kuma zaune a gefenta suna hira kadan kadan
don baa cikakken minti 10 zataji amai yazo mata
Jiddah ta gaisheta da jiki sannan ta shaida mata ga abinci nan ta Kawo mata tazo
taga in akwai wanda zata iya ci
Hudah tace Jiddah bazan iya cin komiba bakina ba tests kuma cikina ciwo yake
Jiddah tace hakuri zakiyi kici saiki sha magani insha Allah zaki samu sauki
Hudah tace uhmm nida samun lpy kuma sai nan da wata tara Jiddah tace
[3/11, 9:34 AM] Naja: 😰😰😰😰😰
AUREN DOLE
😰😰😰😰😰
Book 2
Page 104
🌐🔰 HAJOW 🌐
mufeedamuazuu.blogspot.-com
*Mufeeda Muazu*
Jiddah tace bangane me kike nufi ba Hudah tace duk abinda ake baki sani ba to
wai ina dauke da ciki wata 2 ne ko uku ni nama manta cikin farin ciki Jiddah
tace wai ne ma wannan ai abin farin ciki ne kuma kinga ai kin fita daga
zargin dasu Abbah suke miki
Hudah tace hakane ammah ni gsky bani son wannan cikin zubarwa zanyi ni bazan
iya da wahala ba Jiddah ta bata rai tace nagane abin naki iya tsiya ne wlh gara
ki kama kanki tun wuri kada garin kallon ruwa kwado yai miki kafa wata tazo ta
kwace miki miji kina ji kina gani sai yafi karfinki kuma kin san babu saki a
tsakaninku gara kiyi hkr ku zauna lpy nidai shawara nike Baki
Hudah tace naji kuma ngd tayi murmushi tace me kika Kawo mun Jiddah tace uhmm
nima ban sani ba Ummi ce tace in kawo miki nifa naji mamaki Ashe tana tattalin
jikanta ne kafin yazo Hudah dai murmushi kawai tayi don ta san idan ta biye mata
zataita tsoka nanta ne
Ta bude kula taga tuwon shinkafa ne miyar agushi sai dayan kulan kuma dan-wake ne
yaji mai da yaji da sauran kayan hadi
Plate ta dauko ta zuba dan-waken ta zuba yaji mai yawwa sosai Jiddah irin wannan
yaji haka kadafa yayiwa danmu illah Hudah ta harareta
Husnah dai na gefe tana kallon su Hudah ta manta Ashe Husnah tana dakin sai zuba
takeyi
Hudah ta juya ta kalleta tace wlh saura inji wannan maganar wlh ranki sai ya
baci
Dakin yayi shiru kowa yayi shiru sai Hudah dake ta cin dan-wake Dalhat ya shigo
da murmushi dauke a fuskarsa yace hira kukeyi haka Hudah hararansa tayi ta cigaba
da cin dan-wakenta bai damu ba don ya san neman rigima take Jiddah da Husnah suka
tashi zasu tafi Hudah ta bata rai tace bana son munafunci daga ya shigo sai ku
wani tashi tsaya sukayi suna kallonta
Dalhat yace kuje abinku kunji saida safe sallama sukayi mata suka tafi kusa da
ita yazo ya zauna bata kula shi ba ta cigaba da cin abincinta
Hannunsa yasa a cikin plate din ta bige hannun tace malam meye haka wannan
abincin ba naka bane ga tuwo nan a kula
Murmushi yayi yace dama nasan ba nawa bane irin wannan yaji haka ai da gani
kasan na masu ciki ne bata rai tayi ta dauki plate dinta ta bar masa dakin ta
koma falo .
Shima fitowa falon yayi ya zauna a kujeran da yake fuskantarta yace Hudah sarkin
fushi daga magana sai ki taso ki barni to Allah ya baki hkr don Allah kiyi hkr
akan abinda ya faru.
Ko kallonsa batayi ba balle yasa ran zata tanka shi tashi yayi ya matso kusa da
ita ya saka gwiyoyinsa a kasa yana cigaba da bata hkr sai da yayi kaman zaiyi
kuka sannan tace shikenan na hkr komi ya wuce
Cikin farin ciki ya tashi ya rungumeta yace ngd sosai Allah ya barmu tare
Sakinta yayi ya kalli fuskarta yace don Allah kice kina sona wlh ina matukar
qaunarki murmushi tayi ta mike tsaye ta nufi hanyar dakinta saida ta kai kofa
sannan ta juyo ta kalleshi shima ita yake kallo tace *I LUV U TOO Yaya DALHAT*
tana fadar haka tayi sauri ta shige daki sbd kunya
Dalhat kuwa yana zaune ya kasa motsawa sbd farin cikin daya mamaye shi shi abin
har mamaki yake bashi Ashe Hudah zata so shi yana cikin wannan tunanin ne Husnah
tayi sallama ta shigo hannunta dauke da kula
Dalhat ya taso ya amshi kulan tace hajiya tace a kawo ma Hudah bude kulan yayi
yace amarya ma aka Kawo mana kunya ya kamata tayi sauri ta juya dambu ne sai
kamshi yake
Dakin Hudah ya shiga da kulan a hannunsa tana ganinsa ta koma gado taja bargonta
ta rufe fuskarta wai tana jin kunya....... ...
🌱🌱🌱🌱
Muffy
🌱🌱🌱🌱
[3/11, 9:34 AM] Naja: 😰😰😰😰😰
AUREN DOLE
😰😰😰😰😰
Book 2
Page 105
🌐🔰 HAJOW 🌐
mufeedamuazuu.blogspot.-com
*Mufeeda Muazu*
Bismillahir rahmanir rahim
Kusa da ita ya karisa ya yaye mayafin data rufe fuska,hannunta tasa ta dada rufe
fuska rike hannun yayi rufe ido tayi ta kasa kallonsa murmushi yayi yace ikon
Allah yau kuma ni akejin kunya fuskarta dauke da murmushi tace nidai ka kyaleni
tayi maganar ne cikin shagwaba shi kuma sai abin ya burgeshi kwaikwayonta yayi
yace ni gsky bazan tafi ba sai an bude mun wannan kyakkyawan idon naki mai kama
da zinare
Dariya ma ya bata hakanne yasa ta bude idonta kallon juna suke cikin so da kauna
ita ta fara kawar da idonta
Sannan tace yaya meka Kawo mun ne a kula Dalhat yace aike yar gatace dambune
Hajiya ta aiko miki dashi
Bata rai tayi tace saida na koshi sannan zaa Kawo mun yamutsa fuska tayi ta janyo
kulan ta bude kamshine ya cika mata hancj nan da nan taji amai yazo mata da sauri
ta shige toilet sai kwarara amai take duk ta galabaita da kyar ta fito tana
tangadi kamar zata fadi Dalhat yayi sauri ya tare ya rungumeta yayi a jikinsa
dada shigewa tayi kamshin turarensa yayi mata dadi sosai Dalhat sai sannu yake
jero mata tun tana iya amsawa har ta gaji tambayarta yayi ko tasha maganinta na
dare girgiza masa kai tayi alamar aa
Kwantar da ita yayi ya tashi ya dauko maganin tare da ruwa kusa da ita ya dawo ya
zauna ya tallabota ya bude magungunan ya bata da kyar Tasha tana yamutsa fuska yana
gama bata ya kwantar da ita ya rufeta da bargo sannan ya fita yaje ya rufe kofa
daga nan dakinsa ya koma yayi wanka sannan yayi shirin kwanciya dakin Hudah ya
koma
Koda ya shiga ya tarar tayi bacci gefenta ya kwanta ya janyota jikinsa dada
shigewa tayi sai baccinta take cikin kwanciyar hankali Dalhat kuwa fadawa yayi
cikin kogin tunani yadda sukayi zaman doya da manja ammah wai yanzu sune a haka
cikin soyayyar juna tana sonsa shima yana sonta ajiyar zuciya yayi lallai dole
yayiwa Allah godiya kuma yayiwa iyayensu godiya da suka zaba masa mata tagari mai
hakuri
Da yaso ya cuci kansa saboda wani shirme dada rungumeta yayi tare da manna mata
kiss a goshi yace I really luv u Hudah
A zaune tayi sallah tana addua ya shigo kusa da ita yaje ya zauna harta gama
addu'ointa a tare suka shafa kallonsa tayi a kunyace tace INA kwana yaya amsawa
yayi cikin jin dadi sannan ya tambayeta mezata ci shiru tayi nadan lokaci sannan
yace dan-Wake
Dalhat yace ba jiya kika ci ba kamar zatayi kuka tace ni shi kawai nike so inci
bana shaawar komi in bashiba
Dalhat yace yi hkr ranki ya dade bani minti kadan tashi yayi ya tafi kitchen
Book 2
Page 106
🌐🔰 HAJOW 🌐
mufeedamuazuu.blogspot.-com
*Mufeeda Muazu*
Yayi mata dan-waken sannan ya dafa ruwan zafi ya zuba a flask har daki ya Kawo
mata ya zuba mata a plate sannan ya zuba nasa ya hada tea
Tana kaiwa bakinta tayi sauri ta fito dashi kallonta yayi cikin kulawa yace
lafiya?
Kaman xatayi kuka tace ni ba irin wannan Nike so ba irin na Ummi nikeso Dalhat
yace wani iri ne na Ummi ai duk da fulawa ne itama dashi tayi
Kuka ta fara yi masa tana cewa Allah ba iri daya bane rigima take tayi masa duk ya
rasa yadda zaiyi da ita tashi tayi zata fita tambayarta yayi ina zata turo baki
tayi tace wurin Ummi zani
Dalhat yace haba Hudah kiyi hkr kici wannan din mana duk iri daya ne kallonsa
tayi tace gaskiya bazan ci ba
Idan bazakaje ka samo mun ba ni zanje da kaina shiru yayi na dan lokaci shi
gaskiya yanajin kunya yaje wurin Ummi yace tayiwa Hudah dan-wake ganin ya tsaya
shi bai barta taje ba shi kuma bai tafi ba
Kuka ta saka masa hakuri ya bata yace bari yaje ya samo mata fita yayi gidan gaba
daya restaurant yaje ya siyo mata dan waken yana dawowa kitchen ya shiga ya zuba
dan-waken a kula sannan ya kai mata tana kaiwa baki ta tofar tace wlh wannan ba
Ummi tayi ba tashi tayi ta koma gado ta kwanta tana kuka kusa da ita yaje ya zauna
yana lallashinta ammah ina fir taki yin shiru
Ganin ba sarki sai Allah yasa yasa ya tashi ya shiga side dinsu Ummi a kitchen ya
sameta tana hada breakfast dukawa yayi ya gaisheta yana sosa keya Ummi ta
fahimci akwai magana a bakinsa tambayarsa tayi lpy
Cikin jin kunya yace dama Hudah ce sai kuma yayi shiru Ummi tace mai ya samu
Hudah
Dukar da kai yayi yace wai dan-wake takeso irin na jiya murmushi tayi tace dama
shine ka kasa fada yanzu zanyi mata insha Allah Jiddah zata Kawo mata
Dalhat ya yiwa Ummi godiya sannan ya tambaya ko Abbu ya tashi Ummi tace bai tashi
ba side dinsu ya koma a falo ya tarar da ita gidan tsaf sai kamshi yakeyi ta
gyara ko ina tayi wanka tana kwance a doguwar kujera zuwa yayi ya dago kanta ya
zauna ya kwantar da ita a cinyarsa sai kamshi take zubawa
Dalhat yace yan mata ansha kyau sai kamshi kike zubawa murmushi kawai tayi tace
uhmm waye yan matan bayan saura kwana kadan ta zama mummy
Dalhat yace ni kullum yan mata kike a wurina Hudah tace gara da kace a wurinka
don nasan yanxu da yawan mutane a tsohuwa suke kallona rufe bakinta yayi yace kul
kada ki kara fadan irin wannan maganar a gabana idan ba kina so muyi fada bane
Hannunsa ya kai cikinta yana shafawa yace bari inji lafiyar baby nah cire
hannunsa tayi tace ni don Allah kabari wannan ai rashin kunya ne
Dalhat yace wani irin rashin kunya kuma bayan matatace ke kuma cikina kike dauke
dashi..........
.
Masoyana ina mai baku hkr na rashin jina da kukayi kwana2 ngd sosai da
kulawarku
Book 2
Page 107
🌐🔰 HAJOW 🌐
mufeedamuazuu.blogspot.-com
*Mufeeda Muazu*
Rufe idonta tayi don ita kunya takeji Dalhat yace ni kike jin kunya lallai ashe
zaki wahala gara ma tun farko ki cire wannan kunyar don yanzu ne zamu fara cin
amarcin mu nasan su hajiya sun fada miki zaman aure babu kunya a ciki
Hudah tace ni ba wannan ba ina dan wakena? Dalhat yace Jiddah zata kawo suna
cikin maganar saiga Jiddah ta shigo hannunta rike da basket ganinsu haka yasa tayi
sauri ta aje basket din zata juya Dalhat yace kinzo kin aje abu bako magana
dukar da kanta tayi tace Ummi tace in dawo yanzu ne shiyasa Hudah kuwa duk
kunya ya kamata sai kokarin tashi takeyi ammah ya hana Jiddah dai tana tsaye tana
ganin ikon Allah ya tsayar da ita yana rashin kunya a gabanta tafiyarta tayi basu
ma san lokacin da tafi ba suna can suna rikicin su kuka ta fara yi masa shiyasa
ya kyaleta basket din ya janyo tare da dauko plate ya mika mata kusa da ita ya
koma ya zauna amsa yayi zai bata abaki da farko kin amsa tayi sai daga baya
dai taga bazai bari taci da kanta ba sannan ta Amsa haka yai ta bata a baki har
saida ta koshi
Maganinta ya dauko ya bata sannan shima yaje yayi breakfast dinsa yayi wanka koda
ya fito ya tarar ta fara bacci gyara mata kwanciya
Jiddah kuwa tunda ta tafi take mamakin abinda ta gani lallai yaya Dalhat bashida
kunya ammah kuma taji dadi data ga sun fara zaman lpy gaskiya abin ya burgeta
Rufaida kuwa duk ta kasa sukuni bata ji labarin abinda take sonji ba suna zaune
a falo da Ummi Jiddah da Rufaida
Jiddah tace Ummi kin san wani abu? Ummi tace aa Jiddah tace gaskiya yau su
Hudah sun burgeni
Ummi tace da akayi mene? Jiddah tace wlh bakiga yaddah yaya Dalhat yake
tattalinta ba bazaki taba cewa ga yadda aurensu ya kasance ba da abubuwanda suka
faru gsky naji dadi
Ummi tace Alhmdllh haka ake so Allah ya basu zaman lpy tare da zuria dayyiba
Jidda ta amsa da Ameen Rufaida kuwa wani bakin ciki ne ya kamata Jiddah na kula da
hakan hararanta tayi tare da yi mata gwalo Rufaida taji haushi tace Ummi kinga
Jiddah ko wlh ta kiyayeni
Ummi tace Jiddah INA kula dake fah kin rainata ki fita a idona in rufe Jiddah
tace to Ummi ai saita fada miki abinda nayi mata
Ummi tace Rufe mun baki ni ban san meya hadaku ba sam ba kwa taba zama inuwa
daya sai kunyi fada nan dai tayi musu nasiha mai ratsa jiki duk jikinsu yayi
zanyi
Jiddah tace dama itace bata son zaman lpy sbd wani dalili nata Ummi tace to
yanxu dai komi ya wuce kada in kara gani kuma na kula ba kwa magana da Hudah don
Allah ku gyara
Rufaida tace insha Allah komi ya wuce Ummi tace to Allah yayi muku albarka duk
suka amsa da Ameen Jiddah tace kuma akwai abinda nikeso in fada mata tuntuni
Ummi tace wani irin magana ne haka Jiddah tace na farin ciki ne Ummi ammah
tsakaninmu ne jan hannun rufaida tayi tace kinji yar uwata taso muje
Ummi tayi murmushi tace sannu mai yar uwa ina kuma zaku ana hira Jiddah tace
wurin Aunty Hudah zamu Ummi tace to adawo lpy fita sukayi rike da hannun juna
Ummi taji dadin ganin sun shirya side din Hudah suka shiga a kwance tana barci suka
tarar da ita Jiddah taje dai dai kunnenta tana yafi firgigit ta tashi shagwabe
fuska tayi kaman zatai kuka Jiddah tace ke dallah malama bashi bane da zaki
shagwaba
Hararanta tayi tace bana son gulma Jiddah tace mai ciki Hudah tace wlh ki fita
idona in rufe nifa Auntynki ce Jiddah tace nima haka ai kinga duk sai mu
girmama junan mu
Rufaida tana zaune tayi shiru tana kallonsu zuciyarta cike da tsoro da fargaban
abinda zata fada don a zahirin gaskiya tana son ta nemi afuwar Hudah akan abinda
tayi mata ammah kuma gsky tana jin tsoro
Hudah kuwa tun shigowarsu ta kalleta ta dauke kanta Jiddah tace baku gaisa da
Rufaida ba Hudah tace wacece kuma haka Jiddah tace meye haka kuma bana son
wulakanci
Rufaida tace don Allah kiyi hakuri da duk abinda ya faru ki yafe mun laifukan da
nayi miki Hudah ta bata rai tace ni bakiyi mun komi ba idan ma kinyi keda Allah
Jin haka yasa Jiddah tace haba Hudah kiyi hkr ki yafe mata Allah ma daya
haliccemu munayi masa laifi ya yafe mana balle mu yan Adam.....
Muffy👌🏼
[3/11, 9:38 AM] Naja: 😰😰😰😰😰
AUREN DOLE
😰😰😰😰😰
Book 2
Page 109
🌐🔰 HAJOW 🌐
mufeedamuazu.blogspot.com
*Mufeeda Muazu*
Shiru yayi na dan lokaci kafin yace shikenan kije ammah kada kiyi magriba da sauri
tace to tare da bude kofa zata fita riko hannunta yayi ta dawo ta zauna yace ba
muyi sallama ba zaki tafi kanta a kasa tace wani sallama kuma bayan Wanda
mukayi kissing din hannunta yayi sannan yace sauran ice-cream dinki fah sai da ta
fita a motar ta leko ta windo tace ka aje mun a freezer don Allah kada ka sha
mun kai kawai ya gyada mata gate din gidansu ta bude ta Shiga sai da yaga
shigewarta sannan yayi horn aka bude masa gate ya shige
Shahid ya tambayeta fatan dai lpy don naga jiya a gidannan kika yini yau kuma kin
dawo Hudah tayi murmushi tace lpy klu yaya,Shahid yace to Allah yasa tashi tayi ta
barshi a wurin cike da mamakin canxawarta lokaci guda falon Alhaji ta shiga da
sallamarta cikin nutsuwa ta shiga kusa da hajiya taje ta zauna gaishesu tayi
cikin girmamawa Alhaji yace ince dai ko lpy murmushi tayi sannan tace lpy klu
dama nazo ne in gaisheku kuma in nemi gafararku akan duk abubuwan da suka faru
don Allah kuyi hkr ku yafe mun insha Allah bazaku kara jin wani matsala daga
gareni ba zamu zauna lpy kuma ngd da zabin da kukayi mun hakika da naso in tafka
babban kuskure na bijirewa umurnin ku sai Allah ya soni ya hadani da yan uwa masu
sona kuma masu son suga nabi hanya mai dacewa yanzu nasan duk wanda yabi zabin
iyayensa bazai taba yin nadama ba ko Kadan
Hannun hajiya ta riko duka biyun tana kuka tace don Allah ku yafe mun goge mata
hawaye tayi tana lallashinta tace ki daina kuka mu dama can bamu rike ki da komi
ba kullum addua mukeyi miki da fatan shiriya to Alhmdllh yanzu tunda kin gane
gaskiya Allah yayi miki albarka ya baku zaman lpy Alhaji ma godiya yayiwa Allah
sannan ya sanya mata albarka tare da nasiha mai shiga jiki
Tun daga wannan rana take ganin gata wurin iyayenta da yan uwanta bata da damuwa
ko kadan mijinta kaman ya hadiyeta don kauna tayi kiba tayi haske abinta gashi
cikinta ya fara fitowa wata shida kenan
Ya rage saura kwana biyu bikinsu Jiddah,Hudah itace kirjin biki sai kaiwa da
komowa ake bata gidansu bata gidanta duk ta zama busy ga ciki Dalhat tunda ya dawo
bata side dinsu gashi cikin gida cike yake da mutane kunyar shiga yake wayarta ya
kira yaji tana ringing a kan kujera tsaki yayi ya jefar da wayar ya fito waje
cikin kawayensu ya hangota sai hirar su suke abinsu ko a jikinta bata da damuwa
Sumayya ce ta shigo zata wuce ya kirata yace don Allah ta kira masa Hudah
Sumayya na zuwa wurin tace Maman twins ana kira Hudah tace wane ke kirana nuni
tayi mata Dalhat ta hango a tsaye ya harde hannuwansa yana kallosu tashi tayi zata
tafi Jiddah yace saura kuma ki dade Hudah tace ai dole in dade kema kinsan dole
in kula da mijina
Sumayya tace eh lallai masu miji inace yaushe aka gama guje-gujen baa so muna
dawowa fake muna baki hkr kin tuna ranar da aka kawoki idan kin manta bari in tuna
miki hararanta tayi tace na daiji duk abinda zaki fada sai dai ki fada tana gama
fadar haka tayi gaba abinta....... ,......
Muffy👌🏼
[3/11, 9:38 AM] Naja: 😰😰😰😰😰
AUREN DOLE
😰😰😰😰😰
Book 2
Page 110
🌐🔰 HAJOW 🌐
🌐HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITTER🌐
mufeedamuazu.blogspot.com
*Mufeeda Muazu*
*Ina ba masoyana hakuri na rashin jina kwana 2 ina fatan zaku gafarceni*
Dariya sukayi mata tana tafiya a hankali harta isa gurinsa tana zuwa ya bata fuska
yace kinsan yau zan dawo ammah shine zaki tafi kiyi zamanki kin San zan nemeki
murmushi tayi tare da riko hannunsa tace yi hakuri zo muje binta yake kamar rakumi
da akala har suka isa falonsu ta zaunar dashi kitchen ta shwayam a dauko ruwa da
kofi tsiyaya masa tayi tare da mika masa kin amsa yayi wai sai dai ta bashi a baki
ba yadda zatayi hakanan ta bashi a bakin yana gama sha ta hada masa ruwan wanka
kafin ya fito wanka ta jera masa kayan da zai sa sannan tabar dakin
Wannan karon gidansu ta shiga kowa yaji msmakin ganinta yadda tayi kyau gashi cikin
yayi mata kyau
Aunty Asiya ce ta kirata tace Hudah ina kiyayyar take yanzu nuna mata cikin dake
jikinta tayi kunya ne ya kama Hudah tayi sauri ta fita a dakin
Dalhat koda ya fito daga wanka bai ganta ba sai kayan da ta aje masa a gefen gado
shiryawa yayi ya fita daga gidan bai dawo ba sai bayan sallar isha bai ganta a falo
ba ya shiga bedroom nan ma bata toilet ya bude yaga wayam falo ya dawo yaga an jera
abinci a dining ranshi ya baci ammah ya zaiyi dole ya hakura tunda biki ake kuma
bikin Jidda dole yayi hakuri don tsakanin Hudah da Jiddah sai Allah
Ya gama cin abinci ya koma falo ya zauna yana kallo shiru-shiru har karfe tara bata
dawo ba wayarsa ya ciro zai kirata sai ganin wayar yayi a center table tsaki yayi
wannan wani irin wulakanci ne kwana 2 naya gari tasan yana bukatarta kusa da shi
shine ta tafi tayi zamanta shi yanxu ina zai ganta ta ina zai fara nemanta wayar
Jiddah ya kira har sau uku baa daga ba tashi yayi ya shiga cikin gidan ko zaiga
wani ya aikeshi ya nemo masa ita bai ga wani yaro ba Ummi ne a falon kasa da yan
uwanta gaishe su yayi ya zauna yayi shiru
Ummi ta fahimci akwai magana a bakinshi tambayarsa tayi meya farune Dalhat dukar da
kai yayi yana sosa keya sannan yace Ummi Jiddah nike nema Ummi ta fahimci matarsa
yake tambaya a fakaice murmushi tayi tace inajin suna gidan babanku tunda ta fadi
haka ya san gidansu Hudah take nufi sallama yayi musu ya tafi duk kunya ta kamashi
Gidansu Hudah ya shiga a farfajiyar gidan ya hadu da Jadeed tambayarsa Yayi ina
Hudah take Jadeed ya tabbatar masa suna ciki Dalhat yace ya kira masa ita a corido
ya gansu ita da Sumayya Jadeed ya fada mata sakon mijinta bata rai tayi tace ni
wallahi duk ya takura mun daga dawowarsa bayan na hada masa abinci me kuma yake da
bukata oho masa Sumayya tace ke yake da bukata aje a kula da oga
Tsaki tayi kaman zatayi kuka don ta San jarabar tsiyarsa ne ya tashi ciki suka
shiga ita da Sumayya tayiwa su Hajiya sallama su Jidda sai dariya sukeyi mata duk
ta kule harda kwallarta a compound din gidan ta tarar dashi da Shahid gaishe da
Shahid tayi ta Wuce su tana wucewa Dalhat yayiwa Shahid sallama yabi bayanta
hannunta ya rike yace shine zaki tafi kiyi zamanki ki barni ni daya
Shiru tayi batace komi ba har suka shiga gida rufe kofa yayi hijab kawai ta cire
tayi kwanciyarta a kujera kusa da kafanta yaje ya zauna yana mata tausa duk ta gane
nufinsa banza tayi dashi da yaga shirun yayi yawa ne yace hala dai kin gajine
dagowa tayi Kadan tace kaman ka sani wallahi ji nake kaman anyi min
duka........tashi yayi yace taso muje in gasa miki jikin yadda zakiyi baccinki mai
dadi ba musu ta tashi ta bishi daren ranar dai sun raya shi bisa sunna da safe da
kyar ta iya tashi sbd tsabar gajia
Muffy.....
😰😰😰😰😰
AUREN DOLE
😰😰😰😰😰
Book 2
Page 111
🌐🔰 HAJOW 🌐
mufeedamuazu.blogspot.com
STORY And WRITTEN
BY
*Mufeeda Muazu*
Sai da tayi musu breakfast sannan tace masa zata tafi cikin gida yau zaayi lalle
Dalhat yace mai lallen taxo nan tayi miki babu inda zaki tafi ki barni rokonsa ta
farayi ammah Sam ya shafawa idonsa toka yace bai yadda ta fita ba suna cikin
rigimar ne Sumayya da Jiddah suka shigo yana ganin sun shigo ya tashi ya fita daga
gidan kwallane ya zubo mata sauri tayi ta goge Sumayya tace lpy meyafaru kuna
soyayyar ku abin shaawa kowa mamaki yake Hudah tace wai cewa yayi ko nan da kofa
bai bani izinin in taka ba Jiddah tace kodai kinyi masa wani jiya Hudah tace
wallahi banyi masa komi ba sbd kawai na kai dare sai kace wani wuri naje wai sai
dai mai lallen tazo tayi min anan Jiddah tace shikenan kiyi hakuri ki daina kuka
idan ta gama mana zatazo tayi miki
Ki cigaba da hakuri kin san halin Yaya sai a hankali wani lokacin idan yayi abun
kamar bashi ba share hawayen fuskarta tayi tare da jan dogon numfashi sannan tace
ai dole yayi mun wulakanci dama ba sona yake ba cikin dake jikina kawai yake so
Nine dai da banida zuciya kullum nike manne masa inaso inga farincikinsa Uhmmm
Sumayya tace ba haka bane Kawai kiyi hakuri tunda dai zaa zo ayi miki meye abin
damuwa tashi sukayi sukace dama mun jiki shiru ne shiyasa mukazo mu gani ko lpy sai
anjima ki shirya zatazo tayi miki tana ji tana gani suka tafi daki ta koma ta
kwanta nan da nan bacci mai nauyi ya dauketa bata tashi ba sai wurin karfe daya da
rabi 1:pm sallah ta farayi sannan ta shiga kitchen shayi ta dafa ta soya plantain
ta zuba nata a plate ta zuba masa nasa a kula sannan ta jera a dining table bai
shigo ba sai wurin 2:30pm a falo ya sameta tana kallo tunda ta amsa sallamarsa bata
kara cewa komi ba shima baice mata komi ba ammah yaji dadi a zuciyarsa tabi
umurninsa dining ya nufa ya duba kula plantain ya gani ga kuma flask din ruwan xafi
dariya yayi yasan tayi ne don ta bata masa rai
Zama yayi ya hada tea din ya zuba plantain din a plate sai da ya kusan gamawa
sannan tazo ta zauna a kujeran dake kallon nashi a hankali tace anima za'ayi kamu
zakaje ne kallonta yayi sama da kasa yace kinga nayi miki kama da mai zuwa kamu
girgiza kai tayi tace to nidai zani
Dalhat yace umurni kike bani kome to babu inda zakije da wannan cikin aje a
wahalarmun da yaro kallon mamaki takeyi mass sannan tace don Allah kayi hakuri ta
barni inje kasan fa nice babbar kawa dariya yayi sannan yace babbar kawa yanxu kam
sai dai ta samu wata ke kin riga kinyi nauyi jan kujeran tayi da karfi ta tashi
abinta ta barshi anan.
Wurin karfe 3:10pm mai lalle taxo tayi mata mai kyau kamar itace amaryar lokacin
Dalhat baya gidan har aka gama lallen bai dawo ba don haka ana gamawa ta tashi ta
shiga wanka tana fitowa tasaka ankonta mayafinta da Jakarta ta fito ta rufe side
din da key cikin gida ta shiga inda akewa amare kwalliya itama akai mata Sannan
akayi mata dauri tayi kyau sosai kamar itace amaryar karfe 4:30pm suka tafi wurin
kamu
Book 2
Page 113
🌐🔰 HAJOW 🌐
mufeedamuazu.blogspot.com
*MUFEEDA MUAZU*
Dis page is Dedicated 2 HAYAT BABA ZUBAIRU.Happy birthday wishing u long lyf nd
prosperity🎂🎂🎂🎂🎂
Ana kiran sallar magriba su Jiddah suna shigowa sannan su Ummi suka fita sunyi
mamakin ganin Hudah a dakin tare dasu Ummi Sumayya ce ta tambayeta lafiya muka
ganki anan Hudah tace lpy klu wallahi basu labarin abinda ya faru ta kara da cewa
yanzu shida ganina a side dinmu sai bayan an gama biki Jidda tace kiyi hkr kada
kiyi masa haka tunda dai ya hakura to meya rage kuma
Hudah tace abinda ya rage shine ban son takura ina komawa duk zaibi ya takura min
Jiddah tace nidai banga abin takura ba Hudah tace Alhmdllh ai kema kina kan hanya
gobe ana daureki ai zaki gane Sumayya tace kudai kuka sani ni kunga tafiyata tashi
tayi ta bar dakin Hudah da Jiddah suma suka suka yo alola bayan saisha Ummi ta
shigo a kwance ta tarar da Hudah tambayarta tayi jikin Hudah ta marairaice tace
jiki da sauki
Ummi tace Jiddah taso ki rakata side dinta tunda dai taji sauki Hudah bataso haka
ba ammah ba yadda ta iya dole ta tafi
Asabar :yaune dubban mutane suka shaida auren HAUWA' U ALIYU(JIDDAH) Da Angonta
OTHMAN ABUBAKAR SADIQ(SHAHID) Da RADIYA AHMAD TIJJANI tare da Angonta HAIDAR ALIYU
Da kuma Amarya ASMA'U ABUBAKAR SADIQ (HUSNAH) Tare da Angonta ALIYU HAIDAR AHMAD
An daura aure cikin farin ciki da kwanciyar hankali kowa ka gani zaka San cewa yana
cikin farinciki musamman amare da Angwayen nima Mufeeda cewa nayi Allah ya bada
zaman lafiya Ameen
Yamma yayi anata shirin kai amare gidansu saida aka kaisu wurin iyaye akai musu
fada Jiddah aka fara kaiwa gidanta dake G.R.A sannan Husnah kuma gidanta na Bello
Khaliel sai Radiya da aka kawota gida kafin a wuce da ita giant a dake Dutsen
Tanshi
Hudah na daki sai kuka take Dalhat ya hanata zuwa gidan Jiddah lallashinta yake
ammah sam taki hakura daya gaji da lallashin yayi kwanciyarsa ya kyaleta tashi tayi
ta koma falo tayi kwanciyarta a kujera can dare ya laluba bai jita ba haske ya
kunna yaga bata nan tashi yayi ya fito a falo ya ganta a kujera tana baccinta da
har zai tasheta kome ya tuna oho sai ya fasa daki ya koma da asuba da zai tafi
masallaci ya tasheta sannan ya wuce yana fita ta tashi tayo alola tayi sallah bai
dawo gidaba sai da gari yayi haske a lokacin duk ta gama aikin da zatayi tayi wanka
ta jera breakfast a dining daki ta shige tana jiransa ya dawo da sallama ya shigo
a ciki ta amsa sallamar sannan ta gaishe shi ba yabo ba fallasa
Kusa da ita yazo ya zauna ya janyota jikinsa tare da amsa gaisuwarta yace madam
gaskiya kinyi kyau sosai kokarin kwacewa take ammah yaki sakinta murmushi yayi yace
Gimbiya baa huce ba kenan ayi hakuri ranki shi dade ayi mun afuwa bazan kara ba
bata san lokacin da tayi murmushi ba tace shikenan ya wuce dariya yayi tare da
shafa cikinta yace Babynah Allah ya saukeki lpy amsawa tayi Ammen................
Muffy😘
[4/9, 9:34 AM] Naja: 😰😰😰😰😰
AUREN DOLE
😰😰😰😰😰
Book 2
Page 114
🌐🔰 HAJOW 🌐
mufeedamuazu.blogspot.com
*MUFEEDA MUAZU*
A kunnensa ta rada masa *I luv u* murmushi yayi sbd jin dadin maganar fuskan
tausayi tayi sannan tace don Allah yaya ina neman izini ne Dalhat yace izinin mene
kanwata Hudah tace dama so nake inje gidajen amare shiru yayi baice komi ba gabanta
ne ya fara faduwa kada dai ya hanata sai can yace shikenan kije ammah kada kiyi
dare bana son kina kaiwa dare a anguwa
Mayafinta ta yafa tare da daukar key din motarta tayi masa bye bye harta kai kofa
yace zaki tafi baki bani breakfast ba Hudah tace lah don Allah kayi hakuri mantawa
nayi ga abincinka can a dining sai na dawo fita tayi da sauri don kada ya kuma
tambayar wani abun shima ya fahimci hakan dariya yayi ya tashi ya tafi dakinsa don
yin wanka Hudah kuwa tana fita motarta gidan Radiya ta fara zuwa bata wani dade ba
ta tafi gidan Husnah ta dade a can anata hira sai bayan sallar azahar wurin 2:30pm
sannan tayi musu sallama da gidan Husnah Sumayya ce ta biyota tare suka tafi gidan
Jiddah
Sumayya sai tsokanar Hudah takeyi a hanya wai Allah yasa yan biyu zata haifa tun
tana kulata harta gaji ta kyaleta a daki suka sameta taci kukanta harta gode Allah
Hudah na zuwa ta maka mata duka a baya da sauri ta tashi ganin Hudah ne yasa ta
koma ta kwanta tana hararanta tace sai yanzu ne kikaga daman zuwa ai da kin sani
bakizo ba Hudah tace ai yanxu ma bata baci ba sai in koma tunda baki bukatar
ganina tashi tayi zata fita Jiddah tayi sauri ta riko hannunta tace haba yar uwa
baki San wasa bane Sumayya tace kyaleta ta tafi mugani
Hudah tace ke kuma waya sakoki ciki zama sukayi a gefen gado Hudah tace kinsan da
yaya na fito kuwa da kyar ya barni kuma yace kada magriba tayi mun a waje Jidda
tace aiko bazai yiwu ba ace bazaki kai dare ba Hudah tace to yaya zanyi abinda
yafi karfina dole sai hakuri Jidda ta dauko wayar ta dialing no Ummi tayi bugu daya
ta dauka bayan sun gaisa Jidda tace Ummi don Allah kice yaya Dalhat ya bar Hudah
sai dare sai yazo su tafi tare Ummi tace eh to bazan ce eh ko aa ba don bai kamata
in shiga hurumin da ba nawa ba kuma idan nayi masa magana zai ga kaman itace ta
fada mun kinga zasu iya samun matsala kuyi hakuri kawai
Sallama sukayi Jidda bata so haka ba hawayene ya gangaro mata a fuska Hudah ta goge
mata tace kiyi hakuri nima ba haka naso ba ammah ba yadda muka iya Jidda tace
shikenan yanxu zumuncin mu zai yanke
Hudah tace ki daina fadan haka xumuncinmu bazai taba yankewa ba har a bada kamar
yadda muka taso mukaga iyayenmu nayi haka muma insha Allah mutuwa ce kawai zata
raba mu Jiddah tace ba gashi ba yanzu yaya yana so ya yanke ba Hudah tace wane
mutum ai bai isa ya yanke mana zumunci ba
Sumayya tace Allah sarki Allah ya bar zumunci dukkansu suka amsa da Ameen daga nan
kuma sai hira ya tsinke
Wurin karfe 6:30pm sukayi shirin tafiya Jiddah kuwa kwalla ne ya cika mata ido
Hudah tace hakuri zakiyi kowa da kika ganshi haka aka tafi aka barshi ina nan zuwa
kada ki damu kinji yar uwa goge mata hawaye tayi rakosu tayi har wurin da sukayi
parking din mota Hudah tace to amarya sai munzo gashi gone kallon Sumayya tayi tace
ko ba haka ba
.
.
Sumayya tace kinji Jiddah kyaleta dadin abin ma baa kaiki kina guduwa ba wai ba
kyaso sai kuma gaki da ciki ina kiyayyar take Hudah bata ce komi ba ta bude mota
tayi shigewarta sannan tace kwaji dashi ke kuma Sumayya idan kin gama shirmen naki
sai ki shigo mutafi sallama sukayi mata suka dauki hanyar gida Jiddah ta koma gida
jikinta a sanyaye.......
Muffy😘
[4/9, 9:34 AM] Naja: 😰😰😰😰😰
AUREN DOLE
😰😰😰😰😰
Book 2
Page 115
🌐🔰 HAJOW 🌐
mufeedamuazu.blogspot.com
*STORY And WRITTEN*
*BY*
*MUFEEDA MUAZU*
Bayan wata uku Hudah ce ta fito da tsohon cikinta tana kiran Dalhat shiru bataji
motsinsa ba dukawa tayi sakamakon matsanancin ciwon mara tana cikin wannan hali
Aunty Mufeeda ta shigo da sauri ta karisa wurinta tana tambayarta meyafaru kasa
magana tayi sai ciki da take nuna mata kamota tayi a hankali suka fito a mota ta
sata sannan ta zaga mazaunin direba ta shiga maigadi ya bude musu gate suka fita
asibitin da take awo ta kaita don haka suna zuwa aka amsheta labour room suka shige
da ita don suna ganinta suka gane haihuwa CE
Aunty Mufeeda fitowa waje tayi tana nema layin Dalhat
Koda Dalhat ya dawo yayi sallama yaji shiru ya duba ko ina bai ganta ba ya tafi
side din Ummi nan ma shiru yaji ba kowa a falo dakin Ummi ya shiga ya tarar tana
bacci wayarsa ne tayi kara Aunty Mufeeda ne karan wayar ne ya tashi Ummi daga bacci
dauka yayi tare da yin sallama daga can Aunty Mufeeda ta amsa sannan suka gaisa
anan ne ta fada masa suna tare da Hudah a hospital tana labour sannan tace masa ya
duba dakinta ya dauko kayan da ta hada na haihuwa
Hankalinsa duk ya tashi ya fadawa Ummi da sauri ya fita Ummi kuwa toilet ta shiga
tayi brush ta wanke idonta zani kawai ta daura ta dauki hijab dinta ta sauko kasa
da sauri lokacin harya fito da mota shiga tayi sai asibiti
Tun safe har yamma bata haihu ba hankalin kowa duk ya tashi Doctor ne ya fito daga
dakin duk yayi xufa yace Dalhat ya biyo shi office Ummi tace lpy kuwa Doctor baice
komi ba Dalhat yabi bayansa
Doctor ne ya fara bayani kamar haka a gaskiya munyi iyaka kokarin mu ammah har
yanxu d only solution kawai shine ayi mata C.S wani takarda ya dauko ya bawa Dalhat
yace yasa hannu
Dalhat yace C.S kuma Doctor? Doctor yace eh don aceto rayuwarta da abinda ke
cikinta Dalhat cikin sanyin jiki ya daura hannu akan takardar kenan sai ga wata
nurse ta shigo da sauri tace Doctor kan dan ya fara fitowa da sauri ya tashi suka
tafi dakin dukkansu dakatar da Dalhat nurse din tayi dawowa yayi sai safa da marwa
yakeyi yakasa zama Ummi sai baki take bashi
Doctor na shiga dakin Da na fitowa kato dashi sak irin babansa dan wani lokaci
kadan nakuda ya dawo sabo wannan karon macece bayan 10mins saiga wanni nakudan
lokaci kadan haifo yarta mace ba dadewa mahaifar ya fito saida suka gama gyarata
tsaf aka gyara jariran sannan wata nurse ta fito hannunta rike da namijin da
fara'arta tazo ta mikawa Ummi babyn sannan tace congratulations Dalhat yace ya
mahaifiyar fa nurse din tace tana lpy ta haifa maka jarirai guda uku
congratulations once again Dalhat bai jira ba yayi sauri ya shiga dakin sbd
tsantsar farin ciki su Ummi suka mara masa baya Doctor dinne ya mika masa hannu
yayi masa murna nurses suka mika masu jariran Dalhat hunnunsa rike da mace daya
yaje kusa da Hudah inda take kwance ya riko hannunta yana jin sonta a ransa bacci
take don anyi mata allurar bacci sbd ta huta nurse tace idan ta tashi likita yace
zaa sallamesu don sun dubata sun tabbatar da lafiyarta kalau
Aunty Mufeeda ta kira Hajiya ta fada mata alokacin Husnah na nan tazo ganin gida da
sauri Hajiya ta dafa ruwan zafi ta juye a flask ta hada kayan shayi ta hada mata a
basket tace tayi sauri ta kai musu cikin lokaci kadan labari ya watsu cikin dangi
Hudah ta haifi yan uku
Dalhat ya karbi yaran yayi musu huduba ammah bai fadawa kowa sunan daya sanya musu
ba.......
Muffy😘
[4/9, 9:34 AM] Naja: 😰😰😰😰😰
AUREN DOLE
😰😰😰😰😰
Book 2
Page 116
🌐🔰 HAJOW 🌐
mufeedamuazu.blogspot.com
*MUFEEDA MUAZU*
Bismillahir rahmanir rahim
After four hours Hudah ta farka Ummice a gefenta sai kuma Dalhat dake tsaye a gaban
gadon Ummi tace sannu Hudah rufe ido tayi sbd kunya Dalhat yace baki tambayi
abinda kika haifa ba shiru tayi batace komi ba daya na hannun Ummi biyun kuma an
kwantar dasu a gadon yara dake kusa da nata Dalhat yace yara uku kika haifa biyu
mata daya namiji Hudah dai shiru tayi batace komi ba
Ummi ta mika mata yaron dake hannunta kin amsa tayi wai tana jin kunya Ummi ta mika
wa Dalhat yaron tace bari in tashi nasan ni kikejin kunya tana fita Dalhat ya dawo
kusa da ita ya daura mata yaron akan cinyarta kurawa yaron ido tayi cikin so da
kauna duka yaran ya dauko mata duk tayi musu addu'a kallonsu tayi tace ammah yaran
nan dakai suke kama fah Dalhat yace aa dake suke kama
Wani suna kasa musu Hudah ta tambaya Dalhat yace wani suna kikeso a saka musu
Hudah tace duk sunan da ka sanya musu nasan bazaka zaba musu suna mara maana ba
Dalhat yayi murmushi tare da shafa kanta yace Masha Allah Allah yayi muku albarka
Ameen ta amsa
Dalhat yace namijin nasa masa Hibban matan kuma Kausar da Wahida murmushi hudah
tayi tace masha Allah.Allah ya raya manasu
Bayan 1hr likita yaxo ya dubata lpynta kalau sannan ya sallamesu tun kafin su dawo
mutane suka fara zuwa barka
Dama sun yake shawarar gidanta zaa barta wata kanwar Hajiya zatazo ta zauna da ita
Dalhat yaji dadin haka don gidanta aka dawo da it a
Sumayya da Jiddah Suna zaune a gefenta Sumayya tace kinga Allah ya amsa adduata ko
harda kari ma Hudah tayi murmushi tace aike zan bawa guda daya inba Jiddah daya
Jiddah tace ai muna so wannan babbar kyautace kinga Sumayya ta samu dan zaman daki
dariya sukayi dukkansu.
Hibban ne ya fara kuka Jiddah ta miko mata shi don ta bashi nono Hudah tace wlh
bazata bashi ba sai dai bashi madara ya cika tsotso dayawa Sumayya tace aiko dole
ki bashi tunda babansa ya riga ya biya abu kamar wasa taki bashi Husnah dake gefe
zaune da laulayin cikinta wata biyu ta mike zata fita Sumayya tace ina zakije ana
zaune ana hira Husnah tace kaina ke ciwo zanje in dan kwanta ne Hudah tace Uhmm
manya Husnah dai batace komi ba tayi tafiyarta gidansu tana shiga ta fadawa Hajiya
duk abinda ke Faruwa baa jima da fitar Husnah na ba saiga Hajiya ta shigo sai fada
take tundaga kofa tana shiga dakin ta amshi Hibban a wurin Jiddah dake kuka tana
lallashinsa ta ajiyewa Hudah a cinyarta tace ta bashi nono da kyar tana hawaye ta
ciro nono ta bashi tana cije baki wai zafi yake mata
Ranar suna Dalhat rago hudu ya yanka da Sa guda daya gida ya cika da mutane sai
murna ake mai jego kuwa sai shiga da fita take cikin kaya na alfarma kayan suna ko
da aka tara baa magana saboda tsadarsu da yawansu anyi suna lpy kowa ya watse bayan
suna da wata uku akayi bikin Sumayya lokacin Jiddah,Husnah da Radiya wata biyar
Bayan shekara biyar Hudah na gani da Dalhat tare da yan ukunsu sun fito daga wata
hadaddiyar mota haduwarta ita ke bayyana tsadarsa duk wanda ya gansu sai yaji sun
burgeshi sun kara kyau da haske wani katon super market suka shiga duk inda suka bi
kowa saiya kallesu sunyi siyayyarsu mai yawa sannan suka fito don komawa gida
Hibban ne yace mummy don Allah akaimu gidan Hajiya kausar tace mudai gidan Ummi
zamu Hudah tace to saiku fadawa Daddy ai Dalhat yace babu inda zakuje ku barmu mu
kadai a gida ba tunda mummy taki ta bamu wasu twins din........
Muffy😘
[4/9, 9:34 AM] Naja: 😰😰😰😰😰
AUREN DOLE
😰😰😰😰😰
Book 2
mufeedamuazu.blogspot.com
*MUFEEDA MUAZU*
*Aishatu Shuibu Adamawa kawar kirki ngd sosai Allah ya bar Zumunci Ameen*
*Jinjina Gareku HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS ALLAH YA KARA BASIRA DA HADIN KAI
AMEEN*
Hararansa tayi cikin wasa tace nine ma zan bawa kaina Dalhat yace bari mu sauke su
Hibban insha Allah yau zan baki baby murmushi kawai tayi Tambari suka nufa gidandu
Hudah suka fara shiga Hajiya da Alhaji duk suna falo a kasa su Dalhat suka zauna
gaishe da iyayen nasu sukayi cikin girmamawa Hibban yana zuwa ya hadu da yaron
Husnah mai sunan Alhaji (Abubakar)ana kiransa da Muhseen sai tsalle-tsalle sukeyi
abinda yakeso kenan Hudah tace Hajiya ina Husnan take Hajiya tace taje asibiti
kinsan ta kusa haihuwa Hudah tace Allah ya raba lpy suka Amsa da Ameen
Hajiya tace Hudah Allah yasa dai ba kwayoyin hana daukan ciki kike sha ba Kunya ne
ya kama Hudah ta dukar da kai tace bana shan komi Hajiya Allah ne bai Kawo ba
Hajiya tace Allah ya kawo masu albarka daga nan sukayi musu sallama nan suka bar
Hibban gidansu Dalhat suka shiga anan suka tarar da Jiddah da Radiya kowa da
yaranta biyu duk mata nan wasa ya kachame dasu kausar dama abinda sukeso kenan
bayan sun gaisa da Ummi ne Hudah ta dawo falo wurinsu Jiddah sai hira sukeyi
Jiddah tace kinga yayanki ya hanani aiki wai sai dai inyi business Hudah tace nima
haka ai ya zamuyi sai hakuri haka dai cigaba da hirarsu har na dan wani lokaci
Dalhat yazo ya dauketa yabar su Wahida Abbu da Ummi sai albarka suke sa musu da
fatan Allah ya shirya musu zuria
Sun koma mansion house dinsu dake G.R.A cike da jin dadin yadda iyayensu suke musu
addua
A falo suka zauna Hudah ta dauko musu lemu mai sanyi da kofuna guda biyu ta zuba
musu kusa da ita Dalhat ya dawo yana bata a baki itama har suka shanye Dalhat ya
kalleta cikin so da kauna yace rabin raina kin san wani abu kuwa girgiza kai tayi
alamar aa murmushi yayi yace duk sanda na kalleki sai inji nutsuwa sai nike ganin
duk duniya ba wanda ya kaini Saar samun mace tagari gaskiya yiwa iyaye biyayya
yanada matukar mahimmanci a wurin Da don a duniya ba wanda yakai iyaye son Dansu
don haka bazasu taba zaba masa abinda zai cutar dashi ba duk Dan da yake so yaji
dadin rayuwar duniya to yabi Allah da manxonsa sannan yayiwa iyayensa biyayya
matukar ba sabon Allah sukace yayi ba koba dadi yayi hakuri a gaba sai yaga ribar
biyayya da hakurin da yayi kinga dai misali akan mu rugumeshi tayi tace hakane
mijina fatana Allah ya barmu tare nima ganin nike a duk duniya ba macen data fini
Saar miji nagari godiya da fatan alkhairi ga iyayenmu Allah ya saka musu da
aljannar fiddausi Dalhat yace Ameen
Daga mata gira yayi yace Madam it's tym fah insha Allah yau kwallona zai shiga raga
dariya tayi ta tashi zata gudu nan suka fara zagaye falo daga karshe yayi nasar
kamata dagata yayi cak tana dariya suka shige daki ni Mufeeda dake gefe na jah musu
kofa nace sai anjima.
*Tammat Bihamdulillah*
*Dukkan godiya ta tabbata ga Allah madaukakin sarki data bani ikon kammala wannan
Littafi na AUREN DOLE lpy*
*Masoyana ako ina kuke a fadin duniya a ina godiya sosai Allah ya bar kauna Nima
ina sonku*
*Ina fatan zaayi amfani da darussan dake cikin wanna littafi Wanda na batawa rai
kuma ya gafarceni kunsan Dan Adam ajizi ne inayiwa kowa fatan alkhairi*
*MUFEEDA MUAZU*😘