100% found this document useful (1 vote)
3K views125 pages

Sanadin Caca Complete Hausa Novel by Hausanovels001

Uploaded by

fabdulhamid260
Copyright
© © All Rights Reserved
Available Formats
Download as TXT, PDF, TXT or read online on Scribd
Download as txt, pdf, or txt
100% found this document useful (1 vote)
3K views125 pages

Sanadin Caca Complete Hausa Novel by Hausanovels001

Uploaded by

fabdulhamid260
Copyright
© © All Rights Reserved
Available Formats
Download as TXT, PDF, TXT or read online on Scribd
Download as txt, pdf, or txt
Download as txt, pdf, or txt
You are on page 1/ 125

*SANADIN CACA*

Mallakar SADI-SAKHNA

PROFICIENT WRITER ASSOCIATION

*USERNAMES*
FACEBOOK PAGE:Sadisakhna
WATTPAD:@SAKHNA03
AREWABOOKS:@sadeesakhna
PHONE NO:09035784150
________________________________
*Book 1*
Chp[01]

........"Goje ka saka mana menene haka wai?"


Uwaisu ya faɗa cike da jumuɗin yanda cacar yauɗin ke shiga masa zuciya.
Dular da take bakinsa ya kawar mai kauri anyi mata naɗin manya,banda tashin hayaƙi
babu abinda yake,ga wata hula zungureriyah a kansa,ta fita daga cikin hayyacinta
saboda bala'in dauɗar da tayi sosai. Gashin bakinsa duguza duguza kamar gazagi.
Cikin shaƙaƙƙiyar murya yafara magana,kana jinsa kaji tantiri ɗiban fari.
"Tsoho shin kana nan akan bakarka zakayi cacah dani,kasan fah ba'a wanyewa
lafiyah,sannan idan nayi nasara ko ranka ne billahillaxi saika bani shi,babu
abinda ya dameni,naga kuma da alama ko ƙwandala baka maganinta a jikinka"
Hantar cikin Uwaisu ta kaɗa da maganar goje,amma kuma ta wani bangaren yanajin
ƙamshin samun nasara,musamman ganin yanda yataralakato asa iri ɗaya a
hannunsa,gashi kuma bugu da ƙari goje yasaka shanunsa dayake kiwo jingina,idan ya
cinye wasannan yana da shanu fah kenan sukutum.
Goce hular kansa yayi gefe ɗaya tareda gyara zama akan buzun buga cacar,mutane maza
da mata ƴan duniya suna zaune kowa na harkar gabansa a wajen.
"Hhhhhh goje kenan ai tunda nake bantaba fara caca na tashi banƙare ba,ko a cini
kona ci bana bata baya,gaba na bata bana tsoro kota mutu kokuma tayi rai,ai ninan
uwaisu ɗan marka,dan caca muke rayuwa,caca da rufamana kuma da yaye mana bargon
asiri,anci mana mutunci kuma an yabemu,a cikinta muka buɗi ido tun kai yana
baƙi,gashi har yayi furfura bamu dainaba,dan haka babu jada baya shiga wasa yaro"
Uwaisu yagama faɗa cikeda gadara da kuma yarda da kai,abokinsa Manga sai kirari
yake masa.
Shafa ƙeya goje yayi tareda rishe ido yana dariyar gefen baki,kana ganinsa kam
kasan yaci dubu sai ceto.
Fara zarar katin yayi yana ajiyewa ɗaya bayan ɗaya har yagama ajiyesu a gaban
uwaisu,babu musu kana kuma babu tada jijiyar wuya,kowa yaga wasan indai ya iya
wasan yasan goje ya cinye wasan.
Fitar da kwarkwaron wiwi ɗin bakinsa yayi kana ya miƙawa uwaisu dafaffafen hannunsa
gabansa.
"Tsoho rai kokuma dukiya,cikin ɗaya dole zaka bada ɗaya yanzunnan bakuma sai anjima
ba,dan haka saika hanzarta"
Rawa jikin uwaisu yafara tamkar an jona masa lantarki,don ko ba'a faɗamasa ba daga
ganin soyayyun idanun goje toh fah bazai taba haƙura ba sam.
Juyawa yayi ya kalli manga dayake gefensa,suna haɗa ido manga ya kalli wani gefen
tamkar bai san Uwaisu na wajen ba.
Bai sare ba dai cikin razananniyar murya ya tambayi Manga.
"Manga yaka juya,domin Allah idan kanaga kuɗi a wajenka ka Taimakamin dashi,zan
baka idan mukaje gida"
"Kai kaji wani zance a wajen Uwaisu inada kuɗinne zaka ganni anan ina hamma kaman
wani ɗan tsuntsu,sanin kanka ne a gabanka dai wancan satin nasaka injinnawa a caca
aka cinyeshi,yanzu bana cass bana ass sai Ladi tagama abincin sana'arta take
zubamin bayan tagama yimin tujara."
Duk maganar da suke goje yana jinsu bai motsaba,kana kuma bai ɗauke hannunsa daga
miƙashi da yayi ba.
In ran uwaisu ana ganinsa toda kuwa ya sau fitsari a lokacin,gaba ɗaya tunaninsa ya
kulle,shin a ina zai samo kuɗi yabawa goje.
"Hehehe tsoho kenan,dan kaga ina maka dariya koh,to aradu da kake gani nan ba
mutuncine dani ba,ko ka bani kuɗina kwatankwacin kuɗin saniyar dana saka,wato dubu
ɗari da hamsin,kokuma na tale ka nan wajen na sutale maka fatar jikinka,kuma banga
ɗan matar da zai iya hanani ba kaf garinnan,in kuma kana ganin wasa nake kada ka
fito da kuɗinnan yanzunnan"
Shuru uwaisu yayi yana muzurai,sai lalleƙawa yake yana rarraba ido ko zaiga wanda
zai kwaceshi a hannun goje,amma babu alamar akwai wanda ya kulada mai suke a wajen.
"Wa kake kallo zatonka akwai mai ƙwatarka a wajennan ne heee,kanama bata lokacinka
ne sannan kuma kai baka san dokar kuɗina ba ma,duk bayan minti uku idan ya ƙara toh
zan ƙara dubu ɗaya akai,dan haka zaka bani kuɗina ko saina cire maka yatsu tukunna"
Yafaɗa yana ciro wata wuƙa ƙugunsa mai kaifi,har wani lashe baki yake kaman maye
yaga nama.
Caraf ya canfki hannun Uwaisu yana shirin cire masa yatsu,wani ihu ya kurma tareda
fara dadare,dama gashi da ƴar kibarsa ba ramamme bane kaman gojen,amma yanda ya
riƙeshi yakasa kwacewa kasan goje bakaramin bushashshen ƙashi ne dashi ba.
"Wayyo wayyo do Allah ka ƙyaleni wlh zan baka kuɗinka amma kada ka ciremin
hannaye,kafadamin bayan kuɗi mai kake so zan baka ka rufamin asiri"
Magana yake yana kururuwa mutane har an fara taruwa,amma kaman kurma yana nan
rikeda hannun uwaisu,har yafara saka masa kaifi a hannun na wuƙa,dan dagaske yake
haiƙan sai ya yanki hanunnan.
Taruwa akayi wasu na jan goje wasu kuma suna jan uwaisu daga hannunsa,banda huci
babu abinda yake yana sake riƙo uwaisu,idanuwansa sun kaɗan sunyi jawur.

Ranar Uwaisu yaga hairazin kam,don yahada gumi shirkif ta ciki.


Cikin shaƙewar murya na mai taurin kai goje ya yunƙura tareda watsar da mutanen
dake riƙe dashi,wawuro uwaisu yayi a karo na biyu tareda cewa.

"Ohh zatonku ina wasane,to duk wanda yafasa rabamun ma ya goya kura ba wando a
cikinku,kuma duk mai son uwarsa da haifi wani kokuma ya kwana da pillown ƙasa bana
matarsa ba to ya sake zuwa zai rabamu da wannan tsohon najadun"
Yana maganarne yana nuna dukkan mutanen wajen ɗaya bayan ɗaya da wuƙar
hannunsa,ɗaya hannun kuma ya riƙe uwaisu camau baya ko motsin kirki,ko ya akayi ma
yasamu wannan masifaffen ƙarfin oho.

"Kaikuma shin zaka bani ƙudina kokuma na karbi ranka yan........."

"Tsaya tsaya na baka ƴa ta Sumaimah a matsayin kuɗinka, dan Allah to ka ƙyaleni"

Shuru goje yayi yana zare ido kaman mai nazari,mutanen wajen sunyi mamaki da kuma
sakarci irinna uwaisu,wanne irin abune zaisa uba ya dauki ƴar sukutum mai lafiya da
kuma hankali yabawa mutum irin goje,hakan ma bata hanyar dadai ba wai fansar kansa
yayi da ita a wajen caca. Saidai kuma ta wani wajen hankalinsu zai kwanta,dan da
alama goje zai ƙyaleshi da ransa.

Bayan yagama nazarin ɗagowa yayi da sauri kaman zaucacce tareda sake kallon
uwaisun,saikuma ya buɗe baki yana jijjiga kai.
"Kai shashasha ka maidani dan kaga ina shaye shaye,a tunaninka ni marar
hankaline,taya ƴarka zata fanshi saniyata buleliya da ita ta kiwatu,ina kaita
kasuwa kuɗi za'a bani,ƴar ka fah uban wa zai siyeta idan na karbeta,ko sadaki da
masu aure ke bayarwa ma dubu ishirinne,saboda ka maidani bunsuru bari ka hadani da
mace koh,na maka kama da wanda yahaɗa hulɗa da mata iyeee"

Wannan karon uwaisu kasa magana yayi,sai mutanen wajenne sukayi ta maza.
"Haba goje ba girmanka bane haka ai,tunda har yace zai auramaka ƴarsa a maimakon
kuɗinka kayi haƙuri mana,ai mutum yafi kuɗi koh,kaga tunda innarka tafara tsufa
basai tana yimuku girki bah?"
Wani a cikin mutanen wajen yafaɗa ta sigar lallashi,da alama kuma hakan yafara
tasiri akan sa,dan yaɗan saki wuyan uwaisun ba kaman ɗazu ba.
"Ehh kuma mutum kace wani abun,dama inna kuwa ƙafafunta suna ciwo,bata gama mana
tuwo da wuri mutum sai yunwa taci ta cinye masa,saita samu mai mana girki,nizan
wuce madakatarmu daga nan,ku wanketa ku kaita gidannamu gobe,idan kuma kasake wata
rigimar tasake haɗamu.....hmmmm feɗeka zanyi na bawa su durwa,tsohon banza
kawai,gobe ma kasake kasadar shiga caca babu kuɗi,idan ita sa'ar wasanka ce,gajaman
kawai"

Haka yagama yiwa Uwaisu tass yashuri wasu takalmin fatarsa yabar wajen yana
bobboƙarewa kaman wani mutumin itace. Sudai kowa na wajen ajiyar zuciya yayi,komai
yasaka Uwaisu ma yin caca da wannan oho,mutumin da sai yayi wata churr a jeji ba'a
ganshi ba idan suka iyo sata ko fashi.
Kowa a wajen masu cewa Allah yakara sunfi yawa,yayinda wasu kuma tausayin Sumaimah
sukeyi,baiwar Allah tana ganin rayuwa ta wani irin uba da Allah yahaɗasu dashi,abin
takaicin dama sauran yaranne aka bawa gojen da sauƙi,amma Sumaimah ya mahaifiyarta
zataji,ita kadai ce kaff cikin yayansa ta fitada zakkah na hankali. Kodan yasan ita
ba uwarta a gidan,in badan haka ba taya zai fara wannan abun.
Bagazan bagazan babu kunya bare nadama Uwaisu ya shuri shima nasa takalman yana
baza uwar riga yayi hanyar gida,lokacin cin abinci yayi,zaije duk wacce takeda
girki tagama yimasa tujara ta zuba masa.

_***_

Leƙawa tayi ganin yamma tayi sosai yasa tafara tattara robobinta na abincinta duk
da kuwa bata siyar ba da sauran, dama hakan yakasance al'adar ta ne,bata yarda koda
wasa tayi dare a wajen siyarda abincin,yau shakararta ɗaya kenan da fara
tallen,tunda akayi auren ƙanwarta Shaheedah itace takeyi yanzu,lokacin da tanaji
tana gani tabar karatunta tafara talle tayi kuka sosai da sosai,saidai kuma shin ya
zatayi ne,idan bataje tallenba wanene zai bata abinci taci a gidan,ammi ce dama
kaff cikin matar mai ɗan dama dama,itace kuma take riƙe da ita,taji daɗi ma da bata
gaji da ita ba ai. Sa'arta ɗaya bata tsangwamarta amma kuma bata sakata a zuciyarta
kaman sauran ƴaƴan nata. Hmmm wannan jinkirin aurennata yana damunta sosai.
A yanda aka san yanayin dai wacce taƙi kama kanta itace bata auruwa,amma ita kuma
anata kaddarar kama kanta da tayi tafita zakkah a cikin gidannasu shine ya hanata
auruwa.
Sallama tayiwa abokan tallennata wanda sukam yanzu ma suka fara siyarda
abincin,dukkan su ƙannen bayanta ne sosai da sosai. Saboda kowa cewa yake ta rako
mata tayi kwantai,amma kuma tasan hakan baya wuce nasaba da tuggun dasu inna lami
ke yimata a gida,kasancewar tafi sauran yaransu kyau da kuma soyuwa a wajen kakarsu
wacce ta rasu waccar shekarar.
Tafiya take da tunani fal a ranta,haka kawai takejin faɗuwar gaba wacce tarasa
dalilin faruwar hakan. Botikin shinkafane akan ta saikuma na miya hannunta
ɗaya,gefen kunkiminta kuma ta saƙale bahon data zuba plate da cokala a ciki.
Tazo daidai saitin anguwarsu taji yara sunayi mata magana,amma kuma yafi kama da
tsokana,tohh ita kuma ba mahaukaciya ba kai yakawo haka,ko duk rashin aurennata da
wuri ne yazamo haka.
Waiwayawa tayi ta kallesu,ba wasu yara bane ƙanana da hankalinsu sarai.
"Yee ga matar goje nan tadawo,ohh kowa yaki aurenta sai goje,shima biyansa kuɗin
cacarsa akayi da ita wooo"
Gabanta ne yayi dummm,wannan karon har yafi wanda takeji ɗazu,duk da bazata ce ta
gaskata maganar tasu ba,amma kuma tasan hakan abune da zai iyah faruwa,tunda ita
kanta tasan halin ubannata,babu wanda bai masa shedar caca ba,hattah kayan ɗakunan
iyayensu duk ya ƙararsu a cacah,sunyi kukan sunyi bakin cikin harsun gaji,babu ma
ya ita Kaman duk abin ya fi damunta.
Cikin sanyin jiki kaman babu laka a jikinta taahiga zauren gidannsu,gidane na iyaye
da kakannu mai ɗauke da ƙofofi da dama,dan su kansu ma sunkusa su talatin yayan
vabannasu,banda ƙannen babanta da kuma ƙannensa da kofofinsu.
A gidannsu akwai tsakar gida mai matsakaicin faɗi,duk anan kowa ke fitowa dashi da
yaransa yayi harkarsa.
Tana shiga gidan da idanuwa barkatai tayi arba dukka sun watso mata shi,kana gani
dai kasan wani abun tabbas yafaru ko kuma yana faruwa.
Sauƙe idanuwanta tayi tai ta maza ta wuce ta gabannsu zuwa ƙofarsu,dan tunda taga
dukkan matan a wajen iya amminta ce bata nan,kuma dama itace mace ɗaya a gidan da
bata shiga harkar mutanen gidan sosai,badan bataso ba saidan hakan ba halinta
bane.tasan duk yanda akayi tana ɗakinta dan haka can ta nufah. Tanajin ƙananan
maganganu a cikin kunnenta daga bakunan ayarin matan wajen,amma tayi saurin toshesu
a cikin kunnenta,dan a halin da takeji batada ƙwarin wannan zuciyar najin abinda
suke faɗa ba yanzu badai tukun ko zataji ma.

Babu kowa a ƙofar tasu,dan haka kai tsaye ta ajiye shirgin hannunta ta nufi
ɗakinnasu.
A durƙushe tasamu durƙushe ta ammin ta kifah kanta akan katifar da ita kaɗai ta
rage a cikin ɗakin.
Ko ba'a faɗawa mutum ba yasan kuka takeyi na takaici da kuma baƙinciki.
Cikin rawar murya da duk wanda yajita yasan saida akayi jarumta wajen furtata
Sumaimah tayi sallama a bakin ɗakin.
Saurin ɗagowa Ammi tayi tareda goge hawayen idanuwanta ta kalli Sumaimah ɗin.
"Ohh har kindawo ne"
Ɗaga mata kai tayi kafin itama ta jefeta da tata tambayar.
"Am...mmi ddd....dagskene baba ya badani ga goje a wajen cacah?"
Shuru ammi tayi tareda runtse idonta,shin taya zata bata wannan zazzafar amsar
tayaya? Saidai kuma hakane dagaskene bazata iya cemata ba haka bane,dukda kuwa
abinda zuciyarta keson faɗa kenan.
Ɗaga mata kai tayi tareda saurin kawar da kanta,dan a yanda takeji duk da ba ita ta
aikatawa Sumaimah hakan ba kunyar haɗa ido da ita takeji, ji take da tanada iko to
zatayi koma menene wajen ganin hakan bata faru ba,saidai wacece ita,tayi magana a
goranta mata kan cewar ƴar tace,kawai dan ta reneta.
Shuru Sumaimah tayi itama tana nata tunanin.
Wani abin ma Ita data kame kanta daga dukkan munanan ɗabi'u,yanda dan iska bazaizo
yace yana sonta ba,to shikuma ɗan kirki koda yana sonta bazaizo ba saboda halayyar
mahaifinta da kuma gidansu da bana mutunci ba. Wannan sai taji ma da kwanda tunda
ta amince da wani sakaran ba wannan dodon da ake shirin ƙulla rayuwarta da tasa ba.

Siraran hawayene suka zubo daga kuncinta,bata taresu ba bata kuma tsaida su
ba,barsu tayi lokacin su ne suyi ta zuba kawai dan in akwai wata ƙofar ma da wani
hawayen zai zubo da ta barshi ya zubo........
"Kiyi haƙuri kawai Sumaimah,hakika banji daɗin abinda ya aikata ba,amma kuma banida
tacewa akan hakan,dan har yanzu ma ni ban ganshi ba bare yamin bayanin abinda ya
aikata,saboda yasan banida matsayin da dole saina sani ne inaga. Kije madafa
abincinki yana can,barina yi sallah.

Kashh akan zamu dagata a sabon littafin na sanadin cacah.... Ya kukaji to kuna so?

Littafi na ɗaya ne dana biyu kaman yanda na sabayi,na ɗaya bati siddan,na biyu kuma
Naira 300 ne dan haka zaka iya biya tun yanzu kafin a shiga kashi na biyu.

3131951977
Auwal Sadiya
First bank

Ko katin mtn ta nan


09035784150

VTU ta nan
2347068390570

Ƴan niger ku tuntubi wanann number.


+227 97 21 16 15
----------------------------------------------------

Sadi-sakhan ceh
09035784150
Share please

*SANADIN CACA*

Mallakar SADI-SAKHNA

PROFICIENT WRITER ASSOCIATION

*USERNAMES*
FACEBOOK PAGE:Sadisakhna
WATTPAD:@SAKHNA03
AREWABOOKS:@sadeesakhna
PHONE NO:09035784150
________________________________
*Book 1*
Chp[02]

Duk da cewar tabi zancen ammin ta tashi ta ɗauko abincin,ta daɗe tana rike dashi
bata ajiye ba ballantana kuma tafara ci.
Haɗa ido sukayi da ammi wacce ta idar da sallah,itama ita take kallo. Maganar bata
wuce ba koda yake sannan aka fara,maganganun da suke yimata yawo akai tafara
fitarwa.
"Ammi amma meyasa baba zaimin haka,yanzu duk abinda yakeyi bai isaba sai ya wargaza
rayuwata,meyasa saini ammi uhm. Kinsan kuwa ma wanene gojen koda yake waye kaf
garinnan bai sanshi ba ma. Ammi kaman mahaukaci fah yake in kika ganshi,wlh ko
lungun danaga yabi bana bi saboda tsoronsa,shine fah ya yankawa Ubaidu kafaɗa suna
faɗan daba,ku.....kuma yanzu ace da wanann zan zauna a matsayin miji?"
Kuka ta rushe dashi tareda gyara zamanta a tsakar ɗakin,ta dade danayi ammi bata
hanata ba,ina takeda ƙwarin gwiwar hanata kuka,itama kanta kukan take toh.

"Ammi wlh kasheni zayyi in kuka kaini wajensa,wayyo nikam tawa ta ƙare wlh dana
sani ba dana amince da Bashir dayazo neman aurena wansan shekarar,duk tsiya gwanda
mai neman mata da mahaukaci wlh,wanda a kowanne lokaci zai iya kasheka"
Hannunta Ammi ta jawo ta rike cikin nata,saida ta tattara nutsuwarta kafin tafara
cewa.
"Kiyi shuru haka Sumaimah,Inshaallah bazai kasheki ba,Allah ma zai kawo rabuwarku
dashi kina zaune,dan kame kanki da kikayi da kuma Addu'arki bazata sauƙa kasi a
banza ba,dan haka ki kwantar da hankalinki kinji."
Suna nan zaune Uwaisu ya shigo ƙofar tareda bankaɗa kyauren ɗakin,rarraba ido
yafarayi akan su kamar marar gaskiya,ganin basu ɗaga ido sun kalleshi ba yasa yace.
"Ke amminki ta faɗamiki mai yake faruwa koh,da gobe zanmiki aure tunda ƙinki kawo
miji,amma yanzu shi yaron innarsa tace a bari sai wani satin,dan haka ki shirya nan
da wani satin zan miki aure"
Cikin ɗaga murya da borin kunya yake maganar,daga ammi har Sumaimah babu wanda ya
tanka masa har yayi ya gama.
Har ya saki labulen sai kuma yaƙara buɗewa.
"Yawwa Ammin yara ni akwai abincinnan ne,ɗazu ina waje naga Sumaimah tashigo da
botikin da sauran abinci bata sayar ba to koh......."
"Babu na yara ne,yau banyi dakai ba"
Tafaɗa a daƙile cikin fushi,duk da Sumaimah ba ƴar ta bace amma abin yabata haushi
sosai,duk abinda akewa Sumaimah a gidan bai wani dameta sosai ba indai ba ƴaƴanta
aka taba ba,amma kuma na yau ya ƙona mata rai,musamman yanda tasan ƙoƙarinta da
kuma son iliminta,yanzu duk yatashi a banza saboda rayuwar daza'a jefata.
Ita kanta Sumaimah abin yaso bata mamaki yanda ammin ta tsaya mata a wanann
karon,kuma hakan yamata daɗi sosai,yau dai kam taji tanada uwa,duk da dama ba
mugunta take mata ba tun tana ƙarama.
"Kaman ya yau babu nawa,wai dan wannan abin daya faru ne,laifina kika gani a
ciki,so kike na barshi ya kasheni bayan inada abin bayarwa,ko kin manta ƴa tace
kuma ikona ce,duk kiwonta danayi tayi a gidan menene amfaninsa in bazata yimin rana
ba uhm"
"Kiwonta,harkana da bakin cewa kai kayi kiwonta ma,to naji ikonka ce bance kuma ba
ikonka bace,in abinda mutum yakeyi daɗine ya cigaba dayi maza,batun abinci kuma
nima ikona ne shi,sannan kuma wanda naga dama zan baiwa ina ko"
Daga yanda yaga take magana yasan ranta ya baci da abinda yayi,tabb inaga kuma ƴar
ta yabayar,yasan ma bai isaba ai,Sumaimah dai itace karkatacciyar kukar tasa mai
daɗin hawa.
Sakin labulen yayi yai waje yana kumbure kumbure kaman wani zaki.
Dama daga masallaci ya nufi cikin gidan,daga nan kuwa majalisarsu kai tsaye ya
wuce.
Sallama yayi zauna a kusada Manga aka fara taɗin duniyah.
"Yadai Baban amarya naga kana tsuka"
"Uhm kaidai bari kawai,Deejah(ammi)ce ta ɗauremin fuska tamau abinci ma ta hanani
yau,wai dan saboda nabada auren Sumaimah"
"Ahhh to ƴarta ce,ba ikonka bace,lamarin babu daɗi amma in sun kula kaima ai ba
yanda zakayi ne,yau jimin mata da kilaroro.....amma dai Uwaisu zata daɗe bakaje
gidan caca ba koh"
Manga ya faɗa dan yaji mai uwaisu zaice..
"Bazanje gidan caca ba? Akan me saboda wannan ƙaramin lamarin da mukayi da
yaro,abinda yafi wannan ma ai yafaru munje ballantana kuma wannan,ai gobe ma banda
ranar kasuwa ce zamuje sana'a da zuwa zanyi,amma ka taimayeni jibi zaka ganni"
Dariya Manga yayi kafin kuma yasake ɗago masa wani taɗin.
"Toh ya maganar kuma kayan ɗaki dazakayiwa ita amaryar,kasan dai baka kaita haka ba
ko"
"Saboda ni wani abun zai bani inna bashi ita komai,ai yanda take haka zata bishi
babu abinda ya dameni,karka manta bazai bada sadaki ba fah kaman ko wanne,wannan
kuɗi daya hau kaina shine sadakinta,kaga kuwa haka zan kaita,dan inba aman kuɗi
zanyi ba to bana maganinsa daka ganni nan,innarsa da kuma ita deeja da take tada
jijiyar wuya suyi ruwa sannan suyi tsaki,babu abinda ya dameni."
Yafada yana kaɗe rigarsa.

___***___

Ɗaga cinyar kazar yayi a hannunsa yana juyawa,Taska ya kalla wanda yake ta aikin
ciro gashashshen naman daga cikin wuta.
"Kai taska a ina kuka samo kaji nan"
"Uhm ogah goje a sansanin wani ɗan fulani ne nan gefe da gari"
"Dama akwai kaji kuka gasa mana zomo jiyah,hadda cemin babu komai cikin garinnan
banda waɗancan karashiyoyin?"

Cikin bacin rai yayi maganar yana hararar taska,wanda yake mazari yana sunne kai.
Al'adarsu ce dama a babbaka wuta a gasa kajin mutane da kuma awaiansu idan sunyi
dare a waje basu koma gida ba,duk garin kowa yasan yaran goje da cinye dabbobin
mutane,gashi babu wanda ya isa cewa kanzil,kaima da ana ci babbaka zasuyi su cinye.
Yaran su samari masu tasowa duk ya maidasu yaransa sai abinda yace,wani abun
takaicin kakai ƙara wajen sarki babu abinda za'ayi,dan in dukane ko ɗauri yanda
kasan ka ɗaure itace haka zaka gani,shikansa sarkin ƴaƴansa uku duk yaransa ne,sai
abinda yace shi zasuyi bana ubannasu ba,idan aka masa horo haka zai hanasu zuwa
gida har tsawon wata guda,matansa haka zasu ɗaga masa hankali dole sai ya janye
abinda yace.
A zaune yake akan wata kujera a tsakar dajin ta fatun awakin mutane,da ba shine
shugaban dawar ba,wani mutum ne mungu baƙiƙƙirin dayazo daga sudan. Gabaɗaya duk ya
takuramusu komai shi sai kansa,goje ko shekara biyar baiyyi da zuwa garin ba shida
iyayensa.
Tunda farko dama bai ɗauki rainin hankalin Damazau ba,shugabansu a lokacin.
Kullum cikin sa'insa suke,har goje yayi nasarar yanke maƙogaransa wata rana yazama
shine sarkin dawar,shekara biyu baya. Abubuwa da dama sun faru lokacin,kowa a garin
banda kama sunan goje babu abinda yake,matsi da takuri ya ƙara yawaita a cikin
garin,yayinda su kuma yaransa suka fara fantama sunayin yanda suka ga dama,saboda
yanda goje yabasu lasisin yin yanda ransu yake so a duk sanda sukaga dama.

Tura cinyar kazar yayi a bakinsa ya zuge tsokar kafin ya wullar da ƙashin.
"Shege dama yanada kazi bula bula haka muke cin zomaye,indai bayyi ƙara ba ku dunga
ɗebo mana uku a kowacce rana,in yayi magana kuce yazo yasameni,ƴan kare da jajayen
kunne sai suyita tara dabbobi yawun mutum yana cinƙewa in yagani,su basuci ba basu
bawa mutum ba."
"Angama ogah goje,ai saima ka gansu da rai,manya manya fah,naji ance wai kawun
Ragarus neh"
Yafaɗa yana kallon wani saurayin bafulatani a gefensa riƙe da kwari da baka a
hannunsa.
"Ragarus kace dukiyarku ce muke shirin hawa kai,kaji nace bakwa ci koh,to yazanyi
hakan kuke saika saka sorry fah"
"Ogah kenan ai bai daɗe da dawowa ba ne,dani kaina saina fi haka,dan a bayan
kwanaki kam dole zan more"
"Sheege ɗan kawu,to tsugunna ka dangwali arziƙi"
"Ai ogah wani dangwalar arziƙin ma sai matar ogah tazo gida,zamuyi shagali"
Dariya suka saka da shewa,amma lokaci ɗaya goje ya turbune fuska yana muzurai,wani
kallon tsare rai yayiwa taska,har hakan yakasa sakashi haɗiye naman daya saka a
baki.
"Taskaaah ka iya bakinka fah in kana son kwana da fatar bakinka,yaushe raini yafara
shiga tsakani da har kake haɗani da mace, harda wani zakuyi shagali......hmmm ai
naji haushi ɗazu,wai me yasaka ma ban cirewa wannan tsohon ƴan maraina bane,kamanni
yayi caca dani bashi ko sisi,kuma har yana saka ran cinye saniyata wai,kutt Sailuba
fah yakeson cinyewa wai a caca,kuma ma harda fansar saniyata da wata gajarabil ɗin
ƴar sa,kai ya jawo mata ma aradu,zataci ƙaniyar tane muddin da taka gonata"
"Ayi haƙuri ogah bazai sake faruwa ba"
Taska yafaɗa yana sunkuyar dakai.
Jefah naman dayake hannunsa yayi kan ganyen dayake gabansa,tashi yayi daga kan
kujerar tasa yana gyara zaman wandon jikinsa. Ta saman wutar ya tsallaka maimakon
yabi ta gefe.
Bai waiwayo ya kallesu ba har ya ƙule cikin jejin.
Dukkan sauran yaran kowa taska ya kalla yana jiye masa.
"Kai taska wlh jagos ne,kalli fah yanda ka kunnashi,kasan fah yau ya juƙi hayaƙi
dayawa a sama yake over. Da alama tunda ya nufi gidansa na cikin jeji to saita
Allah kenan,ranar fah dana fishi gurnani naji yanayi a cikin ɗakin,anya kuwa ogah
goje mutum ne kuwa?"
Dukkansu mai bayanin suka zuba ido,saboda jin abinda yafaɗa.
Ɗaya daga cikinsu ne wanda tun ɗazu bayyi magana ba yana gefe,wato Tunga,kuma shine
na hannun daman goje,yafi sanin sirrinsa fiyeda su.
"Kai Ragarus kafiye fah surutu,da alama so kake yasaka shuru na har abada,kuma inna
sakejin kana bibiyar sawunsa na abinda yake saina faɗa masa tamm. Mazaje mugama mu
tafi gida,ogah nasan bazai dawo ba sai gobe,kunsan kuma munada ƴar tsamar da zamu
buga da ƴan solo gobe,tunda sun ƙalubalance mu."
Dukkansu shuru sukayi da zancen,amma daga yanda Tunga yayi magana to akwai ƙamshin
gaskiya a maganar Ragarus kenan.

___***___

Tafiya yake kansa tsaye zuwa cikin dajin,duk da dare da kuma rashin haske,da kuma
hanyar duk ciyawa da itatuwa,amma haka yake jefah ƙafafunsa ko jikinsa,kana gani
kasan yasan hanyar da yarda ƙafafunsa su kaishi.
Yaɗanyi tafiya mai nisa kafin yafara haɗa hanya yana dafe kai,wani numfashi yafara
saki daga cikin ƙirjinsa wanda yake bada sauti mai diri.
A haka yana tafiyar da ƙyar cikin jarumta har ya isa gaban wata bukka ita kaɗai a
cikin dokar ɗajin. Buɗe ƙyauren yayi ya faɗa cikinta,ɗakin vaƙiƙƙirin yake anyi
masa yabe da baƙin fenti, na shuni,wani buzu ne a tsakar cikin bukkar shima
baƙi,bayan haka babu komai a cikin ɗakin.
Faɗawa yayi kan buzun yana riƙe kai,tareda fitar da wani ƙaraji kaman na karshiyah.
Ya daɗe a wannan yanayin yana birgima kafin ya fara fitar da wani numfashi mai
nauyi.
Buɗe idanuwansa yayi wanda sukayi tamkar garwashi saboda jan da sukayi.
Ɗakin ya zubawa idanuwan kaman mai nazari,can kuma sai ya tashi ya zauna. Buzun ya
ɗaga ya ɗauki tabar wiwi ya kunna mata wuta,zuƙar hauka yakeyi mata tana shiga
cikin kansa na tsawon lokaci.
Kaman an tsikareshi yasake jefar da itah yana riƙe kai,da alama dai wata ƙarace
yakeji wanda kunnuwansa basason hakan sam.
Sakin kunnen yayi ya faɗi a wajen tamkar matacce,ko numfashi bayayi na
kirki...........

Ku nima na shiga ruɗani,mai yasameshi haka,suwaye suka fara yarda da maganar


Ragarus🤣🤣🤣.

Littafi na ɗaya ne dana biyu kaman yanda na sabayi,na ɗaya bati siddan,na biyu kuma
Naira 300 ne dan haka zaka iya biya tun yanzu kafin a shiga kashi na biyu.

3131951977
Auwal Sadiya
First bank

Ko katin mtn ta nan


09035784150

VTU ta nan
2347068390570

Ƴan niger ku tuntubi wanann number.


+227 97 21 16 15
----------------------------------------------------

Sadi-sakhan ceh
09035784150
Share please

*SANADIN CACA*
Mallakar SADI-SAKHNA

PROFICIENT WRITER ASSOCIATION

*USERNAMES*
FACEBOOK PAGE:Sadisakhna
WATTPAD:@SAKHNA03
AREWABOOKS:@sadeesakhna
PHONE NO:09035784150
________________________________
*Book 1*
Chp[03]

[Sumaimah a mahangar gani]

Dare yayi sosai,bakajin komai sai ƙarar jemagu da kuma karnuka,wasu na gidanne na
yayunmu,wasu kuma na maƙwantane. Banason haushin karnuka ko kaɗan,to amma kuma
yazanyi da saurayin kakata,shikansa wanda ake shirin ɗaura ƙaddarata da tasa yafi
kowa yawan karnuka a yankinnamu.

Tashi nayi na zauna ina kallon ɗakinnamu,ba wani girma ne dashi ba,amma yaran
dasuke ɗakin Allah yayi yawa dasu,basuda wani takamaimai yawansu,saboda wani
lokacin suna raguwa,yayinda wani lokacin kuma yawansu ke haura misali,kaman dai
yau.
Dan duk matar gidan da mijinta yake ɗakinta nan take koro ƴar ta ta kwana,su kwana
suna birgima suna fitsari,a barni da gyaran ɗakin kullum kaman ibada.
Duk cikin ɗakin nice babba,nayi rayuwa a ɗakin da ƴan matan gidan,a hankali aka
fara aurensu har suka ƙare kaff sauran ni kaɗai,saikuma bazawarai wanda suka dawo
daga gidan nasu auren amma su basa yarda su shigo wannan kurkukun kwana.
Ba ƙarar haushin karen ko kuma gwartin yaranne ya hanani bacci ba,bace abinda ya
faru,tun ɗazu nayi nayi na runtsa amma na gagara,ko nayi niyyar baccin babu abinda
nake gani sai fuskar goje mai kama da dodo,inaga kaff gidannamu babu wanda yakaini
tsoronsa,bansani ba ashe dashi zan ƙare rayuwata.
Ahh anya kuwa nabari a kaini wajennasa wani satin? Zuciyata wacce take suya tayimin
wanann tambayar.
Abu biyu sukazo cikin kaina,shinna gudu kokuma na na kashe kaina?. Dukkansu ba
abune mai kyau ba,amma idan na bari aka kaini in shi ya kasheni shikenan na rataya
a kansa koh?

Tashi nayi daga kan katifar bayan na ɗauke cinyoyin yaran da suke kaina,tsakar
gidan na fito ina kallon taurari da kuma farin wata,sukam sunji daɗinsu sai haske
sukeyi,ko yaushe zanga haske nima a rayuwata oho.
Hankalina yana wajen kallon saman saikuma najiyo kaman alamar matsin mutum a
kewayen dabbobi na gidan.
Gaba nane naji ya buga,mai mutum kuma yake a tuken dabbobi da tsawon darennan.
Da kaman vazan ƙarisa ba karnaje aljanine nayi gamo,saikuma to zuciya da zon
gulma,na dayyi ta maza na nufi kewayen.
A hankali nake tafiya ina sanɗa har na iso daidai wajen ta baya,tsugunnawa nayi na
kara kaina tareda nutsuwa,domin naji mai ake cewa.
Muryar Inna rammah kuma matar baba ta biyu? Itada inna atika, matar kawu Ɗahe. Mai
kuma suke a kewayen dabbobi da daddare,naga dai in wajen dabbobi ma sukaje sukam
babu nasu aciki,awakin ammi ne a wajen sai kuma ragunan mazan gidan da suke kiwo.
Wata zuciyar ce tabani kaddai satar dabbobi zasuyi,ko kuma suyi musu illah,,dan
hakan ba wani babbane daga cikin aikinsu ba,daga su har ƴayansu ba mutuncine ko
tausayine dasu ba,nikaɗai sai Allah muka san baƙar izayar dana sha a hannunsu,damma
wai a hakan basamin wani abun saboda a wajen ammi baba ya damƙani lokacin daya kawo
ni gidannan ina ƴar ƙarama,kuma suna shakkarta itada kayanta.
Kaina na ɗaga kaɗan ina leƙawa domin naga wacce akuyah zasu ɗauka,saidai ga
mamakina ba akuya suke ɗauka ba,rami sukayi a wajen suna binne wani abu da bansan
menene ba.
Can kuma sainaji inna rammah tafara magana.
"Ke wai fah hakanma munyi da gaske,da tuni ƴayan mu suna nan zaune itakuma tayi
aure,da ai bamu yarda da zancen Ƴar boka ba,datace mana muddin wannan ƴa tana
gidannan to ƴayan mu bazasu auru ba. Naji fah kaman cewa yake ɗazu wai inna gonarsa
zai siyar ya kaiwa goje kuɗin,yafasa bashi itah,kiji kayan baƙin asirin da uwartata
tayi mata na farin jini ya yaye tahana ƴaƴanmu masu tasowa aure"
"Iyi kuma fah,bare ma ni mai yara ƙanana ai dole na tashi tsaye ki gafah shekarar
da muka mata maganinnan shikenan sai ƴayanmu suka fara auruwa kaman ana musu ruwan
mazaje daga sama,da kuwa ita kaɗai suke gani da gashi a gidannan,kallon maza
sukeyiwa yayanmu"
"Hmm yanzu dai mungama da wanann,muddin yayi aiki to Baban su Hajjo bazai sake yin
wani maganar fasa aurenta ga goje ba,suje can in ma babbakata zayyi ya babbaka ta.
Itama Deeja(ammi) munafuka saikace bada ita aka haɗa vaki ba lokacin yimata magani
na farko,saboda taga duk samarin ƴaƴan ta ita suke so,yanzun kuma dan taga dukkan
manyan ƴaƴanta sun ƙare shine tace wai yanzu ba ruwanta"
"Wlh ƙarya take kedai bari asiyanta ta taso yanda take ji da yarinyar nan,tun
yaushe ta tashi tsaye idan taga bazata auru ba, to yanzu idan Baban su hajjo yaƙi
aurarta ga goje ya zamuyi kenan?"
"Wlh indai wanann kam ya karye toh haukata ta zanyi,yarinya jarabbabiyah ga kyau
kaman mayyah irinna uwarta,keda bamu kauda uwar ba ai da yanzu bazamu samu kansa
ba,yanda yake son ta kaman zai mutu.....maza ai munafukaine"
"Ko itama mu aikata wajen uwartata ba,duk da bansan Zinarunba amma in haka take
kaman ƴarata kam dole zai jauce akan ta,haka suke da ƙira kaman su sukayi kansu"
"Zakuwa mu sanja mata kamanni,ke nifah na tsani ƴar nan,menene bamu gani ba a wajen
baban hajjo akan ta,indai wannan karon bata bar gidannan ba to kuwa zamuyi babban
shiri,in ma Deejah ce yanzu takeson kareta to da ita zamu haɗa..........."

Bangama jin mummunan labarin da suke ba na sulale a wajen,saboda yanda ƙafafuna


suke rawa bazan iya gama ji ba sam.
Hawayene kawai yake zirara a idona,yayinda dukkan wani abu dayake amfani a cikina
ya dauƙi yajin aiki na wasu daƙiƙu.
Tun inajin hayaniyarsu da shewarsu har na daina ji da alama sun bar wajen,na daɗe
ina zargin mutanen gidannan namu basu san Allah ba,amma yau kam na tabbatar.
Gari yafara haske asuba ta gabato,kafin na bar wajen na nufi ɗakinmu,ikon Allah ne
kaɗai ya kaini ɗakin.
Dana kwanta ma ba bacci nayi ba,zuru nayi har assalatu tayi.

Ɗankwalin danake yin sallah dashi na ɗauka na fita daga ɗakin zuwa inda nake
sallah,a canne ƙofar wani baban yayanmu wanda yagina ƙofarsa amma bayyi aureba,a
wajen nakeyin sallah,saboda ɗakinmu kam nasan bazzayi sallah ba.

Bayan na idar da sallahr na daɗe ina roƙon Allah kaman yanda na saba,yau kam banyi
karatun Ƙur'ani dayawa ba,saboda yanda bacci ke fizgata,ban samu damar komawa
ɗakiba anan bacci yayi gaba dani.

Zafin rana ne yafara cin ƙafafuna,hakanne yasa na tashi na zauna,safiya tayi ashe
har rana tafito bansani ba.
Ajiyar zuciya nayi dan ma yau banice dayin wanke wanke ba,shara kawai zanyi sai
ɗora abincin siyarwar ammi. Dan haka cikin nutsuwa na tashi na ninke abin sallahr
tawa zan bar ƙofar.
Motsin mutum naji hakanne yasa na ɗaga idona.
Da yaya Musbahu na haɗa ido yana tsaye yana kallona.
Rusunawa nayi na gaisheshi,yanada mutunci shikam sosai,dan ko hayaniyar gidan bata
wani dameshi ba,shine babban ɗan ammi,yayi diploma yana koyarwa a makarantar
secondry ta garin.
"Sumaimah lafiya kikazo nan kina bacci,na dawo daga sallah naga kinyi bacci anan"
"Ahh bakomai kawai baccinne ya ɗan daukeni"
"Ohh toh,kiyi haƙurifah da abinda baba yayi miki kinji,in kika jure komai zai wuce
kinji,yau ma nayi masa maganar a masallaci, amma sai ya hauni da faɗa,kuma jiya da
mukayi masa magana yace zai bashi kuɗin yafasa aura miki shi,amma kuma yau da asuba
ya dage sai ya aura miki shi,abin yabani mamaki"
Idon ne ya cicciko lokacin danaji abinda yaya Musbahu yace,maganar dasu inna rammah
sukayi jiyace ta faɗo min araina,wato su yayah Musbahu ne suka tausheshi akan aurar
dani ga wancan dodon,har ya yarda su kuma waɗannan matan suka sake juyar da kansa.
Saurin share hawayen idona nayi tareda jijjiga masa kai.
"Babu komai yah Musbahu in hakan shine ƙaddarata banida zabi illah na
rungumeta,dama dolene bawa yayarda da ƙaddara mai kyau ko kuma akacin haka.
Har nazo fita daga ƙofar tasa yasake yimin magana.
"Kije ammi tana ta nemanki kinji,ga wannan kuma ki boye ki dunga siyan koko,an bani
albashina jiyah"
Yafaɗa yana miƙomin naira ɗari biyar.
Wani kukane ya tahomin lokacin dana saka hannu na karba,wannan karon ban tare shi
ba nayita kunza kayana,tun yana rarrashi na har yabari yabar ƙofar.
Allah ne kaɗai yasan yanda nake ƙaunarsa a cikin yan uwannanwa,da kuma yanda yake
birgeni,shikam ya fita zakkah a gidannan.
Harna isa ƙofar ammi ina kwarara masa ruwan Addu'a ta samun nasara a raina,Allah ya
haɗashi da mace tagari ba irin matan gidannan ba,dan daga kan iyayen har surukan
kaman an cuɗasu an rabasu haka suke.

A baranda na sameta tana tsince shinkafar daza'a dafa in anjima,wajen kaca kaca da
miyar tuwo da kuma kunu,ina yara suka zuzzubar lokacin da suka karya.
Gaisheta nayi kafin na leƙa ɗakin inna rammah mah. Tanata masifah da yaranta suna
rashin ji.
Fuskarta dauke da murmushi da amsamin,kaman ba itace ta gama faɗin kalaman da
mutumin dayasan zai mutu bai kamata ya furta ba.
Tuwo nah na ɗauka naci nakai kwanon wajen wanke wanke.
Bishirah da asiyah ne suke wanke wanken,ƴar rammah da kuma ammi.
Harara ta Bishirah tayi dana ajiye kwanon cikeda tsiwa.
"Wai mutum bazai ci abinci da wuri ba dan mulki,sai an kusa gama wanke wanke ya
kawo kwano"
Kunnenta na riƙe ta bangaren danake,dan abin yayimim ciwo,yarinyar da in auren
shekara sha biyu zanyi saina kusa haifarta take faɗamin wannan maganar.
"Ke wato kin iya rashin kunya koh,yaushene ma kuke wanke wanken,naga saikuyi sati
bakuyi ba nina ke,dan an fara baku shine har kun fara tsiya koh?"
Maganar inna rammah najiyo daga bakin ɗakinta lokacin da Bishirah ta kwanɗa ihu
kaman ina zare mata rai.
"Sake mata kunne to ƴar gadon marasa mutunci,baƙin cikin menene haka da har zaki
cire mata kunne,so kike ki nakasata tayi zaman gida kaman ke?"
Sakin kunnennan ta nayi,yayinda maganganunta kemin zafi a rai,kallon baki isheni ba
nayi mata kafin na ɗau tsintsiya na fita share harabar ƙofar tamu,duk abinta dai
nasan bazata dakeni ba,da dai ta dakeni komai ma tayimin,amma yanzu na wuce
duka,saidai tayi min muguntar boye ta asiri.
Abinda yafarune ma ya faɗomin a rai,hakanne yasa na nufi kewayen dabbobin kaman da
niyyar cewa shara zanyi.
Akan wajen da sukayi binne binnen idona ya sauƙa,tabbas kam ba mafarki nake ba..
Jan lilon ƙafafuna nayi zuwa wajen,tsugunnawa nayi idon kyam akan abinda ƙarfi da
yaji yakeson rabani da gidanmu.
Harna saka hannun zan tone wajen saikuma na tuna maganganunsu,wataƙila inna tone
asirinnan ya karye baba yagane kuskuren da yayi a caca,har ya nemi kin auramin
goje,to amma su inna rammah fah,zasu barni na cigaba da zama harna samu miji daidai
dani nayi aure. Tabbas ba karamin aikinsu bane su aikata abinda sukayi iƙirarin
faɗa.
Inkuma yanda suka fada dagskene na tarewa ƴaƴansu farin jininsu wanda nasan bokane
yafadamusu dan ya ci kudinsu,toh zan tursasa ammi sake cutar dani muddin akan ƴar
tane Asiyah.
Wanda hakan zai zama abune da bazanso ya kasance ba.
Maida kasar dana fara tonewa nayi na binne wajen cikin sanyin jiki,na zabi barin
gidan kawai,koma mai zaimin yayimin Allah ne ke riƙeda rai na ai,wuya kuwa bata
kisa sai kwana yaƙare.
Tashi nayi na barbaje ƙasar tareda fara share wajen,banyi niyya ba amma inna ƙiyi
kar suyi tunanin naga abinda sukayi jiyan.

Wannan wace irin rayuwa ce,ace wai aisiri akayi maka amma ka ƙwammaci ka barshi ya
hau kanka......ke duniyah.

Littafi na ɗaya ne dana biyu kaman yanda na sabayi,na ɗaya bati siddan,na biyu kuma
Naira 300 ne dan haka zaka iya biya tun yanzu kafin a shiga kashi na biyu.

3131951977
Auwal Sadiya
First bank

Ko katin mtn ta nan


09035784150

VTU ta nan
2347068390570

Ƴan niger ku tuntubi wanann number.


+227 97 21 16 15
----------------------------------------------------

Sadi-sakhan ceh
09035784150
Share please

*SANADIN CACA*

Mallakar SADI-SAKHNA

PROFICIENT WRITER ASSOCIATION

*USERNAMES*
FACEBOOK PAGE:Sadisakhna
WATTPAD:@SAKHNA03
AREWABOOKS:@sadeesakhna
PHONE NO:09035784150
________________________________
*Book 1*
Chp[04]
Saida ya daidaita hasken a cikin idonsa kafin ya buɗe idon dukka. A kwance yake a
inda ya suma jiya,wato cikin bukkar,yunƙurawa yayi babu salati bare godiya ga
Allah.
Kakkaɗe jikinsa yayi daga ƙurar dayayi kafin ya fito daga cikin bukkar yayi wata
miƙa.
Ido ya haɗa da karnuka guda uku,murtuƙa murtuƙa a kwance a filin wajen,suna kallon
ya fito suka nufi inda yake.
Feɗuwa yayi dukka suka amsa masa kaman sunji mai yace.
Hanyar dazata kaishi cikin gari ya nufah kansa tsaye yana tafe suna take masa
baya,yanda yake baƙi fuskarnan duk gashi haka suma suke.
Duk hanyar dayabi yara matsawa suke harda samari.
A wajen mai shayin unguwarsu ya zauna akan benci,su kuma karnukan suka tsaya a
bayansa kaman wasu fadawa.
"Kai iliyah yiyomin haɗin shayinnan da kake min,kaga na juyeshi a cikina nan"
Dama murya a shaqe,ta kuma haɗu da tashi a bacci,banda hamami babu abinda yake,amma
hakan ko kaɗan bai dameshi ba,haka wanda yake gefensa ma ko mai zayyi bai isa yace
ya dame shin ba.
Ido suka haɗa da Iliyah wanda yake ta aikin juyah shayi daga wannan kofin zuwa
wannan.
"Amma goje na wata biyar fah ya taru akan ka ko ƙwandala baka rage ba"
"To dolene saina rage koda banni da kuɗi iyee,kai akan shayin zaka dunga
tsayarmin,idan bazaka yimin haɗi ba faɗamin naji"
"Ahah ba haka bane,kawai dai nima kuɗin hannun nawa ne ya......"
"Kaga banason jin wannan muryartaka mai kamada ta ƴan hamsin,haɗomin shayin kasamu
taska injini ya rage maka wani abun,in kuma kasake magana zan baje rumfar nan
yanzunnan,kafi kowa sanin banason ƙorafi tamm"
"To shikenan ogah goje barina gama sheƙawa idi tukunna"
"Wanene kuma idi?"
Goje ya faɗa yana duban mazan dasuke zaune a wajen. Wani tsamurarre a gefe Iliyah
ya nunawa goje. Suna haɗa ido yayi saurin kawar da kai tareda cewa.
"Ahh bakomai Iliyah haɗa masa zan jira ai"
Yafaɗa muryarsa tana rawa. Ganin har bayan yayi maganar goje bai daina kallonsa ba.
"Kai ɗan garinnan ne kuwa,bansan ka anan yankin ba,ka sanni?"
Goje ya tambayeshi yana ƙare masa kallo kaman yaga ɗan ƙwaro.
"Eh .......hhhh to rani nazo,wannan shine karona na farko,wata na guda kenan a
garin"
"Ohh toh...in kanada dabbobi ko wani abu muhimmi karka barshi a waje har zuwa
dare,in ba haka ba yazama na bayin Allah,sannan in faɗa ya kaure a lungunku kaji
ƙarar wuƙa kada ka fito, ina tausayinka shiyasa na faɗa maka"
Ɗaga kai yayi alamar yaji.
Suna cikin maganar ne Iliyah ya miƙowa goje ruwan shayin tareda yankan biredi.
Karba yayi maƙwat saida yayi rabin kofin,kafin yanki rabin biredin ya tauna.
Kafin kaceme yatashi dashi,wata gyatsa yayi kana ya miƙe daga kan bencin.
"Sai gobe kuma"
Dukka a tare suka masa a sauƙa lafiya mutanen wajen.
Cikin gida ya nufah yana haɗa hanya.

Wata ajiyar zuciya suka sake a tare,kaman wanda aka basu horon ɗauke numfashi idan
ya tafi su sake.
"Kai Iliyah wanann ɗin waye shi,shima a anguwar nan yake"
Idi yafaɗa yana zare ido,har sannan hankalinsa bai koma daidai ba da ganin gojen.
Dariyah wani saurayi yayi a gefe kafin yace.
"Goje kenan kake ji,watansa guda baya cikin garin,jiya dai muka ganshi ya
dawo,bakada labarin sunyi caca ne shida baban su ubaidu,ya cinye shi yace yabashi
kudinsa shikuma bashida ko sisi. Dayaga yana shirin yankashi ya fanshi kansa da
ƴarsa,yanzu haka muna nan mun zuba ido wai wani satin za'a ɗaura aure"
"Kai mtsww yarinyar nan kuwa ga kyau ga hankali,wai a rasa dawa za'a haɗata sai
goje,ai an cuceta wlh. Kai mutuminnan fah naji ƙishin ƙishin ma wai asiri ma idan
akayi masa baya kamashi,gashi da wani ɗan banzan ƙarfi,sarkin garinnan ma shayin
horashi yake,shiyasa idan yaci kayanka yanda kasan yaci kayan uwarsa haka yakeyi"
"To kai bakada labarin abinda yayi yai batan zana bashi ba alamunsa,naji fah wai
haddashi a waɗanda suka 'balle masana'antar shinkafa ta garinnan,ƴan sanda sunzo
kama su suka kashe guda biyu. Amma suma sun kama barayin guda uku. An kamashi aka
kulleshi,bamu san mai yayiwa shigaban fursunan ba da kansa yasako shi......hmmm
wannan mutumin ai ya wuce yanda kuke tsammani"
"Kai ku bar wannan zancen haka,tunda munanan dashi ai zaiga komai mah,ya batun ni
honarable neh,kuna ga zaici siyasar nan kuwa,naji ance yaraba mashina a hamsin a
garinnan"
"Rabu damu da wannan barawon,ko tsafi yake da tsohuwar zaba bazan dangwala masa
ƙuri'ah ta ba,haka suke barayin banza,suna zaune a office suna satar kuɗin mutane
da biro,shuru bakajin ɗuriyarsu sai siyasa tazo tukunna........

Barina bar teburin mai shayinnan nayi gaba......

___**___

Gidan matsakaicine kuma na daidai ƙarfi,ginin ƙasane anyi masa ya'be da


sumunti,amma wani wajen duk ya bubbule saboda daɗewa,kuma ba wani kula ake dashi
sosai ba.
Kofah biyune a gidan,inda iyayen goje suke,saidai babansa ya rasu sai inna mairo
kawai ita kaɗaice a ƙofar. Sai kuma ƙofar malam Audu ƙanin babansa da matarsa gaji
da ƴaƴansu,yana aikine a gidan wani alhaji,daga bashi ɗaki a gidan gaji ta tattara
da ƴaƴan ta suka bishi,suna can yau kusan wata shida. Ƙofarsu shuru,anan goje ya
ɗaure saniyarsa.
Saikuma ƙofar goje,shima ɗaki ɗayane na kasa da banɗaki a gefe,kullum ƙofar ɗakin a
garkame take da ƙwado,kaman wani abin arziƙine a ciki ba kayan dauɗa ba.
Sanda gaji tana nan kullum sai sunyi rigima idan ya daki ƴaƴanta in suka shiga
ƙofar,inta fara masifah sai yace zai doketa tukunna tayi shuru,shiyasa tafiyin
masifar idan baya nan,dan a gabansa kam ko mijinnata ma albarka.
Kullum cikin ƙorafi take wai inna mairo tazo itada ɗanta sun takura musu. Shiyasa
da malam audu yasamu aiki itama tabishi,dan itama inna mairon da a birni suke itada
mijinta,yana aikin masinja a kotu,yin ritayarsa ne yasaka su dawowa
mahaifarsu,shekararsu biyar kenan da dawowa.
Amma goje ya fitini garin kaman dama anan ya tashi.
A zaune take tasaka kayan yin igiyarta tanan tukawa,gidan tsitt kaman bakowa,tun
abin yana damunta har ta saba yanzu.
Bayyi sallama ba dan dama bayi yake ba saidai ta ɗaga ido idan taji motsinsa.
Jijjiga kai tayi tareda yimasa magana,ganin ya yaɗau buta yana jijjiga wa,da alama
ba ruwa a ciki.
"Yau kuma daga ina"
"Daga jeji a can na kwana"
"Ohhh gari ya hargitse da abinda ka jawo na auren ƴar gidan uwaisu,sunzo nan jiya
akan batun,Nayimusu kwatancen gidan da kawunka yake,amma sunce abin baya wani
buƙatar manya. Nayi ta zuba idon shigowarka amma banganka ba sai yanzu,wai dan
Allah yaushe zaka daina........"
"Ina zuwa inna barina rage marata tukunna,nasha shayi yanzu a wajen Iliyah"
"Yau ɗin ma,kabiyashi kuɗinsa ne,do Allah ka tausayawa mutuminnan da shan shayinsa
karka karya masa jari"
"Kai daɗina dake inna kowa yazo yamiki ƙorafi akaina saiki yarda wai,Allah zan fara
karya ƙafar duk mai shigo gidannan yana kawo zancena,yanzu dai barina zaga bayan
gida,banyi sallannan da ake da safe bama fah"
"Ehhh bakayi sallahr asuba ba,har goma tayi,goje yanzu goje kanaso kuwa........"
"Kai kai kai inna wai abin magana baya miki yawane,yanzu da kika rikeni da yanzu
nayi alwala,kinga kenan laifinki ne idan banyi da wuri ba koh"
Sakin baki tayi tareda tsayawa da murɗa igiyar tana kallonsa har ya shige cikin
banɗakin,rabonta da ganinsa tun jiya da safe data saka masa koko yasha ya fice,wai
yanzu kuma yazo yana cemata laifinta ne da bayyi sallah da wuri ba,hmmm babu mamaki
ma sauran sallolin babu wacce yayi a ciki,dan hakan ba ƙaramin aikinsa bane.
"Allah ya kyauta"
Tafaɗa tana cigaba da tukarta.
Bayan ya fito daga banɗakin bai tashi zuge zee ɗin wandon a ko ina ba saida yazo
gaban inna mairon.
"To wata sabuwa,shi wandonne duk ka baro banɗakin baka jugeshi ba sai a gabana?"
"Mtsww bazaki gani ganeba wandonne ya matseni daƙyar nage zugeshi"
"Sai akace kuma dole sai kasaka shi koh,zauna muyi maganar nan,dan tana nan a ƙahon
zuciyata da ita na kwana. Inaso kayi aure goje ina so naga wanann rana,amma ban
taba tunanin irin wanan auren zakayi ba,wanda ko a tarihi ban daba jinsa,yanzu
kaida shi babban kobon kunyiwa yarinyar nan adalci kenan iyee,ace kuna wai caca ku
saka rayuwarta a ciki?"
"Inna mai nayine anan wajen,ina lafina a cikin wannan lamarin,ko saboda kullum ni
laifi nake kai. Gayennan bani nace yayi caca dani ba bashi da ko sisi,shikansa
yasan bana ɗaukar asara,kuɗi nace yabani bashida shi yabani ƴar sa. Yanzu ni bakiga
ma cuta tah yayi ba,nifah saniya tah sailuba tah na saka a cacar nan,daya cinyeta
fah shikenan zuwa zayyi ya siyarta,shiƙuwa ƴar sa da mutanen wajen suka roƙeni na
karba wazan kaiwa yasiye ta,dole fah saidai nasaka ta a gidannan nayita kiwon da
babu riba,amfanin ɗayane zata dunga yimiki aiki kinga saiki huta dama bakida
lafiyar ƙafah. To banda wannan ta ina zan ƙaru da ƴarsa faɗamin shi"
"Yanzu ƴar adam ƴar mutane kake haɗawa da wata can dabba,nidai dan Allah in an kawo
yarinyar nan karka cutar da itah kaji?"
"Dan ta wannan ne bani zaki faɗawa ba,ba a kaina zata zauna ba,in ta kiyaye abinda
aka ce mata to ta tsira"
"To naji daɗin hakan,yarinyar nan tausayi take bani sosai. Ya batun inda zaku zauna
toh,ko kai a gyaramuku sashen Kawunnaka ku tare a can,tunda shi baya nan"
"Nida wa zamu tare ɗin,dan Allah ki bar wannan zancen,ba ga nan ɗaki a gefenki ba
ta zauna mana,in zancen Waccan dattijon kike kwanannan zaki gansu sun dawo,waye zai
zauna da wannan matar itada tambadaɗɗun ƴaƴannata"
Inna mairo taji haushin abinda yace,to amma yazatayi ,tasan a kaff rayuwarsa babu
wanda baya maidawa magana in ka ɗauketa,ciki kuwa harda sarkin garin.
"Kabar wannan zancen dama nasan shi kakeson yi,ɗakinnaka dai zaka gyara ku zauna a
can,wanne irin aurene kai kana can ita tana nan,taya zaku fahimci juna a haka."
"Fahimtar juna hhhhhhh wai to kawai tazo gidan ta zauna mana toh,dole sai anyi mata
aure dani tukunna ......afff banyi sallar ba ashe,barina je na gurguzata kafin ta
anjiman tazo"
Tashi yayi da sauri ya nufi ƙofar tasa,inna mairo ta share masa harabar wajen kuwa.
Makulli yasaka ya buɗe ɗakin,bayan ya shiga ya maida ƙofar kaman munafuki.

___***___

Kaya take naɗewa na wankinsu da tayi a injin wanki tana waƙar ado gwanja,kana
ganinta kasan duniya tana gara masa.
"Sakwara daɗi luwai mun samu guri luwai,kai wlh rayuwar masu kuɗi da daɗi sosai. Ba
ruwanka da surfe,ba ruwanka da hura wutar murhu,gas ne kana ɗorawa ka gama,ga wanki
ma hajiya tabarka ka saka a inji,ga cin daɗi ga albashi. Kai kuɗi yayi ni gaji"

Lace na a jikinta mai tsada doguwar riga wanda hajiya matar mai gidan tabata
kunce,tsabar samun guri ƴaƴanta su Atika har kunna kallo suke a babban falo.
Ita tanayi mata wanke wanke da abinci,shikuma Malam audu yana gadi da kuma ban ruwa
ga fulawoyi.
Karaff Atika ta bugo ƙofar ta shigo da gudu cikin ɗakinnasu da aka basu,wanda yake
a boys quarter na gidan.
"Gaji gaji nashiga uku shikenan asirina ya tonu tawa ta ƙare gaji"
Riƙota gaji tayi tana tambayar ta lafiya take wannan hakin kaman ta kashe wani.
"Kee lafiya atika mai yasameki haka,ki nutsu kiyimin bayani mana mai ya faru ne"
"Gaji ki tattara kayanki mubar gidanann,baba ma ki faɗamasa kar ya dawo gidannan mu
tafi gida gaji,mu koma gida kawai"
"Ke dallah kimin bayanin mai yafaru ne wai,mai kikayiwa hajiyanne,naga ɗazu ta fita
daga gidan ma bata nan"
"Eh ta tafi amma komai ta manta saita dawo,shine.....shine.... Tasameni nida alhaji
akan gadonta toh. Toh saita yanki jiki tafaɗi,kuma dama tanada hawan jini.......wlh
gaji inaga ta mutu,idan ta mutu wannan sojan ɗan uwannata bazai ƙyalemu ba sam,kizo
mukoma gida wlh kafin su kashemu"
Sakin hannun Atika gaji tayi ta faɗa akan gado yaraff mai kunnenta yake jiyo mata
haka.
"Atika mai kikace wai...hajiyah ta kamaki da mijinta a kan gadonta,idan ma iskanci
zakiyi kiyi mana,amma taya daƙiƙancinki zaisa ki bari ta kamaku,ni ai mai farinciki
ce idan har yaga yana sonki zai aureki,amma kafin komai ya tabbata shikenan kin
zawo mana asarar wannan arziƙi da muka fara lasa. Taya kike ganin zasu barmu mu
fita daga gidannan iyee batareda sun lahanta muba"
"Gaji bama wannnan ba,ƙanwarta wannan fatin itama ta ganmu,kuma shi sojan yana waje
shiya dawo dasu ɗaukar wani abu a mota"

"Meeee kikkka ceeee shikkenan tafaru ta ƙare,wlh bazan faɗawa malam ba,dolene shima
ya dawo ya karbi nasa luguden,ban isa shansa nikaɗai ba aradu. Ke kuma bari a gama
yimana na nan kema mu tsira na baki naki...........

Littafi na ɗaya ne dana biyu kaman yanda na sabayi,na ɗaya bati siddan,na biyu kuma
Naira 300 ne dan haka zaka iya biya tun yanzu kafin a shiga kashi na biyu.

3131951977
Auwal Sadiya
First bank

Ko katin mtn ta nan


09035784150

VTU ta nan
2347068390570

Ƴan niger ku tuntubi wanann number.


+227 97 21 16 15
----------------------------------------------------

Sadi-sakhan ceh
09035784150
Share please

*SANADIN CACA*

Mallakar SADI-SAKHNA

PROFICIENT WRITER ASSOCIATION

*USERNAMES*
FACEBOOK PAGE:Sadisakhna
WATTPAD:@SAKHNA03
AREWABOOKS:@sadeesakhna
PHONE NO:09035784150
________________________________
*Book 1*
Chp[05]

Ture atika gaji tayi daga bakin ƙofar ɗakin tana leƙawa,cikin ƙanƙanin lokaci ta
haɗa gumi shirkif,banda zagin ƴar tata babu abinda take na aika aikar data jawo
musu.
A kan idonta sojan ya fito da hajiya a hannunsa,fati tana binsu tana kuka,shikuma
mai gidan ya biyosu cikeda kunya da sanyin jiki.
Har sunzo fita daga gidan wasu sojoji guda biyu suka iso bakin ƙofar gidan,magana
suke da ƙanin hajiyan na wani lokaci kafin suka fita daga gidan a mota.
Shima alhajin mota ya ɗauka yabisu a baya.
Kenan gadinsu zayyi kada su fita a gidan komai.
Duk abinda yafaru akan idon gaji itada atika,a tunaninsu idan suka bar gidan suma
zasu fice,saidai da alama ba haka bane,dan sojojin a bakin ƙofar gidan suka tsaya
suna jajjagawa.
Suna cikin haka har yamma tayi liƙis hankalinsu ya gagara kwanciyah,ba halinda
matar gidanne ya damesu ba illah su halin dazasu shiga.
"Hmmm mlm audu har yanzu bai dawo ba,kaddai yasan mai yafaru ya gudu ya barmu a
ciki,tukunna ma mai yasa zasu hanamu fita toh daga gidan"
Kallon uwar tata atika tayi tareda cewa.
"Yanzu haka fatinnan ce tafaɗawa sojojinnan karsu barmu mu fita,dan daman tun a
ɗakin ɗazu tace saita ɗaiɗaita rayuwata nida iyayena,dama ta tsaneni"
"Laaahaulah wala ƙuwwata shik........"
Bata gama salatin ba aka banko ƙofah,Fati ce firiri da ita,gyalene a jikinta
hannunta ɗauke da key ɗin mota tana jijjigashi,cikeda tsiwa takalli gaji tareda
cewa.
"Kar kiyi salati yanzu,ki bari saikinga kina hango wuta kafin sannnan zaki fara
salati.
Don ku fito dasu daga ɗakin zuwa filin gidan"
Tana gama faɗin hakan tafita daga ɗakin,wasu murtuƙa murtuƙan mutane guda biyu suka
fito da gaji itada atika zuwa filin gidan.
"Dan Allah kayi a hankali karka karya min allon kafaɗa,kaga ƙashin na tsufah ne"
Gaji ta faɗa tana sallalami.
Zubasu akayi a filin wajen da sanyi la'asar.
"Don kuyi musu horo wanda zai jirgita kamanninsu nan da zuwa gobe kada su runtsa
idonsu,matsiyata macuta kawai,wato duk abinda anty Abida tayi muku da haka zaku
saka mata,kin tura ƴar ki tana cin amanarta,idan kuka kasheta saiku aureshi ku
mallakeshi,ku a dole kunga gida. Yau kuwa zaku yi danasanin shigowa garinnan ma ba
gidannan ba"
Tana gama maganar kaman jira suke suka hau su gaji da duka ta ko ina babu tsayawa.
Tun suna ganin farar wuta har ja tafara haska musu a idonsu.
Ƙarar buga get ne hasasu tsayawa da dukan domin suga wanene,fati ce ta taka fiƙi
fiƙi zuwa bakin get ɗin.
Da Mlm Audu suka haɗa ido,hannunsa riƙe dana ɗansa na mijin ƙarami,sauran mata guda
uku kuma ƙannen atika suna biye dashi a baya,kayan makaranta ne a jikinsu wacce
hajiyan ta sakasu wata biyu dasuka wuce.
Killer smile fati tasake masa tareda cewa.
"Ahh mlm audu ka dawone to sannunka da zuwa shigomana ciki"
Abin yayi masa bambarakwai,danshi dai yasan wannan yarinyar ba kulashi take
ba,baidai ce komai ba yayi ta maza yashiga gidan.
Dama wai suna ne yana gadi,tun safe fice sai ya wuni bai dawo ba,yanacan wajen
sharholiyarsa,banda gadin ma menene wane aiki zai iya,ko noma ƙaramar gona kasa
nomawa yake a shekara.
Da gaji yafara haɗa ido tayi gurfano kaman mai karbar gafara,hancinta da bakinta
sunyi dama dama da yawu da jini da majina.
Zaro ido yayi yana shirin fita waje da gudu wani soja ya kamoshi ramm ta rigarsa ta
baya.
"Malam ina kuma zakaje,maimakon ka tsaya ka cecemu wato guda kake shirin yi
koh,saikazo duk mu haɗu muyi karbi azabar tare,tunda kaima yar kace ba iya ni kaɗai
ba"
Bayan gaji ta gama bayanin da dashshshiyar muryarta,fati ce ta ɗora ta bashi
labarin abinda atikan tayi.
"Yanzu kaima saika jona su,shima ku haɗashi don"
Aikuwa buɗar bakinsa yace.
"Yallabai wannan labarin da madam ta bayar banida masaniya akan sa,saina wuni bana
gidanann bansan mai ake kitswa,dan Allah ku barni na tafi da sauran ƴaƴan"
"Baaba ya zakace haka,wlh kasan abinda yake tsakanina da Alhaji,naga kasha kamamu
cikin dare,idan kafara magana sai ya baka dubu goma kayi shuru,daga baya kamma
dayace maka aure na zayyi na zama matar gidannan har murna kayi,kake cemin nayi
ƙoƙari da dabara na mallakeshi a tafin hannuna,wai har na samu na fitar da anty
Abida a gidannan"
Kowa a wajen zaro ido yayi da bayanin atikan,ciki kuwa harda gaji,ita nata
baƙincikin ɗaya yanda ake bashi kuɗi duk dare batada masaniyah.
Fati itada sojijinta basu suka bar su gaji ba sai dare,hakan ma suka gamasu da
karnukan su suyita binsu da gudu har gari ya waye,kafin asuba duk sun suma babu
inda yake aiki a jikinsu.

__***__

[Sumaimah a mahangar gani]

Yau da wuri na tashi,ba kaman jiyaba da bacci ya ɗaukeni har rana ta fito na
makara.
Kai tsaye bayan na gyara ɗakinnamu kamar kullum ƙofar su ammin na nufah.
Koko take zubawa yaran da suka kewaye ta a kofi.
Gaisheta nayi kafin na koma gefe na zauna,saida ta gama dasu tukunna,kafin ta
zubamin nawa,jiya girkinta ne da kuma yau,gobe da jibi nasan na inna rammah
ne,akwai rowar abinci kenan. Yanzu su biyune a ƙofar Aina'u amaryar baban tayi yaji
bata nan,wannan kamma inaga auren tacan tacan,dan ita irin matannane masu shegen
son abin hannun miji,idan akwai to da zama,amma idan babu saita ɗebi jaraba tai
tayi babu gairah babu dalili. Shikuwa baba samunsa ɗaya idan yayo caca ta gara
masa,inkuwa ba haka ba saidai kowa yasan ta kansa,dan kuɗin sana'ar tasa ma ta Aune
Aunen kayan abinci dayake a kasuwa kullum su yayah Musbahu ne masu fama da cikaton
uwar kuɗin ma ballantana kuma riba.
Hannun nasa na karbi kokon da ammi ta miƙomin,bayan na gama tunanin na yi faɗi ba'a
tambayeki ba.
Bayan mun gama gyara wajen nayi kafin na hau kiciniyar ɗora abincin Siyarwa,yau
kasuwar garimu ce,dan haka da wuri ake yi kuma yafi na kullum yawa.
Banason wannan ranar ta zagayo,saboda nafi daɗewa a wajen tallen,ga tarin marasa
ɗa'a a wajen,saidai kuma ta wani wajen nafi sonta,dan nima inayin wani abun nawa
natafi dashi,inna samu riba na saka a asusu.Kuma itama ammi tana sallamata idan na
dawo.
Bayan abincin ya kammalu shiryawa nayi nazo ɗauka zuwa kasuwar,shinkafa da miya ce
da kuma waje,sai kabeji.
Nida Asiyah muka tafi,dan tunda aurena za'ayi dole itama tafara zuwa dan ta gane
kan siyar da abincin.
Kodaɗɗun kayana ne a jikina normal na tsakar gida atampa,sai barin hijabin dana
saka,wanda yafara mutuwa ta sama saboda tsufah. Ba wai kayane aka wareni ba'ayimin
ba,dama gidaje dayawa masu irin ƙarfinmu daga shekara sai shekara suke ganin
ɗinki,hakan ma atampar roba ce. Sauran yara kowa uwarsa na ƙoƙarin ganin tasake
masa,wanda kuma ƴan mata ne sun fara hira samarinsu suyi musu. To ni kuwa ciki
wannene nakeda shi ɗaya,shiyasa a gidannamu nafi kowa ƙarancin suturar sakawa,hana
rantsuwa nema Yah Musbahu yayimin ankon ƴan matan gidan da akayi wata shida dasuka
wuce,shine na samu nake ado dashi ranar juma'a.
Kasancewar kasuwar da ɗan tazara tsakaninta da gidanmu,shiyasa saida muka dan taka
kafin muka isa.
Wajen rumfata ta kullum na ajiye kayan,itama Asiyah na sauƙe mata nata,yarinyar ba
wata babba bace a shekaru,amma nan idan anjima in tafara magana da masu siyan
abinci samari,sai ka ɗauka wata hamshaƙiyar budurwa ce,abin yana bani mamaki yanda
muhallinnamu gaba ɗaya ya koma haka.
Jejjera komai nayi a muhallinsa na fara zubawa wanda suka zo siyah,wanda dama
costomominmmu ne na kullum,sai kuma waɗanda ba'a rasawa.
Hankalina ya tafi wajen zuba abincin,buƙatata na sallami wadanda suka rufemin
kai,ohh abin babu daɗi idan aka rufeka kana zuba abincin,wai a hakanma Asiyah na
taimakona da zuba miyah,da haka zanyi tayi ni kaɗai,tunda naso ta dunga rakoni amma
ammi bata maida hankali da zancen ba,sai yanzu da tasan dole zan bar gidan ai
gashinan ta haɗani da ita koh.
Jinayi an yafato hijabi nah ta gefe,dama kuma naji hayaniya a kasuwar,dan dai bana
ganin mai yake faruwa ne saboda mutanen dasuke kaina.
Juyowa nayi na kalli indo wacce muke zama rumfah ɗaya,saidai ita gwaten doya take
kawowa.
Idanunta a zazzare take nunamin wani waje da yatsunta.
"Ke Sumaimah kalli gacan goje agonki zai sokawa wani wuƙa"
Wani dummm gabana ya bugah,cikin firgici na kalli inda hannunnata ya nuna. Daidai
kuwa lokacin da ya burma wuƙar a cikin dattijon daya cakwane wuyan rigarsa a
tsakiyar kasuwar.
Wani kaɗawa hantar cikina tayi take na fara jijjiga kai kaman wata ƙadangaruwa,ba
fah kuma mafarki nake ba koh,dagaskene wani a kashe a gabana akan idona.
Jini ne yafara feshi daga cikin mutumin ya wanke hannun gojen wanda yake riƙeda
wuƙar a hannunsa,kowa yaga abinda ya faru,amma kuma tsoro da firgici bazai bar
mutum ɗaukar mataki ba.
Bayan ya sakeshi ya faɗi kafin mutane suka riƙoshi aka nufi asibiti dashi.
Hannunsa ya yarfe yanda jini ya wankeshi sharkaf,wani ne daga gefensa ya miƙomasa
tsumma,shima da alama ɗan iskanne kuma yaron sane,dan kansa sai kace gonar
ayah,anyi wanann abin da suke cewa dadah.
Jikin wata katanga ya samu a gefensa ya zauna tamkar bashine ya ɗauki rayuwar wani
ba,ko nace lafiyar wani.
Tabar wiwi aka miƙomasa ,wani kuma ya kunna masa ashana,buuuu hayaƙi ya turnuke
fuskar tasa,baka ganin komai sai gashin kansa mai kama da ciyawa a tsatstsaye.
Innalillahi wa inna ilaihi raji'un,ai a zaune take wani satin i yanzu ƙasa ta
rufemin ido,gwanda ma tun daga yanzu nafara bankwana da mutane ina neman gafarar
su,danna san ana kaini gidan wannan azara'ilun duniyar tofah saidai sunana kawai
dazai saura a doron duniyah.
Indo ce ta watsamin ruwa a kan fuskata,sai sannan tayi firgit na kalleta.
"Wayyo Sumaimah lafiyar ki kuwa,tun ɗazu nake tabaki amma ko motsi bakyayi,saida na
zuba miki ruwa kafin kika dawo hayyacinki"
"Iyee ...uhm inaga suman zaune nayi,me...uhmmm"
Kasa ma ƙarisa maganar nayi,dama kuma bansan bai zance ɗin ba,dan gabaɗaya notin
kaina ya kwance.
"Nasan mai yake yawo a cikin kanki,amma ki kwantar da hankalinki,bazai taba kasheki
ba sai kwananki ya ƙare,wancan ba naji ance wai cunensa yayi ga cibiyar tsaro cewar
dashi a fashin da akayiwa gidan gwamnati,amma in bahaka ba bai cika kisa akai akai
ba,nina sanshi ai anguwar mu ɗayah"
"Hmmmm indo kenan,so kike nace na yarda da maganarki ko mai,kawai dai kina faɗane
dan na kwantar da hankalina,saidai wannan batun babu ma shi,dan raina ya daɗe da
tashi ya tsaya,inaga kuwa bazai taba sake komawa ya kwanta ba har zai sanda
azara'ilu ya zare shi"
"Haba Sumaimah kar kice haka mana,ba kyau mutum yayi ta zatawa kansa mutuwa fah"
In jinta tana ta daɗin bakinta amma ban bata amsa ba,idona nasake mayarwa wajen da
goje yake shida mutanensa,dan bana tunanin zansake sakewa nayi abinda ya
kawoni,jikina ma yayi sanyi da zuba abincin,Asiyah ce take ta zuba Musu,dan in
sunyi magana ma ba jinsu nake ba,saidai nace uhm uhmuhm.
Har zuwa yanzu tabar hayaƙin yake shaƙa bai daina ba,saidai babu hayaƙin kaman na
ɗazu,dan kana iya gano dodanniyar fuskarsa ma daga nesa.
Karaff kaman abin rashin sa'a muka haɗa ido tashi.
Wayyo bammasan mai nakeji a cikin zuciyata ba a lokacin,gashi kaman abun tsafi
kokuma nace ya riƙemin idanuwa na gagara ɗaukewa,wani irin hargitsi nake ganowa a
cikin idon da babu ɗigon salama a cikinsu,raina banda kuwwar neman tsira babu
abinda yake.
Wata ƴar jarumtace ta gifta mun,wacce tasakani saurin ɗauke idona daga cikin
nasa,wayyo nasan shikenan sai ya yanka ni,wayyo wayyo shikenan ya kamani ina
kallonsa,nasan irin wadannan mutanen kuwa basaso a kallesu shikenan tawa ta ƙare.
"Sumaimah kingani yaronsa Tunga yana tahowa nan wajen,kuma da alama wajenki
zaizo,dan ke yake kallo wlh".
Meee shikenan ta faru ta ƙare,indo ke tauraro mai wutsiya ce,bakya faɗan abin
alkhairi.
Zuwa zayyi ya fizgeni yakaini wajensa,nima ya yankamin hanjin ciki kaman wancan
mutumin.
Da ƙasan ido nake kallon wanda aka ƙira da Tunga ɗin,kuma dagaske inda nake yake
nufowa babu makawa........

Littafi na ɗaya ne dana biyu kaman yanda na sabayi,na ɗaya bati siddan,na biyu kuma
Naira 300 ne dan haka zaka iya biya tun yanzu kafin a shiga kashi na biyu.

3131951977
Auwal Sadiya
First bank

Ko katin mtn ta nan


09035784150

VTU ta nan
2347068390570

Ƴan niger ku tuntubi wanann number.


+227 97 21 16 15
----------------------------------------------------

Sadi-sakhan ceh
09035784150
Share please

*SANADIN CACA*

Mallakar SADI-SAKHNA

PROFICIENT WRITER ASSOCIATION

*USERNAMES*
FACEBOOK PAGE:Sadisakhna
WATTPAD:@SAKHNA03
AREWABOOKS:@sadeesakhna
PHONE NO:09035784150
________________________________
*Book 1*
Chp[06]

[Goje a mahangar gani]

Kwanannan ban san mai yake damuna ba,amma baƙinciki nakeji a cikin raina,duk yanda
zanyi shaye shaye bana jin zafin zuciyata yana sauƙata,raina jini yake so na dunga
ɗauka a koda yaushe. Hakan yake raɗamin a kowanne lokaci.
Yanzuma wannan mayaudariin daba maganinsa nayi ba yau bazanyi bacci ba,mutane gani
suke kaman shune na dayayi shine yasaka na yanke masa hanji ,basu san shiɗin muna
fikin ƴan fashin makwantanmu ne ba.
Zanyi fashi zan ɗau jini a garinnan,amma bazan bar wani daban yazo ya kafa tasa
kujerar ba,saboda wannan garin nikaɗai ne,idan ba goje ba to kuwa ba kowa.
Duba inda nake tara dattin tabar hannun nayi,abin ya ban mamaki danaga na tara har
kusan kwarkwaro bakwai,da duk yanayin danakeji daga na shata nakeji ya sauƙa,amma
yanzu baya sauƙa sai nasha dayawa tukunna..
Magana naji Ragarus yanayi,banji abinda yace da farko ba,iya ƙarshen kawai na kama.
".......itace fah wacce ogah zai aura wani satin"
Inda idonsu yake kallo nima nakai nawa idon,da wata farar yarinya na haɗa ido. Abin
yabani mamaki yanda ta tsaida idonnata cikin nawa,dukkuwa da yanda nau'ikan tsoro
suka bayyana akan ruhinta. Ban ɗauke nawa idon ba,dama abune da bana tunanin na
tabayi wa wani a rayuwata,wato ɗauke ido,bansan wata abu wai ita kunya ko tsoro
ba,wannan abubuwa banida su a halittata..
Ɗauke idonnata tayi tana diriri,kaman an kama munafuki,haka kawai sainaji dabani
dariyah,kana ganinta kasan tsoro ya cikata da haɗa idon da mukayi.
"Ogah barina je na siyo maka abinci a wajenta,kaga saikaji ma ko yana da daɗin da
inta dafa zaka iya ci,ko ya kace"
"Zancen banza kenan kaidai kawai kace bari kaje kasamu damar yi mata magana kuma ta
zubamaka na bati,kafi kowa kuma sanin banason raini. Dan haka idan kaje karma ka
ambaci sunana a wajen"
Juyawa nayi na cigaba da tunanin dayake cikin kaina.
Inaji yana mayar masu yanda sukayi da ita,wai daya tambaya daƙyar ta faɗamasa
sunanta saboda tsoro.
"Sumaimah"
Na maimaita a raina danaji ya faɗa,hmmm ina tausaya mata inta shiga shirgina,indai
zata kama kanta to babu ruwana da itah.

Ƙarar jiniya naji na ƴan sanda,ina jin su Tunga suka tashi tsaye,so suke nace musu
mu tafi kaman koyaushe,saidai yanda na jingina da jikin katangar banason na tashi.
Muryar DSP ce ta ziyarci dodon kunnena,hakanne yasaka ni dagowa na kalleshi.
"Goje abubuwan da kake a garinnan kare bazai ciba,dan haka ka biyomu ofishimmu
yanzunnan kaida yaranka,dolene ka fuskanci hukunci,sannann kuma ka biya tarar
mutumin daka buɗewa ciki. Babu wanda yafi ƙarfin doka duk shu'umancin sa"
"Hannu ɗayane kawai ya soka masa wuƙa,kuma wannan hannun na gojene,dan haka a
dokance iya gojene zai biku kawai koh,don haka muje.
Kai Tunga ko zata mutu ko kuma tayi rai to a ƙaddamar,in kunji lafiya ku sama ta
gora kawai"

Murmushi nayi lokacin dana shiga motsar ƴan sandan,idon DSP yayi zuru zuru,da alama
ya ankare da saƙon dana aikawa su Tunga.
Kishingiɗa nayi a cikin mota kafin a isa,har bacci ya fara ɗaukata.Duk daren
duniyata yanda naga ranar haka nake ganin daren,musamman ma idan na taimaki
wani,kokuma wani yayimin abu ban ramaba,narasa mai yasa nake haka,shin kowa haka
yake ko kuma ni kaɗaine tawa halittar daban.
Amma yau kam tunda nayi abinda rannawa yakeso to da alamar zan iya samun bacci.
Saida naji motar ta tsaya kafin na tashi zaune,dama bacci nake so nayi inda
wadancan yaran bazasu takuramin ba,haka ma inna a gida,tunda zan kwana a wajen sai
nayi ta bacci babu wani shedule a kaina.
Suna buɗe bayan motar na nufi ɗakin danake zama idan na biyosu,babu wanda yafi doka
injisu da faɗa,to gashi na kawo kaina amin hukunci.
Maganar DSP naji yana yiwa wani ɗan sanda da muke tafiya tareda shi,hmmm su gama
abinsu ma,daga ƙungiyar BC(black cobra) sun dawo gobe da yarjenjyata ta shiga
ƙungiyarsu,to bazasu sake gani na ba ma,nasan zuwa lokacin nafi ƙarfin wannan
kurkunnasu,duk da yanzu ma zancen manyan garine yasaka nake biyosu,amma wannan
shine na ƙarshe,shiyasa nazo nayiwa wajen bankwana.
"Kai copur wannan abinda ake yi masa ya ƙare daga yau,ku kaishi cell ɗin da ake
saka mai laifi irinnasa,sannann gobe a miƙashi ga kotu,dan ƴan uwan wanda ya sokawa
wuƙa sune suka kawo ƙara,kuma sunce kotu zasu kai ƙarar"
Da nayi niyyar na ƙyalleshi na wuce,saidai kuma zuciyata bazata iya ba,in ba
gargaɗi nayi masa to bazanyi baccin danake mararin yi ɗin bama
Dawowa nayi da baya har zuwa inda yake tsaye,da wani tulelen cikinsa a cikin
rigarsa,an bubbunka haram ciki ya nuna alama.
"DSP sambo in kana cin ƙasa kasani ka kiyayi ta shuri,babu ruwana da wata ƙara
dazasu kai,abune ya haɗani dashi shiyasa nayi masa hukunci,da kunsan abinda yake
muku a garinnaku ma da godiya zaku min.
Sannan da kake wani tada ƙayar baya nasan biyanka kuɗi sukayi koh? In mutum yasamu
kuɗi kuma iyalansa yake tunkara dashi. To in kanaso suci wannan kuɗin cikin
lumana,ƙaramin yaronnan ya dunga zuwa makaranta da ƙafafunsa,sannan wannan ta gidan
kar ta haihu lokacin ta bayyi ba.
Shi dana sokeshi ya rayu bari muga in muka mata tiyatar cikinta zata rayu?....."
Cikin sigar jan kunne na ƙarisa maganar ina jaddada masa gargaɗinnawa da
idanuna,aikuwa hakan yayi aiki,dan lokaci ɗaya gumin tashin hankali ya lullube
jikinsa sharkaff..
Bansake bi takansa ba na nufi ɗakin dana ke sauƙa innazo,har copur ɗin ya buɗemin
ƙofah.
Ai wannan mutumin dan basu san sharrinsa bane da kuma makircin daya haɗamin harma
da garin gabaɗaya,dana kasheshi ma da sai hakan yafimin daɗi.wawaye duk a zatonsu
harda ni a lalatacciyar satar da aka yi musu,sun raina aikina ma da alama.
Mutum yayi sata a garinnan ko ya kwashi tsiya,inda ma kajine ko akuyah idan za'ayi
gashi da sauƙi,amma kuɗi kan basuda wannan arziƙin..
Ina nan kwance akan katifar ɗakin har bacci ya ɗaukeni.

__***__

Tarin bola ce tsiri guda kaman zata dabo sama,da alama duk faɗin birnin garin anan
suke tara tarkashen sharar.
A can cikin bolar saika kula ga hango motsin mutane ledodi sun lullubesu,suna nan
kwance har yanzu basu tashi daga suma ko baccin wahala ba.
Malam audu ne yafara buɗe idonsa tareda ture ledar da take kansa,waya sani ma kota
kashi ce.
Tashi yayi daƙyar ya zauna yana nishi,saboda tsamin da jikinsa yayi.
Gabas ya kalla kana da yamma,mai kuma suke a tsakiyar bola da ranar Allah.
Zaro ido yayi lokacin daya tuno izayar da suka sha a jiya a gidan dasuke aikin.
Gefensa ya kalla inda gaji ke kwance shame shame akan wasu tsummokara,saikace
mahaukaciyah.
Ƙoƙartawa yayi yakai hannunsa ya kwaɗa mata duka a kunkuminta,aikuwa ta saki
azababben ihu tana wangale baki.
"Wayyo wayyo kunkumina ku taimakeni jama'a zai cire"
"Ke dallah tashi mubar wajennan idan zamu iya tashi,waɗancan dangin fir'aunan bayan
gari suka kawomu cikin bola"
"Bola kuma wacce iri"
Itama ta yunƙura tana kallon tsummokaran da take kai"
Motsin Atika da sukaji a gefensu ne ya sakasu waiwayawa,kuma gaji ta fasa faɗin
abinda yazo bakinta.
Kuka take tanan kururuwa kaman a cikin bacci,da alama abinda yafaru jiyanne yake
dawo mata.
Jijjigata gaji tayi cikin baƙin ciki,dan koma mai yafaru ai ita ta jawo musu,da
yanzu sun gama aikace aikacen gidan suna karyawa da lafiyayyen abinci.
"Shegiyar yarinya mai ɗuwawun bin maza,ai gashinan abinda kika jawo mata,in sonsa
kike tun farko da ki faɗamin mana asan surkullen da za'ayi,amma daga ke har
ubannaki dayake garorine ku kagu jimanaye kunga kuɗi,sai karba kawai kuke bakwa
tunanin mai ya faru. Ban tashi sanin mai yake faruwa ba sai ranar dazan sha duka
tukunna.
Sai ku tashi mu tafi ai .......ahhh......."
Shuru tayi tana jujjuya kunkumi,dan dama sojan kunkuminnata yayi ta sambaɗawa
kulƙensa.
Hararar malam audu tayi dayayi mata sannu,yunƙurawa tayi ta shi kana ta tashi
sauran yaran wanda suke baccinsu hankali kwance.
Bayan sun tashi a wajen tafiya suka farayi zuwa tasha,kowa sai komaɗewa yake yana
tafi kaman horon cikin film ɗin mayu.
Duk inda suka wuce kallon su ake,amma ko a jikinsu,tsamin da ƙashushuwansu suke ma
ya isa.
Sa'ar da sukayi daga inda suka zubar dasu bashida nisa da tasha,saidai kuma ba a
nan gizo yake saƙar ba kuɗin motar komawa garinnasu ne aiki.
Tun safe suke tashar har yamma,ganin bazasu samu mota ba yasa suka samu wani waje a
tashar suka zauna.
Hayam hayam kowa sai baza hamma yake kaman zaici babu,idonsu yayi zuru.
"Yanzu kana gani zamu mutu bazaka nemo mana abinda zamuci ba,huhulahu kawai"
"Wai nikam gaji meyasa tunda kika shi a cikin bolar nan ni kike sauƙewa tujara,ya
isheki fah haka,wlh zan sake mangareki ba ruwana da ciwukan da suke jikinka"
"Hehehe to ko sun duka ƙwalƙwalwarka ne take faɗa maka zaka iya dukana
iyeee,kalleka fah kaima a doddoken kake ba iya ni kaɗai ba,ƴan ƙafafunka ma daƙyar
kake ɗagasu sai kace lagwani. Kaff danginku haka kuke sai kace ƴaƴan kunika,zama
dakai yasa duk ƴaƴana haka suke ƙafafu kaman liƙo cikin kuwa kaman randa,ni ba
abinna zagesu ba kaima haka kake. Shiyasa nake mamakin ya akayi goje yakeda ƙira da
ƙarfi,ubansa da uwarsa ba haka suke ba,har Addu'a nake ko ƴaƴana zasu iyoshi,na
huta da aikin kashinsu da yawa,yaro in ka haifeshi bazayyi tafiya ba sai ya shekara
uku tukunna wani abin ma..........."
"Dan Allah gaji kiyi shuru haka,dan Allah ku bar faɗannan sai munje gida,kowa sai
kallon ku yake"
Kaman tayiwa dutsi magana ko kallonta basuyi ba,wata harara malam audu ke yiwa gaji
kaman idonsa ya fito,dan yaji zafin wannan wankin babban bargon da tayi masa a
tasha.
"Hmmm ke yanzu har zakice ma danasanin aure na kikeyi,daɗinta ma mu gidanmu ba mayu
bane bama tanɗe kuruwar mutane,kowa yayiwa wannan ubannaki shaidar ko tsuntsune ya
gifta da kan gidanku sai ya tanɗe kuruwarsa. Bandama ƙaddara data haɗani take,kaff
abokaina da ƴan uwana babu wanda yayi na'am da aure na dake,nima kaina bansaniba ko
tanɗeni kikayi"
"Hhhhhh narasa mai zan tanɗa inma maitarce sai kuruwarka,ko ban tanɗe ta bama a
tanɗen take,dan daga ganinka yanda kake haka ma kuruwar taka take"
Tashi atika tayi tabar wajen,kowa sai kallonsu yake amma su babu ruwansu,ina
zatakai wannan abin kunyar,wai dama haka auren yakene,kowa na ganin hanjin
kowa,shiyasa fah ta tsani aurenma ita a rayuwarta,tafiso kawai a hole in holewar
tazo a wuce wajen.
Tana cikin tunaninne taji muryar wani ɗan garinsu. Juyowa tayi suka haɗa ido da
tasi'u,shima da yace yana sonta,kayan gwari yake kawowa daga garinnasu zuwa
nan,dama sana'arsa kenan.
"Lahhh tasi'u kaine"
"Ehh nine atika mai kike anan wajen ga jikinki duk ciwo?"
Inda inda tafara na ƙaryar dazata yimasa,can kuwa wani abu ya faɗo mata a rai.
"Uhmm dama gida zamu tafi to shine jiya barayi suka shiga mana gida,bayan sun ƙwace
komai kuma suka yimana duka"
"Innalillahi garin ya haka,in su malam ɗin suke,dama tafiya gida zanyi ko zakuzo mu
tafi kawai,saidai zamuyi dare a hanya saboda motar tawa batada gudu"
"Babu komai hakanma mun gode,barina ƙirasu toh"
Wajen iyayennata ta koma,zuwa yanzu sun daina faɗan kowa ya karyar da kai yana
nishi na wahala da yunwa.
Lokacin data faɗamusu yanda sukayi da tasi'un ba ƙaramin murna sukayi ba.
Biredi ya siya musu da zobo irinna ɗurawar nan ganin sun fita hayyacinsu.
Kaman almajirai kuwa haka suke turawa a cikinsu,kowa so yake yayi maganin yunwarsa.
Banda ruwan albarka babu abinda suke masa,kaman basune sukayi masa cin mutunci ba
dayace neman auren atika,a ganinsu shi ba sa'anta bane,yanzu gashinan babu kunya
suke masa godiya daya taimakesu.
(Shiyasa a duniya ba'a son kaci mutuncin mutum ko ya yake kuwa,saboda Allah ne
kaɗai yasan ranar da zai maka rana,a lokacin da bakayi tsammani ba. Allah yasa mu
dace dai.)
Daff da magriba suka kamo hanyar garinnasu,tunda suka tafi wata shida sai yau zasu
koma,dama ance in daɗi bai kawoka gida ba wuya ai zata kawo ka.
Shuru sukayi a cikin bodin motar a tsakiyar kayan miyan da bai siyar ba,sai wulla
ido suke,ga motar batada gudu ko kaɗan,ko yaushe zasu isa oho.
Kaman a sama sukaji muryar tasi'un yana tashinsu,abin kunya sunyi bacci duk sunyi
rugu rugu da tumatir ɗinsa,wani abinma hadda taruhu da tattasai,gasu da ɗanyen ciwo
a jikinsu.
Banda mutsu mutsu da nishin azaba babu abinda suke.
Motar ba wani tudu bane da ita,amma saida sukayi dagaske kafin suka iyah fitowa,ko
tsayawa yimasa kyakykyawar godiya basuyi ba suka shige gida,dan basa cikin
hankalinsu.
Lokacin gari duru duru yake ana shirin ƙiran assalatu.
Inna mairo ta fito da butarta zata shiga banɗaki sai ganin mutane tayi sun shigo
gidan,salati tafara jiki yakama karkarwa,dan tayi zaton gamo tayi,saikuma ta kula
ashe su gaji ne
"Gaji kuma?"
Tafaɗa cikeda mamaki.

Littafi na ɗaya ne dana biyu kaman yanda na sabayi,na ɗaya bati siddan,na biyu kuma
Naira 300 ne dan haka zaka iya biya tun yanzu kafin a shiga kashi na biyu.

3131951977
Auwal Sadiya
First bank

Ko katin mtn ta nan


09035784150

VTU ta nan
2347068390570

Ƴan niger ku tuntubi wanann number.


+227 97 21 16 15
----------------------------------------------------
Sadi-sakhan ceh
09035784150
Share please

*SANADIN CACA*

Mallakar SADI-SAKHNA

PROFICIENT WRITER ASSOCIATION

*USERNAMES*
FACEBOOK PAGE:Sadisakhna
WATTPAD:@SAKHNA03
AREWABOOKS:@sadeesakhna
PHONE NO:09035784150
________________________________
*Book 1*
Chp[07]

Butar hannunta ta ajiye tana kallonsu,sune kuma da gaske,tayiwa kanta wannan


tambayar.
"Gaji kune da asubar nan haka,mai ya faru kukayi wujiga wujiga haka?"
Bude baki tayi zatai magana ƴar ta ƙarama ta rigata,tunda su ba ciwo a jikinsu.
"Yaya ce tayi soyayya da Alhaji,shine wasu sojoji sukayiwa su baba duka suka
jefarmu a bola"
Kunya ce takama su kaman zasu nutse a wajen.
Saurin wayancewa inna mairo tayi,musamman ganin yanda gaji ke kallon ƴar tata
farida kaman zata cinyeta ɗanye.
"Ohh to Allah ya tsare gaba,yanzu kuzo ku zauna,barina fito daga banɗaki na
haɗamuku ruwan wanka kuyi mamatsa jikinku."
Cije baki gaji tayi,so take tayi magana amma kuma tana tsoron kar inna mairo ta
hana su ruwan kaman yanda tayi niyya.
Kafin gari ya waye duk sun wanke jikimsu sun sanja kaya wanda inna mairo ta ɗauko
musu a sashennasu,dan ko ɗakinta basu bariba tun asubar,bare su taka cikin gidan
suga mai ya sauyah.
A daren tayi musu abinci mai sauƙi sukaci,hankalinsu ya dawo kansu.
Da safe kuma tasiyo musu burofen da masu shago suka buɗe.

Gaji ce tafito daga ɗakin tana kallon gidan,babu abinda ya sauya a cikinsa,saima
fess da yayi kaman bashine sansanin shirgi ba lokacin da suke nan. Ƙofarsu ta nufah
domin taga mai ya sauya,tun kafin ta ƙarisa tajiyo kukan saniya,abinne yabata
mamaki,saniya kuma a ƙofarsu?.
Turus tayi ganin kewayen ƙofar tata cikeda abincin saniyar da kuma kashinta,wajen
sai kace kewayen dabbobi.
Cije baki tayi tareda ƙiran sunan goje da ƙarfi har ƙasan maƙoshinta.
"Gojeeeeeee!!!"
"Na'am"
Taji ya amsa a bayanta.
Wani dum ƙirjinta ya doka saboda firgici,dan batayi tsammani yana gidan ba kuma ya
jita,tafaɗa ne kawai yanda zuciyarta tafara tafasa.
"Miye kike ƙwalamin wannan ƙiran kaman zaki ƙare min suna daga dawowarki iyeee"
Diriricewa tayi tana inda inda,in a lokacin bayane zata iya maida masa magana,amma
yanzu gani tayi gabaɗaya ya sauya mata,jikinsa ya sake murɗewa,gashin bakinsa sun
sake tsayi,ga wani uban tabon yankan wuƙa a dantsensa na dama. Ji tayi kaman wani
jaki yana tunkarota"
"Uhm dama dama bakomai bane,kawai gani nayi ka maida mana ƙofar kamar kewayen
dabbobi daga tafiyarmu"
"To wa yace ku tafi ɗin,sanda kuke nan na tasheku na saka ta ne,ina saida kuka tafi
yawon maularku tukunna,kunje kun saida musu hali sun koroku rana tsaka,mutane sun
zaman zamansu zaku dawo ku damesu. In nan ba inda zanje kuma ban sanja ba,duk wanda
ya damu mutane ko ya nemi neman rigima,saina yanke masa wata gaba ta jikinsa,daga
ke har mijinnaki da kuma tarin tsiyar ƴaƴan ku"
Muryar inna mairo yaji,hakanne ya tsaya da yiwa gaji tatass wacce take gabansa,tana
jinsa amma babu dama ta rama sai yace zai bugeta kokuma yasaka ta a kewayen
karnukansa.
"Kai goje kaine fah bakada gaskiya anan wajen,saboda kai kasaka musu dabba a
ƙofarsu,sannu kuma tayi magana kace ba madu ba bukar. Kaje ka sunce saniyarka ka
maidata inda take da,wato gefen ƙofar ka,ni banga mai zakayi da saniya ba ma"
"Kyauta tace ta farko dana samu sanadin ƙarfina da ƙwazo nah,idan na ganta tana
tunamin dani jarumine,dan haka babu inda zan kaita anan zata zauna a gidannan.
Tunda kinyi magana zan turo Ragarus ya ɗauketa a wajen"
Cikin tafiya ta izzah ya nufi hanyar waje,wani baƙin kare yana binsa a baya..
Sai bayan ya fice tukunna gaji ta saki wani numfashi data riƙe tun ɗazu.
"Uhhh nina manta ma da wannan basamujen yana gidan,gabaɗaya mutum sai murɗewa yake
kaman wani dodo...abinnan yana cimin tuwo a ƙwaryah,kaf cikin yarana babu wanda
yake ɗaga cikin plastic na ruwa saboda lalaci,amma shi kalleshi har tanki ma zai
iya ɗauka. Narasa mai yakika yimasa yana yaro ya zama haka,kaima da ka sani ai da
kayiwa yaranka,waɗannan masu kama da agwagin"
Oh gaji har yanzu kina nan da ɗabi'arki ta zagin ƴaƴan ki,koma dai ya suke ai sune
naki,kuma su Allah yabaki"
"Ehh zakice haka man saboda naki jarumine,nawa kuwa ƴaƴan nasan in kinshiga ɗaki
dariya kike musu,kin gansu kaman buta"
Kasa riƙe dariyar ta inna mairo tayi,wanda hakan ya ƙara ƙular da gaji tazo har
wuyah.
"Kinga ya isa haka ni bazan biyeki ba,kujira yaxo ya daukemuku saniyar ku gyara
muhallinku ku koma"
"Mee kashin saniyar tasa na wata da watanni mu zamu gyara masa,zancen banza ma
kenan,jakunan ku kuka maidamu keda shi komai,yanda kuke da iko da gidannan fah muma
haka mukeda iko dashi"
Jijjiga kai inna Mairo tayi cikeda takaici,ta dawo ai za'a cigaba daga inda aka
tsayah.
"Nina fara gajiyah da mitarki gaji,in sun dauke saniyar ku jirashi yazo ya gyara
muku wajen,kuce sai ya tattare kashin tunda saniyarsa ce tayi"
Yawu gaji ta haɗiye muƙutt,saboda tasan inna Mairo gatse tayi mata,hakan bazai taba
faruwa ba.

__***__

A zaune take a gaban wuta ta haɗa gumi sharkaff tana suyar awara,gabadaya
hankalinta yana wajen,buƙatar ta ta gama soye uban taragon awarar dayake gabanta.
Dama sana'arta ce tun tale-tale kowa yasan ta da ita.
Atika ce ta shigo ƙofar da sauri daga wajen inna Mairo take,kana ganin yanda take
zumuɗi kasan gulma ce take cinta a rai.
Ɗaga kai gaji tayi ta kalleta tareda mikamata wata awarar wacce ta suyah.
"Hungo dan Allah atika zubawa farida Ta ɗari biyu ta kaiwa wani a waje,sannan kema
kizo ki kintsa ki tafi wajen tallen ki,kuma maza ki hanzarta kada a gama siyan na
kowa a bar naki yayi kwantai mana. Kince nayi miki da ƙwai nayi miki,amma tun ɗazu
sai yada kai kike kinƙi tafiyah"
"Ohh gaji zan tafi dai,yaushe ma ranar tayine wai,wani abu fah nazo dashi nake son
na faɗamiki. Wai kiji ashe Goje aure zayyi?"
Tsayawa ta juya awarar tayi tareda juyowa tana kallon Atika,alamu duk sun nuna bata
yarda da abinda tace ɗin ba"
"Ke bana son ƙarya,kaff garinnan wacece zata auri wannan dodon,in zakiyi ƙarya ma
kiyi wacce kunne zai yarda da ita"
"Wlh gaji da gaske nake,kuma gobe nema ɗaurin auren,gashinan inna Mairo ta gyara
ƙofar gojen,kuma yanzunan aka kawo mata saƙo,kayane a ciki sabi na mata ta siyah
wai na Amaryar ne"
"Ke ƴar nan,ƴar gidan wanne shashan ubanne zai bawa goje ƴar sa,kalan ya danneta
sai ƴaƴan hanjinta sun fito nan take?"
"Uhm ai bakiji ma abinda naji bane jiya a wajen talle,har nunamin itama akayi,gata
kyakykyawa da itah,ƴar gidan Mijin su inna rammah ce fah ƙawarki,wai a wajen caca
dasukayi da goje ya cinyeshi,shine da bashida kuɗi yabashi ita"
Sakin baki gaji tayi tana kallon atika kaman ta samu TV.
"Duk yaushe haka ta faru a garin bansani ba uhm,barina gama suyar awarar nan zanje
gidan naji komai ai"
"Ko kuma ki bari sai da daddare ba,kinga babu wanda zaisan kinje,ni labarin naji
wai ƙawar indo ce ma nan maƙwantanmu"
"Wai tagamu da ƙaddara,muma da muke gida ɗaya dashi muke ganin takanmu balle ita
mai zama dashi? Amma kuwa Mairo bata kyauta ba,duk ana wanann zancen bata faɗawa
malam ba,saboda sun rainashi basa ganinsa a uban goje koh? Bari kuwa ya dawo da
faɗamasa yanda ake ciki,duk wacce za'ayi ma ayi"
Tafaɗa tana cigaba da suyar ta.

___***___

[Sumaimah a mahangar gani]

A zaune nake ina tilawar qur'ani,yau wacce rana banje talle ba,tunda akayi auren
masu zuwa tallen ban taba fashi ba sai yau.
Ban san na saba da zuwan tallen ba sai yau,dan jina nake duk wani iri tun safe,na
rasa ma mai zanyi a gidan.
Abinci dama banice nakeyi ba su suke kayansu,iya abincin siyarwar ammi kawai nake
sai shara da kuma wanke wanke wani lokacin,saboda duk mai abinci burinta ta gama ta
kwasa da yawa itada ƴaƴan ta. Wannan mummunar al'adar dasu ce yasa na huta kokuma
nace na tsira daga yi musu girki.
Bayan nagama karatun shuru nayi ina tunani,inason yin karatu mai zurfi,amma nasan
hakan bazai taba yiyuwa ba,musamman ta muka taso a gidan da babu wanda ya damu da
wani abu wai shi ilimi.
Alamar takun sawun mutum naji,hakanne yasa na buɗe idona,Asiyah ce a tsaye akaina
tana min kallon marar daraja.
"Wai kizo inji ammi tana nemanki"
Kawar da idona nayi akan ta tareda cewa.
"Kice ganinan zuwa"
Bata sake cewa komai ba tabar wajen,tafiyar ta bani da kallo,bansan lokacin da
dariyah da kubcemin ba. Tafiya take tana turo kunkumi baya,ƙirji kuma gaba,wanda
yake kaman allo babu komai a jikinsa,dan ko ƙirgen danginma bata fara tukunna.
Hmm nace a raina tareda cewa....'in kikayi haƙuri ma nono kam zai fito miki har ki
rasa yanda zakiyi dashi indai kinyi gado. Dan ammi Allah yayi mata arziƙin nono har
cinyarta suke tabawa,inda tanada ƙiba da za'ayi mutanennan ne masu nonon su yafi
girman ɗansu idan suka haihu,amma kasancewar rayuwar tada tsinci kanta sai yazaman
basuda girman sai tsayi,in bata saka riga ba sai suyita rito kaman igiya....
Kunkumine dai da ƙyar ki samu,dan kaff ƴan ɗakinnasu a shafe suke ta baya.
Kawar da wannan marar amfanin tunanin nayi na tashi zuwa wajen ƙiran da akayi min.
Yanzu nagama kuwa tunanin yanda take,ina shiga ɗakin da ɗaurin zani a kunkumi na
sameta,tana goge tsakar daƙin dan ba laifi tanada ƴar tsafta,shiyasa nake sallah a
ɗakinnata da rana hankalina kwance.
"Ammi gani,Asiyah tace kina ƙirana"
Ɗagowa tayi ta kalleni saikuma tace.
"Ohhh ehh haka,zauna barina gama wannan goge gogen tukunna,ai takaicinnan ya
isheni,ace bakada ƙaramin yaro,amma ko yaushe kana cikin goge fitsarin yaran wasu
can"
Ban tofah komai ba a cikin sababin da takeyi,sai zama kawai danayi ina jiran ta
kaman yanda tace.
Bayan ta gama wata leda ta miƙomin baƙa da kaya ciki.
Mamaki ne ya cikani,ban yi ƙasa a gwiwa ba na tambayeta.
"Ammi wannan kuma na menene"
"Mairo ce ta kawo ɗazu wai kayanki ne"
"Mairo kuma...."
"Innar goje"
Tayi saurin katseni,dan tasan konayi nazari akan sunan bazan ganota ba. Saurin a
jiye kayan nayi kaman wanda suka ƙona ni,kuma hakane ƙona ni sukayi a zuciyata.
Hannu na ɗora akan ƙirjina ina ƙoƙarin hana zuciyata fitowa daga cikin
ƙirjinnawa,dan naga kaman hakan take ƙoƙarin yi.
"Sumaimah yakamata zuwa yanzu kin fara kwantar da hankalinki,domin razanar da kike
ko shiga ƙunci bashi zai hana a fasa ba,koda an fasa kaiki gidan goje to babanku
bazai iya biyan kuɗin dayake binsa ba,karki manta in akwai kuɗin goje a wajenka to
duk bayan wani lokaci ƙaruwa yake har sai sanda ka biyashi,in kuwa kaki biyansa to
ranka yake ɗauka a matsayin kuɗinsa. Kinga kuwa in kinga an fasa aurennan to saidai
ya ɗauki ran sa kenan a matsayin kuɗinsa,shin zaki iya zuba ido ya kashe mahaifinki
ne kina ganin kuma zaki iya cetonsa?"
Shuru nayi ina saurarenta,zancenta gaskiya ne duk da kuwa ina jiyo son kai a
cikinsa,da ƴar ta ce za'a kai gidan goje bazata bari ba,saidai uban kowa ma ya mutu
a gidan. Amma ni ji yanda take zaromin bayani dallah dallah saboda na amince,tafi
kowa sanin kuma inna shiga gidan nima bazan fito da rai ba a hannunsa,saidai kuma
ya zanyi dama kullum amfani ake da sanyin rai na da kuma karayar zuciya ta,ga kuma
bugu da ƙari banida gatan dazai tsayamin a wannan cutarwar da ake shirin yimin.
Kaman yanda ta faɗa kuma bazan iyah guduwa ba ya kashe mahaifina,duk da baya yimin
abinda uba ke yiwa ƴaƴan sa,amma shiɗin mahaifina ne bazai kuma tashi daga wannan
matsayin ba har abada. Gashi kuma shikaɗai ya ragemin a duniyah,bansan ƴan uwan
mahaifiyata ba ko ɗaya,tun ba ƴar nan bace a yawon ci rani ya aurota,bayan yayi
mata ƙarya kala kala ta yarda ta biyoshi garinsu,duk da taga ba haka bane amma ta
zauna dashi,saidai mai hakan bai isaba saida matansa suka kasheta. Wannan zaluncin
har ina?
Kukane ya kubcemin wanda ammi take ganin na auren goje ne,amma va haka
bane,abubuwan da suka haɗu sukayimin yawa na shekara da shakeru nake son na rage
zafinsu da kukan.
Bata rarrasheni ba bata kuma hanani ba,saima tashi datayi tabani waje tana min
kallon tausayi,bazanga laifinta ba don tayimin iya ƙoƙarinta a matsayinta na
mariƙiyata,kuma ina yabama ta bazan taba mantawa da halaccinta ba har abada,koma
mai zanji tayimin a baya,matsayinta danake gani na mahaifiya bazai taba bacewa daga
kan idona ba.
Kayan na ɗauka cikin sanyin jiki na nufi ɗakinmu wanda zuwa gobe zan barshi na tafi
wata rayuwar,ban taba kawowa barin gidan a wannan lokacin ba,dudu zancen auren
bayyi sati ba da farawa,gashi gobene ɗaurashi uhmm rayuwa mutum yana nasa Allah ma
yana nasa..

Wayyo nikam har banaso gobe tayi na rubuta auren Sumaimah da goje,ku kanku kunsan
bata dace dashi ba kohhh........duk mai wata idea to muhaɗu a commen secition toh🤣
🤣🤣

Littafi na ɗaya ne dana biyu kaman yanda na sabayi,na ɗaya bati siddan,na biyu kuma
Naira 300 ne dan haka zaka iya biya tun yanzu kafin a shiga kashi na biyu.
3131951977
Auwal Sadiya
First bank

Ko katin mtn ta nan


09035784150

VTU ta nan
2347068390570

Shaida kuma ta nan


09035784150

Ƴan niger ku tuntubi wanann number.


+227 97 21 16 15
----------------------------------------------------

Sadi-sakhan ceh
09035784150
Share please

*SANADIN CACA*

Mallakar SADI-SAKHNA

PROFICIENT WRITER ASSOCIATION

*USERNAMES*
FACEBOOK PAGE:Sadisakhna
WATTPAD:@SAKHNA03
AREWABOOKS:@sadeesakhna
PHONE NO:09035784150
________________________________
*Book 1*
Chp[08]

Washagari da safe da sanyin jiki na tashi da kuma bacci,saboda jiya da daddare


vansan lokacin da baccin wahala ya ɗaukeni ba.
Hamma tayi tareda yin mika,uhm yanzu shikenan nagama kwanan gidanmu sai kuma na
kabari dazan tafi kwanannan koh.
Nafaɗa a raina..
Yunƙura nayi zan tashi sai naji ƙarar keda,kayan da ammi tavani jiya ne wai inji
innar goje,ni ma manta dasu sai yanzu,saboda lokacin data bani ko buɗewa banyi ba.
Ledar na kunce domin naga menene a ciki. Kaya ne kala uku,biyu riga da skirt ɗaya
kuma doguwar riga,dukkansu atampar roba ce amma sabi ne,saikuma hijabi ɗaya da kuma
takalmi na roba.
Duk da cewar nasan matsayin auren da kuma wa zan aura ɗin,amma banyi tsammanin haka
rayuwar aurena zata kasance ba,nayi zaton kodah bansamu kaman yanda nake tunani ba
amma dai zai fi haka,saidai kashsh tsugunne bata ƙare min ba,don da alama akwai
sauran rina a kaba.
Jikina na kalla bayan na ajiye kayan akan katifah ta,babu lalle babu kurkur irinna
amare dasuke,haka nake a koɗe kaman amaryar mutuwa.
Katifah ta nasake duba,ita ɗin ma ƴan matan gidanne suka gama da itah na karba,to
ko kuma a wacce zan cigaba da kwanciyah oho,koma tabarma ce duk Allah ne kaɗan
yasani. Dan banji kodah wasa wani yace an siyamin wani abun ba. Nice ma na bawa
indo ƙawata kuɗi ta siyamin kayan aikin gida,tunda daga nan gidansu babu nisa saita
kaimin idan suka kaini.
Guntun hawayen da bansan dalilin zubarsa ba na share kana na fita waje.
Da ubaidu nayi turuss a hanya zai shiga ƙofar mu. Wani tsayayyen kallo yayi min
kafin yace.
"Farar mace(yanda yaka ƙirana) ke kuma yanzu wannan gazagin zaki aura?.......wai ai
ta ƙaremiki farar mace danni ma lokacin daya sauƙemin allon kafaɗa na daɗe banyi
motsiba,wannan inaga ba mutum vane inaga"
"Kai menene haka ka tsayar ta kana ƙara rikirkitata bayan wanda take ciki,kaima ai
shirginsa ka shiga shiyasa yayi maka haka,idan tayi duk abinda yace indai ba shine
magajin fir'auna ba ai bazai yi mata komai ba. "
"Hmmm ammi zakice haka,to har aka gama abin ɗaura auren fah baya nan,ance ma wai
tun jiya yana jeji"
"Oh an ɗaura aurenne"
"Eh an ɗaura yanzu,wani ƙanin babansa ne yayi masa wali,mai anguwa ne yabada dubu
goma sadakin gojen"
"In kuɗin toh yake"
"Vaba ya karba,tacan ma ya wuce wai zaije ya siyo dawa dashi,dama jarinsa ya karye"
"Kutt wai nikam Baban yara ina zaije da wannan halinne,yarinyar nan ya bayarta
saboda abinda ya aikata,bai siya mata komai ba irin wanda uba ke yiwa ƴar sa,sannan
kuma bayan haka wani maga Allah yabada sadaki wanda haƙƙinta ne shima kuma ya
karbeshi?"
Cikeda takaici take magana,kanaji kasan ranta ya baci,itama kenan daba ita akayiwa
ba,inaga kuma ni,yazanji kenan.
Kallon su kawai nake a nutse,amma cikin raina a dagule yake.
Kallona ammi tayi da sigar rarrashi zatayi magana. Inaa banason wannna rarrashin da
babu abinda yake ƙaramin sai raunin zuciya,a barni kawai da daɗin bakinnan,lokaci
ne kuma daya kamata nayi jarumta,tareda tarar duk abinda yake shirin tunkarata.
Aurene burin kowa yacika an riga an ɗaura shikenan,Allah yabani ikon ɗaukar duk
abinda zai biyo baya. Dan haka saurin katseta nayi tun kafin tace wani abun.
"Bakomai ammi tunda an ɗaura auren zance ya ƙare,Allah yabani ikon cinye
jarrabawata"
Daga Min kai kawai tayi,da alama tausayina ne ya kamata,ni yanzu banason mutane
suna nunamin wannan tausayin ma,don ba komai zai kawomin ba bace karyar zuciya.
Shigesu nayi nakoma ɗakinmu don bansan mai zanyi a cikin gidna ba,babu wani taro
sosai har yanzu,da alama kosai yamma ƴaƴan gidan zasu zo.
Ban daɗe da shiga dakin ba najiyo sallamar indo itada shareefah,ita Shareefah
ƙawata ce ta hadda,ita kuma indo a wajen abinci muka haɗu da ita,dukkansu sunada
mutunci sosai,don sune ma masuyimin siyayyar dazan bukata,duk da nasan a yanwancin
abin sun Cikaminne da kuɗinsu,godiya nayi musu har bansan adadin ta ba.
Kaman yanda na faɗa kuwa sai wajen la'asar kafin mutane suka fara shigowa
gidan,inda tani za'a biye to bazan so kowa yazo ba,dan ba komai yake kawosu ba face
gulma da ganin ƙwaƙwaff.
Fitowa ta daga banɗaki kenan na iyo wanka,da cewa nayi ma bazanyi ba,Shareefah ce
ta tursasa min,ita kam indo inna ce shikenan,tunda aka fara zancennan koyaushe mita
take wai an cuceni,nice ma nake tarar numfashinta wani lokacin.
Murya Aisha naji tashigo gidan ƴar inna rammah suna gaisawa da matan gidan dasuke
tsakar gida.
Wani mai chemist take aure a can tsallekenmu Abdullahi,saurayine yayi
karatunsa,dani muka fara soyayya dashi muna haɗuwa dashi a hanyar makaranta,harna
fara sonsa kuwa saboda barkwancinsa,zuwansa gidannan na farko Aisha taɗora ido a
akansa. Nan duniya kuwa tace shi take so kaman zata mutu,ta shirya ƙarya da gaskiya
wai ai saurayinta ne nice na ƙwaceshi.
Ko ya akayi rana tsaka mun fara soyayya yace nan duniya aisha yake so,abinnan ya
ƙonamin rai har kwana nayi ina kuka. Haka ina gani akayi aurenta dashi waccar
shekarar,suna nan zaune itada shi,tana ma da yaron ciki.
Har yanzu wannan abin yana ƙonamin zuciya,musamman yanzu idan ya ganni yayi ta bani
haƙuri yana cewa ba laifinsa bane,duk da nasan ba laifinsa bane amma kuma yanda
yake tunanin muyi mutunci hakan bai kasance ba. Kowa a gidan yasan babu wanda yayi
wannan aikin sai inna rammah,amma haka aka zama makafi akan lamarin.
Ido muka hada da itah na kawar da kaina zan wuce.
"Amarya ykk,tun ɗazu naga kina ta kallona,kinga yanda na sanja nayi kyau koh,to ina
samun cima da kuma kulawa yanda ya kamata,tunda na auri mai hankali da nutsuwa,ba
ɗan daba mai suffar mahaukata ba"
Ɗan murmushi nayi mata,dan wlh har raina ta bani dariyah,wai fah ita a hakan dani
take.
"Mashaallah kam aisha kinyi kyau abinki ina miki murna,amma kuma nai hasken ciki
kika yi koh,jiki kuma dama haka na sanki baki ƙaru ba,inmiki fatan Allah ya raba,ni
barina tafi ko"
Na zaga ta gefenta na wuce,ita kanta tasani inaga mantawa tayi,inada sanyin rai
amma kuma bana ɗauka irin wannan maganar sam.
Duk inda na baza kunnena maganganu kawai nake ji suna shigomin,wasu na jijjiga kai
wasu kuma kawai na basar.
Su Shareefah sai baki suke bani,a tunanin su hakan yana damuna,basu san an shani na
warke ba.
Zuwa yanzu dare yafarayi,mutanen da suka zo kowa ya fara tafiyah gidansa.
Riga da skirt ɗin daya fi ɗan kyau a cikin kayan na saka,dan har an fara shirye
shiyen kaini gidana.
Ba laifi kayan yayi min kyau anyo masa ɗinkin zamani,kuma ya ɗan kama jikina kaɗan.
Bayan nasaka kayan hijabin na ɗauka na saka,ta gefen idona naga Shareefah sai
kallona take.
Kallonta nayi dauke da murmushin ƙarfin hali akan fuskata.
"Menene yafaru Shareefah kike kallona haka kaman wadda zan tafi inda bazamu sake
haɗuwa ba"
"Uhmm ba wai tafiyarki ne yasakani kallonki ba,abubuwane da yawa acikin kaina na
gameda yanda rayuwarki da sauyah Sumaimah,a islamiyyah kinfi kowa ilimi,haka ma a
makarantar safe da mukayi JSS,ke kikemana na daya,amma haka kika daina zuwa
makaranta lokaci ɗaya. Wlh banaso naga mace mai ilimi wacce take son cimma burinta
na ilimi kuma hakan bai faru ba. Inama munada ƙungiya masu irin wannan aikin,da sun
hana wannan aurennanku saboda cutarwa ne.
Amma kuma tunda ya riga ya faru yanzu abinda zakiyi shine yin abinda Allah yace a
gidan aurenki Sumaimah,wannan mutumin da muten ke ƙira da dodo kokuma ɗan
daba,kefah yanzu ya tashi daga wannan matsayin ya koma mijinki aljannarki kuma
duniyarki. Yanzu duk wata ragama na linazamin aurenki yana hannunki. Nasan kina
tsoro Sumaimah kuma bazan ce ki daina tsoronsa saboda nasan hakan abune mai
wuya,amma ki tuna abu ɗaya ke macece,kinada baiwa a matsayinki na ƴa mace. Duk
kwarjinin na miji da wuyar sha'ani kisa a ranki zaki iya dashi,in kikayi hakan sai
kiga komai ya tafi a tsari mai ma'ana"
Ƙirjina ne ya buga kana wasu hawaye masu ɗumi suka zubomin,tabbas idan da yana
matsayin ɗan daba a wajena to fah yanzu a matsayin mijina yake. Wannan wasu tarin
gaskiya ne masu zafi da kuma matuƙar ɗaci Shareefah ta tunamin,wanda kuma komai
zanyi hakan suke bazasu canja ba.
A sanyaye na gama shiryawar Ƙanwar babammu Baaba Ladi ta kamo hannuna muka fito..
Dan dama ita ke kai duk wata yarinya da akayi aurenta ɗakinta..
Bayan mun fita su indo ne suka biyo bayanmu muka fito daga ɗakin
Da ammi naci a karo a bakin ɗakin tana kallona.
Wani kukane naji ya ƙwacemin da bansan ta ina ya faro ba,idan nace babu shaƙuwa
tsakanina da ammin to nayi babbar karya,dan tun vanni da wayo na tashi na ganta,da
daɗi da babu daɗi dai haka ta riƙeni.
Cikin raunanniyar murya nace.
"Ammi .........."
Ban iya cewa komai ba dan babu kalmar dazata sake fitowa bayan wannan ɗin.
"Babu komai Sumaimah,ki daure aure dama shi yaƙin matane,kowacce mace da haka ta
girma,balle ke naki da kuma tsoro,dan haka saikin haɗa da haƙuri kinji...bazan samu
damar rakaki ɗakin ba dan haka kuje Allah ya ƙare yabada zaman lafiyah....saikuma a
yayyafi juna na abinda ya faru"
Ɗaga mata kai nayi kawai,dan narasa ma mai zance.
Hanyar waje muka nufah,baba kam tunda ya karbi sadaki na babu wanda ya sakashi a
idonsa,dan haka ba zancen yin sallama dashi,in yana nan ma mai zaice min,shiba
wa'azi sai min ba ko nasiha,dan in kura zatayi maganin zawo tafara daga kanta
tukunna.
A ƙafa muke tafiya shuru babu wanda yake cewa komai har muka isa anguwar su gojen.
Ohh ni Sumaimatu ina ganin rayuwa,aure a yanzu ko maƙwantanku ne sai anje da mota
an zagayo dakai. Amma ni ganida ƴan rakiyar da sayyadarmu mukazo. Kodayake ana ta
kai waya ke ta kaya na samu ma na tsira da raina da lafiyata.
Baaba ladi ce a gaba,itakuma tayi sallama da muka shiga gidan.
Muryar wata matace daga wata ƙofa ta amsa,kanajin hayaniyarta tun daga bakin ƙofar
gidan da yara. Da alama itace matar ƙanin babannasa,wai dagajin muryar ya kuwa
jarababbiyace,danni tsabar zama da masifaffu tun daga muryaru nake ganesu.
Iya amsa sallamar bai isheta ba saida tafito daga ƙofar tana riƙeda kunkumi a
gabanmu.ohh dama ba ramammiya bace yanda nake hasashenta,tanada ƴar ƙiba. Magana
tafara cikeda isa da gadara.
"Ohh amarya ce ta iso sannu zuwa,gashi ango kuwa tun jiya babu shi babu labarinsa.
Sunana gaji matar kawunsa nima nan uwarsa ce da........"
"Dan Allah gaji ya isa haka,yanzu suka shigo maimakon ki tarbesu kibasu wajen zama
kuma kin tsaya kina surutun da bashida amfani"
Yanzu wata dattijuwa ce tayi magana,wacce na tabbatar itace kenan innar goje kuma
surukata. Ita kam tanada kirki da kamala a ido sabanin matar data ƙira da kanta
Gaji. Indai haka innarsa take to albasa batayi halin ruwa ba. Koba komai naji daɗi
da innarsa ba masifaffiya bace..
Bin innar gojen mukayi zuwa ƙofarta bayan mun wuce gaji a tsaye tana mita.
Ruwa ta kawomana tareda yimana sannu dazuwa.
Gaisuwar mutunci sukayi da Baaba ladi,alamu ya nuna dama sunsan juna kenan..
Bamu daɗe da zama ba baaba ladi tace zasu tafi,yanda kuka san na jawo ta na zaunar
da ita haka naji.
Wasu hawaye ne suka fara zubomin ganin da gaske fah tafiya zasuyi su barni.
"Toh Mairo ga nan amana mun kawo miki na ƴar mu,don Allah a dunga duba zamannasu,mu
zamu tafi Allah ya kare tsautsayi"
"Ahh har zaku tafi daga zuwa,kuma bakuga ƙofar inda zata zauna ɗin ba"
Zaro ido nayi wacce ƙofar zan zauna,dama ba anan zan zauna ba a wajenta ɗakin
danake hangowa?
Innalillahi kaddai can wani gun za'a kaini wajensa,inda zaiji daɗin kasheni hankali
kwance koh"
"Ahah mukam zamu tafi,inyaso saiki rakata da kanki mairo"
"Lahh ya kusa dawowa ma da kun tsaya kun gaisa koh"
Dukkansu zarowa ido sukayi hardani wacce zan zauna dashi ɗin.
"Ahah mairo nikam tafiya zanyi,bansani ba ko su ƙawayennna ta zasu tayata zama
kafin yazo"
"Ahah"
Suka bada amsa a tare suna zare ido.
Yau na shigesu ni ɗiyad zinaru,haka zanyi rayuwa dashi ???
Ina gani babu kunya dukkansu suka shuri takalmansu zuwa gidansu a kwanciyar
hankali,nikuma inna mairo ta nufi ranaki ɗakin gogan.
Sai wasu kalamai take min da banajin abinda take faɗa.
Ƙofar a kewaye take da ginin bulo,ɗaki ɗayane sai banɗakinsa a gefe . Buɗe ɗakin
tayi muka shiga..
Babbar katifa ce a ƙasa sai akwatin kayansa,a dungun ɗakinɗakin akwai fankar ƙasa
da kuma wani tsohon rediyo.. Kana ganin ɗakin kasan da bahaka yake ba,gyara yasha
na wucin gadi.
Dan ga nan inda aka rurrufe shirgi a gefe.
A kan katifar tayimin nuni dana zauna.. Magana take cikin sanyin murya,amma kaman
mutum mutumi haka nake kallonta bana cewa uhmm bare uhmuhm. Kaba ɗaya raina ya fita
daga gangar jikina yaje wani gu ya buyah..
Bayan ta fita na daɗe a zauna hakan ban motsa ba,dan ji nake kaman in kan zare.
Can bayan wani lokaci nafara jin alamar sautin sawun mutum yana tahowa,zan iya
rantsuwa bana Inna bane,in kuwa banata bane to na waye.
"Na mutuwarki ne"
Wata murya wacce nasan ta ruhina ce ya raɗamin a cikin kunne nah.

Littafi na ɗaya ne dana biyu kaman yanda na sabayi,na ɗaya bati siddan,na biyu kuma
Naira 300 ne dan haka zaka iya biya tun yanzu kafin a shiga kashi na biyu.

3131951977
Auwal Sadiya
First bank

Ko katin mtn ta nan


09035784150

VTU ta nan
2347068390570

Shaida kuma ta nan


09035784150

Ƴan niger ku tuntubi wanann number.


+227 97 21 16 15
----------------------------------------------------

Sadi-sakhan ceh
09035784150
Share please

*SANADIN CACA*

Mallakar SADI-SAKHNA

PROFICIENT WRITER ASSOCIATION

*USERNAMES*
FACEBOOK PAGE:Sadisakhna
WATTPAD:@SAKHNA03
AREWABOOKS:@sadeesakhna
PHONE NO:09035784150
________________________________
*Book 1*
Chp[09]
Runtse idona nayi,bana ma son naga mai zai kasance.
Buɗe ƙyauren ɗakin yayi ya shigo,da farko bai kulada ni ba sai daya waiwayo tukunna
muka haɗa ido.
Kallon mamaki yake bina dashi,nasan bazai wuce nazari yake ba akan mai yakawoni
cikin ɗakinnasa..
"Keeee"
Ya faɗa cikin shaƙyƙyƙyiyar murya,wacce take ɗauke da gajiya da kuma takaici.
Shuru nayi ban amsa ba,dan banida wannan ƙarfin halin.
"Wai ba magana nake miki ba,ko ke kurmiya ce bakya magana?"
"Uh.....uhm... Iyee na'am"
"Me ya kawoki cikin ɗakina,duk filin dayake cikin gidannan ki rasa inda zakiyi
burki sai cikin ɗakina,mai kike nufi wai anan zaki zauna"
"Ahah dama inna....."
"Mtsww tashi ki fita ki bani waje,idan kuma kika sake na ƙara ganin ƙafafunki a
kusada sansani na......saina karya dukkan ƙasusuwan jikinki na babbakeki na ciyar
da su durwa"
Me wai ni irin wannnan kashedin haka..
Miƙewa nayi daga kan katifar ƙafafuna suna rawa,haka na jasu zuwa bakin ƙofar,ina
jin idanuwansa akan ƙeyata kaman zasu bula su shige,ban waiwaya ba harna fita daga
cikin ɗakin.
Tafiya nake kaman ina kan glass har na isa bakin ɗakin inna Mairo. Ƙwanƙwasa mata
nake a hankali harna fara da ƙarfi ganin bata buɗe ba.
Cikin muryar bacci tabude kofar tana kallona,nima kallonnata nake har sannan
hankalina bai gama kwanciya ba.
"Sumaimah lafiya kuma na ganki anan,gojen bai dawo bane koh......"
"Yadawo koroni yayi,yace idan na sake zuwa kusada ɗakinsa sai ya kasheni"
"Me kisa kuma wacce iri?"
"Dan Allah inna karki sake cewa ba koma,idan kika maidani zai kasheni nikam....."
"Kinga kwantar da hankalinki,shigo nan mu kwanta,idan gari ya waye saina ɗauko miki
kayanki a ƙofarsa,sanda komai ya daidai ta in yaso saiki koma"
Jinta kawai nake lokacin dana afka cikin ɗakinnata,dan dama abinda nakeso kenan
nakuwa samu,zama da ita daram ba ruwana da wani ɗakin goje,haka kawai ana miji miji
ya kasheka a banza..
Gado biyu ne a ɗakinnata,mai rumfa da kuma ƙarami na ƙarfe,shima akwai katifa akai
saidai ƙarama,tsayawa nayi inna kallon ɗakin na jiyo muryar innan.
"Ga nan gado saiki kwanta,da su Atika ne suka kwana a kai,to yanzu sun koma wajen
uwarsu tunda suka dawo. Sai ki dunga kwanciya anan kafin komai ya daidai..
Ɗaga mata kai kawai nayi banyi magana ba,ina jin haƙarƙarina akan katifa na saki
ajiyar zuciyah,koba komai iya yau kam ai na tsira.

[Goje a Mahangar Gani]

Dawowa ta kenan garin cikin darennan,kwana guda da yini bana nan ina can sansanin
ƙungiya BC sun gayyaceni na zama ɗaya daga cikin ƙungiyarsu. Tun wancan satin suka
turomin takardar gayyata,sannan basu yarda naje da kowa ba idan zanje
wajensu,saboda tsaro.
Fitinanniyar ƙungiya ce data addabi manyan ƙasa dama cibiyar binccike,saboda
ƙungiyar tayi ƙaurin suna wajen fashin manyan bankuna da kuma gidajen ƙusosin
ƙasa..
Kowa yasan labarinta da kuma irin aika aikarta,saidai babu wsnda yasan sunzo sun
buya a wannan ƙungurumin daji.
Abune mai wahala su ɗauki wani yazama ɗaya daga cikinsu,saidai idan sun bincika
sunga ehh ya cancanta.
Kamanni da labarin salona ya isa garesu,banida wani sha'awar shiga ƙungiyar,amma
kuma ban sani Meyasa wani abu na cikin kaina yake kwaɗaita min shiga ɗin,koba komai
baifi ƙara kwarewa ba,kuma dama irin wannan farmaki mai aji nakeson naga inayi..
A bakin jejin su na tsaya jiya,daidai inda suka kwatantamin,saida nayi kaman sa'a
guda a wajen kafin naga wasu majaze da baƙaƙen kaya sun nufo inda nake..
Wani baƙin ƙyalle suka yafamin a kaina,kana suka riƙe hannu na muna tafiya.
Cikin duhuwa muke shiga har muka zo daidai wani bakin wani kogon ɗutsi mai masifar
girma.
Wasu dakaru ne a wajen a tsaye da manyan manyan bindigogi a hannunsu..
Shigewa mukayi cikin kogon mai lunguna da saƙo kala kala.
Wani sansani muka zo mai matsakaicin fili da mutanen da zasu kai shida a
wajen,dukkansu baƙaƙen kaya ne a jikinsu,saidai akwai guda ɗaya wanda shi nasa
kayan ja ne.
"Barka da zuwa wannan ƙungiya Goje,mun samu labaranka da yanda ka kawar da yaronmu
na garinku,da farko munso yin maganinka,sai kuma mukaga hakan dakayi ma daidai
ne,dan kafishi jarumta da kuma kwarjini.
Munyi farinciki daka karbi gayyatar mu kakuma yarda cewar zaka........"
"Dakata a takardar ba'a nuna karbi aikinku ba,kawai takardar amsa gayyata ce,ko
banyi daidai ba"
Nafaɗa ina kallon cikin idonsa,dan haka kawai naji banji tsoronsa ba,duk kuwa da
yanda suffarsa ta zama abar tsoron..
Tsuke fuska yayi,lokaci ɗaya kuma yasake ta tareda yin shu'umin murmushi.
"Ehh kuma hakane ka faɗi gaskiya,rashin tsoronka ya burgeni. Kaman yanda kake gani
nan shine sansanin BC,kuma basai nayi bayani ba kasan menene aikinmu tuntuni. Nine
mai faɗa a ji na huɗu,akwai sauran mutane uku a sama na. Shugaba da kuma
mataimakansa. Babu wanda yasan wanene shugaban wannan ƙungiyar,shugaba na biyu kuma
ni kaɗaine na sanshi sai Shugaba na uku zamu haɗaka dashi idan ka amince da zama
ɗayan Mutane biyu da suke kulada reshe biyu na wannan ƙungiyar,Idan ka amince da
wannan aiki nan gaba zamu iya baka damar riƙe sansaninka na garinku. Wanda kana da
wannan damar idan ka nuna mana waye kai,saika haɗu da shugaba na uku. Abinda kuma
shine muhimmi bamu yadda wani yasan da wannan maganar ba"
"Harshe zaku yankemin in wani yasani? Da kunsan inada wannan inaga bazamu zo nan
daku ba. Ni zan tafi in kun gama faɗin abinda kuke ganin yakamata na sani"
"Uhm ba matsala zaka iyah tafiyah,kanada damar yin tunani har nan da kwana uku,zuwa
sannan zakaga ɗan aikenmu izuwa gareka"
Daga haka nayi sallama dasu muka fito daga wajen nida wanda suka rakoni.
Ajiyeni kenan da sukayi yanzu a ƙofar gida suka tafi. Garin yayi tsitt bakajin
komai sai ihun mutanennamu wato karnuka,da alama dare yayi kenan.

Cikin gidan ma shuru yayi kaman babu kowa a ciki,duk wannan hayaniya ta gaji da
ƴaƴan ta yanzu shuru kaman basa nan.
Ƙofata na nufah kaina tsaye,mamaki abin ya bani dana ga ƙofar ɗakina a buɗe,ban
kawo komai ba dan nayi tunanin ko inna ce tayi min shara,saboda dama takanyi min
idan na ɗau lokaci. Aikuwa indai hakane nasan saita zubarmin wasu abubuwan,na tsani
a tabamin shirgina..
Toh ikon Allah,dana shiga warin wannan tsinken da take sakamin naji( turaren
tsinke).
Takalmin kafata na cire na wurgashi wajen danake ajiyesu,gobe sai nayi gyara
kenan,don duk ta ɗebi shirigina ta rufesu a gefe..
Waiwayo wa nayi wajen shimfiɗi na zan kwanta,da mutum nayi arba a zaune akan
katifar,nidai nasan babu wanda muke irin wannan wasan dashi,da har zaizo kan
katifata ya zauna,ba kuma barawo bane,inda shine bazai zauna shuru kaman ya mutu
ba.
Lura danayi kaman macece tunda harda lullubi akan ta yasa na tunada wancan auren.
Kutt amma wannan cin fuskar yayi wa,nace su kawota ta dunga aiki basai an ɗaura
mata aure ba,masu kwainanen gari sunce ba haka ba,yanzun kuma na yarda da hakan bai
ishesu ba sai an kawo ta cikin ɗakina.
Cikeda hassala nayi mata magana,danaji taƙi amzawa nayi zaton rai ni ne,sai kuma
naga jikinta yafara rawa,wato tsorone yasakata kasa magana,hmmm mata dai,shiyasa
fah a rayuwata na tsani sabgar dazata haɗani dasu,sunada wuyar sha'ani sosai..
Bayan tafita daga ɗakin ajiyar zuciya nasake,gajiyar dana ɗebo ce ta dawo cikin
kaina,ga kuma nauyi da kaina yake..
Ohh no bai kamata naji wannan muryar ba yau.. Na faɗa cikin gajiyawa ina dafe kaina
wanda nake jin jijiyoyin sa suna rirriƙewa.
Jujjyawa kan nake ina duban ɗakin,yanzu taya zan fara neman abinda zan busa a
ɗakin,nasan babu makawa inna ta zubar da waɗanda na ajiye.
Faɗawa kan gadon nayi ina kallon silin ɗin dana haɗa da jarida da kuma lilo.
Dummm komai naji ya ɗaukemin,vanda juyawa babu abinda duniyar tawa takeyi,a haka na
kasance har bacci ya ɗaukeni.

[Sumaimah a mahangar gani]

Hannu naji yana bubbagani,can kuma sai naji murya ƙasa ƙasa tana min magana..
Saida baccin ya dan bar idona kafin na naji ashe inna ce take tashina.
"Ƴar nan tashi kiyi sallah anyi assalatu,ko bakyayine"
Tasake maimaitawa a sanyaye.
Juyi nayi kafin na tashi zaune,ohh ban taba tunanin kwana na nafarko a gidan zanyi
bacci hadda juyi ba kamar haka.
Kallonta nayi da farin hijabi a jikinta,hannunta riƙeda carbi tana kan sallaya.
Na lura da hakanne saboda hasken ɗan Club da ake haɗawa ya haska ɗakin..haka kawai
naji ta burgeni,indai bawai mantawa nayi ba,tunda nake babu wanda ya taba tashina
sallahr asuba a gidan mu.
Saƙƙowa nayi daga kan gadon wanda yanxu yazama nawa.
Inda buta take ajiye na nufa na ɗauka domin zuwa banɗaki.
Bayan na idar da sallah gaisheta nayi ta amsa cikin sakin fuska,har zuwa lokacin
lazimi takeyi,nima danaga haka ban koma baccin ba saina fara nawa.
Muryar ta can sama sama naji tanamin magana,firgit na kalleta,kenan bacci na cigaba
dayi a zaune.
"Sumaimah ki koma ki kwanta mana,ke ba kaman mu ba da baccin mu yanzu yayi
ƙaranci,bare kuma kunsha hidimar biki,ki koma kiyi baccin ki kinji"
Ɗaga mata kai nayi,dan dama hakan nakeso.
Muryar inna naji tana magana da wasu yara,hakanne yasa na buɗe idona,lokacin rana
ta fito tangargar.
Fitowa nayi daga ɗakin na zauna a tabarmar da take zaune..
"Kin tashi kenan,ga abin karyawa toh.."
"Ɗumamen tuwo ne sai kuma wani ɗan kwano da awara a cikin kaman guda bakwai,sai
kuma kofin kokoh"
"Hmm kiyi haƙuri fah ƴar nan,amarya da aka sani da cin kaji a ranar farko kega
abinda kika samu,wlh banda kuɗine,awarar ma a wajen gaji na karbo nace ta bawa
baƙuwa"
Allah sarki tausayinta ne yakamani,hmm batasan a hakan kayan daɗi tabani ba akan
abinda nake ci a gidan.
"Lahh inna karki damu,shimfiɗar fuska ma da kika bani tafimin komai da kike
tunani,fatana Allah bamu ikon zama cikin aminci"
"Ameen ƴar nan,gaskiya ko kusa baki dace da wancan huhun ba,kawai dai ƙaddara ce da
idan tazo baza'a tsallake ba. Sannan dan Allah kiyi haƙuri da son kaina,dan lokacin
da naji wannan batun nayi niyyar na hanashi,amma kuma sai nayi tunanin wataƙila
sanadin shiryuwarsa ne aurennaki. Yanzu dana ganki ma na ƙara tabbatar da hakan,dan
inaga sai an zage garinnan kafin a samu mace irinki,kiyi haƙuri kiyi haƙuri kinji"
"Inna kidaina bani haƙuri,nima lokacin da Naji labarin kwana nayi ina Addu'a akan
Allah kar ya hadani dashi,amma dana ga an ɗaura aurena dashi jiya sai nayi tunanin
inaga shine mafi alkhairin dana daɗe ina roƙon Allah yabani,dan haka ki daina
wannan bada haƙurin ba laifinki bane,fatana Allah yabani ikon jure duk abinda zaije
yazo."
"Ameen kiyi ta haƙuri da sannu zakiga mafita"
Zancen duk ya isheni,tunda gani nazo gidan to kuma banason tuna wai dama ban xo
ba,dan haka nayi ƙokarin kawar da zancen..
"Uhm inna wanne aikin za'ayi ne a gidan?"
"Ehh toh banice yanzu da tuwo ba gaji ce take saita bani,wanke wanke kuma atika ce
take,idan bata nan kuma ninayi in su farida suna nan su jijjiƙa"
"Toh bari naje na gaishe ta ma,sainaji wanne aiki zan kama mata"
"Ahah kijidai ku gaisa,amma batun aiki ko zakiyi ma ai sai kinyi kaman sati ko sati
biyu,dan haka kada ki damu kanki atika ai tana nan zata zo tayi wanke wanken"
To nacewa inna tareda kallon inda uban tulin wanke wanken yake,wasu manyan tukwane
na abincin siyarwa da kuma su kansu kwanikan abincin siyarwar sun cika wajen
famm,ƙudaje sai bin miyar data bushe suke,kaman dai na gidanmu haka yake..

Sallama nayi a bakin ƙofar,babu wanda ya amsa,sai hayani ya suke,inaga ma basuji


shigowa ta ba.
Ban dai yi ƙasa a gwiwa ba na ƙarisa wajen da suke zaunen.
Gaji ce suke ta musu itada wata matashiyar budurwa,wacce ta juya bayan ta can.
"Haba gaji,idan baki yarda dani ba wazai yarda da nine,nace miki ban ɗau kuɗinki
ba,yakikeso nayi ne wai?"
"Atika nafasan halinki,kwanannan na kula bakida kuɗi,koya nayi wasafai dana wa
ɗebewa zakiyi,ya za'ayi ace har dubu biyu ta b'ata a cikin cinikin"
"To shikenan ai gani ki cazeni mana,kokuma ka jaka ta nan"
"Ohh shasha zaki mayarni ma,na caje........"
"Salamu alaikum"
Nasake sallama dan su san ina wajen..
A tare suka juyo inda na ɗora idona akan Budurwar..
"Atika??"
"Na faɗa cikeda mamaki"
Wani kallon juya ido tayimin tareda cewa cikin muryar duniyanci..
"To ya ranki,kinyi mamakin gani nane komai?"

Littafi na ɗaya ne dana biyu kaman yanda na sabayi,na ɗaya bati siddan,na biyu kuma
Naira 300 ne dan haka zaka iya biya tun yanzu kafin a shiga kashi na biyu.

3131951977
Auwal Sadiya
First bank

Ko katin mtn ta nan


09035784150

VTU ta nan
2347068390570

Shaida kuma ta nan


09035784150

Ƴan niger ku tuntubi wanann number.


+227 97 21 16 15
----------------------------------------------------

Sadi-sakhan ceh
09035784150
Share please

*SANADIN CACA*
Mallakar SADI-SAKHNA

PROFICIENT WRITER ASSOCIATION

*USERNAMES*
FACEBOOK PAGE:Sadisakhna
WATTPAD:@SAKHNA03
AREWABOOKS:@sadeesakhna
PHONE NO:09035784150
________________________________
*Book 1*
Chp[10]

Atika....dama ƴar gidannan ce? Nayiwa kaina wannan tambayar,har sannan ban gaskata
hakan ba.
Tun tana yarinya dama na santa,fitinanniya ce ga faɗa ga kuma kwaɗayi na abin
hannun maza..
Ko zuwa na na ƙarshe ma a wajen talle saida ta nemi muyi,nice na shareta kaman bata
wajen,gashi idan taga wani yana ciniki ita batayi zaka ga jaraba da msganganu,dan
ma ita bata kwantai,dama ƙirarinta kenan,idan tayi ma mutanenta zasu saye ta..
Tabb dole kam tayi,yanzu nagane dalili ba'a ƙasa ta ɗiba ba.
Ko hanya banason mu haɗu da itah,ba kunya takeji ba saita tara maka mutane,ashe
zamuzo mu haɗa gida ɗaya da ita ma,tabbb ɗi jan.
Dauke kaina nayi daga kanta na kalli gajin.
"Uhm Inna gaji ina kwana,an tashi lafiya?"
Wani rausaya tayi tareda gyara ƙunzugun zaninta,nasan bazai wuce nace mata inna ba
yasa ta wannan shan ƙamshin.
Amsawa tayi a fizge tareda cewa..
"Amarya bakya laifi ko kina kashe ɗan masu gida,ya kwanan amarci keda
angonnaki,naji su farida sunce wai a wajen mairo kika kwana,ince dai ba wani abin
cutarwa yayi miki ba koh"
Ta faɗa tana ƙara matsowa kusa dani tareda rage murya. Lallai wannan matar akwai
gulma,ji yanda ta lanƙwashe murya kaman rantse duniya zakace tausayina take
ji,kaman ba itace suke husuma da ƴar ta akan kuɗi ba..
Ƴar dariya nayi ta wayance wa kafin nace.
"Ahhah babu komai inna gaji,ba abinda yayimin,kawai dai zan zauna a wajen inna ne
na ɗan wani lokaci kafinna koma sashen mijinnawa,ni barina tafi idan babu wani
abin"
Miƙewa nayi xan bar ƙofar muryar Atika ta tsayar dani.
"Lahh gaji kin manta wanke wanken can fah,cikina jiya ciwo yake ban kwanta da wuri
ba,shiyasa na makara da safe banyi wanke wanken ba,ga kuma talle da zan fita,gaji
ko zata taimakamin dashi dan Allah"
Kaman zatayi kuka take maganar harda sakin wani munafukin nishi,shuru nayi naji
abinda gajin zatace.
"Ohh ehh hakane kam bazayyi wu harki gama wanke wanke ki fitamin da awarar nan ba.
Sumaimah in bazakiyi komai ba ko zakiyi wanke wanke can kai,yi haƙuri nasaka amarya
aiki"
Banyi mamaki ba,dan dama nasaka a raina hakan zata faru,saurin haɗiye takaici na
nayi tareda ajiye murmushi akan fuskata na kallesu..
"Ahh ba komai ai bari nayi wanke wanken toh"
"Yawwa to bari zan kawo miki omon yin wanke wanken."
Inna wacce tafara tuka igiyarta sai gani tayi nafara jijjiƙa kayan wanke
wanke,mamaki abin yabata tasaki baki..
"Ahh keda nace ki barshi akwai meyi"
"Ahah vakomai inna,wai atikan ce cikinta yana ciwo batayi bacci da wuri ba saita
makara,gakuma zata fita talle"
"Atikance ta faɗa miki haka,zancen banza kenan,yarinyar da har nayi bacci na tashi
fitsari na ganta ta shigo gidan,itace za'ace batada lafiyah,kawai dai suda sun iya
rainawa mutane hankali kai.. Kin ajiye kwanukannan barinaje na samu gajin,wannan ai
rashin daidai ne,daga kawo ki gida jiya har an baki aiki yau"
"Waye ke nema na gani nan nakawo mata soso da omo,harda za'ace wani ban kyautaba na
bata wanke wanke,menene rashin kyautawar tawa a ciki iyee,dan kawai maiyin aikin
batada lafiya nace tayi na rana ɗaya shine abin magana,bata wanke wanken a gidansu
ne? Naga kowa a garinnan yasani itakeyin aikin gidnasu kaff,ba wani gata ne da
itaba ballantana a ce bata tab'a yi ba.
Ni nace me a gidannan,kullum sai nayi tuwo na ciyarda wata,ko a bani cefane ko ba'a
baniba sai nayi tuwo,akwai wanda yake taimakata da ƙwandala a gidannan ne?
Da nace tayi na kwana ɗaya,to yanzu na fasa,wanke wanke da shara kullum ita zata
dungayi a gidannan,indai har wasu suna so na dungayin abinci dasu"
Tana gama faɗin hakan ta zefamin soda da soson wanke wanken.
Wayyyo Allah nah yanzu da soda zan dungayi,ni wanke wanken bai dameni ba kaman
sodar,jikina kwata kwata baya sonta ko kaɗan,nan da nan hanni na sai ɗaɗe ya
tsatstsage..
Wani tarin abune yazo ya tarimin a maƙoshi,wato inna kula inaga ƙalubalena na gidan
ba goje bane kenan gaji ce.
A hankali nake yi ina duba hannuna ko yayi wani abun har na gama
tsaff,Alhamdulillah bai tsage ba amma yayi za sosai,to yau kenan nasan nan da wani
ɗan lokacin zai fatattakema.
Bayan nagama barandar inna Mairo na koma na zauna,ido na tsurawa yanda take tukawa
nayi,abin abin sha'awa,inaso naga mutum yana sana'a.
Da farko taso bani haƙuri akan abinda yafaru,nice naƙi na ɗauko wani zancen,zamane
da allah kaɗai yasan ƙarshensa,idan yazamo kullum sai ta bani haƙuri to abin bazai
tafi daidai ba..
Hira muke jefi jefi,tana bani labarai na zamansu a garin da baban goje yayi
aiki,wani nayi dariya wani na jijjiga kai.
Ƙarar buɗe ƙofar goje nayi,hakanne yasa na juya da sauri wajen,wash ashe yana
nan,harga Allah ni manta ma dashi..
Nufo idan muke yayi kamar kullum da riga da wando a jikinsa ƙanana masu duhu,Allah
ne kaɗai yasan yaushe suka ga ruwa..
"Innna ykk"
Yafaɗa yana zama a bakin barandar.
"Kalau mana nake,kaman yanda ka sanni,ina ka shiga kwana biyu,sai kuma ka koro
matarka jiya da daddare koh"
Runtse ido nayi ƙirjina yana lugude,inda inna tana ganin zuciyata da batayi wannann
maganar ba,na samu bai kula dani ba a wajen,yanzu ta saka ya juyo da idonsa inda
nake.
Wani kallo yayi min kaman yaga dutse kafin yace.
"Kwana biyu naje wani wuzilinne shiyasa kika jini shuru,batun wannan kuma dama fah
tun farko na faɗamiki,zuwa tayi tai abinda yasaka tazo,ke na kawowa ita,in bakyaso
ta tashi ta tafi ubanta yabani kuɗina. Amma batun ta zauna a sashe na ban yadda da
wannan ba sam."
"Hmmm kaidai kace haka,zata zauna a wajena na ɗan wani lokaci,idan kun shirya saita
koma ɗakinta"
"Ɗakinta kuma,akan idonki fah mukaxo nida yarana muka gina ɗakinnan,yanzu rana
tsaka lokaci guda kin bata shi?"
Ganin yafarajin haushin abinda inna ke cewa ne yasaka ni yimata alama da ido,kaman
kuwa ta gani saida sanja zancen. Amma kuma tasake kwafsawa.
"Sabo dayi gawa da gatsine,saida ranar Allah tayi kafin ka fito,ita matar taka inka
fita karyawa saika kawo mata nata,tunda kasan a ƙarƙashinka yanzu take koh"
"Wajen Iliyah zanje nasan ya ajiyemin,daga can zan wuce saina juyo kuma"
Huhhh na sauƙe ajiyar zuciya,ganin bai ɗaga zancen da innan tayi masa ba,da alama
bayason duk wani zance daya shafeni ne inaga.hmmm niyafimin ai,gaba takaini gobarar
titi a jos.

__***__

"Audu ya dai wajen aikin,naji ance wai ka dawo kenan bazaka komaba"
Uwaisu ya tambayi Audu baffan goje.
"Inakuwa komawa,waccar yarinyar ta rabani da samun arziƙina,tabarni da zaman
majalisa da shan lofe"
"Yarinya kuma wacce kenan?"
"Ƴar wajena mana Atika,matar gidance takamata da mijinta,shine fah suka yi mana
korar kare gabaɗayah"
"Hhhhhh hoɗan kace tayi gado kenan,ka manta yanda kake lokacin da muna
matasa,yayanka yayi ta fama dakai,yanzu ma nasan ba sanja sani tayi ba saidai ya
ragu kawai,kai anyi yawan duniya fah"
"Jiya ba yau ba ba,ai wannan yarinya uwaisu inaga da damani ta shanye,dan ita bayan
halina hadda na uwarta tahaɗa ma,nida zan samu na bada itah a cacar ma wani ya
ɗauka wlh inaso"
"Ahh ba saika jarraba ba,inda mai rabo ai sai ya ɗauka,amma kana ganin zata yarda
kayi biyan caca da itah,tunda kace gaji ta iyoo to ba fah kasan sai ankai ruwa
rana"
"Ehh to kuma kace wani abun,amma dai uwaisu tundaga wannan lamarin ka daina caca
koh?"
"Ina kuwa ina nan inayi,yau ma inada wata caca da wani ɗan fulani,naji ance bai iya
ba so yake ya gwada,wayo zanyi masa muyi,idan nayi nasara saina tambayeshi yabani
ƴar sa,kasan su fulani da kyau,yanda na rabu da tawa ƴar nima saina auro wata a
sanadin caca Audu"
"Kai car uba,amma uwaisu kai maƙurane,kana da dabara sosai,kuma kaman wannan
sanadin cacar na aure abune mai daɗi da sauƙi,kana cinye mutum saiya baka ƴar
sa,babu ruwanka dayimata wata wahala,tunda anriga anyi yarjejeni ya. Muje nima
zanga yanda zata kaya,baza'a barni a baya ba sam"
Tashi sukayi da hnazarinsu zuwa sansanin da suke cacar.
Kamar kullum a cike yake da mutane kowa na sha'anin gabansa..
Bayan sun isa wajen da goje uwaisu ya haɗa ido,saidai yau ba caca yake ba,a gefe
yake da a zaune yana duniyar tunani. Bayan sun haɗa ido kowa kawar da nasa yayi
kaman baiga ɗayaba,saikace ba surukai bane.
Manga ne a zaune shida dan fulanin suna ta surutu da hausarsa wacce bata fita.
Suma zama sukayi a wajen aka fara dasu.
"Ɗan fulani so kake kafara caca?"
"Ehh fah,naga abun tana kawo Cede sosai,wani daya ci jiya kawai sai ya ɗebe
dukka,nima inason na ɗebe dukka yau"
Kallon kallo sukayi a tsakaninsu su uku,kafin uwaisu yafara magana..
"To shikenan karka damu,idan kayi nasara zaka ɗebe dukka,amma kafinnan mai zaka
saka wanda in an cinye ka aka bayar?"
"Uhm zan caka komai amma banda sanuwa,bama bada sanuwa a wannan wasan"
"Ehh to naji,ni zan saka gonata,idan kayi nasara ka ɗauka takace"
"Dagaske kake,gona noma babba zaka bani inna yi nacara?"
"Ehh amma kai mai zaka saka,kana da ƴaƴa mata ne?"
"Eh inada ƴaƴa mana,huɗu mata sai maza biyu,sauran basa nan suna gurin innarsu,tare
muke kaɗai da Deejah,itace kuma babba"
"Uhm to zaka saka Deejah idan nayi nasara ka bani aurenta?"
"Na baka Deejah kabani gona inna ci,kaikuma ka ɗauki deeja inka ci,amma Deejah
ƙarama ce,aurenta sai shekarar gaba. Bazatayi aure yanzu ba,amma zanbaka ita
wajenka. Saidai Deejah tanada......."
"Kaga tunda ka amince a fara kawai,koda tanada wani masoyin babu shi yanxu sai ni"
"Ba masoyi gareta ba tanada......"
"Bar wannan zancen kayi shi daga baya,yanzu dai a fara"
Mutane kowa hankalinsa wajensu ya koma lokacin da suka fara,ana haka har cinye ɗan
fulani a caca,kowa a gun dama yasan uwaisu wayo yayiwa ɗan fulani dan ya auri
ɗiyarsa,ko kunya bayaji yarinya ƙarama gashi tsofai tsofai,tausayin ɗan fulani ne
ya kamasu ganin cutar da uwaisu yayi masa,saidai kuma babu yanda zasuyi tunda
yayarda.
"Yanzu ka cinye Deejah,a wajenka zata zauna kenan?"
Dariyah uwaisu yasaka tareda shafa gemunsa cikin shauƙi,ehh yanzu nine mijin
Deejah,zan riƙeta a wajena a nan da shekara ɗaya takai aure"
"Ohh kada ma kayi alƙawarin auren Deejah,nidai tunda na baka ita kanada ikon kayi
duk abinda zakayi da itah........uwaishu ya ɗauki Deejah,jauro ya rabuda Deejah,yau
zanyi barci na more babu Deejah.....heeho jauro yaji daɗi yau ya rabu da Deejah"
Kokararsa yaja a ƙasa yayi ihu kana ya sheqe da dariyah.
Da mamaki kowa a wajen yake kallon jauro,wanda yake murna da farinciki kaman anyi
masa albishir da kujerar makkah.
"Kai jauro ƴar ka cefah zaka rabuda itah,amma kuma kake wannan murnar?"
Manga ya tambayeshi cikeda mamaki.
"Ahah Deejah ɗiya ta ce amma nasan Altine wayo tayimin tabani Deejah ta gudu,ni
nasan ba jini na ba Deejah,don batayi kama da mutane ba wanga ɗiya,Hoɗan hanci
kaman 'bauna fah take,kullum jeji take wuni saboda fitinarta,gata da aljanu masu
saka wutar nan,mun take musu gidansu da shanu suka shiga jikin Deejah,sannan uwarta
tana duba ƙasa suma suka sake shiga jikin Deejah,kai Deejah dai ba mutum ba
kawai,kows ya gudu ya barni da Deejah fah. Nima yanzu na rabu da Deejah
shikenan,uwashu ni zani gida na shaida mata,gobe zan kawo maka Deejah,dama kuwa
tanason zaman birni. Yanzu saina ajiye jakar kuɗina a ko ina tunda babu Deejah.
Hoɗan caca ta rabani da Deejah nikam naji daɗi"
Ɗora sandarsa yayi a kafaɗa ya tafi yana faɗa. Wani suman tsaye mutanen wajen
sukayi,banda shi uban gayyar dayake jin abin kaman a mafarki.
Bayan wajen yayi tsitt na wani lokaci dariya sukaji an kwashe da itah a
bayansu,suna juyawa suka ga ashe gojene.
"Ohh dama wannan baban Deejah da take yawo cikin dare a daji,muma kenan zamu huta
masu zaman daji da gamuwa da itah,babu dama karenmu yakama zomo saita tumurmusheshi
ta ɗauke. Tunda zata dawo cikin gari da zama mayi farauta cikin kwanciyar hankali"
Yana gama maganar ya tashi shima yabar wajen yana dariya,tunda kuwa goje yayi
dariyah to abin mai muni ne sosai......

Littafi na ɗaya ne dana biyu kaman yanda na sabayi,na ɗaya bati siddan,na biyu kuma
Naira 300 ne dan haka zaka iya biya tun yanzu kafin a shiga kashi na biyu.

3131951977
Auwal Sadiya
First bank

Ko katin mtn ta nan


09035784150

VTU ta nan
2347068390570

Shaida kuma ta nan


09035784150

Ƴan niger ku tuntubi wanann number.


+227 97 21 16 15
----------------------------------------------------
Sadi-sakhan ceh
09035784150
Share please

*SANADIN CACA*

Mallakar SADI-SAKHNA

PROFICIENT WRITER ASSOCIATION

*USERNAMES*
FACEBOOK PAGE:Sadisakhna
WATTPAD:@SAKHNA03
AREWABOOKS:@sadeesakhna
PHONE NO:09035784150
________________________________
*Book 1*
Chp[11]

[Sumaimah a mahangar gani]

Kwanci tashi hausawa kecewa a sarar mai rai,yau satina a guda kenan a gidan
aurennawa.
Abubuwa da dama sun faru,wanda duk yawancinsu na rashin daɗi ne. Mutanen gidan
kaman dama jira suke nazo,kowa ya daina komai a gidan na aikace aikace,inka ɗauke
awara kawai da gaji takeyin kayarta. Itama wani lokacin nice ke haɗa wutar,ko
dolene ma in mutum yaga abinda nake ya tausayamin kuma yaji haushina,nima haushin
kannawa nakeji,to amma ya zanyi. Yanda gaji ta faɗa hakane ita ke ciyar da gidan
kusan,nima ta wani wajen inaganin ƙoƙarinta akan hakan.
Dan haka dolene nayimata aikace aikace,duk da kuwa sunyimin yawa,ranar dana gwada
cewa bazanyi ba zage zage tafara da gori,wanda duk akan inna mairo ya ƙare. Nikuma
tausayin dattijuwar nake sosai,shiyasa nakeyin komai da jikina zai ɗauka indai gaji
zata ƙyalemu.
A bangaren goje kuwa bazance lafiya ba,har yanzu babu abinda dai ya haɗani
dashi,tunda ba zaman gidan ma yake sosai ba,in ya shigo ma iya karnukansa ne a
gabansa. Abinda nake masifar tsoro kenan,hakanne yasaka inna tace ya fita dasu
waje.

Yanzu nagane da wuri nake gama ayyukana na samu waje na zauna,muyi ta hira da
inna,kwana biyun farko dana ta'ba soda hannuna ya tsage danayiwa gaji magana cewa
tayi ita taga damar siyah. Inna data kulada hakanne ta bani kuɗi na siyi sabulu.
Ɗakin inna nufah ina ta tuna tunane wanda suka zama aikina na kodayaushe,tun ina
saka ran mafarkin samun rayuwa mai sauƙi yanzu na cire wannnan a raina,haka ƙaddara
take kuma a haka zan ƙare inaga.
Turuss nayi a bakin ƙofar,inna nasamu tana shishshirya kayanta a wani bakko,wani
razana nayi kaman ɗan da uwarsa zata tafi ta barshi.
"Inna ina zakije?"
Nafaɗa a sanyaye.
Itama diriricewa tayi,kaman da alama batasan zan shigo ɗakin ba.
"Uhm ɗiyar nan wlh garinmu zanje,ɗan ƙanina ne yayi aure sannan kuma anyi mana
rasuwa wancan satin,da tun wancan satin naso tafiya,to kinga bazan tafi na barki ke
kaɗai daga zuwa ba,shiyasa nace barina dakata saikinyi ko satine tukunna"
Haɗiye hawayena nayi,banason tafiyar tata,amma kuma wacece ni dazanyi sanadiyyar
hanata zuwa taga danginta. Cikin dauriyah na gyara muryata na tambayeta.
"Inna inkin tafi yaushe zaki dawo?"
"Uhm zanyi kaman sati biyu tunda ina tunanin na barki,amma da wata biyu nake ko
ɗaya"
Datace sati biyu har zan roƙeta ta rage,saikuma naji ashe dannice ma shiyasa zatayi
sati biyun.
"To shikenan inna Allah ya dawo dake lafiyah,amma kunyi sallama da gojene,nasan yau
ba lallai yadawo ba sai dare"
"Ehh nasani ai shiyasa mukayi maganar dashi jiyah"
Gyalenta tasaka na biyota zuwa waje,ƙofar gaji tashiga wadda kaman kullum take fama
da yaranta,Atika bata nan tafita talle.
"To gaji nizan je gida,sati biyu zanyi na dawo,don Allah gaji ki kulada itah,ki
daina yimata wannan abin dan Allah yabaki dama,kar watarana goje ya tareki bazakuyi
da daɗi ba......."
"Haba mairo yakamata ki kama girmanki fah,fisabillillahi mai nayiwa yarinyar
nan,dan kawai nace ta tayani aikace aikace,in batayimin ba akwai yanda zan amfaneta
ne,kawai saidai in ta ciyar da itah. Dazakice goje yagani shima nasan babu abinda
zaice,tunda kowa yasani dama dan haka ya yarda tazo gidan,saboda da dunga aiki ta
fanshi kuɗin da ubanta yakasa biya a caca"
Jan ƙafafuna nayi na bar ƙofar,kunnuwana bazasu iya jure jin waɗannan kalamai ba
masu matuƙar ɗumi,duk da cewar nasan gaskiya take faɗa ba ƙarya ba.
A bakin fita ƙofar gida na tsaya ina jiran inna harta fito,murmushi na ƙaƙalo nayi
mata lokacin da muka haɗa ido,don banason tafara bani wannan haƙurin,itama tasan
hakan shiyasa bata ɗagomin zancen ba.
"To Sumaimah ni zan tafi saikuma Allah yasa na dawo,ki duba ban kaɗen katifata
akwai ɗari biyar ki dunga siyan koko da safe"
Kukane ya kufcemin lokacin data fice daga cikin gidan ta tafi.
Shikenan saini kaɗai a gidan,in kasheni ne ma zasuyi daga goje har gajin babu mai
ƙwata ta a wajensu.
Da gudu na nufi ɗakinnamu nida itah na faɗa akan katifa,kuka nake ta rubza har
saida nayi na ƙoshi kaina yayi ciwo kafin nai shuru.
A haka bacci ya ɗaukeni bansani ba.
Ƙiran sallahr azahar ne da wani masallaci gefe damu suka ƙwallah ya tasheni,hamma
nayi ta yunwa kafin na saƙƙo daga kan gadon innan.
Har na idar da sallah cikina yana ƙara na neman abincin,ganin abin baxai kainiba
yasa na zari takalmina na nufi ƙofar gaji.
Rabon abinci take a kwanuka ƙanana,kowa sai an zuba masa nasa.
Muna haɗa ido da itah ta watsamin harara tareda cewa.
"Mayyah kawai,ni banga amfanin zuwanki gidannan ba sam,shi wanda ya ajiyeki ko oho"
Naji haushin abin amma ya zanyi,mutumin daya ke nema ina zayyi iyayi.
Cakuɗaɗɗiyar jallof ɗin ta yafata a kwano a turomin gabana.
"Gashinan wlh kaɗan zan baki,tunda ko ɗora girki bakiyi ba yau,wannan na wanke
wanke da sharar da kikayi ne"
Ɗauka nayi bance komai ba na fita daga ƙofar,a raina ji nayi gwanda ma gidanmu,ko
ba komai ranar girkin ammi mutum zaici abinci ya ƙoshi,amma kuma gwanda ban babu
jarabar su inna rammah saina gaji,sannan kuma babu zuwa talle kullum.
Ɗakin innan na koma na zauna,kallon abincin nake kaman za'a bawa ɗan yaye.
Nasaka hannu kenan a ciki na jiyo muryar Shareefah a kofar gidan,sallama take tayi
amma bata shigoba,da alama tsoro take kar goje yana gidan.
Fitowa nayi da sauri na tareda ina murna,bayan sati guda wani ya tuna dani ya nemi
inda nake.
Ɗakin innan muka shiga da ita,sai ɗari ɗari take idonta akan ƙofar goje,nasan shi
take dubawa ko zata gani,amma saina sake tambayarta.
"Wakike nema ne Shareefah kike ta juyawa?"
"Kutt harma tambayata zakiyi,wannan mijinnaki mana,ke kina gida bakiji abinda yayi
limamin gari ba koh"
Zaro ido nayi tareda jijjiga kai,bansan mai yafaru ba dagaske,taya zan sani ina
zaune a cikin gida.
"Bansani ba mai yafaru,mai yayiwa liman ɗin"
"Bawai liman ɗin yayi wa ba,ɗan gidan liman fah ya ɗauke,har yanzu bai dawo dashi
ba wai sai yayi sati a wajensa,anyi magiyar amma shuru,kinsan in suka kai mutum
wannan madakatar tasu kuwa saita Allah"
"Mai.....mai ɗan liman ɗin yayi masa"?
"Bai faɗi mai yayi masa ba,kawai cewa ake wai dan liman ya zagesu ne a mubarin
huɗuba"
Hannayena karkarwa suka farayi,dan kawai anyi maganar ka a mumbari saika saci ɗan
liman?.
A tabarmar ɗakinna zauna dana tuna ashe a tsaye muke shigowarmu ɗakin. Itama zama
tayi tana cigaba da bani labarin wane hali garin yake ciki.
Dungurar kwanon abincin nayi da ƙafata,sai sannan na tuna ashe fah abinci nake.
Kwanon na kawo tsakiyar mu,cikeda kunya nayiwa Shareefah tayin abincinnawa.
Itama ta kulada hakan,dan kallon tausayi tafara yimin,kafin ta jijjiga kai alamar
bazata ciba.
"Uhm Sumaimah abin ya ɗauremin kai,ya naga kayanki kuma a nan ɗakin?"
"Anan nake kwana ai,mai kike gani"?
"Abubuwa dayawa,Sumaimah nasan mijinki abin tsoro ne kowa yasan haka,amma anan kam
naga rashin wayonki da rashin dabararki wacce da nasanki da itah. Shin idan baki
tunkareshi ba kin gyarashi taya zakiyi rayuwa mai kyau,wlh Sumaimah mutane irin
goje idan suka gyaru matansu suna morewa,kuma ko wannan abin dayake a gari zai
bari,kowa fah ke yake tsammani kiyi tasiri a rayuwar goje,saboda gani ake silar
shiryuwarsa ce a aurenki,amma kuma ki gudu ki dawo ɗakin innarsa da zama?
Ko.........."
"Kiyi haƙuri kiyi shuru haka Shareefah,nikuwa nasan cewar akwai haƙƙinsa
akaina,amma karki manta bafah nice na gujeshi dan raɗin kaina ba,yacemin idan ban
fitaba zai hukuntani,idan kuma nasake dawowa saidai wata bani ba. To kece zakijene
iyee faɗamin"
Sakin ajiyar zuciyah Shareefah tayi kafin tace.
"Ehh to kuma hakane,amma mai zai hana ki fara wasu dabaru dazasu janyo hankalinsa
gareki a sannu"
"Kaman me kike gani zanyi,ni tsoronsa nakeji Shareefah,saidao tunda nazo gidannan
bai tabayimin komai ba na mugunta,sai gaji ce dai......"
"Uhmm na gaji mai sauƙi ne idan har kika fahimtar dashi yagane muhimmancinki,shizai
yimiki maganin gaji,koda da wahala amma ki gwadah kinji,komai zaizama labari
Sumaimah"
Naji daɗin hirar da mukayi da Shareefah sosai,duk da bata daɗe da gidan ba ta
tafi..
Bayan ta tafi har na tashi zanyi wanka naji sallamar yaro.
Jikina yana rawa nafito daga ɗakin,ƙanin Shareefah ne nasanshi a islamiyyah.
Kwano ne a hannunsa ya miƙomin yana cewa..
"Addah Sumaimah waigashi inji addah Shareefah"
Karba nayi cikeda sanyin jiki kafin nace yayi mata godiya.
Bayan koma ɗaki buɗe kwanon nayi,shinkafah da miyah ce a ciki. Babu bata lokaci
kuwa nafara hannu baka hannu ƙwaryah,idona har zubar da hawaye yake,ban taba zaton
zan samu abinci mai ɗumi a lokacin naciba..
"Nagode Allah yasaka da alkhairi Shareefah"
Nafaɗa akan la'b'baina.
Bayan na tashi abincin fitowa nayi da kwanon zan wanke,haɗa ido mukayi da wasu maza
kaman guda biyar,kowa da kalar tafiyar dayakeyi.
Hankali kwance suka shigo gidan kaman ɗakunan iyayensu. Ina kallonsu har suka shige
ƙofar gojen. Can bayan shigarsu shikuma ya shigo gidan,shida wannan mutuminnasa da
indo tacemin sunansa Tunga.
Magana mai muhimmanci sukeyi da alama,ganin yanda suka tattara nutsuwarsu waje
ɗaya.
Bayan sun gama maganar wucewa goje yayi,ko inda nake tsaye da kwano a hannu bai
kalla ba. Ɗauke idona nayi daga kallon dana bishi dashi,charaf muka haɗa ido da
Tunga,lokaci ɗaya tsoro yakamani,kar naje yaga hararar danayi masa ya faɗamasa ya
babbakani. Saidai maimakon irin fuskar sauran shi murmushi yayimin saina kwantar da
hankalina kaɗan.
Ƙarisowa inda nake yayi tareda cewa.
"Sumaimah koh?".
Ɗaga masa kai nayi a tsorace.
"Kidaina wannan tsoron haka,yaƙin dayake gabanki baya buƙatar tsoro,kuma ma kallon
dutse kukeyiwa pillow dan dun ganshi baƙiƙƙirin a launi,macijin da kike tsoro
bashida dafi a bakinsa,koda yanada shima baya saran wanda suke nasane,kicire tsoro
ki tunkareshi,ta hakanne maimakon ya sareki saidai yakareki daga masu kawo miki
hari. Nizan tafi munada meeting ne,ki riƙe zancena kana kiyi nazari akai"
Kallo nabishi dashi har ya shige wajenda sauran suka shiga,jijjuya maganar tungan
nake a cikin kaina ,haƙiƙa sunada nasaba da abinda Shareefah ta faɗa min.
Nariga na shigo gidan,hanyar fita daga shikuwa ban ganshi ba,in hakane kuwa yazama
dole na dage matuƙa wajen kawo mafita.
Harkar gabana nacigaba dayi,ina jiyo hayaniyarsu a ƙofar,dan ba ni kaɗai bama har
gidan ma ana jinsu ta ko ina.
"Allah yasadai ba tattaunawar kashe wani suke ba"

Littafi na ɗaya ne dana biyu kaman yanda na sabayi,na ɗaya bati siddan,na biyu kuma
Naira 300 ne dan haka zaka iya biya tun yanzu kafin a shiga kashi na biyu.

3131951977
Auwal Sadiya
First bank

Ko katin mtn ta nan


09035784150

VTU ta nan
2347068390570

Shaida kuma ta nan


09035784150

Ƴan niger ku tuntubi wanann number.


+227 97 21 16 15
----------------------------------------------------

Sadi-sakhan ceh
09035784150
Share please

*SANADIN CACA*

Mallakar SADI-SAKHNA

PROFICIENT WRITER ASSOCIATION


*USERNAMES*
FACEBOOK PAGE:Sadisakhna
WATTPAD:@SAKHNA03
AREWABOOKS:@sadeesakhna
PHONE NO:09035784150
________________________________
*Book 1*
Chp[12]

Hamma yayi kana yasake kishingiɗewa a kan gadon ammin,kallonsa tayi da mamaki kana
tace.
"Yau bakada wajen zuwane tun ɗazu kake kwance anan?"
"Uhm to kusan,in ma inada shi fah? Inna fita kuce bana zama a gidan,yau kuma na
zauna kinamin kora da hali"
"Ohh baban ubaidu yaushe nayi maka kora da hali dan......."
Asiyah ce ta bankaɗo labulen ɗakin ta shigo kanta tsaye babu alamar dakatawa,duk da
kuwa taga takalmin babannasu a ƙofar ɗakin.
(Abinda akasari yake faruwa a gidaje kenan,musamman gida irinnamu na hausawa,kaɗan
suke kiyaye wannan. Sai kaga yaro ya shigo ɗaki da gudu kuma iyayensa suna
ciki,shin kozai iya arba da abinda bai kamata ya gani ba duk bai dameshi ba sam.
Allah yasa mu gyara.)
Fasa cigaba da maganar tayi tana kallon Asiyah.
"Kekuma menene kika shigo kan mutane kaman doki?"
"Uhm wai ana sallama da baba a waje"
"Waye ko halliru mai gerone,dan munyi dashi dama zaizo ya karbi guntun kuɗinsa"
"Ahah bashi bane,wannan wani bafulatani ne da wata yarinya"
Hantar cikin uwaisu ce takaɗa dayaji ance yarinyah,yau kwana huɗu kenan da faruwar
lamarin tskaninsa da jauro,tun yana tsammanin ganinsa washagarin ranar har ya
daina,kwatsam sai gashi.
"Baban ubaidu ƙalau kake kuwa,yanaga kayi wani fayau kaman wanda yaga fatalwa?"
"Ahah bakomai barinaje naji damai yazo"
Daga haka bai sake cewa komai ba ya fita daga ɗakin.
Cikin sanɗa kaman wanda kura ke jiransa a zauren yake tafiyah har ya isa ƙofar
gidan.
Da jauro suka haɗa ido,saikuma wata yarinya a bayansa butu butu da ita kaman ƴar
tashe,wani wandone a jikinta mai kamada ƙanzo,sai wata yagyagygyiyar riga,kanta
kuwa ba kitso ba,wani irin gashine kaman sumar mahaukaci.
Ƙiru idonsa ya sauƙa akan ta,aikuwa lokaci guda ta sauya kallon idonta,kamar
girarta zata haɗe,wani gurnani take fitarwa daga maƙogaronta kamar kare,ga
haƙoranta kamar na kifi saboda tsini. Yanda ubannata yafaɗa kuwa hancin saikace na
'baunar,dan a manne yaka a tsakiyar kumatunta.
Wani jirrr uwaisu yaji daya daɗe yana kallonta,ransa kam baya hango masa alkhairi a
jikin wannan halittar.
"Kai hauka kakeyi,caca mukayi zaka bani ƴar ka ba wannan aljanar ba,dan haka tun
dare bayyi maka ba ka tattara ta ku koma inda kuka fito"
Har uwaisu ya juyah zai koma gida jauro ya biyoshi cikin gidan. A filin da matan
gidan suke taruwa suka tsaya,da anata hayaniya kowa sai yayi shuru yana kallon
uwaisu da kuma ɗab fulani wanda ya biyoshi,ga kuma yarinya a gefensu.
"Dakata uwaisu,mun riga munyi yarjejeniya dakai,kanason ɗiyata in kaci cacah,nikuma
zaka bani gona idan naci. Yanzu kuma kace bakashon ɗiyah,wannan zancen bazai yiyu
ba. Ga ɗiya nan na kawo maka,koka so kokuma ka so anan zata zauna. Tacemin tanaso
ta zauna yanzu koni ban isa fiddata cikin gidanna ba"
Sakin baki uwaisu yayi yana kallon jauro cikeda takaici.
"Ohh a zatonka wannan abun zan aure kenan"
"Niban ce maka ka aureta ba,amma yanzu a wajenka zata zauna,itama dukiyarka ce daka
ciyo a cacah. Sannan saida zan faɗamaka tanada matsala na aljanu ,ba rayu a cikin
mutane ba,amma kace bakason jin komai daga bakina. Yanzu kuma nakawo maka ɗiya kace
ba haka ba?".
Faɗane ya kaure tsakanin jauro,yana sai ya tafi uwaisu yace saidai ya tafi da ƴar
daya kawo.
Gurnani sukaji a bayansu irin wanda uwaisu yaji Deejah tayi ɗazu a waje.
Kowa idonsa kanta ya koma,in ka ɗauke uwaisu da jauro sauran mutanen gidan basu san
ma itace tayi ba,saida suka ga tana buɗe baki,idonta akan kazar inna rammah,wacce
aka kawo mata a haihuwar danta na ƙarshe,maimakon ta yanka taci saita barta tana
yimata ƴaƴa.
Wata super Deejah tayi akan kazar ta tumurmusheta a ƙasa,kaza tana ihu tana komai
haka ta saka bakinta ta tusge kanta,jini faca ya 'bata gaban rigarta.
Jefah kazar tayi a ƙasa tana kallon tana dariyah,wuta ce buuu ta fara babbake
kazar. Bayan ta gama babbakewa daukarta tayi ta murmushe gashin jikin,sai turiri
take amma ko zafi bataji. Yagar cinyar kazar tayi ta zuge a bakinta,suna nan tsaye
suna kallonta har ta gaigaye jikin kazar ta jefar da kayan cikin.
A lokaci ƙalilan Deejah tagama da kazar inna ramman,kowa a gidan ya sandare a tsaye
yana kallonta,iya jauro ne kawai abin bai dameshi ba.
"Ke bani ruwa"
Tafaɗa tana kallon inna ramman,dan dama itace ta kusada ita a zaune. Bata yi motsi
ba kana batace komai ba,dan har yanzu abinda ya faru baigama jeruwa a cikin kanta
ba.
"Nace ki bani ruwa na sha,ko kema saina babbakeki na cinye kai,wannan ƙaramin naman
ba wani ƙoshi nayi ba dama,baba ne yace zai kaini gidan sabon babana shiyasa ban
fita farauta ba"
Maganar cikin msifah take yinta kaman tana ganin hanjin mutum.
Da rawar jiki inna ramma ta tashi ta nufi ransa ɗebo mata ruwan,baƙin ciki biyu,an
kashe mata kazarta da ko korarta mutum yayi sai taji haushi,ga kuma ƴar ƙaramar
ifiritiyar yarinya tana aikanta.
Fizge ruwan Deejah tayi daga hannun inna rammah bayan ta kawo mata,ƙwatt ƙwat take
zubawa a cikin harta shanye shi.
Miƙa tayi kafin ta kuma sake kallon inna ramman.
"To kaini ɗakinki zanyi bacci,kece mamata daga yau,ina son mutum mungu naga wani
baƙin ɗauri yana bin ruhinki,dan haka ke munguwa ce"
Zaro ido inna rammah tayi,wai anya kuwa ba mafarki take ba,wannan wacce irin
aljanace,duk biye biyenta bata taba tunanin zata gamu da aljani ba a ido da ido sai
yanzu.
"Bazaki kaini ɗakinnaki bane da kanki,zatonki inna bi baƙin zarenki bazan gano inda
kike kwana bane,na miki mutuncine danace ki kaini dakanki"
Sake razana inna rammah tayi da tsawar da Deejah ta daka mata,wuce gaba tayi tana
binta har suka je shige ƙofar tasu.
Kowa sauƙe ajiyar zuciya yayi,yayinda kallo kuma yakoma kan jauro,wanda shine silar
kawo musu wannan masifah. Ammi ce tayi ƙarfin halin yin magana ganin kowa yarasa
bakin cewa uffan.
"Baban ubaidu mai yake faruwa ne,wannan bafulatanin fah,sannan itama waccar aljanar
wacece"
Shuru uwaisu yayi yana kallon ƙasa,ta ina zai fara kenan?
Ganin bashida tacewa yasa jauro gyara murya ya jiye musu labarin abinda ya
faru,tundaga A har Z,sannan kuma ya ƙara da cewa.
"Da yayi zaton wayo yayi min,ni daka ganni nan nasan caca fiyeda yanda kake zato,da
nayi niyyar cinyeka na ɗau gonarka,amma daka naji ɗiyata kakeso da aure saina gano
bawai cacar ce a ranka ba,so kake ka cuceni. Nikuwa saina barka kayi nasara saboda
na rabu da Deejah. Tunda aka haifeta bamu taba hutawa ba,saboda tsabar ta lokaci
guda na tashi naga innarta ta gudu,matar dana auro ma daga baya tace zata
zauna,ganin abin yafi ƙarfinta itama ta gudu. Ko yaushe cikin gina bukka muke,bama
bacci sabo kar takasa mana wutah,nasha guduwa na barta idan ta shiga daji,amma
dayake aljanunta ne suke taimaka mata take tsiya saidai kawai na ganta ta biyoni.
To yanzu tunda tace zata zauna a wajenka watan hutawa ta yakama,zanje na ɗau matata
da ƴaƴana mucigaba da zama"
Yana gama faɗar haka yafita daga gidan hankalinsa kwance.
Cikeda takaici ammi ta kalli uwaisu bayan jauro ya tafi.
"Yanzu wagari ya waya baban ubaidu,munyi munyi dakai ka daina wannan cacar,manyan
unguwa sun yi maka magana,amma kaƙi ji sam. Wato da ƴar kyakykyawace ɗiyar fulani
saidai muji zaka aure ya koh,a sanadiyyar cacar nan ka ɗauki ƴar ka ka bawa wancan
shashan,kaikuma da a tunaninka saika auro wacce ranka yakeso? Saboda kai kanaso
kaga daidai?"
Haɗiye wani abin baƙinciki tayi bayan tayi masa kallon takaici tabar wajen.

Cikeda borin kore kunya ya kaɗa rigar sa yabar gidan,amma kana ganin fuskarsa kam
kasan abin ya dameshi.
(Hmm baka ga komai bama)
Ammi tana shiga ƙofar tasu taji ihun inna rammah a ɗaki.
Ƙarisawa ɗakinnata tayi da sauri dan ganin mai yafaru.
Leƙawa tayi ta samu aljanar da aka ƙira da Deejah ta kafa haƙoranta a cinyar inna
ramm,irin wanda tayiwa kazarta ɗazu.
Ammi ce tashiga ɗakin ta janye ta daga jikinta,jini sai zuba yake a wajen.
"Wayyo na shiga uku,cinyeni zatayi nima kaman yanda ta cinye kazata,wlh bazan zauna
ba uwaisu ya kawo abinda zai halaka ni ya halaka ƴaƴana"
A bangaren Deejah kuwa ammi tana banbareta daga jikin rammah ta koma kan gadonnata
tasake kwanciyah luff kaman ba ita tayi ba.
"Rammah mai kika mata ta cije ki?"
"Ammi ganemin wannan masifar,tace a ɗakina zata zauna na kawota,wai kawai dan taga
ɗana akan gado saita jefoshi.Aradu badan na cafkeshi ba a ƙasa zai faɗi,haushin
hakanne yasa na mareta,aikuwa tafara wannan gurnanin,wai ba'a dukanta,kannaceme
naji ta maƙare a jikina tana yakushi na. Muna haka zanina ya kunce,tana ganin
cinyata ta gasa min cizo.Wani zafine ya jiyarceni shiyasa na zuba ihu. Dan Allah
Ammi ki taimakeni na fitar da ita a ɗakina"
Deejah tana jin abinda rammah ta faɗa ta ɗago idonta.
"Idan kukayi yunƙurin ta'bani saina bunkawa ɗakinann wuta na babbakeshi,ke kuma
idan kika sake shiga in muna fada to ɗakinki zan koma da zama. Zanyi bacci kafin na
tashi ku sama min abinci,idan ba haka ba kaza ta gaba ce abincin na,sannan duk ɗan
daya shigo ina bacci saina karya ƙafarsa".
Tana gama faɗin haka ta koma ta kwanta.
"Kinji koh ammi dan Allah........"
"Ahah dakata bakyajin abinda tacene,ko bakiga yanda tayiwa kazarki ba kai,bazaki
ɗau darasi daga haka ba. Ni kinga tafiya ta ba dani ba.
Takaicine ya ishi rammah,hakanne yasa ta fito filin ƙofar tasu tana safa da
marwa,burinta kawai uwaisu ya shigo gidan ta direshi da masifah,a jima ta leƙa
ɗakinnata,duk sanda ta hango Deejah a kwance tana birgima akan gadonta sai wani
takaici ya jiyarce ta.
Tun tana tsammanin jiran uwaisu shuru shuru har yamma tayi,bata manta ba kuwa yana
shigowa tasha gabansa.
"Allah ya shigo dakai,maza kasan yadda zakayi ka fitarmin da waccar halittar daga
ɗakina,dan wallahi bazan zauna da itaba,saidai na bar gidannan akan haka"
"To yanzu ykk so nayimiki kenan,shigowata kenan tun fitata,baki bani abinci ba kuma
kece da abinci"
"Abinci zancen abinci ma kake kenan,to ni tunda ka kawo wannan masifar ko ruwa ban
saka a bakina ba,kanace wasa nake koh,koka fita da ita kokuma nayi gidanmu. Kalli
inda ta cijeni fah har yanzu jini bai tsaya ba"
Masifa rammah take kan gari ya gari,akan koya fitarda Deejah a ɗakinta kokuma ta
tafi gidansu.
Ganin abinnata bana sanyi ne nan kusa ba yasa uwaisu ƙirna mazan gidan akan su fito
da Deejah a cikin ɗakin.
Ubaidu aka ƙira yaran gidan maza kaman su biyar akan su fito da itah.
"Haba baba kace yarinya ce ƴar shekara sha biyu,miye kuma sai an ƙiramu kusan mu
biyar,saikace wani gardi"
Ubaidu yafaɗa da sanda a hannunsa yana dariya rainin hankali"
"Uhm uhm ubaidu kudayyi a hankali,bakuga yanda tayiwa kazar rammah bane ɗazu,nan da
nan fah ta cinyeta a gabanmu,kuma itama kanta ramman data cijeta saida fatar da
ɗaye"
Ammi tafaɗa cikeda tsoro.
Duk cikin mazan babu wanda ya yarda da zancen ammi,amma dai basu ajiye sandan ba
suka shiga dashi.
Deejah tana ganin shigowar mazan da sanda ɗakin ta tashi ta zauna.
Kallonsu take kafin idonta ya sauƙa kan rammah da uwaisu waɗanda suka shigo daga
baya.
"Mazakuyimin da waɗannan sandunan,ke kika turo su ko dan kawai zan zauna a ɗakinki?
Kaikuma dan kawai nace na yarda ka zama ubana na biyu shine zaka saka a dakeni"
Cikeda mamaki bawai na tsoro ba take kallon su dukka,baƙincikine yasake shaƙar
rammah,musamman data gano inda dejah ta kwanta,tajiƙe wajen jaraff da fitsari,hmm
dama yaushe za'a raba wannan da fitsari,da batayi kashi bama.

Yakuke ganin shin Deejah zata fita daga ɗakin ramma kuwa????

Littafi na ɗaya ne dana biyu kaman yanda na sabayi,na ɗaya bati siddan,na biyu kuma
Naira 300 ne dan haka zaka iya biya tun yanzu kafin a shiga kashi na biyu.

3131951977
Auwal Sadiya
First bank

Ko katin mtn ta nan


09035784150

VTU ta nan
2347068390570

Shaida kuma ta nan


09035784150

Ƴan niger ku tuntubi wanann number.


+227 97 21 16 15
----------------------------------------------------

Sadi-sakhan ceh
09035784150
Share please

*SANADIN CACA*

Mallakar SADI-SAKHNA

PROFICIENT WRITER ASSOCIATION

*USERNAMES*
FACEBOOK PAGE:Sadisakhna
WATTPAD:@SAKHNA03
AREWABOOKS:@sadeesakhna
PHONE NO:09035784150
________________________________
*Book 1*
Chp[13]
"Ehh nina ɗakkosun su fita dake,au harma mamakin hakan kike,da a tunaninki zan
zauna dake ne a ƙarƙashin rumfah ɗaya,kalli fah yanda kika jiƙemin gado,abinda ko
ɗana baya yimin ƙatuwa dake. Ubaidu kuyi ta dukanta,shegiya aljana kawai"
Ubaidu ne yakai hannu zai zawota daga kan gadon ta goce.
"Ohh dama ta gaske kuke,naga aljanuma ai da basaso na zauna a jejinsu mun daidaita
ballanta na kuma ku,nafiku iskanci bari ku gani. Kekuma da banyi niyyar yi miki
komai ba,amma tunda kika nunamin kalarki bari kiga tawa"
Tana gama faɗin hakan ɗakin yakama da uwa ta ko'ina,tsakiyar gadonne kujera
ne,cikin ƙankanin lokaci hayaƙi ya turnuƙe ɗakin.
Fita sukayi da ciki kowa yana toshe hanci saboda numfashinsa daya shaqe,rammah kuwa
sai ihu take tana neman agaji na ɗakinta dayake shirin zama toka.
Ruwa aka fara zubawa,jama'a tana kawo ɗauki daga waje,daƙyar aka samu wutar ta
lafah,kayan ɗakinta kam saidai wasu idan tayi.
"Jama'a ku taimaka ba kwa ganin ɗakina ne,komai na fah yana ciki,wayyo Allah na"
Burburwa rammah take tana birgima a ƙasa,sai riƙeta ake zata faɗa cikin wutar,gidan
yacika da mutane da kuma hayaniya.
Har dare yayi gidan bai lafa ba,rammah kam ita akayiwa,babu abinda ta tsira dashi a
ɗakin sai ginin kawai,zuwa lokacin tama daina magana sai bin mutane da ido.

___***__

[Sumaimah a mahangar gani]

Jiya harna kwanta inajin hayaniyar su Tunga a ƙofar goje,bansan lokacin dasuka
tafiba har bacci ya ɗaukeni. Ko a nan suka kwana ma oho.
Yanzu dayake ni kaɗai ce a ƙofar innan kaman kullum bayan nayi sallahr asuba komawa
bacci nayi,bani na tashi ba saida safiya tayi.
Kuɗin koko nah na miƙa ta katanga maƙwantanmu yaranta suka miƙomin,bayan na shanye
na haɗa kayan wanke wanke nayi. Yau dawuri nagama ba kaman koda yaushe ba,mai
yafaru gaji basa 'bata kwanuka da yawa ba yau?.
Bayan nagama vanyi shara ba,saboda gidan bayyi dattiba shima kaman koyaushe,sai a
sannan na tuna ashe ƴaƴan ta basu kwana jiya gidan ba,suna can gidan kakaninsu.
Har na zauna goje ya faɗomin a rai,koya fita ko yana nan oho.
Tashi nayi a hankali na nufi Ƙofar tasa,zuciyata ta kasu kashi biyu,ɗaya nacewa kar
naje,yayinda ɗaya kuma take cewa na kawar da tsoro na naje na duba.
Shurun danaji ne yasaka na kula babu mutum a ƙofar ya kulle ma da makulli. Saidai
kaman yanda Tunga yafaɗa kam anyi taro,dan wajen kaca kaca yake kaman kasuwa.
Kalle kalle na fara a ƙofar,banma san haka take ba sai yanzu,ba laifi tanada ɗan
girma..
Banɗakin na tura shi a buɗe yake,saida na razana dan yadda yahaɗa uban datti na
ganyen bishiyar dayake zubowa a maƙwantai.ga kuma kaya daya jibga a cikin banɗakin
na wanki.
Komawa ɗakin inna nayi na ɗauko tsintsiyah,na yanke hukuncin share wajen,koma mai
zayyimin saidai yayi,wahala bata kisa indai ba kashenin kuma zayyi ba.
Tsakar ƙofar na fara tattarewa dattin na share,kana na koma kan banɗakin. Kayan
daya tara himmm a na ɗebe,har ƙwari sunyi gida a ƙasansu saboda daɗewa da sukayi a
wajen.
Banyan shima na gama shareshi kayan na ɗebo na fito dasu zuwa ƙofar inna.
Dama inada sauran sabulun da inna tabarmin dashi na wanke kayan tass,nasha wahala
kam kafin su fitah,saboda dauɗar da sukayi ba kaɗan bace.
Bayan nagama shanya su nan da nan suka bushe,da sauri kuwa na ɗebe su na naɗe. A
bakin ƙofar ɗakinsa na ajiyesu na dawo da sauri saboda kar yazo ya taradda ni a
wajen.
Daga ƙofar tasa bayan na fito wajen gaji na shiga na ɗora mata girkin rana,dan
indai tace zata bani abinci kaman na jiya bazai isheni ba.
Kaman kurame tsakanina da itah haka muka gama girkin,ta zubamin nawa na ɗauka na
dawo.
Bayan naci nayi wanka na nai bacci,gidan shuru babu wanda zanyi magana dashi,nayi
kewar inna sosai.
Da daddare har na rufe ƙofah naji ana bubbugawa,ban buɗeba sai nace wanene?.
Shuru naji babu amsa,har gaba ya buga,can kuma sai naji kamar muryar Atika tana
nishi.
Buɗe ƙofar nayi na sameta a tsugunne a bakin ƙofar tana riƙeda ciki,sai fidda wani
numfashi take na wahala.
"Atika lafiya mai yafaru naganki a nan da darennan?"
"Ni in zaki matsamin na shige ki matsamin,wayyo cikina sai tsage wayyo na shiga
uku,Sageer ya cuceni yagama dani"
Matsawa gefen nayi kaman hoto na bata waje ta wuce,duk yadda akayi akwai wata a
ƙasa,kuma da alama batason gaji ta sani.
Bayan na bita zuwa ɗakin gani nayi ta ciro tsumma a ƙasanta ta ajiye,duk ya baci da
jini,jikinta sai rawa yake amma dan dauriyar zuciya haka ta gyara jikinta a
daren,zanin inna ta ɗauka da ta saka kafin ta dawo ɗakin.
Nidai har sannan ina zaune kaina yayi murfi da wannan lamari,yau mai nake gani haka
a kan idona ni Sumaimah.
Gadon da nake kwana lokacin da inna tana nan ta nufah zata kwanta,bayan ta ciro
wani magani a jakarta tasha. Kasa jurewa nayi hakan yasa nayi magana,ko bazata
kulani ba saina tambaya..
"Atika menene haka yake faruwa,kaddai......"
"Ehh shine,abinda kike tunani ba shiɗinne dai wato ciki. Ciki na zubar saboda
banaso gaji tasani shiyasa ka na shigo nan,ko zaki faɗamata kai?"
Maganar tata ta dakeni sosai,wai anya kuwa tasan girman laifin data aikata kuwa,har
take da bakin wannnan ƙwarin gwiwar?. Nida bani na aikata ba har yanzu jikina rawa
yakeyi,wai wannan wane irin zamani ne Allah ya kawo mu ne haka,ace irin wannan
babban laifi yazama ruwan dare kowa yi yake?
Cikin sassanyar murya ta jan hankali na fara yi mata magana.
"Atika kinsan irin tarin girman laifin da kika aikata kuwa,kinsan shin wane muni ne
dashi dakuma matsayinsa a musulunci harda mahaliccinki. Sannan kinsan irin wuƙar da
kika ɗauka kike da'bawa kanki saboda wannan halayyar. Inda kinsan me waɗannan
abubuwan suke nufi da bazaki aikata abinda kike ba,koda kuwa anyi yunƙurin
tursasaki ne,amma kuma wai da saninki kike aikatawa,kisa fah kikayi atika naran da
bai yiwa Allah komai ba. Abinda Allah maɗaukakin sarki yace.
”daka ɗauki ran bawansa wanda ya kasance bai aikata komai ba ko mumini,gwanda ka
yaye sama da ƙasa idan har zaka iyah”
"Amma ke kin aikata hakan hankalinki kwance kinzo nan wai kin 'boyewa gaji kada ta
ganki saboda kina tsoronta ita ta haifeki,shikuma wanda ya halicceki a gabansa
kikayi komai batareda kina tsoron yana ganinki ba. Kuma a hakan ace za'a ga daidai
a rayuwa?"
Tunda nafara maganar shuru kakeji bata ce komai ba,sai can naji alamar sheshshekar
kukanta.. Shin magana ta ce tasakata kuka ko kuma ciwo takeji oho.
"Hmmm Sumaimah kenan,a zatonki ni banajin zafin rayuwar dana tsinci kaina naganni a
ciki.Ni bazanyi aure ba,banga wata fa'ida da yinsa ba,indai aure irinna iyayenmu ne
gwanda banyi ba. Mace na buƙatar namiji da kuma kayan more rayuwa,wannan yake kaini
wajen maza"
"To idan kuwa hakane yake kaiki wajensu akwai fa'idar yin aure kenan,tunda abinda
kika lissafo suma suna cikin aure,sannan batun bazakiyi aure ba saboda kinga
rayuwar iyayenki hakan ba hujja bace dazata baki lasisin yin zina da kuma kashe rai
Atika"
Zuwa yanzu raina ya baci da furucinnata,wannan wane irin son raine mu mutane muke
da shine.
"Kinga Sumaimah dan na barki kinyi wannan maganganun kuma kinga sunyi tasiri akaina
bashine zai baki damar faɗamin maganganu ba,rayuwa tawa ce,nikeda ikon yin abinda
naga dama da itah. Banga abinda zaisa nabar ciki a jikina kam na haifeshi na
shege,saidai in narasa yanda zanyi,ai hausawa suna cewa da kunyar duniya gwanda ta
lahira"
"Allah koh,zamuga in muka je ko hausawan zasu ƙwaceki ai,Allah ya shiryeki dami
gabaki ɗaya"
Ina gama faɗin hakan na haura gado na kwanta,ita sani ai duniya ce ta ishi kowa
riga da zani harda na yafawa ma.
Da asuba tayi ni kaɗai na tashi nayi sallahta,atika nasan ko wannan abun bai faru
bama ba sallahr asuba zata tashi ba,inaga kuma ta samu dalili.
Bayan nayi sallahr ban komaba saina cigaba da karatu,ina jinta tana tsuka na
dameta,bance mata komai ba ban kuma daina ba har na gama.
Na gama rufe ƙur'anin kenan naji muryar goje a bakin ƙofa,wani daram naji wanda duk
sanda nayi arba dashi sai hakan ta faru,ko yaushe zan saba da wannan mutumin oho.
Da sauri na jawo ƙafata na fito wajen,muna haɗa ido dashi na sunkuyar da kaina.
"Keee wacce irin mai kan tumakai ce ke? Tun shigowarki gidannan nace ba ruwanki da
shirgina amma bakiji ba koh,wato kilaroro zakiyimin irinna ku na mata,an zugaki
kidunga shiga harkata koh?,meyasa kika tabamin kayana dasuke banɗaki,nasan ba inna
bace tun da bata nan"
"Kayi haƙuri tunda bakaso hakan bazai sake faruwa ba,naga wajen yayi dattine kayan
ma kuma sun daɗe a wajen,shiyasa na gyara saboda na samu ladan yiwa miji aiki"
"Hehehe miji? Tanan kika bullo,saboda kinga gidanmu ɗaya shine har nake magana kina
mayar min koh. To tunda miji zaki yiwa aiki kizo sashena na baki aikin miji ki
dungayi,ba aikin miji kikeso ba,zaki samu ai akwaishi da yawa"
Yana gama faɗin hakan ya shige ƙofar tasa yana tafiyar isa,jikinnan a murɗe kana
ganin hakan ta jikin ɗamammiyar rigarsa.
Nashiga uku ni Sumaimah mai yake nufi da zai bani aikin miji,ni mai yasama na shiga
shirginsa ne bayan ya hanani,yanzu gashi na jawowa kaina,ko mai zai faru oho?.
Haka ina ji ina gani na kawar da waɗannan zullumin na nufi sashennasa kaman yadda
yace.
Wannan shigar har nafijin tsoro akan shigar danayi jiyah,ga sanyin safiya sai
karkarwa nake.
A zaune yake akan wani tsohon bokiti na ƙarfe a tsakiyar filin wajen,duk sanyinnan
da ake daga shi sai singlet da three quater na wando.
Wayyo nikam ko maza haka banason ganinsu a irin wannan shigar ballantana wannan mai
suffar dodannin..
Jan ƙafafuna nayi har gabansa na tsugunna,gudun kada na tsaya ma na gamu da wani
laifin akan wanda nayi.
Ƙaremin kallo yake kaman mage tasaka bera a gaba,saida yayi ya isheshi dan kansa
kafin yayi wata ƴar dariya.
"Tunda kin zabi shiga rayuwata,duk da cewar na gargaɗeki to ba komai zan barki ki
shiga,da farko dama ina neman sabon yaron dazai dunga kula da saniyar can,tunda
gaki tazo gidan sauƙi,zaki dunga ɗebo ruwa a rijiyar ƙofar gida kina min wanki da
kuma bawa saniyah kina cikamin zan dunga bar miki makullin ɗakina ki dunga
gyarawa,komai yazamo yanda nake sonsa,idan har naga kuskure guda ɗaya daga cikinsu
toh ki saurari hukuncinki a matsayinki na wacce takasa cika ayyukan miji"
Yanda kake faɗan mijin kasan abin wasa ma ya maida kalmar,wai harda saniyah zan
kulada itah,babu wanda ya fi batamin rai ma kaman ɗiban ruwan,saboda kawai ya
tozarta ni bazai iya bawa yara su ɗebo ba saini? Menene laifina dan nayi masa wanki
nayi masa shara,ni wanne irin mutum ne haka Allah ya hadani dashine kam.
Allah ka dubeni ka fitar dani daga cikin wannan ƙaulin.

Littafi na ɗaya ne dana biyu kaman yanda na sabayi,na ɗaya bati siddan,na biyu kuma
Naira 300 ne dan haka zaka iya biya tun yanzu kafin a shiga kashi na biyu.

3131951977
Auwal Sadiya
First bank

Ko katin mtn ta nan


09035784150

VTU ta nan
2347068390570

Shaida kuma ta nan


09035784150

Ƴan niger ku tuntubi wanann number.


+227 97 21 16 15
----------------------------------------------------

Sadi-sakhan ceh
09035784150
Share please

*SANADIN CACA*

Mallakar SADI-SAKHNA

PROFICIENT WRITER ASSOCIATION

*USERNAMES*
FACEBOOK PAGE:Sadisakhna
WATTPAD:@SAKHNA03
AREWABOOKS:@sadeesakhna
PHONE NO:09035784150
________________________________
*Book 1*
Chp[14]

Har na gama aikina na yau ko yaushe a gidan da safe,Ƙwalƙwalwata ta gagara barin


Tunanomin abinda gojen yacemin,tabbas kam yanzu na yarda ba daidai yake da sauran
mutane ba,wai a hakan ma yanda nake tunanin zayyi min bai yimin ba.
Na ƙara tabbatarwa bazan taba samun matsugunni a wajensa ba ballantana nayi wani
tasiri a cikinta,amma kuma ta wani wajen a zuciyata yana cemin wataƙila tunda har
ya yarda na taba kayansa zan iya samun nasara koda watarana ne. Duk da cewar
ayyukan daya bani mutum ko ƴar sa ne bazai saka ba ballantana kuma matarsa,koda
yake mai yasa hakan zai dameni,nasan dama bazan samu wannan matsayin ba,ga
kuma.....
Firgit nayi na dawo daga duniyar tunanin jin an wullomin abu a jikina,ɗaga ido nayi
caraf sai a cikin na goje,wanda yake min kallo mai haɗe da harara.
Saurin sauƙe idona nayi,ananne naga ashe makulli ya wullomin,na dakinsa ne kenan,na
faɗa a raina.
"Kije kewayen can saniya ta tana ciki,daga yau kulada ita yana hannunki,akwai
abincin ta a gefen wajen,sannan ki cikamin randa ta kullum da ruwa,ki gyaramin ɗaki
waɗancan yaran sun wargaza shi,amma ki tabbatar komai yana muhallinsa,naga kin iya
wanki akwai kayana suma ki wanke su"
"Toh shikenan"
Har yakama hanyar fita waje sai kuma ya dawo,.
"Ko ɗayane ya kuskure vakiyi ba.......saikinyi ɗiban ruwa sau ashirin kina yiwa
gidannan ban ruwa,idan kuma ya wuce ɗaya baki cikaba sai na rufeki a ɗaki da su
durwa,basai na faɗamiki abinda zasuyi ba kinsan menene"
Yana cikin maganar ne ƴaƴan gaji suka shigo gidan da gudu sun dawo cin ɗumame daga
makaranta,gudu suke basu kulada wanda yake gabansu ba,aikuwa suka bangajeshi zasu
wuce basuma kulaba.
Har sun kusa isa ƙofarsu ya daka musu tsawa.
"Kaiiii.....dukku ku dawo nan ku zube"
Wata karkarwa suke amma ba bakin magana,su haɗune,ƴar babbar itace mai bin
atika,sai kuma ƙannenta biyu maza ɗaya mace,ƙaninta ne gaji take goyo ta yayeshi.
"Dan Allah yayah goje kayi......"
Kallon da yayi matane tayi shuru bata ƙarisa ba.
"Jeki ƙofata ki ɗaukomin bokitin danake zama,dama tunda kuka dawo babu wanda na
saita a cikinku koh,ita kanta uwartaku dama na kula ta mantani har maganata take
ina jiyota daga ɗakina. Ku fara tsallen ƙwado kuna zagaya gidannan,kuga ƴan iska
koh.

Samun waje yayi ya zauna yana kallonsu suna kewaya gidan,banda ihu babu abinda
suke,abinka da yara har tausayinsu ya kamani.
Bakiti na ɗauka bayan gama yimasa sharar ɗakin da kuma tsakar wajen,kayan da za'a
wanke na zakuɗo a ɗakinnasa masu ɗan banzan datti,duk sun rine ga hamami kaman zan
yi amai..
Ta gabansa na wuce na nufi hnayar waje ɗebo ruwan,haka kawai sainaji gidan yamin
duhu rana ɗaya,ashe gaji nafila ce akansa. Tunda nazo gidan yaune ya taba kaiwa har
zuwa yanzu yana gidan..
Dana kawo bakin ƙofar gidan tsayawa nayi ina kallon wajen,nasan mutane zasuyi ta
kallona suna maganganu akai,shiko kunya bayaji ace matarsa zata ɗebo ruwa,ko yara
mata basa ɗiban ruwa balle matan aure,hmmm nice ma nake mutunta auren,shi mutumma
baya mutuntawa ballantana wani aure a wajensa.
Tafiya nake kaina a ƙasa na nufi wajen ɗiban ruwan,Allah ya taimakeni ma babu nisa
daga gidan..
Ban taba tunanin fitata tafarko a gidan ɗiban ruwa zanje ba.
Sau uku nayi randar tasa ta cika,saniyar dayake faɗa itama na kai mata ɗaya,saina
sake ɗebo wasu guda biyu na wankin kayansa,nima saina haɗa da nawa ma na wanke..
Duk ɗiban ruwan danake ta gabansa nake wucewa,har sannan izaya yake yiwa yaran gaji
bai gama ba,tabb lallai gaji tana tsoron goje,duk abinda yake shiru taƙi yin
magana,yanda take da ƴaƴan nan kaman rayuwarta amma tayi shuru?
"Kutashi ku tafi,gobema ku sake tafiyah ta rashin ladabi,kuje ƙofar ku ku ƙiramin
atika yanzunnan"
Yana cewa ya sallamesu da gudu suka shige ƙofar tasu suna kuka.
Can kaman bayan mintuna Kursiyyah ƴar babbar tafito daga ƙofar tana matsar hawaye.
"Yayah goje wai inji gaji batanan bata kwana a gida ba"
Dariyar gefen baki yayi yana jijjiga kai.
Ɗaga murya yayi yanda gajin zatajishi.
"Ke gaji,wato ni zakiyiwa iya shege koh,makaho kika mayarni komai,yarinyar ba ita
nagani cikin dare tashigo gidaba?. Kinsan Allah kafin na ƙirga Uku kota fito kokuma
nazo da kaina na ɗauketa,abin kuma bazayyi muku kyau ba"
Ƙirgen zai fara,ganin abin zai baci nida kwainane cikin rawar murya nace.
"Uhmm....bata ƙofar inna gaji"
Wani kallo da yatsomin da ɗazu nasamu ya manta da shafina.
"Tana ina toh,ohh daga zuwanki gidan kema har an fara munafurci dake ko?"
"Ahah ahah wlh ba haka bane,kawai ina kwance ne da daddare tace na buɗe mata
shine......"
Bai bari na ƙarisa wanke kaina ba ya buɗe muryarsa yana ƙiran atika.
"Ke Atika wlh in baki fito daga ɗakinnan ba idan nazo saina yayyaga ki"
Yana gama magana kiriff saiga Atika a waje tana rarraba ido,duk da tana ƙoƙarin
boyewa amma kana ganin rawar da jikinta yake kasan tsoron karonnata dashi take.
Da hannunsa ya nuna mata gabansa taje ta tsugunna.
Sunkuyar dakai tayi takasa haɗa ido dashi.
"Uban me kukaje yi keda Sageer A asibiti jiyah?. Wato ciki kukayi tare saboda ku ga
tantirai shine kuka zubar koh,kowa a wajen sai faɗa yake cewar ke ƴar
gidanmuce,saboda ki jawo min raini a gari koh. Ku a hakan har shegune gu da zaku
iya kashe rai,ko ni bana ɗaukan rai sai mutum yamin laifi,shi cikin da kika yi
fadamin wane laifi yayi."
"Wayyo dan Allah yayah goje kayi....."
"Shuru kada ki kuskura ki faramin wannan Kalmar da banaso ɗin. Kinsan mandotary ne
sai kin Kwashi naki kason,shima abokin shan shagalinnaki yana can wajen yarana suna
morewa,ke kuma anan zan miki naki a gida.
Ke wakike kujera koh a sunan na yaran manzo(kursiyyah)je ki ɗaukomin wani cable na
birkin keke yanan a maƙale a gefen ɗakina"
Jijjiga kai Atika tayi tana kuka jin abinda za'a ɗauko,da alama dama kaman tasan
karo. Ni da bani za'a duka bama nima karkarwar nake,wankin nake da sauri ina
gurzarsa kar a haɗa dani.
Wacce aka aika ɗin ta tafi saigata da dawo kuwa,miƙa masa tayi yana karba tabar
wajen,ƙofarsu ta shiga,da alama taje faɗawa uwarta abinda yake faruwa ne.
Mummurɗa shi yayi yai masa tuka,iya ƙarfinsa ya zage ya tsula mata a cinyah,wani
ihu ta kurma wanda nasan ana jiyota a maƙwantansu,innalillahi yanda nake zatonsa
ashe ya fi haka.
Tsula mata yake tana burburwa saida yayi mata Goma kafin ya dakata,nishi take tana
maida ajiyar zuciya kafin ta tashi ta zauna,tana kaiwa hannun ta bangarori da dama
na jikinta,inda duk zafin dukan yake ratsata.
"Kinsan dukan danayi miki na menene koh?"
"Jijjiga kai tayi alamar ba ta saniba"
Ohh baki ma san mai kikayimin ba,zaton ki dan kin sheqe ayar kine kaɗai zan bata
lokaci na wajen yimiki haka,kinada wannan darajar,ai ba sheqe ayah ba in kinaso
kije kasata ma bai dameni ba,amma gonata da kika shiga shiyasa nake miki hukunci
saboda karki sake shiga.
Meyasa kukaje asibiti kukace cikina ne a jikinki,wani na turoku bana son a sani kar
asirina ya tonu. Koba haka kukace ba keda bunsurunnaki?"
"Eh.....eh haka muka ce"
"Meyasa to kuka ambaci sunana a sharholiyarku,wato saboda kun rainani koh,kin taba
ganin nayi irin wannan ƙarƙantaccen aikin?"
"Ahah baka taba,sunƙi zubar mana da cikinne wai sai mun kawo shaidu,shine mukace
naka ne,kace kuma idan kazo abin bazayyi kyau ba. Wlh ba hakan muke nufi
ba,kawaidai mun faɗa ne dan suyi mana aikin"
Wata dariyah yasake yi ta gefen baki,kana ya sosa ƙeyarsa da kan cable ɗin..
"Lallai yarinyar nan kin dakeni da mamakinki,yanzu da badan yarona yazo ya faɗamin
ba saboda ya jiku,saidai ayi ta faɗan na miki ciki a cikin gari,a zubarmin da
mutunci. Ni bansani ba ashe so kike na miki ciki,toh shikenan bazan miki ba ni nafi
ƙarfin haka,amma in hakan kikeso zan saka a sake yimiki wani,idan kikaje zubarwa
kice goje ne yasaka ayimin,shine kuma,ya turo yace ya zubarmin....barinaje na dawo
na kaiki cikin maza biyar su yayyagaki,wannan da kikayi ba iskanci bane ai"
Oh dama wannan laifin tayimasa shiyasa yake jibgarta,nifah nayi zaton ma bayaso ta
dunga iskanci ne,tabbb lallai Atika ma tanada kasada sosai.
Wani ihu tafara tana haɗa hannaye,roqonsa take bilhaqqqi,amma saima ya rufe ido.
"Dan Allah dan ya rasulullahi Yaya goje kayi haƙuri,wlh bazan ƙaraba na tuba,gaji
kizo kI ceceni wayyo gaji."
Tunda ake ƙwallon ball da ƴaƴan nata bata yi ko tari ba sai yanzu ta fito,haba a
matsayinta na uwa kuma tana jin kukansu dole abin yayi mata zafi.
Da goje suka haɗa ido lokacin data fito ɗin,kana ganin fuskarta kasan in ranta dubu
ne to duk ya baci.
"Amma dai goje tunda ka daketa tabaka haƙuri ai shikenan zance ya wuce ko"
"A tunanin ki? Har yanzu banji muryar kaina tace na barta haka ba,kee tashi kije
ranar can ki zauna"
Filin tsakar gidan ya nuna mata wanda yayi zafi zau da rana,ki saka gwiwoyinki a
wajen ki tsaya haka,karki tashi har sai nazo na ce hakan. Ban gama dake ba
tukunna,zanje ba sallami wancan abokin aikinnaki ne"
Har zai fita ya kalli gaji ya kalleni,wani dumm naji mai kuma nayi yanzu.
"Ban yarda ta tashi ba kokuma abata ƙwayar abinci ko ruwa,idan kika bata...naji
labari saina sakaki a ɗaki da karnuka sun yayyagaki. Ke kuma idan ta bata abinci
kokuma ta tashi a wajen baki faɗamin ba,nasamu labarin ke zan yiwa abinda na faɗa
zanyi mata"
Ya ƙarisa maganar yana tabbatar min,ɗaga kai na fara ba tsayawa har ya fita ban
dainaba.
Shanyar kayan dana wanke nake,sai ji nayi gaji takama kafaɗata ta jefar dani
ƙasa,tohh ni kuma mai nayi,wato yakama dukan ƴaƴan ta tashaqa bari ta huce akaina
ni marar galihu.
Kallonta nake da mamakin mai kuma nayi ni,ƙasar da take bakina nake sharewa,saboda
yanda na kifu a bakin.
"Nikuma gaji mai nayi miki"
Yau ko inna ma bance ba,dan na kula matar batada darajar daza'a mutuntun tata,kuma
ƴaƴan ta ma ai haka suke ƙiranta.
"Ohh baki ma san mai kikayimin ba koh? Nakula hadda wani sanja murya ma kike,dan
kinga mijinki yayiwa ƴaƴana fata fata shine hakan yamiki daɗi koh?"
"Taya za'a duka wani mutum yaji daɗi,indai bashine marar imani ba,kuma dai naga
kina gani wanda yayi dukan nima ba ƙyaleni yayi,bare kice nina zigashi"
"Zigo? Kima zigashin mana,kekam ai a tafin hannuna kike in shi ya gagareni,nasha
neman maganin tanƙwasashi abu ya gagara,saboda asiri baya kamashi,amma kekam ina ba
irin jikinsa ne dake ba koh. Wato saboda ke ga munafuka hadda faɗamasa atika a
ɗakin mairo ta buya koh,ke a dole zakiyi gwaninta a wajen wadda bai ɗaukeki mutum
bama ballantana kuma matarsa,saboda kallon kuɗin caca yake miki,ko saniyar daya
ciyo a kalankuwa tafiki daraja a wajensa,ganinki kike mace amma keba mace
bace,wacce namiji yakasa ɗaga ido yakalla za'a ƙira mace,kuma batun Atika yanzu zan
dauketa a wajennan,inkin isa ki faɗa ki gani. Abinci kuma zanga wanda zai sake baki
a gidannan,aiki kuma babu fashi saikinyishi"
Maganganu taci gaba da gasa min masu zafi,haushine ya turnuƙeni zuciyata tana
zafi,ina na ɗebi iya inda zan iya ɗauka,dolene na fesar mata da sauran.
Kallonta nake tana ƙoƙarin isa inda atikan take.
"Hmmm wai gaji saboda kina matsayin matar ƙanin baban mijina,matsayin uwata aka
baki ne,ke baki san in kinkai mutum bango ki dakata bane? Harda zaki ƙirani ba mace
ba,shiyasa ai naga ƴarki da take kasa darajarta a waje kowa ya ɗauka kaman karya
za'a ƙirata da mace koh,kokuma ke da bakisan soyayyar miji ba yanacan gidan karuwai
a can yake wuni,ke bakida aiki sai dafawa ki ciyar masa da ƴaƴa za'a ƙiraki da
macen. In kincika macen kema da ki hanashi zuwa wancan ƙazamin gidan mana.Ai gwanda
ni ba mata yake biba ya ƙyaleni,ra'ayine bayayi,kekuwa fah yanason matan amma mai
yasa ya tsallakeki.
Sannan dakike cewa wai inna isa na faɗamasa zatonki idan kin ɗauketa a wajen zanyi
shuru ne? Wlh saina faɗa,haka kawai ki ceceta nayi shuru ya gano ya fatattakani bai
dameki ba ko,nina aiketa yawon sharholiyar komai.
Abinci kuma kada ki bayar,nima kuwa bazan sake miki komai na gidannan ba,inkin ban
abinci nayi miki,in baki bani ba nima bazanyi ba,inji ce ni saida mai nayi aiki"
Ina gama faɗin haka nakama hanyar ɗakina da sauri,saboda kada ta biyoni ta
fatattaka ni kaman yanda ta naga tana huci,cike kuma da mamakin irin furucin dana
yi.
Haba ai dole nayi,ko damo aka matsa ai dole yayi cizo,wanka zanyi na kwanta,nasan
dole goje zai dawo basai dare ba,saboda ya ajiye atika a tsakar gidan. In yaso
saina tambaye shi naje gidan su Shareefah,nasan zan samu abinda zanci a gidan.

Littafi na ɗaya ne dana biyu kaman yanda na sabayi,na ɗaya bati siddan,na biyu kuma
Naira 300 ne dan haka zaka iya biya tun yanzu kafin a shiga kashi na biyu.

3131951977
Auwal Sadiya
First bank
Ko katin mtn ta nan
09035784150

VTU ta nan
2347068390570

Shaida kuma ta nan


09035784150

Ƴan niger ku tuntubi wanann number.


+227 97 21 16 15
----------------------------------------------------

Sadi-sakhan ceh
09035784150
Share please

*SANADIN CACA*

Mallakar SADI-SAKHNA

PROFICIENT WRITER ASSOCIATION

*USERNAMES*
FACEBOOK PAGE:Sadisakhna
WATTPAD:@SAKHNA03
AREWABOOKS:@sadeesakhna
PHONE NO:09035784150
________________________________
*Book 1*
Chp[15]

[Goje a mahangar gani]

Har na fita daga gidan rai na bai daina zafi,lallai wannan yarinyar wuyanta yayi
kauri. Lokacin danaji maganar nan baƙaramin baci raina yayi ba,kaman ni....nine
zatace nayi mata ciki,kai barima na koma nasake tattaka ta dan ubanta.
Juyawa nayi gidan,har nafara shiga na hango gaji ta jefar da Sumaimah a ƙasa,wato
akan ta zata huce saboda na daki ƴar ta ko.
Maganganu gajin tafara faɗawa Sumaimah,wacce kana ganin fuskarta kasan abinda take
faɗamata ba ƙaramin zafi suke mata ba. Kai mata mata.....shiyasa fah ni banason
shirgi dasu,wato rashin shiga harkarta da banayi shima abin magana ne da har za'ayi
mata gori dashi.
Niyyar ƙarisawa nayi,ganin gaji tana shirin ɗauke Atika daga inda nace ta
tsugunna,dama nasan hakan zata faru,tsoratar da Sumaimah zatayi ta ɗauketa daga
wajen,musamman data ganta wawiyah ce batada wayo.
Siririyar maganar ta naji,cikin sanyi take amayarwa gaji duk maganar data fesa
mata,dama ta iyah magana haka,nida nayi zaton ma kurmiyace. Tun bata kai haka ba
muna yawan cin karo da ita a hanya in zata makaranta,sai ta juyah da gudu kaman
taga aljani,tun abin yana bani mamaki har na daina.
Amma yanzu ta dawomin da mamakina,ina ganinta wawiyah ashe tanada wayo,ehh tunda
gaji tasaka wannan magana da alama takaita bango ne.
Fitowa nayi daga gidan na tafi inda su Tunga suke hukunta Sageer,har na isa wajen
da tunanin faɗan matan a raina.
Lokacin dana isa wajen sun mammaujeshi sun ɗaure shi,a zaune suke suna taɗin
siyasa,na wani chairman paty dayake so muyi masa aiki.
Ina isa wajen sukayi shuru tareda bani gaisuwa,amsawa nayi kana na samu waje na
zauna.
"Ogah goje gashi nan mun ɗan tabashi kaman yanda ka nema. Iya shegen ma ya iya
kawai,ashe ƙaramin ɗan iskane,daga dukan farko fah ya rojaye kaman wata ƙanƙara"
Ragarus ne yafaɗa yana cigaba da jujjuyah sandar hannunsa.
"Hmm ku sunceshi ku kaishi ƙofar gidansu,duk ya isheni bana ma son ganinsa,ku
tabbatar kun bar masa jan gargaɗi a rubuce na saka hannuna"
Dama duk masu bin matannan suna lalatasu yanda kasan ƴan daudu haka suke,sai shegen
surutun tsiya da ƙarya,matan ma sun fisu ƙwari. Ko mai ma matan suke gani a jikinsu
oho.
Jawabin da chairman party yafaɗa suka maiyarmin,akan yanaso muyi masa aiki,saidai
suyi masa badai ni ba,dan inada wani aiki da zamu fita da ƙungiyar DC,Jiyah suka
turomin takardar inda zan samesu da daddare,za'a tattauna yanda plan ɗin zai
tafi,nasan bazai wuce sati ɗaya ba samu fita aikin.Bazan faɗawa sauran abinda yake
faruwa,iyah Tunga ne kawai yasan zancen. Yau ma nake shirin naɗashi shugaba mai
riƙon ƙwaryah kafin na dawo,bazayyi yu dan bana nan na hanasu yin aiki ba,musamman
kuma dana san zasu samu kuɗi sosai idan sunyi ɗin.
"Bakomai za'ayi masa aiki,duk da bananan a lokacin,amma zan yimasa gargaɗi kaman
ina nan. Zanyi tafiyah maybe wani satin,zan iyah kaiwa satin ban dawo ba,dan haka
Tunga zai zagorance ku idan bana nan.
Basuji daɗin abinda nace ba,sannan nasan dole zasuso sanin ina zanje,amma koda zasu
sani ba yanzu ba tukunna.
Jeji na nufah Ina riƙe kai,wannan ciwon kan narasa daga ina yake zuwa,duk sanda
nafara jinsa saina dunga jin kaman ba nanne yakamata na kasance,kaman inada wani
wajen bayan nan,kaman akwai wata rayuwar bayannan danake da itah. To amma a ina
take,yaushe zan bar wannan masifaffen ciwon dayake juyar da rayuwata,haka nake
kwana na tashi,amma tunda nake bantaba jin nutsuwa ba,kullum acikin duhu
nake,lokaci lokaci ko a bacci ina hango wani haske ɗan ƙarami a can nesa,sai nayi
gudu nayi gudu inaso na kamoshi sai ya bace ya ƙyaleni ni kaɗai.
Ƙarisowa wajen bukkar tawa tacikin jejin nayi,da sanina nayi mata fenti baƙi,saboda
a baƙin wajen kawai nake iyah bacci ,hakan ma nafison cikin jeji,shiɗimma ba cikin
salama ba,sai an kai ruwa rana,kowa ka tambayeshi yasan ba ƙalau nake ba,akwai
abinda yake cin rayuwata da kaɗan kaɗan.
Bani na tashi daga baccin wahalar daya ɗaukeni ba sai a kusan la'asar.
Tashi nayi naga abinci Tunga yakawomin,dama hakan yakasance al'adarsa,bansan mai
nayi masa ba ya damu da rayuwata,shin mai nakeyi daya kamata a damu dani?.
Banci da yawa ba na ajiyeshi nabar bukkar. Kai tsaye gida na nufah,nasan waccar
sheɗaniyar yarinyar ba lallai ne ta tashi ba tana wajen.
Duk hanyar danabi yara guduwa suke,wasu nayi ƴar dariya wasu kuma na jijjiga
kai,amma dai hakan yana min daɗi,naga ana tsorona,koba komai zan jini tamkar sarki.
Pa kwance na ganta luff a inda nace ta tsugunnan,inuwa har da kusa iso inda take.
"Keee...."
Firgitt tayi tatashi zaune,jikinta sai rawa yake na azabar data sha,kaman wacce
tayi wanka da rairayi,ƙasa take kallo,amma kana iya gano bushasshen hawayen daya
haɗu da ƙasa a fuskarta.
"Tashi ki tafi,gobe ma ki sake sakoni cikin sabgarki"
Yunƙurin tashi tayi,mangar mangar tanufi ƙofar su,wato sai gida an doki kare aka,da
sanda yaje satar kajin gidan basu sani ba kuwa.
Takardar da aka aikomin nake karantawa,abinnan yana bani mamaki,yaushe inna ta
sakani a makaranta ne,kwata kwata bana tuna shigata makaranta,amma kuma ina karanta
abinda aka rubuta da hausa da kuma turanci,ko yaren turanci akayi sainaji inajin
mai akace,har naji inason na maida amsa kuma da yaren.
Ƙarar motsin tafiyar mutum naji,hakanne yasa ajiye takardar ina jira naga wanene
zai shigo.
Sallamar Sumaimah naji a bakin ƙofar,saida tazo bakin ƙofar naga kayan dana bata
wanki ne a hannunta.
A bakin ƙofar ta tsaya,ita bata shigo ba ita kuma bata koma ba,ganin abin har
yafara bani haushi yasa nace.
"Idan bazaki shigo ki ajiye ba toki koma dasu"
Da sauri kaman jira take ta tsallako cikin ɗakin,a gaban akwatina ta
tsugunna,dayake can take kallo sai hakan yabani damar kallon bayanta. Atamfah ce a
jikinta sabuwa,tunda nake ban taba kallonta da sabon kaya ba sai yanzu..
Zuge akwatin tayi ta jera kayan a cikin tass kafin ta mayar ta rufe. Kallon ɗakin
nake sai a sannan ma na kulada gyaran da tayiwa ɗakinsa,harda yanar gizon da take
jikin ɗakin duk ta cireta,nayi ƙarya idan nace bayyi kyau ba.
Tashi tayi zata fita saikuma ta tsayah,kallonta nayi anan nagane abu takeso
tace,ganin yanda bakinta yake motsi.
"Menene"
Na tambayeta saboda na hutasar da itah,nasan in dai a hakanne saimu wuni batace
komai ba,so nake kuma ta tafi tabani waje akwai abinda zanyi.
"Uhmm ......uhmm dama inaso nake gidan su Shareefah ne ƙawata,babu nisa kafin
magriba zan dawo"
Shuru nayi ina nazarin maganar tata,shin dama na taba cewa karta fitane,intanaso da
koma gidansu ma mana,yau ubanta yabani kuɗina yace ƴar sa ta dawo gida ba riƙeta
zanyi ba,wani salon munafurci ne hakan ko mai?.
"Shin dama tunda kikazo gidannan kinji nace kada ki fitane?"
Saurin jijjiga kanta tayi tana wasa da ƙasan rigarta,sai tayi kamar an tare bera a
buhun daddawa.
"Ahah ba haka bane,Allah ya hani mata da fita daga gidan mazajensu batareda izinin
mazajen ba,idan kuma mace ta aikata hakan to mala'iku zasuyi ta tsine mata har taje
ta dawo,shiyasa idan mace tanason gujewa hakan to ta tambayi izinin mijinta a duk
lokacin dazata fita waje"
"Tohh wata sabuwa,da ba'a garinan kike ba sai nace a ina kikaji,jeki idan zaki wata
anguwar ma kada ki sake zuwa kimin wannan iyayin"
"Toh nagode"
Bata jira na bata sake cewa komai ba ta fita da sauri daga ɗakin.

••∆∆∆••

Tunda ƴan gidan sukaga Deejah ta ƙona ɗakin rammah kowa yake masifar tsoronta,komai
tayi babu wanda yake cewa uffan a wunin ranar..
Da dare yayi ɗakin yara ammi ta nuna mata,kaman bazata shiga ba kuma sai ta nufi
ɗakin,shigarta keda wuyah sukaga yaran ɗakin kowa yana fitowa da gudu,da suna ihu
wasu kuma suna matsar ƙwallah.
Matan gidan duk wadda da yaranta a ɗakin fitowa suka yi,jin ihun yara yaƙi ci yaƙi
cinyewa.
Asiyah ce tayi ƙarfin halin faɗin abinda ya faru,tunda ita da ɗab girmanta,dan
zasuyi shekaru ɗaya da Deejah.
"Muna kwance kawai ji mukayi ta fara dukanmu,wai duk mu fita daga ɗakin mu koma na
iyayenmu,ba kowa yaƙi ajiyeta a ɗakinsa ba,itama bazata kwana da kowa ba,kuwa wai
duk wanda yasake shiga ɗakin saita vabbakeshi da ransa..
Shuru sukayi suna sauraran Asiyah,yayinda kowa yakama hannun ɗansa yana
rarrashinsa,kowa ta abinda yake faɗa ya shige ƙofarsa.
Washagari da safe kamar kullum hayaniya ta kaure ko ina,itadai rammah ranar a
gidnasu ta kwana,saboda anyi ta bata baki ta zauna tace sai uwaisu ya rufa mata
ɗaki kafin ta dawo,yanzu dole zaije ko ina fallan kwano yake ya nemo yazo ya
rufamata ɗakin..
Fitowa tayi tana mitstsika ido,jikinta duƙu duƙu yanda ta kwanta haka ta tashi.
Ƙofar su ammin tashigo ana zuzzubawa yara koko zasu tafi makaranta.
Tana zuwa batayiwa kowa magana ba ta ɗauki ɗan botikin kokon ta kafa a
bakinta,ƙwatt ƙwatt saida taga bayansa ta ajiye tana gyara baki.
Yaran da suke zaune a gaban ammi suna jira a saka musu,ganin abinda ya faru suka
fara kuka wasu harda burburwa. Sakin baki ammi tayi ludayin garwayawar a hannunta
tana kallonta.
"Innar ubaidu wai baki gama saka sukarin bane,ki miƙomin nasamu nasha na tafi gonar
can yaukam na dubo,zamu mai taki"
"Uhmm koko kam ai ya ƙare"
"Ke wannan wanne zancen shashanci ne,idan kunyi abincin siyarwa ku hanani yau kam
ai nina saya da kuɗi na koh"
"Ehh nima danace maka ya ƙare ai bani na shanye da ƴaƴana ba koh? Ƴar ka ce ta
shanye"
"Wacce ƴar tawa wai,ya faɗa yana banƙada labulen ɗakin"
Da Deejah suka haɗa ido tana suɗe bokitin kunun,dariya tayi masa irin ta aljanu,da
haƙoranta kamar tsitstsige.
"Na shanye baba,na shanyen kunu,aradu ga zaki kamar an saka zuma,wanda wanccan
babannawa yake bani babu suga haka,ashe bayyi ƙaryaba daya ce a cikin gari daɗi
kukeji,ko kazar gidannan dana ci jiya tafi zomayen jeji daɗi ,ai nikam naji daɗi na
tunda na dawo nan da zama"
Wani irin rammm gaban uwaisu ya buga,shida yake cewa yau zai maidata wajen ubanta
yabashi haƙuri,shine zatace wai bazata koma ba anan zata zauna,in shi ina zama da
aljana gida ɗaya,kokon da za'a rabawa yaran gidan harda shi,ta kafa kai ta
kwankwaɗeshi,da wanne tukunn zaiji? Ga gyaran ɗakin ramma ma zaizo yayi.
Jefarda bokitin tayi can gefe,barass kuwa ya rabe biyu,dama yaji jiki sosai.
Hanyar waje ta nufah tana goge hannunta a jikin kayannata,jinin kazar jiyama yana
jikin kayan.Wato haka takeyi shiyasa inta zo kusan mutum warin dauɗa ya dameshi.
Tana fita daga ƙofar Ammi ta kaɗe zaninta ta tashi,kallon uwaisu tayi tareda cewa.
"Inka fita ka siyomin bakitin roba a waje,a gaban idon ka ta fasamin nawa"
Tunzurowa yayi jin abinda tace.
"Mai kike nufi kenan,komai tayi nizan biya,saboda nine nayi ko?"
"In bakaine kayi bama ai ta dalilinka tazo gidan tayi,tunanin ka kenan ni zan dunga
ɗaukar asara,saboda nice nayi cacar aka kawomin ita?"
Buuu ya kaɗe rigarsa yayi hanyar waje,da Rabi yaci karo a hanyar mashiga matar
ƙaninsa umaru.
Kuka take ta girmanta,hannunta ɗauke da matacin ƙosan ta. Saida tayi kukan ta matse
kafin tafara magana cikin masifah.
"Wlh bazan yardaba,uban me akemin a gidan dazanyi haƙuri,ba'a ɗaukemin sabulu
ba,magani kokuma ishashshen abinci,nazo na samo kuɗin jarin da taimakon ƴan uwana
ina sana'a,kuma azo a nakasa ni wlh sai an biyani,in ba haka ba wlh ɗan sanda zan
ƙira"
Tsayawa uwaisu yayi yana kallonta tana masifah tana kuka,ta inda take shiga batanan
take fita ba,buɗe baki yayi zai tambayeta yaji wata matar tana faɗamasa abinda ya
faru.
"Waccar ƴar taka da tazo jiyace tana suyar ƙosai tashigo ƙofar,batayi wata-wata ba
ta dira akan suyar ƙosanta,wanda ta tara a cikin matacin duk ta cinyeshi,a garin
ɗiban ƙosan kuma ta zubar mata da man suyar wanda yake kan wutah"
Runtse ido uwaisu yayi yana maimaito jawabin,iyah jiya kawai aka kawota amma tayi
asarar da baisan adadinta ba,wannan wace irin masifah ce,tunda yake ko ƴaƴan sa
basu taba yimasa abinda tayi ba. Shin ta inama zai fara,gashi tafita waje,yasan a
can ma dole sai tayi wani abun. Cikin sanyin jiki ya fita wajen,jikinsa ya haɗa
gumi shirkif,duk da sanyin safiyar da ake.

Littafi na ɗaya ne dana biyu kaman yanda na sabayi,na ɗaya bati siddan,na biyu kuma
Naira 300 ne dan haka zaka iya biya tun yanzu kafin a shiga kashi na biyu.

3131951977
Auwal Sadiya
First bank
Ko katin mtn ta nan
09035784150

VTU ta nan
2347068390570

Shaida kuma ta nan


09035784150

Ƴan niger ku tuntubi wanann number.


+227 97 21 16 15
----------------------------------------------------

Sadi-sakhan ceh
09035784150
Share please

*SANADIN CACA*

Mallakar SADI-SAKHNA

PROFICIENT WRITER ASSOCIATION

*USERNAMES*
FACEBOOK PAGE:Sadisakhna
WATTPAD:@SAKHNA03
AREWABOOKS:@sadeesakhna
PHONE NO:09035784150
________________________________
*Book 1*
Chp[16]

[Sumaimah a mahangar gani]

Ina komawa ɗakin inna tsalle na farayi da murna,banyi zaton zai barni na fita hakan
cikin sauƙi ba.
Sai yanzu ne zan yi fita ta daɗi,ba wancan ɗiban ruwan ba,shikenan idan naje sai
magriba nadawo.
Hijabi na saka wanda inna mairo tayimin a auren,babu laifi mai kyau nekam a daidai
kuɗinsa.
Takalmin shima na ɗakko,dan tunda aka kawoni gidan ban ta'ba sakashi ba sai yau.
Bayan na shirya ƙofar gaji na shiga yi mata sallama,hmmmm zata kulani ne ma,tana
fama da jinyar ƴar ta.
Nazo shiga ƙofar tsayawa nayi jin abinda suke cewa.
"Ai duk laifinkine gaji,tun yausshe kike cewa zaki yi maganinsa har yanzu abu
yaƙiyi,kai ba abin ka ɗakko masa ƴan daba ba shine shugabansu,mutanen garinma
tsoron hukuntashi sukeyi,sannan asiri tun yaushe kike cewa zakiyi har yanzu bakiyi
ba"
Atika ce take faɗa tana kuka saboda gaji tana dunduma mata jikinta take faɗa.
"Dallah yimin shuru,ke bakiga abinda kikayi ba koh,kinje kinyi ciki a wajen zubarwa
kince nasa ne,dama ai dole zance ya koma kunnensa,kuma sanin kankine ba shuru zayyi
ba da wannan lamarin.....waccar yarinyar cema dole zata shiga hannuna na kamata
gamm,har wuyanta yayi ƙwari tana gasamin magana son ranta? Lallai batasan wacece
niba da alama"
Jijjiga kai nayi jin maganganunnasu ba wasu sabi bane,dama na saba dajin irinsu tun
a gidanmu.
Ƙarisawa nayi cikin ƙofarta ta bakina ɗauke da sallama,sun ɗan razana saboda
tsarguwar kona ji mai suke cewa,nikuwa ban basu ƙofar dazasu san cewar na jisun ba
sam.
"Uhm gaji nizan tafi gidan ƙawata saida magriba zan dawo"
Wata harara ta maka min,daganan bata sake cewa komai ba tacigaba da kulada ƴar
tata,nima kuma daman ban tsammaci amsar ba,na faɗa mata ne saboda haƙƙinta ne a
matsayinta na wacce muke zaune gida ɗayah.
Tafiyah nake cikin nutsuwa hankali kwance har na isa gidan su Shareefah,kasancewar
ranar asabar ce nasan daman tanan bata tafi makarantar islamiyyah ba.
Da tsalle ta tarbeni tana murna muka zauna,sai dariyah take tarasa abincewa,da
alama zuwannawa yayi mata bazata.
"Shareefah ya mutanen gidan?"
"Uhm gida kalau yanzu nnan ummah kuwa ta tafi gidan suna"
Bayan mungama gaisawar shuru nayi,idan nace banajin yunwa wlh nayi ƙarya,jikina
karkarwa yake kaman an jonamin lantarki,kunya nake ji na roƙeta abinci,amma haka na
daure na tambaya.
"Uhm.....Shareefah yunwa nakeji kunada abinci dan Allah"
Zaro ido tayi tana tafe kirji,da alama ta kulada yanda jikina yake karkarwa ne.
"Nashiga uku Sumaimah ji yanda jikinki yaje karkarwa,bankula ba saida kikayi magana
nagani. Abinci babu yawa yara sun cinye,amma barina kawo miki sauran kici,inyaso
saina yimiki wani abun ko ɗan wake ne"
Tana gama faɗin hakan ta tashi da sauri ta kawomin,tuwon shinkafa ne da miyar
taushe.
Malmala biyu ce,saboda yunwar danake ji nan da nan na cinyeshi,kai abinci rahama
nan da nan naji jina da ganina sun dawo waral.
Tashi nayi ina tayata muna jefah ɗan waken dayake da yawa tayi harda na gidan,zance
muke wanda yawanci rabinsa na islamiyyarmu ne,yanda take bani labarin ƙawayenmu
zasuyi aure,wata ƙwallah ce ta zubomin nayi saurin gogewa,uhmm su zasu auri wanda
suke so suma suna sonsu.
Shareefah ta kulada yanda yanayina ya sanja,ta buɗe baki zatayi magana kenan Hamisu
yashigo ƙanin Shareefan.
"Anty Shareefah gacan ƴan sanda zasu tafi da baban Anty Sumaimah caji office"
"Me ubana kuma? Toh mekuma yayi za'a kaishi caji office"
Shareefah ce ta kalli hamisun cikeda damuwa,musamman ganin yanda yanayin ƙawar tata
ya sanja.
"Hamisu mai yafaru,anya kuwa kaji daidai?"
"Wlh shi naji ana cewa,wai wannan ƴar da aka bashi a caca ce take jawo,ta zubarwa
matar gidan man suyar ƙosai ta cinye ƙosan kuma,sannan ta ƙone ɗakin inna rammah.
Amma abinda yasa aka kamashi yanzun wai wani yaro ta bulawa kai da dutsi,yanzu haka
an tafi asibiti dashi kaman bazayyi rai ba,shine da batakai ɗauri ba aka kama
Babanku sai yayi biyan kuɗin magani"
Duk maganar dayake ban fahimce shi,wacce ƴa aka bashi a sanadin caca kuma,bayan ni
daya bayar wata kuma aka kawo masa? Shareefah na kallah wacce iyah ita kaɗaice
nasan zata bani amsar wannan tambayar,dan daga ganin yanayinta ya nuna tasan kwanan
zancen.
"Wacce ƴa yake magana akai ne Shareefah?"
Shuru tayi da bazata bani amsa ba,can kuma saita kwashe abinda ya faru ta
faɗamin,yanda baba yayiwa ɗan fulani wayo dan ya auri ƴarsa,ƙarshe kuma rishe ya
juye dashi......wai ni meyasa irin wannan abubuwan suke faruwa da garinmu ne,kodan
muna lungu shiyasa abubuwan ashsha sukayi yawa kai. Cikin garin Kwalin ma haka suke
fama da irin waɗannan abubuwan?.
Jijjiga ni Shareefah tayi,tana zaton koh suman tsaye nayi,habadai wannan abun
yasakani suman tsaye? Ai naga wanda ya fishi ma.
Ɗaɗɗaya nake jefah ɗan waken a bakina,ɗazu yabani sha'awa sosai,amma yanzu ya fita
akaina sam,saboda abinda yafaru.
Tundaga lokacin kuma zancen namu yakoma na Deejah,sabuwar ƙanwar tawa,wani abun
nayi dariyah wani na jijjiga kai,ance dai mugunta babu kyau,amma wlh banji
tausayinsu ba sam,suma ji yanda naji inda daɗi.
Idan an kwana biyu zanje gidan nima na ganta,yanda ake bani labarin kam batada
maraba da aljana.
Ganin duhu yafara yasa na tashi zan tafi,har sannan umman Shareefah bata dawo ba.
"Toh Shareefah barina tafi gida nikam duhu ya fara"
"To shikenan Sumaimah kici gaba da haƙuri komai zai zai zama tarihi,karkiyimata
wanke wanken gobe,kiyi zaman ki,zan aiko miki da abin karyawa Inshaallah,to wai shi
meyasa bazai dunga baki abinci bane,ba zamansa kike bane?"
"Bamu kai kan wannan ba tukunna,amma kuma a yanda na kula kaman yanada sauƙin kai"
"Eh toh hakane,kaman yanda kika ce zan dunga kawo miki abincin har sai lokacin da
taga gurbinki kuka daidai ta,shima kuma dan Allah Sumaimah ki dunga gwada dabararki
irin ta mata akansa,idan kinga kuma abin bazai gyaruba sai a san nayi"
Kallonta nake da tana maganar,shin ana samun ƙawa irinta kuwa yanzu,nikam duk da
banyi sa'ar mijiba amma ƙawa kam mashaallah kawai zance.
Rungumeta nayi ƙyam ina mayar da kukan dayake idona,saboda godiyar danake son
yimata ma bazai isa ba.
Bayan munyi sallama hanyar gidannawa na kama,ɗazu Shareefah tace ko zanje caji
office nace mata bazani ba. A tambayar danayi iyah gidnasu kawai na tambaya,koda na
tambaya ma nai zanje na iyo,nace masa me? A matsayina dai na ƴar sa ina fatan Allah
ya rage masa nauyin ruwan daya jawowa kansa,har ya jawowa wasu ma.
Lokacin dana isa gidan wasu masallatan ma ana ƙiran sallah. Kaman kullum gaji tana
ta fama da yaranta,nidai bance mata na dawo na wuce ƙofarmu.
Alwalar magriba nayi na shiga ɗaki,riƙeta zanyi ba lallai na fito ba sai gobe. Ta
wani lokacin gwara gidannan,koba komai mutum zai samu nutsuwa da daddare.
Bayan nayi isha fitowa nayi zan shiga banɗaki,goje nagani da wasu baƙaƙen kaya ya
fito daga cikin ɗakinsa,wata hula yasaka a kansa itama baƙa irin kayan
jikinnasa,yana rataye da wata baƙar jaka.
Bai kulada ni ba saboda yanda na ɗauke numfashina har ya wuce,ban taba ganinsa da
irin waɗannan kayan ba,inda banga yanayin jikinsa ba da kuma kayan,bazance shine
ba.
Ina kuma zaije da darennan sanye da waɗannan kayan,rai na dai bai kwanta da
lamarinba na shige banɗakina.

__***__

[Goje a Mahangar gani]

Daidai misalin ƙarfe 8:00pm na dare na shirya cikin kayan da suka aikomin,wanda
shine unform da kowa zai saka na fita aiki.
Bayan nagama saka kayan ɗaya jakar na ɗakko,bindiga ce a ciki sabuwa dal babba mai
babban aiki,sai kuma wasu ƙannan bomb guda biyar,sai kuma hula mai tare poison gas
guda biyu da kuma wuƙaƙe ƙanana wanda ake sakawa a jiki saboda kota kwana.
Jinjina kai nayi ina mamakin ƙaurin suna irin na wannan ƙungiyar,dole manyan
sojojin ƙasa da jami'an tsaro su bazama neman ganin sun wargaza ya kam. Makamansu
ko wasu sojojin basu da su. Anya kuwa babu hannun wani babban ƙasa a cigaban
ƙungiyar nan. Oho koma menene su suka sani,ni ina ruwana.
Daukar jakar nayi na lanƙaya a bayana,yayinda nake duba agogon hannuna naga lokaci
shima duk yana daka cikin abubuwan da suka aikomin dashi.
Bayan na fita daga gidan hanyar bakin gari na nufah,inda jan jira motar dazata
ɗaukeni.
Banyi minti talatin ba kuwa sai gata tazo,baƙace dal mai numfashi,kota chairman ɗin
garinmu bata kaita ba.
Buɗe gidan baya nayi na shiga,drivern yaja muka nausa wata hanyar da tayi jejin.
Wannan karon basu rufemin idi ba har muka isa sansani wancan lokacin.
Shiga mukayi cikin wajen,wannan karon ba hanyar da mukabi wancan lokacin muka bi
ba,watace daban.
Mutumin daya tabeni a karon farko yauma dashi nayi arba,saidai yanzu suit ne a
jikinsa yana hakimce a wata jar kujera,wajen ya ƙawatu kam sosai,babu yanda za'a yi
mutum yasan akwai wannan daular anan wajen haka.
Mutanen wajen na kalla mun kusa mu goma sha huɗu dukkanmu sanye da kaya iri ɗaya.
"Uhm uhm to abokan aiki barkanku da isowa,sabin zuwa kuma muna yi muku barka da
shigowa. Dukkanku sabine tunda baku taba haɗuwa da ogah na uku ba,saidai wasu a
cikinku ba wannan ne aikinsu na farko ba,wasu kuma yanzu zasu fara.
Mun taraku ne saboda akwai aikin dazamu fita yau,saidai inaga bazayyi ba,dan har
yanzu jirgin da muke jira ya kawomana kayan aiki da kuma bayanan yanda abin zai
kasance bai iso ba.Ɗaya yaranmu dasuke dajin Kaduna su sunfita aiki,ku kuma sai
munga taku alamar."
Zancen banza kenan,dama kawai taramu sukayi su ganmu,shiyasa fah na tsani zama a
ƙasan wani.
Tashi nayi na tsaye zan fita daga wajen batareda nace wani abunba.
"Kai goje ina kuma zakaje,inkana shugaba a sansaninka kayi abinda kaga dama,har ka
ture wani daga kujerarsa ka hau,to anan karkayi wannan tunanin sam,in mutum a
cikinku yana cin ƙasa to nan ta shuri ce"
Juyowa nayi na kalleshi,ohh tsoro yake karna yi wani abun na karbi kujerar sa
komai? Har yavani dariya ma.
"Hmm haba ogah da gimanka kafara wannan maganar tun yanzu? Gida dai zantafi,tunda
abinda nazo dominsa bazai faru ba"
Sauƙe ajiya yayi ganin ba abinda yake tunanin bane,wanne wawa ne zaizo waje lokaci
guda yakai farmaki,ai sai yaga kamun ludayin kowa tukunna.
"Ba tafiya kowa zayyi ba,munada wajen motsa jiki da horo,a can zaku zauna har zuwa
lokacin dazaku fita aiki"
Toh hakan bai wani batamin rai ba,dama ina buƙatar hakan,sannan nariga na sallami
yarana ma kafin nazo ɗin.
Har mun tashi zamu bar wajen wani ya shigo wajen da sauri.
Gaban wanda ake ƙira da ogah na huɗun ya nufah,ƙusƙus sukayi magana,daga nan sai ya
fitah.
"Toh da alama ma basai munyi jiran ba,mission ɗinku a yau sai fara,an kawo kayan
aiki da bayanan"
Yana faɗan hakan ya fitah,kayan aiki kuma,bayan waɗanda suka bamu hadda wasu zasu
sake bayarwa..
Muna dai nan zaune suka fara shigowa da wasu jakakkanuna daban.

Wasu motocine dogaye masu tafiyah irin cikin sirinnan a jeji,su zamu shiga zuwa
garin gwagwalada. Daga nan kuma a sanar damu wa zamu ƙwamushe.
A yanda naji ana faɗa wai zamu kai sati biyu kafin mu koma gida,na fadawa Tunga
sati guda kuma zanyi,nasan zasuyi ta jiran dawowa ta,gashi babu dama in ana cikin
aiki mutum ya yi waya gida.

Littafi na ɗaya ne dana biyu kaman yanda na sabayi,na ɗaya bati siddan,na biyu kuma
Naira 300 ne dan haka zaka iya biya tun yanzu kafin a shiga kashi na biyu.

3131951977
Auwal Sadiya
First bank

Ko katin mtn ta nan


09035784150

VTU ta nan
2347068390570
Shaida kuma ta nan
09035784150

Ƴan niger ku tuntubi wanann number.


+227 97 21 16 15
----------------------------------------------------

Sadi-sakhan ceh
09035784150
Share please

*SANADIN CACA*

Mallakar SADI-SAKHNA

PROFICIENT WRITER ASSOCIATION

*USERNAMES*
FACEBOOK PAGE:Sadisakhna
WATTPAD:@SAKHNA03
AREWABOOKS:@sadeesakhna
PHONE NO:09035784150
________________________________
*Book 1*
Chp[17]

"Kufitar dani a wajennan nagaya muku,akan me banci sisin kowa ba kuce zanyi kwannan
cell"
Jijjiga ƙarfen ɗakin uwaisu yake yana ihu maganganu,tunda rana yake wannan abin har
dare yayi,ɗazu kamma abinnasa yafi yawa dayaga lallai a nan wajen zai kwana.
Ƴaƴan sa basu tabayin abinda zai kawoshi nan wajen ba duk iya shegensu,sai gashi
wata can daba jininsa ba tasaka shi shiga wannan ɗakin.
Wari da zarni duk sun isheshi,tun yana toshe hanci har ya daina yafara zage zage.
Abincin da aka turo masa a kwano tunda rana ko kallonsa bayyi ba,dan rainin hankali
yana cikin wannan abinma zasu kawo masa abinci. Cigaba yayi da maganganunsa,ganin
har yanzu babu wanda ya kulashi a cikinsu,sai kace ma basu san yanayi ba.
"Nace muku ku buɗeni na tafi gida,meyasa zaku rufeni anan wajen banyi laifin komai
ba,wacce tayi hakan ai yakamata ku kamo bani ba"
"Dama da bamu ganta bane ai muka kamaka,ƴar ka tayi ayyuka laifi a gari ta gudu,a
ƙa'idar kame kuma dama idan ba'aga ƴa ba ana iya kama uba ko uwa,in ba'aga miji ba
ana iya kama mata. Dan haka bazamu sakeka ba sai ka an biya beli kokuma mun kama
ƴar ka tukunna,domin laifukan da tayi da yawa.ta karya jari,ta ƙone ɗaki,ta nakasa
yaro,sannan kuma ta kaji da dama"
"Wai inji uban waye yace muku ƴata ce ne? In banda munafurci kowa a garinnan yasan
kan yawan ƴaƴana,yasan babu wannan abar a cikinsu,haka kawai ga can ubanta a jeji
baza'a kamashi ba saini,da girma na da komai,dan rashin adalci"
"Kaga dan Allah kayi mana shuru,wanne girma gareka,duk garinnan babu wanda baisan
irin abinda kake aikatawa ba,naga a irin waɗannan laifinnaka ka tura ƴarka auren
goje saboda ka hallaka rayuwar ta. Duk da haka baka saduda ba kake ƙoƙarin cutar
ɗan fulani ka aure ƴar sa. Dayake Allah ba azzalumin bawa bane sai ya nuna maka
ƙarshenka,indai baka daina abinda kake ba ai bakaga komai bama. Kuma kayi shuru ka
cika mana kunne,su wanda suka jigaka a cacar su zo su karbeka mana"
Shuru uwaisu yayi tareda samun waje ya zauna,duk abinda Ƴan sandan suka fadamasa
babu ƙarya ko ɗaya a ciki. Taya zaiga laifinsu gaskiya suke faɗa,ƙanana dasu suna
cimasa mutunci. Inda yakama girmansa kaman sauran sa'anninsa na anguwa duk haka
bazata kasance ba.
Tunowa yayi lokacin da aka kai wani dattijo a unguwarsu gidan kurkuku da ɗansa yayi
sata,a ranar muganen anguwa aka haɗu harda ɗansa Musbahu aka fito dashi. Amma shi
dayake babu wanda yake daraja shi dashi da babu duk ɗaya,ko mutum ɗaya bai gani ba
yazo wajensa. Duk mai yajawo masa banda budurwar zuciyarsa.?
Cikin sanyin jiki ya koma ya zauna a ƙasan cell ɗin,abincin da aka kawo masa ya
buɗe,jallof ce cakwaɗaɗɗiyah,baka bambamceta da farar shinkafah inba kaga abin
taruhu a jikiba.
Haka yasaka hannunsa ya yasa yakai bakinsa,saida ya runtse ido kafin ya
hadɗiye,saboda yanda take faɗa da maƙogaransa kan bazata shiga ciki ba.

[Sumaimah a mahangar gani]

Da safe ina zaune naji muryar hamisu ƙanin Shareefah,tashi nayi na fito daga ɗakin
na karbi kwanon hannunsa.
Godiya nace yayiwa ummansu da Shareefah kafin koma daki na rufe ƙofah.
Ƙosai ne a ciki mai zafi sannan aka soyah,da murnata na zauna na cinye tass nasha
ruwa.
Gado na koma na sake kwanciyah ban fita ba kaman koyaushe,dan dama haka na kimtsa
zanyi ɗin.
Can wajen kaman shaɗayan rana naji ana ƙira sunana,muryar namiji ce amman ba goje
bane.
Saurin tashi nayi zaune na mutstsike idanuwana na fito.
Da tunga muka haɗa ido yana can ɗan gefe da baranda a tsaye.
Muna haɗa ido murmushi yayimin kana ya kauda idonsa.
"Ina kwana matar ogah"
Uhm wai matar ogah manya,na faɗa a raina,a fili kuwa ɗan murmushi nima nayi tareda
cewa.
"Lafiyah kalau Tunga ya zirga zirga"
Amsa wa yayi a taƙaice kafin yafaramin bayanin abinda ya kawoshi.
"Uhm gashi wannan ki riƙe a wajenki,nasan ba lallai yabaki wani abun ba dazai tafi"
Mamaki yabani ganin ya miƙomin dubu biyu.
"wannan kuɗin fa na menene"
"Ko zaki siya wani abun idan buƙatar hakan ta taso,yace bayan ya tafi na kula da
duk al'amuransa,baice da harda iyalansa ba amma kuma ninaga kema yakamata a baki
wani abin a kuɗin da muka samo,koba komai bazaki rasa abin siya ba"
"Kulada al'amura,tafiyah yayi ne?"
Na tambaya cikeda mamaki.
Shima saida ya zaro ido jin irin tambayar danayi masa,yo ba dole yayi mamaki
ba,yaji mata batasan mijinta yayi tafiyah ba.
"Ohh bakisan cewar yayi tafiyah,wani aikine ya taso wanda ya samu bada daɗewa
ba,shine suka nemeshi jiyah akan zai fara aikin,yacemin dai na kula masa da komai
sati guda zayyi ya dawo. Laah kuma hakane ba lallai ki sani ba,dan yace na faɗamiki
kada komai da kike na aikinki ya sauyah,kiyi shi tamkar yana nan"
Ɗaga kai nayi a zahiri,yayinda ta baɗini kuma zuciyata tayi baƙiƙƙirin,wato zayyi
tafiyah amma bai faɗamin ba,saima aikowa dayayi akan nacigaba dayimasa gyare
gyare,tunda yake baisan cina ko shana ba saidai nayi masa aiki koh? Idan dan yana
ganin ya sameni ne ta sanadin caca ai Ko dabbarsa ma ta sanadin wasan kalankuwa ya
samota,amma yana kulada ita sosai,sai nice wato zai maida goruba koh?.
Ɗagawa Tunga kai kawai nayi,dan bansan mai zance masa bama. Allah ya dawo dashi
lafiyah,shine abinda nasamu cewa bayan Tunga ya tafi. In kulada shi yaso ya bani
haƙuri,ganin banason hakanne yasa ya tafi.
Ina nan tsaye a wajen naga gaji ta fito daga ƙofarta,wajenda kayan wanke wankenta
suke,ƙuda yabisu yabisu har sun bushe saboda daɗewa a wajen.
Tsayawa tayi a gaban kayan tana kallonsu, kursiyyahce ta kawo kwanon dataci awara
zata ajiye a wajen.
"Ke kursiyyah kije ki ƙiramin kawule ya debomin ruwa kuyi wanke wanke"
"Wai nikam gaji wlh bazanyi ba,haka kawai naga tun safe aka ce Atika tayi tace
bazatayi ba,saini za'a saka"
Ƙofar tashige tana wani wantsala kamar tarwaɗa. Nidai ina nan tsaye ina kallonsu.
Da rana ma hamisu ne yasake kawomin abinci,amma sannan kam nace masa kada ya sake
kawowa.
Dan kafin ya kawomin kursiyyah ta kawomin shinkafa da wake mai da yaji,wai gashi
inji gaji nacigaba da aikina na safe.
Murmushi nayi ganin kwana ɗaya kawai harta daddara ta dawo hanyah. Ban musa ba na
karba,danni ma daman hakan nakeso,banason kawomin abincin da ake daga gidan su
Shareefan.
Ɗaukar daya nayi daga cikin abincin naci,ɗayan kuma na ajiye na yamma.
Washagari da safe ɗumame kaɗan ta gaji tabani,duk yadda naso abin ya tafi yanda
zamuyi zaman lafiyah nasan hakan bazai faru ba sam,dan haka tunda nice mai son mu
daidaita dole ni zanyi haƙuri da itah,kaman yanda naga inna tana yi da itan,gobe
inna zata yi sati guda da tafiyh,sauranta sati ɗaya ta dawo kenan.
Kuɗin da Tunga ya kawomin na ɗako dubu ɗaya a ciki.Soda ta kawomin nayi wanke
wanken,sabulun danakeyi dashi ma dama yaƙare wanda inna tasiyamin,nayiwa goje wanki
dashi.
Hijabina na saka wanda nake sallah na fito waje ko zanga wani a cikin yaran unguwa
ya sayomin sabulu da omo.
Na ɗan daɗe a tsaye kafin na samu wani almajiri da robarsa a hannu yana wurgawa
sama.
"Dan mallam dan Allah zo na aikeka mana"
Na fada ina ƙirnsa da hannuna,tahowa yayi da hanzarinsa,kayan jikinsa na kalla,duk
sun yayyage sunyi daƙan daƙan dasu,yana dosoni sai zarnine yake tashi. Wai rayuwa
kenan,wato idan kaga rayuwar wani dole ka godewa Allah.
"Iyah ta gani"
"Yawwa dan Allah omo zaka siyomin da sabulu a wancan shagon"
"Tah"
Karba yayi ina kallonsa ya nufi shagon,kasancewar ba nisa ina hangoshi har yaje ya
dawo.
Hamsin na dauka a kuɗin na bashi,ya karba yana godiyah ya tafi,nikuma na shigo
gida.
Ƙofar gaji na shiga siyan awara,tunda nasamo sanji.
Sallama nayi ta amsa ciki ciki,bata huce ba kenan.
"Gaji a bani awara ta ɗari"
Nafaɗa ina miƙamata gudan ɗari biyar ɗin da aka bani a canji,tsayawa tayi tana
kallon kuɗin naɗan lokaci kafin ta karba.
"Tohh amarya an fara samun kuɗine a wajen miji?"
"Amarya bazata samu kuɗi ba dole sai in miji ne yabata?"
"To ba cass bare ass,kana kuma babu jiyarar ƴan uwa,ai dole mu tambaya"
"Akwai wasu marasa cass da ass ɗinma a gidan dasuke siyan kayan masu cass da ass
ai"
Hmm tace kawai kafin ta ƙirgamin awarar,dan tagano da Atika nake ƴar ta,shigar kaya
a gidannan wanene ya kaita,kuma ba sana'ar fari bare ta baƙi,kuɗin jikinta sunfi na
jarin awarar ma.
Canjina ta miƙomin na ɗari huɗu da kuma awarar tawa.
Karba nayi bansake cewa komai ba na bar ƙofar,zama nayi na cinye tass nasha ruwa
kafin na fito yin wanke wanken.
Ga ɗiban ruwa ma yana jirana na randa ta data goje,da kuma saniyar can,dan dai kar
a ɗaure dabba a hanata abincine tausayi ma bazai barka ba,da wlh bazan sake bata
komai ba sai ranar dazai dawo,hmmm ga gyaran ɗakinsa ma,shima bazanyi ba sai ana
gobe zai dawo inyaso.
Wani satinne ina? Kafin sannan ma idan nayi sa'a inna tadawo lokacin.
__**__

"Toh sabon salo lallai yarinyar nan in banyi da gaske ba tsoronta zan faraji a
gidannan..a ina tasamu kuɗi haka hadda sanja ɗari biyar,naga siyayya tayi na sabulu
da omo ma a leda"
Buɗar bakin kursiyyah wacce take zaune a gefe sai cewa tayi.
"Ai inna Tunga ne wannan abokin yahya goje ya kawo mata kuɗin,dan ina banɗaki naji
yana cewa wai,gashi ta rike kafin gojen yadawo. Tafiya yayi kuma zayyi sati bai
dawo ba"
"Ke ƴar nan,kenan baya garin? Haba biri yayi kama da mutum,shiyasa ban ganshi ya
shigo gidan ba har zuwa yanzu,wato kuɗi aka kawo mata ta dunga kashewa kafin ya
dawo koh. Kuma ta rasa mai zatayi sai siyan omo da sabulu?"
"Wanke wanke zatayi mana dashi"
"Naga na aika ki kaimata sodar wanke wanken,wanne iyayine sai tayi da omo,kaman
wata ƴar gayu,kowa ma ai da sodar yakeyi"
"Ohh gaji baki sani ba,ranar naji tana faɗawa inna wai intayi da soda hannunta
tsatstsagewa yakeyi"
Barin ƙirga awarar gaji tayi tana kallon kursiyyah,wacce tagama shirin fita tallen
safen.
"Oho dama hakane,ya akayi bansan zancen ba kuwa,ni inacan ina tunanin banza,ga
hanya mai sauƙi wajen kamata da hannuna,sai nayi mata abinda da ƙafarta zatazo har
wajena ta tsugunna,badai ni take mayarwa magana ba"
Gaji ta ƙarisa maganar tana murmushin mugunta.

Oohp anan zan tsaya fah sorry baikai sauran ba da shafi huɗu,wlh na gaji ne
shiyasa🙏🏼 muhaɗu gobe kawai.

Littafi na ɗaya ne dana biyu kaman yanda na sabayi,na ɗaya bati siddan,na biyu kuma
Naira 300 ne dan haka zaka iya biya tun yanzu kafin a shiga kashi na biyu.

3131951977
Auwal Sadiya
First bank

Ko katin mtn ta nan


09035784150

VTU ta nan
2347068390570

Shaida kuma ta nan


09035784150

Ƴan niger ku tuntubi wanann number.


+227 97 21 16 15
----------------------------------------------------

Sadi-sakhan ceh
09035784150
Share please

*SANADIN CACA*
Mallakar SADI-SAKHNA

PROFICIENT WRITER ASSOCIATION

*USERNAMES*
FACEBOOK PAGE:Sadisakhna
WATTPAD:@SAKHNA03
AREWABOOKS:@sadeesakhna
PHONE NO:09035784150
________________________________
*Book 1*
Chp[18]

Nafito kenan daga ɗaki naga ɗan gaji kursiyyah tana wanki da sabuluna,mamaki abin
yabani sosai.
Da sauri na ƙarisa wajen nace.
"Kursiyyah me kike da sabuluna,bakuda shi ne saikin ɗau nawa?"
"Bamudashi ya ƙare,shine gaji tace na ari naki taga kin sayo rannan"
Jimmm nayi ina jinta cikeda takaici,wannan wacce irin rayuwa ce,ace mutum bashida
katabus na rayuwarsa,kallon sabulun nayi a hannunta ya kusa ƙarewa saura
ƙiriss,gashi gobene cikar sati guda da goje zai dawo,inna ma a satin gaba nake saka
ran ganinta.
Miƙa mata hannu nayi ta bani sabulun,bance komai ba na nufi ɗaki,kuɗin dana ajiye
dubu ɗaya a wanda Tunga yabani na tafi zan ɗauka,dan omon danake wanke wanke dashi
shima ya ƙare,saina siyo dukka.
Kwanon na jawo a cikin carbet ɗin inna inda kuɗin yake,amma mee.....ina buɗewa dubu
ɗaya tace ɗaukeni a hankali.
Wata razana nayi ina jijjiga kai,ahah ahah haka bazai faru ba samm,meyasa toh
meyasa hakan zata faru?
Waye ya ɗaukemin kuɗi,sannan a wanne dalili?
Hawayene suke zubomin ina kallon kwanon,amma sam na gagara taresu ballantana na
hanasu fitowa. Saida nayi mai isata kafin nayi shuru,nasan babu wanda ya haɗa
abinnan sai gaji,wato ita dai duk hanyar dazaya wulaƙantani in bata bi ba batajin
daɗi koh?.
Tunani natafi meyasa toh ta aiko ƴar ta ta ɗaukemin sabulu,sannan kuma suka sace
min kuɗin,kaddai gaji ta gane banason wanke wanke ko wanki da soda kai?? Inkuwa
hakane wannan kam shine dalili.
Tunowa nayi da kayan goje da ban wanke ba akan sai yau tukunna,ga kuma gyaran
ƙofarsa shi ba na tashi sam.
Guntun sabulun na ɗauka nafita waje,wankin kayan zanyi kafin lokaci ya ƙure.
Basuda yawa kayan dan haka sabulun ya isheni na wanke su tass,ina gamawa ƙofarsa
naje na gyara itama kafin na dawo ɗaki na kwanta.
Sauran wanke wanke shikuma ya zanyi dashi,shine hanyar abincina kaɗai,dan haka dole
nayi,kuma ko a shari'ah tafita tunda tabani abinda suma dashi suke wanke wanken.
Shareefah ce tafaɗomin a raina,amma nayi saurin kawarda tunanin ta,ahah bazayyiwu
dan naga tana taimakamin shikenan daga matsala ta tasomin saina tunkareta
ba,rayuwata ce gidan aure na ne,dan haka dolene na maganceshi da kaina basai wani
ya taya ni ba.
Ina nan kwance ina duniyar tunanin kirsiyyah tashigo da kwanon abincina,dayake na
kula bashine target ɗinta ba hanani abincin,koban je ba tana kawomin.
Ajiyewa tayi a tsakar ɗaki,harta tashi zata tafi nace.
"Ke kursiyyah a cikinku waye ya shigo ɗakinnan ya ɗauki dubu a cikin kwano?"
Dafe ƙirji tayi tareda zaro ido,daga nan kuma saita zunduma ihu ta fita da gudu
tana kuka kaman na zare mata rai.
Da kallo na bita bakina a sake,anya waɗannan yaran mutanene,yara ƙanana daku amma
duk kuna fanɗare,tashi nayi na zauna,dan nasan gaji tana zuwa. Aikuwa hasashena bai
tafi a banza ba,in gama zama najiyo sababinta tana tahowa.
"Dan tsabar munafurci da samun wajen zama,har kin samu bakinda zaki ƙira ƴaƴana
barayi,uban me kika taba kamasu sun ci miki tunda kike?"
Har ɗakin tashigo ta riƙe kunkumi tana tayi,nidai kallonta nayi sau ɗaya kafin na
ɗauke idona. Ta inda tashi ba tanan take fitaba harta gama wanda ya isheta tafitah.
Wani hawayennne naji yana shirin zibomin na takaici,kai.......shima bai isa ba,yayi
ta jiƙemin fuska Kenan,ya isheshi haka yayi rabonsa.
Kwanon abincin na ɗauko na cinye,dama ban taba ƙoshi dashi ba,cikina har ya saba da
wannan.
Alwala na ɗauro nayi sallah,daga nan kuma sai bacci,dan shikam babu laifi ina
samunsa a gidan,bakaman gidanmu ba.
Ban daɗe da kwanciya ba kukan saniyar goje ya tasheni,da sauri na fito daga ɗakin
na nufi kewayennata,kar itama a sace ta kamar kuɗina,goje yazo yace nina sayar
ta,inada a ranar kwanana ya ƙare a duniyah.
Bayan mutum naga yana jujjuyata,gabana ne yayi rass,ban saduda ba dai nayi ta maza
na leƙa.
Da Tunga muka haɗa ido,aikuwa sai na sauƙar da ajiyar zuciyah himmm.
Shima daya fuskar tawa saida yayi murmushi.
"Ohh kinace barawo ne,in banda abinki wanene a cikin garinnna sai saci sanuyar
goje?"
"Uhm to duk da hakan dai"
"Dama nazo gyara wajennata ne,wataƙila gobene zai dawo,duk da yace ki kulada ida
amma nasan ba lallai ki iya gyara wajen ba."
"Hakane kam nagode sosai tun......uhm wai menene ainihin sunanka ne?"
Danni banason waɗannan sunayen haukar dasuke sakawa kansu..
Jimm yayi kaman mai tunani,can kuma sai yace.
"Sunana Al'amin"
"Suna mai ma'ana amma ka boyeshi,nagode al'amin barina tafi to tunda naga kaine"
Ohh a zuciyata ji nake kaman nace masa su gaji sun ɗauke kuɗin daya bani,amma nasan
hakan ba abune mai yiyuwa ba,bazan iyah faɗaba sam.
Haka na bar wajen na nufi ɗakin inna.
Tun ana gobe goje zai dawo har an kwana huɗu babu shi babu alamarsa,inna ma dazata
dawo tun jiya bata dawoba.
Ko bazasu dawo bane guduwa sukayi suka barni,ni bata goje nake bama,in yanaso kar
ya dawo tacan tacan huta roro,amma inna ji nake kaman mahaifiyata ce ta tafi
tabarni.
Jiya bacci dan barawone shiyasa yasamu damar ɗaukata,tunani sunyimin yawa
barkatai,ga kuma ciwon ta hannyena sukeyi na yin amfani da soda.
Da ita ake amfani a komai na gidan,har wanka ma saita aiko su kursiyyah waisu
kawomin,saboda tsabar munafurci da mugunta.
Duk matakan danake bi wajen bata taba hannuna sosai ba dole saida tayimin illah a
ƙarshe,kwana biyar ne kacal dana fara amfani da ita,amma sai kace an saka hannyena
a wuta matar ta tashi haka suka koma.
Shi kansa abincin ma bata bani wanda zai isheni yanzu,banda karkarwa babu abinda
jikina yakeyi wani lokacin.
Gunwa zanjene ma da matsalata,gidanmu zanje wanda sunsan dama da hakan suka kawoni
dan su rabu dani,kokuma ƙawar tawa da banida aiki sai ɗora mata wahala. Gaskiya
hakan da kunyah,zanyi haƙuri na zauna,idan har ajalina kenan Allah yasa na cika da
imani.
Warware hannyen nayi da tsumman danake sakawa indai zan taba ruwa,ko kuma abu wanda
zamemin illah.
Hanyar wajen saniyar sa na nufah domin zuba mata abinci,da inajin haushin sakamata
abinci,amma yanzu itama tausayinta nakeji,wai a yanda nake ɗinna ita kuma dani ta
dogara na zuba mata abinci,nida ko bani nawa ya isheni ba'ayi.
Kwanonnata na ɗauke zan ɗebo mata dusa,saidai me.....da kayan goje na haɗa ido a
cikin kewayen saniyar,duk ta takasu sunyi duƙu-duƙu kaman basu taba ganin ruwa ba.
Innalillahi wa inna ilaihi raji'un. Shine dai kaɗai abinda bakina yakeda ƙarfin
amsabatawa.
Ɗiban kayan nayi na taho dasu zuwa ƙofarmu. Sakasu nayi a gaba inda kallonsu,harda
singlet ɗinsa da komai ma na kayansa aka zuba a wajen,sai zarnin fitsarin saniyah
sukeyi.
Yanzu shin taya zan fara wanke kayannan,kayana ma bana wankewa bazan iya ba,hannaye
na bazasu iya gurzawa su fita ba,inaga kuma waɗannan harda su jeans,na iyah
wankewa.
Sakasu nayi a cikin ruwa na zuba sodar akai na ajiyesu,idna suka jiƙa saina wanke.
Tun da rana har dare,idan naje wankewar ina fara mitstsikawa in ciwo ya ratsani
saina ajiye na tafi,naga ta kaina nikam a gidannan,taya zan rayu da haka?.
Da daddare haka nayi yarfe hannu har bacci ya ɗauke,yanzu yakai ko tafasu a sallah
banayi,inaga idan naje asibiti yankesu zasuyi suce sun rube,inaji ina gani za'a
maidani kuturwa???? Gaskiya gobe dole nasan abinyi.....
Washagari da safe na tashi zan yunƙura kenan naji zuutt a marata..wata sabuwa kenan
inji ƴan caca.
Wayyo shima ciwonnan wannan watan kam da yayimin uzuri mana,kenan wasa wasa na kusa
wata a gidannan.
Yunƙurawa nayi na tashi zaune ina cije baki,saboda riƙewar da marata tayi gamm.
Banɗaki na lojana naje,daga nan na dawo ɗaki na kwanta,shigowar kursiyyah nagani da
ajiyemin ɗumame. Yauda masifa kenan,na faɗa a raina.
Cinye tuwonnan zanyi bazan barshi ba,idan kuma ta gano naci tuwonta banyi wanke
wanke ba bansan yazamu ƙare ba.
Duk da ciwon danake ji haka na daure na sauƙa ƙasan ɗakin,buɗe kwanon nayi mukayi
ido da ido da karin tuwon guda ɗaya. Dama kullum ɗaya take sakamin kaman rai..
Miyar babu daɗi haka na suɗeshi,jinsa nake kaman nama saboda yunwa.
Amai nafaraji yana tahomin,dan dama ko a gida haka nakeyin al'ada da wuyah,kowanne
wata saina sha wahala a ranar farko.
Komawa nayi kan gadon inna,nayi rigingine ina kallon sama,saboda amai ɗin ya koma.
Idan na bari tuwonnan ya su'buce daga cikina bansan lokacin dazan samu wani abincin
ba a yau.

[Goje a mahangar gani]

Kwana goma kenan tunda muka tafi wajen aikin,fasa banki mukaje yi a gwagwalada,to
bayan munyi da alama ƴan sanda da sojoji sun sani da wuri,hakanne yasa aikin ya
baci,aka kashe wasu daga cikinmu,wasu kuma aka kamasu. Mudai bamufi mu huɗu ba muka
tsira a cikin mutum sha biyar .
Jeji muka furma da guda har sannan kuwa bamu jefar da kuɗin da muka ɗebo ba yana
wajenmu.
A jejin muka buya tsawon wannan lokacin,saboda neman da jami'an tsaro suke mana.
Munsha baƙar wuyah muka dawo sansanin ƙungiyar.
Masu jiran ƙofar ne suka buɗe mana muka shiga,bayan sun gama bincike mu tukunna.
A gajiye muka wuce inda ogan yake muka jefa masa jakunkunan kuɗin.
Saida ya ƙaremana kallo saikuma ya tuntsire da dariyah yana nuna mu da hannu.
Yayi kaman daƙiƙa biyar yana wannan dariyah kana kuma yayi shuru yana goge hawayen
da dariyar ta sakashi.
"Ku kalleku sai kace birirrika,da kyau da kyau,ni banyi zaton ma zaku tsira ba
wlh,danaga baku dawo ba inace na kasheku ne"
Numfashina sama sama yakeyi saboda baƙinciki,yayinda zuciyata ke rayamin na
kasheshi kawai ya daina numfashi. Saidai haka na danni zuciyata nayi masa tambaya.
"Meyasa kake tunanin zamu mutu?"
"Saboda nina ƙira ƴan sanda da sojoji na faɗamusu zakuzo yin fashi a banki. To ya
kaji toh,duk lokacin dana ɗebi sabin yara haka nakeyi musu,tahaka nake gwada
jarumtar su,shiyasa bamuda mutane dayawa sai jarumai. Ya kaji salo.........."
Tun kafin ya gama maganar nakai masa wani farmaki,fitt na so yanke
maƙogaransa,saidai dayake ya san dabarun faɗa yagoce da sauri na sameshi a
jijiyoyin wuyan sa na dama.
Ihu yasaka yana dafe wajen,yayinda jini yafara tsartuwa yana wanke rigar jikinsa..
Yaran dazuke wajen da gudu suka ɗaukeshi zuwa wani wajen da bansan inane ba,yayinda
nikuma wasu suka rirriƙeni zuwa wani ɗaki mai kama da prison.
Idona a tsaye yake gamm babu alamar tsoro ko kuma nadamar abinda nayi masa,hasalima
takaici naji da ban yanke maƙogaronsa ba.
Ina nan a cikin cell ɗin har tsawon kwana uku,waɗanda suka kawoni wajenne suka fito
dani.
Kaya suka miƙomin iri ɗayah da wanda ogan yake sakawa,cikin girmamawa suka miƙamin
kayan tareda yimin alamun na biyosu.
Wani ɗaki suka nunamin nashiga,akwai gado a ciki da kuma banɗaki,ba laifi yayi kyau
kam.
Wanka nayi na wanke wannan ɗauɗar jejin,duk da ma ni ba gwanin tsafta ba,amma naji
daɗi sosai.
Kayan da suka bani na saka kana na fito.
Cigaba da sakeyi da binsu har mukazo wajenda aka taramu da farko.
Maimakon ogannmu yanzu wani mutumine sanye a suit akan kujerar.
Bashida suffar ƙarfi amma kuma yana da suffar sanin duniya akan fuskarsa,sannan
kuma kana ganinsa kasan kuɗi ya zauna masa.
Murmushi yayi kana ya min alamar na matso,ba musu kuwa cikin nima nuna isata na
ƙarisa wajen.
"Goje kake da suna koh? Ka burgeni sosai ka burgeni da jarumtar daka nuna
jiyah,wanda hakan yasa na baka matsayinsa,shiyasa ka ganka da waɗannan kayan.
Saidai ba tsallen da kayi ya kawoka tabb da rijiyah,idan ka sa ke yin wani to zaka
jika a ciki tsundummm,wanda zaka iya yin dubu baka fito ba.
Nine shugaba na ukun da ake cewa zaku haɗu dashi in kuka tsallake aikin farko,a
samana akwai shugabanni biyu,ni nabiyun nasani bansan na farkon ba,shigaba na
biyune yasan wanene na uku. Dan haka barkanka da zamowa na hannun damana"
Tafi yafara yayinda sauran ƴan kungiyar ma suka fara,lallai wajennan akwai
haɗari,jiya na lahanta shugabansu har sun maidani a matsayinsa??.

Littafi na ɗaya ne dana biyu kaman yanda na sabayi,na ɗaya bati siddan,na biyu kuma
Naira 300 ne dan haka zaka iya biya tun yanzu kafin a shiga kashi na biyu.

3131951977
Auwal Sadiya
First bank

Ko katin mtn ta nan


09035784150

VTU ta nan
2347068390570

Shaida kuma ta nan


09035784150

Ƴan niger ku tuntubi wanann number.


+227 97 21 16 15
----------------------------------------------------
Sadi-sakhan ceh
09035784150
Share please

*SANADIN CACA*

Mallakar SADI-SAKHNA

PROFICIENT WRITER ASSOCIATION

*USERNAMES*
FACEBOOK PAGE:Sadisakhna
WATTPAD:@SAKHNA03
AREWABOOKS:@sadeesakhna
PHONE NO:09035784150
________________________________
*Book 1*
Chp[19]

Gyara tsayuwa ta nayi bayan sun gama tafin.


"To nagode shugaba da wannan karramawar,amma batun rijiya ni dama dana so yin
tsalle ba nufina zuwa wajen rijiyah ba,kaine ka kaini wajen rijiyar,dan haka yin
tsallena na faɗa rijiyar ma duk yana wajenka. Mun tafi akan zamuyi sati ɗaya,gashi
munyi sati biyu bamu koma gidaba"
"Karka damu da wannan zaku kowa zai iya tafiya gidansu,aikinnan ya gamu saurna kuma
nagaba idan yataso.
Kuɗin da kuka samu nasarar ɗakkowa kungiya bazata karba ba an bakushi ku raba,su
ɗau kashi ɗaɗɗaya su baka kashi biyu."
Naji daɗin kuɗin tunda dama abinda yakawoni kenan ,amma nayi mamaki da banjisu a
cikin raina sosai ba.
Mota DON3 ɗin yabani kyauta,saidai nace masa banaso,danna kula a ɗan tsorace yake
dani karna yi masa tawaye kaman oganmu,amma ni bashine a gabana ba sam,so nake naje
naga wacce wainar su Tunga suke toyawa.
Madadin haka wani na ɗauka a mutane wajen ya tuƙoni zuwa garinna mu wanda yake
district ɗin gwagwaladanne.
Da daddare na iso,ban wuce gidaba sai kawai na nufi madakatarmu,babu kowa dan haka
kai tsaye ɗakina dayake cikin jejin na nufah.
Jakar kuɗin na ajiye kawai nayi kwanciyata,saboda narama baccin wahalar da banyi ba
kwana da kwanaki.
Hasken ranar daya hudo ta rufin ɗakinne ya haske ido na,wanda hakan yasakani yin
miƙa na tashi na zauna.
Fitowa nayi daga cikin bukkar na nufi kogi,wanda yake a ɗan gangare idan mutum yayi
ƴar tafiyah.
Wanka nayi kana nayi alwala,salloli biyu ake bina,isha asuba da kuma azahar wacce
akayi yanzu..
Ina cikin yin sallahr Tunga ya shigo bukkar,ganin ina sallah yasa ya tafi.Nasan
abinci zaije ya kawomin.
Bayan na gama jakar kuɗin danazo da itah na buɗe buzun dayake tsakiyar ɗakin,kuɗin
na zuba a ciki sauran kuma na barsu a jakar.
Jakar kayan aikina ma bazan koma da itah gidaba duk anan zan barsu.
Shigowa yayi yana cikin rarraba kuɗin a kan buzu,kallo ɗaya yayi musu ya kawar
idonsa tareda miƙamin kwanon abincin daya riƙo.
"Ogah ga abinci,ka dawo kuma babu magana sai kawai naganka a jeji"
"Kamawa tayine,a gajiye nake shiyasa banshiga garinnan ku ba,ya aikin dana barku
dashi ya tafi?"
"Yatafi yanda ake so,kawaidai kuɗinne bai bamuba,ana wannan matsalar sanjin kuɗin"
"Ga wannan ka bi kan kowa da rabonsa,ni barina wuce gida na sanja kaya"
Kuɗin na miƙa masa dami masu yawa,cikin fara'ah da washe baki kuwa ya karba.
"Ogah ta samu kenan,shiyasa fah mukeyinka,inka samu kana yaga mana,ba kaman tsohon
kwarkwaroncan ba daka gama dashi"
A ƙaramar jaka na saka sauran kuɗin wanda zanyi amfani dasu na fitoh.
Hanyar gida na nufah,kaman kullum kowa ya ganni sai ya sanja hanya.
Ina shiga ƙofar tawa na ganta kaca kaca,yanda na tafi haka na dawo na sameta babu
abinda aka taba.
Buɗe ɗakin nayi na shiga,shi da alamar anyi masa shara kaman sau ɗaya dana
tafi,cije baki nayi ina jijjiga kai,lallai ma yarinyar nan ta rainani.
Cire kayan jikina nayi na zubasu gefe.
Gajeren wandona da singlet nake nema,amma banga waɗanda nake son sakawar ba,nan na
tuna su na cire lokacin dana tafi.
Fitowa nayi na nufi kewayen saniyata,tana kallona tafara jujjuyawa,gabanta ƙwaraff
babu abinci ko kaɗan. Saidai kuma amma babu rama a jikinta,to yaushe kenan take
bata abinci,kodai ba ta bata kai?.
Ƙofar innan nashiga a zuciye,mai zan gani kaya nagani a cikin bokiti an jiƙasu.
Kuma indai ba gizo idanuna yakeminba kayana nagani a jiƙe a cikin bokiti,wannan
kuma wanne wari suke fitarwa haka.
Nasan dai kayana duk dattinsi bazasuyi wannan warin ba.
Dan takaici bansan lokacin dana bankaɗa labulen ɗakin innan ba na shiga.
A kwance take sai sharar bacci take hankalinta kwance,wani cije baki nayi tareda
runtse ido,zuciya ta tafarfasa take,yayinda ƙwaƙwalwata ke kwaranyomin wanne nau'in
hukuncin dazanyi mata.

Fita nayi daga ɗakin naƙira su durwa wanda na barsu a wajen Tunga,ɗazu da suka
ganni a hanya suka biyoni,bokitin data jiƙamin kayannawa na ɗauka na shiga dashi
cikin ɗakin shima......hmmm yau waye zai hanani hukuntaki,na daɗe banga wanda ya
rainamin hankali kamar ta ba.

[Sumaimah a mahangar gani]

Bayan na gama cinye tuwon inanan kwance naji kursiyyah tashigo ɗakin.
"Sumaimah wai kizo inji gaji kiyi wanke wanke,ko bakisan hadda kwanukan yin awara
ba a ciki?"
"Kije kice mata yau baxan iya yin aiki ba banida lafiyah"
"Chabɗi wlh ba wani rashin lafiyah,bakida lafiyar ne zaki cinye kuma tuwon dana
kawo miki? Ai wlh saina cewa gaji wai kince bazakiyi ba ne"
Tana gama faɗin hakan ta fita daga ɗakin,runtse ido na nayi lokacin da cikinnawa
yayi wani danƙa kaman zai cire taciki.
Tun safe nake juye juye akan gadon,bani na samu bacci ba sai wajen azahar tukunna.
Baccin duk da yana cikeda yunwa amma yana min daɗi sosai. Kaman a sama naji sauƙar
ruwa a jikina,wata ajiyar zuciya nasaki tareda tashi na zauna ina rarraba ido.
Warin kashin shanu naji a cikin ruwan haɗe da warin soda. Tofarwa wanda yashiga
bakina nake ina tari. Har sannan ban dawo hayyacina naga waya aikatamin hakan
ba,amma nasan ba maiyyimin wannan aika aikar sai gaji.
Juyowa nayi,saidai maimakon naga gajin,da fuskar kare muka haɗa ido yana min
gurnani,saikuma wasu ƙafafu a tsaye. Binsu nayi da kallo zuwa sama,har idanunnawa
suka haɗu dana goje,wanda ƙasumbarsa ta ƙara yawa,ga idonnan kaman na zaki yaga
abin farautarsa.
Ihu nakeson yi kozan tashi daga mafarkin danake,amma kuma nasan ba mafarkin bane
zahiri ne..
Matsawa nake da baya har nakai jikin gini akan gadon,tunda nasan shine ban ɗaga
idona na sake kallonsa ba.
Magana yafarayi da wannan maganar tasa mai diri.
"Yaushe nayi wasan dazaki rainani,shin abinda nasakaki kenan dana tafi,nace miki
kada ki karya ɗaya daga cikin ayyukan dana sakaki,amma wani abin takaicin ko guda
ɗaya daga cikinsu bakiyi ba,wato duk abinda zanyi nayi koh?"
"Dan Allah kayi haƙuri wlh"
Fizgo hannuna yayi ya jefani a tsakiyar ɗakin,jikina banda karkarwa babu abinda
yake,saboda razanar danayi jinina ya tsinke sai zuba yake duk ya bata kan gadon da
kuma jikina,nasan yagani amma ko a jikinsa,Allah yasama yasan menene.
"Ki rufemin baki,kada ki kuskura ki ambaci wannan kalmar da na tsani jinta in
anyimin laifi wato haƙuri,saboda bana haƙurin"
Since sarƙar jikin karen hannunsa yayi,da alama banni dashi zayyi ya
fiffigani,aikuwa hakanne dan sunshe shi yayi yana shirin barin ɗakin.
Wani takaici ne gamida baƙin ciki suka tokare min maƙoshi,take kuwa sukayi nasarar
kawarda tsoronsa dayake cikin zuciyata,yazamana haushinsa da kuma mamaki irin na
halinsa sunfi gaban tsoron danakeyi masa. Wannan ba mutum bane,taya mutum zai dunga
jin tsoron halitta irin wannan ma.
"Dakata kada ka fitah"
Nikaina nayi mamakin umarnin dana bashi,yaushe nasamu wannan jarumtar haka?
Tsayawar kuwa yayi bai fitan ba,ba wai danna isa ne yasakashi tsayawar ba,saidan
mamaki daya cikashi.
Juyowa yayi tareda ɗaga gira yana kallona,yayinda nima na ɗaga nawa idon nasaka su
a nasa,saƙo nake son isarwa da ruhinsa bawai shi ba,saƙon kuma bazai kai inda
nakeso ba idan ba idonsa nake kalla ba.
"Badai kasheni kakeson yi ba,idan kasheni zakayi ka kasheni da kanka,basai kasaka
halittar da batayiwa Allah komai ba ɗaukar rai,Naga abubuwa da yawa a rayuwata
sannan duk da banda galihu a duk ina naje,amma hakan bashi zai saka nakasa tsarewa
kaina darajata wanda Allah yabani na ƴa mace. Bana fatan labarin mutuwa ta ya yaɗu
cewa karene ya yayyagata a ɗaki har ta mutu,gwanda mutane suce mijinta ne ya
yankata,wanda bai san cinta ba,baisan shanta ba,baisan ya ta kwana ko ta tashi
ba,dabbarsa ta fita daraja,Dan kawai yayi tafiyar da bata san ya tafi ba,yadawo
yaga batayi aikin daya sakata ba,bai tambayi dalili ba kawai sai ya yankata. A
wannan tafiyar bai ajiye mata abinci ba ko kuɗin magani,sannan bai bata izinin
tafiyah ko ina ba,shin dutse ya ajiye kamai,saniyar sa ya damu da itah akan a bata
abinci,amma matar da ajiye ko oho. Duk da hakan tayi iya koƙarinta wajen ganin cika
umarnin daya bata,amma ƴan gindasu sunƙi barinta ta cika ɗin,shikuma bai biɗi sanin
daliliba hukunci kawai ya iya zartarwa na son kansa."
Kukane ya kufcemin na abubuwan da suka faru a gidan wanda suka dawo cikin kaina.
"Indai wannan rayuwar ce mai kamada ta bautar mutanen farko to wlh ka kasheni goje
bana tsoro,duk hukuncin dazaka min na daɗe da sanin kwatankwacinsa,kaya da kake
faɗa kuma ƴaƴan gaji ne suka zuba a kewayen saniya,na kasa wankewa ne saboda
hannyena ciwo ne dasu......bazan iyaba ka ɗau raina kawai kaman yanda kake iƙirari
ko yaushe,ka ɗauka kawai na huta,dama tunda nake mai na tsinta na farinciki a
duniyar ne??? Kullum zullumin mai zai faru. In baka kasheni bama yunwar cikina zata
kasheni,gaji bazata sake bani abinci ba nasan,saboda bazan iya yimata aikin da
innayi take bani ba. Dan haka ni gwanda ka kashenin ma kafin yunwar da kasheni"
Rarrafawa nayi na riƙe ƙafar wandonsa,har raina ni na gaji da wannan zaman rayuwar.
Jikina karkarwa yake na wuyah,dakuma kukan danakeyi,karen dayake gefena sai gurnani
yake,amma ba tashi nake ba,na daina ma tsoronsa,mai jiran mutuwa wanne tsoro zaiji
ne"
"Tashi .....ki tashi nace"
Abinda yakeson nayin nasan bazan iya ba,amma barina gwada nagani.
Miƙewa nayi daga rarrafen inaso na tsaya akan ƙafata,wani juuuuu jiri
yaɗebeni,kafin idona ya rufe sai naji ni a hannun mutum ba tsakar ɗaki ba.

Nauyi idanuwan sukayimin,amma haka na dage na buɗeshi,akan farin cilin idonnawa ya


sauƙa,fanka tanayi walwal a samana.
Gefe na kaikaita kaina na kalla,window nagani na glass ga kuma farin fenti,tunani
na fara na shin a ina nake ne.
Yunƙurin tashi nayi sai naji hannuna a ɗaure,hannayen na kalla duk an ɗaɗɗauresu da
bandeji,da alama magani aka shafamun to waye yayi min.
Allura na gani a ɗayan hannun wata igiya tayi sama ruwa yana shiga jikina,Asibitine
wai??
Na tambaya a raina,gyaran murya naji hakanne yasa na kalli mutumin dayake kan
kujera a zaune,tun ɗazu yake kallo na ban kulaba.
Ƴar razana nayi ganin ya kafeni da ido.
"Meyasa kika taba abinda kinsan jikinki bayaso?"
"Soda ce"
"Ban tambaye ki menene ba,cewa nace meyasa kike amfani da itah,bayan kinsan jikinki
bayaso,Tunga ya faɗamin cewar yabaki dubu biyu,mai kika siya toh?"
"Uhm na ajiye banganshi ba,wanda na siya kuma......"
"Ƴaƴan gaji sun sace,sannan sun ɗauke wanda kika siyah"
"Uhm"
"Sannan kayana ma sune suka saka a wajen saniya"
Nan ma ɗaga masa kan kawai nayi,tunda hakanne kuma ya riga ya gane.
"Wajibine na gyara saitin gidannan,ke kuma kina zaune suka miki hakan ke ga
asararriyah koh?.tunda kin tashi barina je na dawo,ga nan abinci a gefen gadon kici
ki gyara jikinki zan dawo na maidaki gida inna gama abinda zanyi"
Ɗaga kai nan ma kawai nayi,
"Bakya magana ne,ɗazu ban tambayeki ba kikayi da faɗi ba'a tambayeki ba,yanzu kuma
kinkoma kurmiyarki"
Daga haka cikin tafiyarsa ta isashshe ya fita.
Mamaki ne yakamani anya kuwa ba mafarki nake ba,wai asibiti ya kawoni?"
Ledar daya kawomin na buɗe,maltina ce a ciki da kuma peak na madara,sai magani a
ciki. Ɗaya ledar kuma indomie ce aka soya ta da ƙwai.
Toh ikon Allah....Sumaimah zataci daɗi kenan..
Nafaɗa a raina bansan sanda murmushi ya ƙubcemin.

Littafi na ɗaya ne dana biyu kaman yanda na sabayi,na ɗaya bati siddan,na biyu kuma
Naira 300 ne dan haka zaka iya biya tun yanzu kafin a shiga kashi na biyu.

3131951977
Auwal Sadiya
First bank

Ko katin mtn ta nan


09035784150

VTU ta nan
2347068390570

Shaida kuma ta nan


09035784150

Ƴan niger ku tuntubi wanann number.


+227 97 21 16 15
----------------------------------------------------

Sadi-sakhan ceh
09035784150
Share please

*SANADIN CACA*
Mallakar SADI-SAKHNA

PROFICIENT WRITER ASSOCIATION

*USERNAMES*
FACEBOOK PAGE:Sadisakhna
WATTPAD:@SAKHNA03
AREWABOOKS:@sadeesakhna
PHONE NO:09035784150
________________________________
*Book 1*
Chp[20]

Zamana na gyara a tsakiyar gadon na saka wannan kayan daɗin a gabana,saida na cinye
indomien tass kafin na buɗe peak ɗin,itama gamawa nayi da itah na ɗauko itama
maltinar. Saidai ita ban sha dayawa ba na ajiye,dan batayimin daɗi sosai ba kaman
wancan madarar.
Wata nurse ce ta shigo ɗakin hannunta ɗauke da littafi tana rubutu.
"Mrs goje ruwanki ya ƙare koh?"
Tafaɗa tana kallon hannuna na hagun,oh ni na manta da ruwan dayake shiga jikinnawa
ma.
Matsawa kusa dani tayi ta zare ruwan,iyah canular kawai tabari a jiki.
Murmushi tayimin da muka haɗa ido.
"Hhhh kin burgeni wlh,bakida lafiya amma kin cinye abincinki tass"
Kunya ce ta kamani,hakan yasa na sunkuyar dakai,hmm batasan rabona da abinci ya
isheni bane shiyasa.
"Karki damu babu wata matsala,tunda kina cin abinci basai an sake saka wani ruwan
ba,ga magunnan dazaki dunga sha da shafawa duk ya siyo ɗazu,saiki dunga kulawa
sosai karki ƙara taba abinda jikinki bayaso"
Ɗaga mata kai nayi alamar na fahimta.
Har tazo fita saita sake dawowa,
"Yawwa ya kawo kaya akan ki sanja,dan haka idan kin gama kizo office ɗinmu daga kin
fito ta gefennan kiyi wanka,yace yana zuwa yanzu"
"Ohh nama gama bari kawai mutafi"
Binta nayi a baya a hankali har muka isa office ɗin nasu da tace,a matsayina nasan
bankai har a kaini wajen ma'aikatan jinya nayi wanka ba,ya danganta ne da wanda ya
kawonin shiyasa ka.
Bayan nafito daga wankan bandegi da sake sauya min na hannunsa,wanda na ga ashe sun
cire fatar jikin hannun ne. Doguwar riga ta miƙomin maroon mai kyau da
mayafinta,sai pad dakuma pant.
Karba nayi na koma banɗakin na shirya kafin na sake fitowa.
Kasancewar ban iyah surutu ba musamman da wanda bansani ba,shiyasa na zauna nayi
shuru.
Muna nan zaune kaman kurame naji muryar gojen suna magana da wata nurse,lokacin ana
ƙiran magriba a wasu masallatan.
Yana shigowa dani muka haɗa ido,nayi saurin sauƙar da kai,wai karfa in mukaje gida
ya casa ni,dana tuno rashin kunyar danayi masa jiyah.
"Oh sainace ki fito tukunna zakizo mu tafi,ko baki ganni ba kai"
"Uhm naganka"
Binsa nayi kaman jela a baya ina ta kakkare jikina saboda mayafin bashida girma,dan
ma dare ya ɗan fara shiga.
Wani mashin naga mun nufah sabo irin bajaj ɗinnnan mai babban mazauni a baya.
Saida ya hau yafara diri kafin na hau bayan,dadumeshi nayi ƙanƙam,saboda ban taba
hawa mashinba.
Nasan yajini dan har ƴar tsuka yayi amma baice komai ba.
A hankali yake tafiyah wanda nasan saboda nine har muka iso gida.
Sauƙa nayi daga kan mashinɗin ina rarraba ido.
"Nagode"
Nafaɗa a hankali,bai kalli inda nake ba ballantana ya amsa,duk da nasan yajini
sarai.
Kafe mashin ɗin yayi ya nufi cikin gidan,nima binsa nayi a baya,mamaki yabani ganin
ba hanyar ɗakinsa yayi ba.
Ɗakin ya shiga ya tattaro kayansa wanda ya juyemin su a jikina,harda zannuwan gadon
wanda ya nabata da jini da kuma ruwan daya zuba duk ya tattaro ya fito dasu waje.
Ɗakinsa ya sake nufah sai gashi da bargonsa da zanin gadonsa nan ma.
Dukka zubasu yayi a gabana,nidai ina nan tsaye ina kallonsa,jikina har yafara
karkarwa,kaddai yana nufin a darennan zan wanke duk uban kayannan kai?.
Wuceni yayi ya shiga ƙofar gaji,can sai gashi ya fito Atika tana binsa a baya,
itada kursiyyah.Taci kwalliya da alama fita zatayi a daren.
A tsayawa suka yi a gefe dani suna kallonsa.
"Ku ɗauki wannan kayan ku wanke su a darennan,idan har suka kai gobe baku gama ba
wlh kunji na rantse sai na ɗaureku na tsawon satin bakuga rana ba.
Sannan idan kungama ku cikamin randa ta da ruwa"
Sakin baki mukayi haddasu muna kallonsa,hanyar ƙofar sa ya nufah hankalinsa kwance.
Bayan ya tafi juyowa atika tayi tana kallona.
"Wannan aikinkine ko,kema nan tantiriya ko,wato bari ki juyashi shikuma ya
juyamu,toh baki isa ba,dan kuwa ke zaki sha wahala ma idan hakan za'ayi,ina zai
tafi ya barki a gidan"
"Menene me naji ana cewa ne? Kekam ba fita zaki bane mai kike anan,ko ta dawone
dama ba mutuwa tayi ba da mukaga ya fita da itah"
Kallon gaji nake tasaka wani figalallen hijabi,da wani zaninta mai kama da three
quarter na wando,wai a hakan sallahr magriba da dungura,wato da suka ga yafita dani
ɗazu so sukayi ace na mutu.....hmmm mai nayiwa waɗannan mutanen suka tsaneni ne?
Ganin gaji tafito yasa Atika rushewa da kuka tana bubbuga ƙafa,kaman ba itace take
magana yanxu ba cikin tsiwa..
"Gaji kiji wani sabon salon iskanci,ɗazu da kikaga yafita dai itah,ashe suman ƙarya
tayi,suka fita taje ta kitsa masa munafurci,yana shigowa ya jibgo wannan uban
wankin wai mu yi shi a darenann,nida ko nawa ma bannayi shine zaice wai muyi mata
wankinta da nasa??? Nikan wlh gaji bazan iyaba,Allah gaji ki ɗau mataki"
Atika ta faɗa tana rushewa da kukan munafurci.
"Ke ƴar nan mai kikecewa,ayi mata wanki,akan uban me za'a maida ƴaƴana bayinki,ƴar
gwamna ce ke ko ƴar sarki,toh wlh baxai yiyuba komai za'ayi saidai ayi,kuma kwanon
abincin ki a gidannan babu shi,idan yunwa zata kasheki ma saidai ta kasheki"
Nidai ina nan tsaye in jinsu,ganin jiri yana ɗibana yasa na juya zan shiga ɗaki.
Gaji ce ta jawoni baya ina shirin faɗuwa,da ƙyar na tsaya akan ƙafafuna. Hannu ta
ɗaga zata shararamin mari,da sauri na rife ido ina jiran naji da wanne waje zai
saƙƙo.
Naji ƙarar marin amma kuma banjishi a kuma tu na ba.
"Kambuuu nika mara goje ina matar kawunka zaka mareni,saboda kai......"
Wani marin yasake kifa mata ta ɗaya kuncin daidai buɗe idona,kutt dama goje gaji
yamara,kai matar kawunnasa?..na faɗa a raina ina zare ido.
"Kona daɗa miki ne,kukuma saboda kun rainani nasakaku aiki maimakon kuyi shine kuka
tsaya kuna zage zage koh,ku faɗamin Nida na sakaku kuke zagi kokuma itah. Duk ina
sane da abinda kuka aikata bananan,har kayana kuka ɗauka kuka saka a wajen kashin
shanu ko?....daga kyau aikin gidannan kaff nasake ganin wanda yasakata
tayimasa,saina cire masa ƙafafu da hannaye,in yaso ayi masa aikin da dalili"
Ƙwafah yayi mai ƙarfi yafita waje yana huci.
Oh ni inaganin ta kaina a gidannan,ko ina ba sauƙi.
Ɗaki na wuce na barsu a wajen,duk yadda zasuyi ma suyi.
Can wajen goman dare har nayi bacci naji ana buga ƙofar tawa.
Buɗewa nayi muka haɗa ido dashi,ledar dayake hannunsa ya miƙomin,hannu nasaka na
karba ya bar wajen..
Bayan na koma ɗakin zama nayi na buɗe ledar,soyayyar doya ce da ƙwai sai
balangu,ikon Allah mai ya shiga kan gojene yake siyomin waɗannan abubuwan.
Bandai sake kawo tambaya tabiyu ba nafara kaiwa cikina.

___***___

*Overall military security headquarter division in barrack*

...ABUJA...

Tashi yayi tsaye cikin bacin rai ya buga hannunsa akan desk ɗin,wani tafarfasa
zuciyarsa takeyi na bacin rai. Ga girma yazo masa amma common case ɗaya ya gagara
gamawa dashi ya huta?.
Runtse ido yayi tareda cije fatar bakinsa ta ƙasa..
Kallon Gen Saeed yayi wanda yake gabansa a Tsaye.
"Kana nufin kacemin har yanzu baku gano sansanin Wannan ƙungiyar BC ba"
"Eh ranka ya daɗe,har yanzu bamu gano daga inda suke ba,Banida cikekken bayani
sosai akan su har yanzu,gashi cibiyar tsaro ta ƙasa Civil security headquarter tana
buƙatar karban aikin,saboda wannan a harinnasu na ƙarshe a gwagwalada sunyi babban
ta'adi sosai"
"Ta bincike akan su yana tafiyah normal,meyasa yanzu ake samun matsala akai?"
"Ranka ya daɗe kafin na karba Gen Ahmad Aliyu Hamma ne yake jan ragamar binciken,to
tunda ya rasu kuma......"
Shuru yayi yana kallon fuskar Air mershall Aliyu Hamma,saboda ambaton ɗan sa dayayi
kar abin ya kasance cikin matsala,saidai kuma ya kula hankalinsa baya kansa sam.
"Shirya min koma gida David,kafin na dawo Ka tabbatar kaida jami'anka kun samo wani
abu gameda su,domin banason wanann aikin yabar Military ko kaɗan,Civil security
bazasu iyah da wannan abinba sam,zan nemi yin magana da president akan lamarin"
Yana gama faɗin hakan ya dashi ya fitah. Babban mutum ne yafara manyanta,amma kuma
kasancewar a ƙuruciya ba'a zauna ba,jikin yana nan kaman bana dattijai ba,duk da
daman bawai tsoho bane ba.
Combo ɗin motocine a ƙofar office ɗinnsa,yana fitowa ta tsakiyan ya shiga,suka ja
zuwa gida.
Babu nisa gidannsa dan haka da wuri ya isa katafaren gidannsa wanda yake da
kwarjininsa kaman an jefoshi.

Motocinsa suna shiga gidan na Mrs Aliyu Hamma wato Hajiyah Maryam kuma suna shirin
zasu fita daga gidan.
Har an tada motar da take cikin suka tsaya,fitowa tayi daga cikin motar tana kallon
A.M aliyu ta cikin farin glass ɗin idonta.
Farace tass ƙirar fulani,sannan kuma tanada kamammen jiki,duk da ta ɗan ga jiyah
amma jikinta sam bai nuna ba,kana kallonta batayi kama da iyayen da za'a ƙirasu
masu sanyin rai ba,dan ko a gidan kowa yasani hatta barrak ɗin,daka shiga shirgin
Hajiya Maryam kwanta kaje da kanka ka faɗa hallaka,domin bata barin kota kwana,kowa
abinda taga dama take fesa masa,ciki kuwa har shi kansa mijinnata bai isa ba.
Ƴaƴan ta huɗune a gidan Saleem Da Sameer ƴan biyune,saikuma Maimuna da fatima itace
ƴar auta. Duk duniya su kaɗai take gani da gashi a rayuwarta,duk da cewar basune
kaɗai ƴaƴan A.M Aliyu Hamma ba,yanada wani ɗan Wato Ahmad Aliyu Hamma,shine babban
dansa kuma mahaifiyarsa ta rasu. Saidai shima ya rasu sanadiyyar hatsarin
mota,shekara biyar dasuka wuce. Wasu sunce a garin ba hatsari bane haɗashi aka
akayi,saidai babu wanda ya isa ya ɗago zancen har a yanzu....
Sameer soja ne kaman Ahmad sanda yakesa rai,saidai shi ba'a bangaren bincike yake
aiki ba.
Saleem kuma Medical lab scientist ne,yanada sha'awar nazari akan abinda ya shafi
bincike,musamman abinda ya haɗa da yanayin rayuwar mutane.
Sai kuma Maimuna lawyer ce,saidai ita ba wani cikyakykyiyar lafiya ce da ita
ba,tayi aure amma batayi sa'ar miji ba,Allah ya haɗata da shashasha,gata da sanyin
hali itada Saleem. Ita kuma fatima wacce ake ƙira da fatee,karatu takeyi,sannan ita
halinsu ɗaya da sameer wajen zafin rai,sune suka iyo mahaifiyar tasu wato hajiya
Maryam........
Ƙwasƙwas take tafiyah harta iso kusada shi.
"Abban fatee yana ganka ka dawo da wuri haka?"
Shuru yayi baice komai,dan indai abune daya shafi tsaronsa bayayin maganar da
itah,saboda shi kansa yasan bai yadda da itah ba sam.Kawar da tambayartata yayi ta
hanyar cewa.
"Ina zaki bayan Mammamah batada lafiyah"
"Taro zanje na manyan matan ƙasa,yanada muhimmanci,kar kace komai dan bazan fasa
tafiyah ba ma,sai kace kana magana da ƙaramar yarinya,zazzabi ne fah zata iyah
kulada kanta ai"
Tana gama faɗin hakan bata tsaya tambayar mai ya dawo dashi ba ta yi gaba.
Jijjiga kai yayi ya ƙarisa cikin gidan,shima dama yasan dole sai tayi maganar banza
ga mahaifiyar tasa,yarasa meyasa taƙi jinin Mahaifiyarsa,bayan ita kuma kullum
cikin son Maryam ɗin take,duk sanda yayi yunƙurin sakinta itace take hanashi har
aka kawo wannan lokacin,tun abin yana damunsa har ya daina ma.
Ba sashensa ya nufah ba,sashen mahaifiyar tasa ya nufah,daɗin yanada uwa
kenan,tunda mata bazatayi aikinta ba....

Sorry amin afuwa kunji labari yayi tsallen kurege ko?? Karku damu zan haɗashi waje
ɗaya,kuma da sannu zaku gane......

Littafi na ɗaya ne dana biyu kaman yanda na sabayi,na ɗaya bati siddan,na biyu kuma
Naira 300 ne dan haka zaka iya biya tun yanzu kafin a shiga kashi na biyu.

3131951977
Auwal Sadiya
First bank

Ko katin mtn ta nan


09035784150

VTU ta nan
2347068390570

Shaida kuma ta nan


09035784150

Ƴan niger ku tuntubi wanann number.


+227 97 21 16 15
----------------------------------------------------

Sadi-sakhan ceh
09035784150
Share please

*SANADIN CACA*

Mallakar SADI-SAKHNA

PROFICIENT WRITER ASSOCIATION


*USERNAMES*
FACEBOOK PAGE:Sadisakhna
WATTPAD:@SAKHNA03
AREWABOOKS:@sadeesakhna
PHONE NO:09035784150
________________________________
*Book 1*
Chp[21]

Saida A.M Aliyu yaje kusada sashen Mammah kafin ya yiwa masu take masa baya alamar
su tsaya,dan tasha faɗamasa batasan yana shiga mata da wasu masu tsaron lafiyarsa
wajenta.
Tafiyah yake shi kaɗai har ya shiga falonnata na farko,gabaɗaya wajen idan mutum
yashiga sai ya ɗauka cewar a cikin faɗar gargajiya yake,amma ta faɗa a gani.
Kasancewarta daman ita ƴar sarautar Zaria ce.
Hadimai ne suke ta kai kawo wajen ganin wajen ya kasance tsaff kuma mai ƙamshi da
daɗin gani.
Tun a wajen ya cire takalmanta yana taka carfet ɗin daya shimfiɗe wajen har zuwa
bakin turakarta.
Mai aikinta ce ta hannun damansa tayi masa iso kafin ya shiga. Dama da itah sukazo
gidan tunda akayi aurenta,kusan itace ma tayi rainon A.M Aliyu.
"Ranka ya daɗe tace zaka iyah shiga"
Ɗaga kai yayi daga nan yasaka kai zuwa cikin ɗakin,a zaune take da farin mayafi a
jikinta ta lullube ko ina da shi,da kaɗan kake gano jar doguwar rigar da take
jikinnata. Akan sallayah take hannunta ɗauke da carbi,da alama lazumi takeyi..
Tsugunnawa yayi a gabanta tareda kama hannunta ya riƙe,yana masifar son mahaifiyar
tasa,sannan baya tunanin akwai ranar dazai daina alfahari da ita,kasancewarta mai
dattako dakuma tausayin na ƙasa da itah,shi bai san meyasa matarsa takasa godewa
Allah da irin wannan suruka data samu ba.
Murmushi tasakar masa mai taushi tareda dafa kansa,duk da kana ganinta kasan
dattijuwa ce,amma kuma a yanayin kallonta bazaka ce ta haifi A.M Aliyu ba.
"Mai samu wannan gwarzon jarumin haka?"
"Mammah wannan case ɗin na BC ya dameni,tsawon shekara bakwai tun Ahmad nada rai
shima yayi iya ƙoƙarinsa,amma har yanzu abu ya gagara,mun kasa gano sirrinsu da
kuma inda suke"
Murmushi tasake sake masa wanda yakesa yaji duk damuwar sa ta kau.
"Karka damu Abban Saleem komai na duniya a sannu ake binsa,sannan da sannu lagonsu
zai karye kuyi nasara akan su,naga a labarai wai sun kai hari Local govt ɗin
gwagwalada koh?"
"Hmmm haka fah,Gen Saeed ne akan aikin,amma da alama shima abun yafara
gagararsa,gashi gwamnati na shirin ɗauke case ɗin daga wajenmu ta maidashi
ƙarƙashin Civil security,wanda kuma nasan bazasu iya da aikin ba,yanada hatsari
sosai"
Cikeda damuwa ya ƙarisa magana,duk da shi jarumine kuma wanda baya juya ƙasa da
wuri,amma ga mahaifiyar tasa shi mai raunine dayake buƙatar tallafinta.
Tausarsa ta dungayi da kuma bashi baki har hakan yayi tasiri a ransa.

___***___

[Sumaimah a mahangar gani]

Yau kimanin kwana uku kenan da kaini asibiti da goje yayi,abubuwa da dama sun
faru,ciki harda samun sauƙi danayi na hannuna,bana komai a gidan saidai nayi wanka
na kwanta. Abinci kuwa kullum sau uku goje yake kawomin a rana,kuma dukka mai daɗi
da rai da lafiyah,shikansa na kula shigarsa ta sanja ba kaman ta da ba,yayi kaya da
yawa kala kala,mashinɗin daya kaini asibiti dashi ma ashe nasa ne,koda yake siyasa
ta zo ai dole su samu kuɗi.
Hannayena sun warke sai sa'ba da sukeyi,kasancewar maganin mai tsada ne da kuma
kyau.
A bangaren su gaji kuwa ko kallon rashin arziƙi basa yimin,saboda mungun gargaɗin
da goje yayi musu,kullum da safe zan jisu suna faɗa akan wanke wanke,ko leƙasu
banayi balle nasan mai sukeyi.
Yanzu ma a zaune nake ina kallon jikina,naƙara ɗan haske da kuma ƙiba,a iya kwana
biyu kawai. Ashe dai hutu yanada daɗi,inaga tunda nayi wayo ban taba yin hutu kaman
wannan ba.
Ledar dana gama cin indomie na ɗauke da kuma kofin na fita da su.
Da gaji muka haɗa ido tana ɗiban itace a wani fili dayake gefen ɗakunan inna mairo.
Harara ta maka min amma batace ƙala ba,nima daga kallo ɗaya bansake kallonta ba na
saka ledar a shara na wanke kofina.
Koba komai dai na huta da muguntarta koda na kwana uku ne,dan har yanzu ban daina
tunanin wataƙila goje zai daina bani abinci idan na warke.
Tsintsiya na ɗauka na share ɗakin da kuma barandar,har zan tafi wata zuciyar tace
da na gyarawa goje sashensa ai tunda na samu sauƙi.
Cikin kasada kuwa na nufi ƙofar tasa,tayi datti kam ba laifi,haka yake rayuwa a
ciki,koda yake kanna zo ma ai haka yake,kuma dan ya kulada ni kwana biyu bashi yake
saka cewa wai ya shiryu bane daga yanda yake wata zuciyar ta fadamin.
Randarsa kam a cike take da ruwa,kasancewar yanzu hamisu ne ƙanin kursiyyah mai
wanann aikin.
Makullin daya bani kwanaki na saka na buɗe ɗakin,hannu na saka ina kaɗe
hancina,banda hamamin maza babu abinda ɗakin yake.
Uhmm hali zanen dutse.
Na faɗa a raina,wangale windown ɗakin nayi dana ƙofar,kayansa daya zuzzubar a ƙasa
na ɗebe na saka su a gefe.
Saidai na fara da gyara fasalin ɗakin kafin na share shi,kayan daya 'bata kuma na
fito dasu daga ɗakin,shin zanyi iya wanki kuwa dana fito dasu.
Tunani nake hannuna a kunkumi ina kallonsu,duk da hannuna ya warke amma bai gama
komawa daidai ba,idan nace zan murza kayan wanki toh sai koma baya.
"Dama waye yace kiyi aiki da kika tsaya kina tunani,ko shima salon gulamane kai
kice bansan cinki ba ban san shanki ba,ballantana halin da kike ciki"
Zabura nayi na ɗan koma gefe,saboda na bashi damar shigs ɗaƙinnasa,danna tare bakin
ƙofar,dama yana bayana tun ɗazu kenan?.
"Kayi haƙuri,kawai naga zan iyah shara ne shiyasa"
"Eh to kuma shi wanki da bazaki iyah ba sainace saikinyi koh?"
"Ahah ..uhmm...."
"Ɗauresu ki sakasu gefe zan bayar a wanke,sannan kizo ki zauna akwai maganar da
zamuyi"
Dumm naji kaina yayi,magana da goje? Uhm
Ɗaure kayan nayi kaman yanda nace,kana naje gabansa na zauna,idon yana kallon
tsakar ɗaki,shikuma yana zaune a bakin katifa.
"Tunda yanzu kin warke saiki faɗamin dame dame kikeso na kayan abinci,kinsan dai
bazan jure kullum in zan zubawa cikina abinci saina haɗo dake ba koh?"
Ɗaga kai nayi alamar ehh,aikuwa naji wata tsawa kamar a sama.
"Nida kai nayi miki magana dabazaki buɗe bakinki ba,kodan nayi jinyarki saina zama
abin wasanki kai?"
"Ahah kayi haƙuri,ehh na warke zan dunga girkin za'a iyah siyowa,itace ne saikuma
kayan abinci,inda abubuwan aiki daban su tukunya"
Kaman mai aljanu jin abinda nace kuma sai ya maida muryarsa yanda take.
"Tom shikenan,zan aiko Tunga ya kawo in anjima,ba lallai yau na dawo ba,sannan inna
tace na faɗamiki Yau zata dawo,munyi waya da ita da wayar ƙaninta"
Duk da a razane nake bansan lokacin da murmushi ya kubcemin ba.
"Dan Allah toh shikenan barinje na gyara mata ƙofar sosai"
Tashi nayi zan fitah da sauri,har na manta baice na tafi ba.
Saida naje bakin ƙofa naji maganar sa.
"Na sallameki ne?"
"Au ehh um toh"
Nafara shirin dawowa ina inda inda.
"Jeki kawai"
Yafaɗa yanayin wata ƙaramar tsuka.
Uhm kai kasani dai nafada ina yin sashennamu da saurina.

Bawani gyara ƙofar take buƙata ba,amma haka nasake gyarawa dai,saboda murnar
dawowar innan.
Bayan na gama wanka nayi nasaka kayana na zaman gida.. Ina kwance har bacci ya
ɗaukeni.
Can kaman a mafarki nake jiyo sallamar mutum a baƙin ƙofar ɗakin.
Ɗan kwalina na ja na yafa na fito,himm naci karo da kaya a bakin ƙofar ɗakin.
Buhun shinkafah ƴar gwamnati,galon ɗin manja dana mangyaɗa,katton ɗin taliya ta
leda,buhun gari na semo,macronni indomie harda su doyah da dankali.Sabon Risho a
kwalinsa da kuma jarkar kananzir babba a ciki damm. Sabulai na wanke dana wanki
masu kyau,harda macline.
Zare ido nayi ina dafe ƙirji,wannan kayan fah,wanene yayi batan kai ya shigo dasu
haka?anyah bana gidan chairman bane ba kuwa.
Ina nan tsaye nayi suman tsaye tunda yashigo giɗan hannunsa riƙeda jakakkuna guda
biyu,wani yaro ma yana biyeda shi da wata leda a hannunsa.
Dariyah Tunga ya tuntsire da itah ganin na ƙamekam kaman wata soja.
"Matar ogah wannan kallon fah,ogah yacemin dama kunyi maganar dashi ina,kan cewar
za'a kawo. Ga wannan jakakkunan ɗaya naki ne ɗaya kuma na inna,wanann kuma wai ki
soya shi ku dunga miyah dashi"
Jakakkunan na bi da kallo,sannan kuma da ledar da yaron ya miƙamin.
Har sannan ko ƙala ban ce ba,wasu kuɗaɗe yasake ƙirgowa ya miƙomin,hannu yana rawa
na karba inaso naji su kuma na menene.
"Wannan kuma yace ki riƙe ki sayi abinda kikaga babu,in sun ƙare kiyi masa
magana,ga yaronan zai dunga shigowa yana miki aika,inya kama sai ku dunga bashi
abinci. Idan babu wani abin ni zan tafi"
"Ba.....bbbu komai ammmm....mmma kuwa ba mafarki nake ba?"
"Wanne mafarki ba mafarki,namune yake shirin hawa mulki,da kuma sabon ainkin ogah
da yayi shima suka biyashi da tsoka,muma yanzu mun daina satar kajin
mutane,gwangwajewa muke da daɗi,muma muka ci bareke matar ogah,ai ki sake jansa a
jiki ki lashi arziƙi tunda Allah yakawoki a daidai sanda yayi kuɗi,dama ku kuke
ganinsa kaman mungu,amma oga goje ai akwai kyauta,saidai in bata biyo ta kanka ba
baya tunawa da shafinka. Inkika bi a sannu zaki gane kansa,kuma zakiji daɗin zama
dashi,sannan akwai abu ɗaya danake son kiyi a rayuwarsa,in lokacin yazo da kanki
zaki tambaya kuma nayi alƙwarin zan sanar dake.....zo mu tafi Yusuf"
Yafaɗawa yaron suka fitah waje bayan sun barni a duhu tsulum da bayyanar tasu.
Ledar da take hannuna na buɗe,kaji ne Yankakku an gyarasu tass. Samun waje nayi na
ajiyesu tareda ƙirga kuɗin dayake hannuna,dubu ashirinne ciff.
Komawa ɗaki nayi na ajiye kuɗin da jakakkunan danaji kaman kayane a ciki.
Sauran kayan ma duk ɗakin na kaisu na ajiye,da nayi niyyar kaisu ɗaya ɗakin inna ne
wanda babu komai a ciki,saikuma na tuna akwai masu halin bera a gidan sosai,karsu
yi ɗan halin irin wanda sukamin a kuɗina.
Babu abinda zan taba sai inna ta dawo,ko wanne lokaci nasna zata iya dawowa a yau
ɗin.
Dan har yanzu ban yarda Tunga da gaske yake gojene ya aikoshi ba tabbb wayaga
duniya sabuwa.

__**__

"Wlh gaji da gaskene nake miki,wannan yaron yayah gojenne ya dunga shigowa da kayan
abinci yana jibgawa a ƙofar inna mairo wajen Sumaimah,hadda wasu jakkuna da bansan
menene a ciki ba"
"Ke ƴar nan banason ƙaryar banza fah"
"Hmmm kinace wai ƙarya nake,ki zo ki leƙa ki gani mana,gatacan tana shiga dasu ma
ɗakin innan"
Jirif gaji ta tashi daga kason abincin da take ta leƙo ƙofar innan,daidai lokacin
da Sumaimah take jan buhun shinkafar zuwa cikin ɗakin innan.
Zaro ido tayi tana kallon sauran kayan da suke wajen,katton ɗin taliyah dana
macaroni,kaman taje ta ɗebe haka takeji.
"Kambuuu wanne ƙusane yabasu waɗannan kayan abincin haka"
"Ohh baki sani ba,wanda goje yakeyiwa aiki shine ya tsaya takarar ɗan majalisa,kuma
ana tunanin shine zaici,har mashin ya siya fah saboda dal kina gani yake hawa.
Sannan kwana biyunnan kullum sai an kawowa Sumaimah nama da shayi mai kauri,kina
gani ma sanda take zubawa a shara"
"Cabɗi wannan shine ka tura mutum rana an janyeshi cikin fadama,shegiyar yarinya
haka zatayi ta famtamawa yanzu muna kallo....inaa aradu hakan bazai faru ba,bari
Atika ta dawo daga talle musan nayi.hakama malam,ai dolene muma yabamu tunda ina
matar ubansa,bazayyiyu a dangwali na banzar nan babu mu ba kam.."

Toh fah

Littafi na ɗaya ne dana biyu kaman yanda na sabayi,na ɗaya bati siddan,na biyu kuma
Naira 300 ne dan haka zaka iya biya tun yanzu kafin a shiga kashi na biyu.

3131951977
Auwal Sadiya
First bank

Ko katin mtn ta nan


09035784150

VTU ta nan
2347068390570

Shaida kuma ta nan


09035784150

Ƴan niger ku tuntubi wanann number.


+227 97 21 16 15
----------------------------------------------------

Sadi-sakhan ceh
09035784150
Share please

*SANADIN CACA*

Mallakar SADI-SAKHNA

PROFICIENT WRITER ASSOCIATION


*USERNAMES*
FACEBOOK PAGE:Sadisakhna
WATTPAD:@SAKHNA03
AREWABOOKS:@sadeesakhna
PHONE NO:09035784150
________________________________
*Book 1*
Chp[22]

[Sumaimah a mahangar gani]

Tun ɗazu nake zuba idon ganin inna,motsi kaɗan saina leƙa ƙofar gida,safa da marwa
nake yanzu ma a kan baranda ina tunanin anya kuwa zata dawo ɗin,ganin yamma tana
shirin yi amma shuru bata dawo ba.
Kasancewar ban buɗe stove ɗin na fara amfani dashi ba,kawai murhu na haɗa na gyara
naman,saikuma na tafasa taliya..
Har na juya zan koma ɗaki sainaga inna Mairo tashigo gidan,magana suke da almajirin
daya shigo mata da kaya,wani farinciki na tsinci kaina dashi,ban lokacin dana tafi
da gudu na rungumeta ba.
Dariyah tayi tana cewa.
"Allah sarki,duk da na tafi na barki amma kike murnar dawowa ta,nayi zaton ai
zakiyi fushi ganin na ƙara sati guda"
"Uhm naji haushi kam har kuka nayi,amma ya wuce tunda kin dawo,zo muje ki zauna ki
huta,daga gani kin gaji"
Jan hannunta nayi muka shiga cikin ɗakinnata,saidai tundaga bakin ƙofah danaga ta
tsaya nasan abinda yabani mamaki ɗazu tagani,wato kayan da goje ya kawo.
"Sumaimah wannan abin kumafah,waye ya kawo wannan kayan haka?"
"Uhm goje ne ya saka Tunga ya kawo ɗazu,wai yakamata mufara abincinmu"
"Eh to yanzu ba zancen abincinba,a ina yasamu kuɗin daya siyo waɗannan kayan,a
sanina dashi bashida ko sisi,ko wajen mai shayi ma bashi ake rubuta masa,taya
yasamu wani kuɗin siyan waɗannan kayan"
Cikeda zullumi take maganar,kanaji kasan bata yadda da kayan ba.
"Nima na faɗi haka sai Tunga yace wai ɗan siyasar su ne yaci,suma haka suka samu
kuɗin dayawa,inaga kuma shugaba"
"Oh na manta ma da abin zabe,in hakane shikenan Allah ya kyauta,amma zan sake
tambayarsa,kai wannan ƙasa tamu wai dan zakaci zabe sai kayita rabawa matasa kuɗin
al'umma?. Allah ya shirya shuwagabanninmu kawai"
"Ameen ya Allah"
Gyalen dayake wuyanta ta ajiye tareda zama a bakin ƙaramin gadonta.
"Yana sameku Sumaimah ya mutanen gidan,da zan shiga ƙofar gaji nace mata na
dawo,sai kuma naji wai ta tafi anguwa. Wannan kayan ki gyarasu mana shima abin
girkin ki buɗe ki jerashi,ina kin iyah amfani dashi?"
"Ehh na iya,ina dafawa yaya Musbahu indomie a nasa na ƙofarsa"
"Yawwa toh ki shirya komai,ai dama da kinyi tun ɗazun basai kin jirani ba"
To nace tareda ɗakkowa kuɗin daya bani ɗazu na miƙa mata.
"Inna gashi wannan ai a ajiye inda abinda za'a siya na amfani"
"Ahah ki riƙe a wajenki tunda kece mai siyan abubuwan,ni bazan riƙe kuɗi ba a
hannuna,kiyi yanda ya dace kawai,in neman shawara ce saiki tambayeni,amma batun na
karba bai taso ba. Sannan a kayan ki ɗebi wasu ki kaiwa su gaji,duk da an san zaman
da akeyi amma tayi ƙoƙari sosai nayin abinci"
Maida kuɗin nayi inda na ajiye,abincin na zuba mata taci sannan muka hau hira,wadda
duk na abinda ya faru ne da batanan,wani tayi dariya wani kuma ta jijjiga kai.
Abinda take cewa kawai nayi haƙurine watarana zai wuce,a lokacin baya bana yarda da
zancen ta,amma yanzu nafara yarda da zai wuce watarana sai labari.
Kafin dare na shirya komai yanda zanyi amfani dashi,Sannan su gaji ma na cire musu
wanda zan kaimusu.
Jakakkunan da Tunga yabani kuwa kayane a ciki na sakawa,kowanne kala uku da hijabi
da takalmi flat mai kyau,idan nace banyi murna na wlh ƙarya nake,ko a mafarki
bantaba tunanin samun kayan a lokacin ba.
Tunda magriba nake jiran naji gaji ta dawo,amma sai bayan isha tukunna naji
muryarta tana magana da hamisu akan wai bai ɗebi ruwan da ta sakashi ba.
Sallama nayi na shiga,hannun ɗauke da kayan dana kai musu,shuru tayi da faɗan tana
kallona,duk da bani take kallo ba sai abin hannuna..
Washe baki tayi tana min magana,abinda tunda nake bata taba yimin ba sai yau.
"Ahh Sumaimah kece da darennan,naji Addah Mairo ta dawo ko,yanzu nake shirin zuwa
nayi mata sannu da dawowa ai"
Wai meee?? Ba mafarki nake ba kuwa,gajice take waɗannan kalaman masu daɗi.
Dawowa nayi daga mafarkin dana tafi nace.
"Ehh ta dawo run ɗazu da bakyanan,ga wannan kayan abinci ne,sannan inna tace mu
faɗamiki ta gode sosai,zamu dunga girkinmu yanzu"
"Ahhh me yayi zafi daza'a raba girki haka rana tsaka,mai zai hana ma ni zan dungayi
kaman koyaushe,kice mata ta kawo kayan girkin za'a dungayi ba matsala"
Anya kuwa gaji tanada kunya? Nayiwa kaina wannan tambayar,juyowa nayi ina mata
kallon mamaki.
"Ahah karki damu gaji babu komai zan dungayi,yanzu ai gurege yazo ga harawa,koda
zata kare walau nan kusa kokuma ya daɗe,amma dai yanzu kam zaici ya more. Kuma
karki damu inna bazata ƙwace gonar marigayi ba a hannun babansu Atika,sannan kuma
injin markaɗenta ma bazata karba a wajensa,dama ina dasu ake ciyar da gidan,yanzu
babu mu a ciki kuci iyah ku kaɗai"
Ban tsaya jin abinda zatace ba na fita daga ƙofar bayan na ajiyemata kayan,a zaton
ta duk abinda take ba'a sani ba,nunawa take kaman ita take ciyarda gidan,bayan
gonar da ake noma hatsin ba nasu bane,injin markaɗen da baban su Atika yasaka yara
suna aiki dashi yana karbar kuɗin duk na inna ne.
Kayan aikina da nazo dasu na fito dasu,tunda nazo gidan yau wata na guda sai yau
zanyi wani abu na ƴan cin kaina.
Kula tuwo da miya na ɗakko na abincin goje,saikuma kwanukan da zanyi amfani dasu na
aikace aikace.
Da daddare ban sake abinci ba,kasancewar wanda nayi ma na rana bamu cinye ba,kuma
goje yace ba lallai yadawo ba.
Dan haka hirarmu muka sha har bacci ya ɗaukemu,cikin farinciki da annashuwa.

__***__

"Haba Inna yanzu kina nufin nakoma gidan nan wannan yarinyar tana gidan?"
"To ya kikeso muyi,munje wajen boka ance duk abinda zamuyi a banza ne,asiri bazai
kamata ba,saboda aljanun dasuke jikinta suna shirin maidata irinsu ma"
Shuru inna ramma tayi tana jin innar tata,jiyah aka rufa mata ɗakinta da zana zata
koma kafin damina,da uwaisu yazo haka ya ƙarashi jiransa taƙi binsa su koma,wai
dole sai Deejah tabar gidan tukunna..
Shikuwa ya faɗamata da yana da yanda zayyi da Deejah,da kowa yayi maganinta shine
zai fara,don ko baccin kirki bayayi tun zuwan Deejah rayuwarsa,kullum cikin fargaba
yake kar a zo ace masa tayi kaza,wai duk duniyancin da yayi bai taba zuwa wajen ƴan
sanda ba saita dalilin wannan shegiyar yarinyar.
Tattara kayan inna ramma tafara,dan tasan yanda uwaisu yake a wannan halin tsaff
zai ce in tana so kada ta dawo.
"Toh yanzu inna yakike so nayi ne,ko roba fah banni da ita in kika ɗauke wanda suke
tsakar gida,gabaɗaya waccar ƴar ta ƙona su wai......."
"Kinga ni wannan maganar ta isheni,dama me kike dashi a dakinnaki ne banda wanann
tsohon gadon da ru'be da fitsari,in zaki tafi ki tafi"
Ammi tana rabon abinci da tsakar rana taji sallamar rammah ta dawo.
Tana shigowa ko kallon ammi batayiba ta shige ɗakinnata,babu laifi an maida ginin
da bulo,amma rufinne dai saidai tayi haƙuri sai a hankali.
Tsayawa tayi a tsakiyar ɗakin tana kame da kunkumi,shikenan wai ta rasa komai
kenan,kuma ace tabar ƴar nan bata ɗau fansa ba,gashi inda ta cize ta har yansu yaƙi
ya warke,jiyama saida taje asibiti aka yimata wanki..
Hawayen idonta ta share tareda dunƙule hannu tana cije baki,fitowa tayi wajen ammi
kawai dan ta samu wanda zai tamka mata.
"Ina nawa abincin naga kin gama rabawa"
"Ban kasa dake ba,saiki bari idan kinyi na dare saki ci"
"Kutus....kina nufin kice baki zubamin ba,wlh saina ci toh"
Wani kwano ta hanga an zuba shinkafar mai kama da dawa saboda jawur da itah,kuma
yafi na sauran yaran yawa.
Ammi tana kallonta ta ɗauki abincin amma ko yunƙurin hanata ta ɗauka batayi ba,har
ta wuce kufayin ɗakinnata.
Bata daɗe da shiga ɗakin ba Deejah tashigo ƙofar tana wuwwula karan dayake
hannunta,rarraba ido tayi akan kwanukan abincin,amma bata ga robarta ba wacce ammi
tace a ita zata dunga zuba mata abinci.
"Ina robata take,dan anga na daina cinye abincin yaran gidannan shine za'a ɗauke
robata to kuwa saina......."
Cikin ƙaraji take magana irin ta tantiran yarannan,ganin haka yasa ammi cikin rawar
jiki ta nuna mata ɗakin rammah.
"Na zuba miki ramma ce ta ɗauke wai saita cinye"
"Abincinnawa?"
Da gudu tayi ɗakin rammah tana ƙaraji kaman an wullata.
Rammah wacce ta ajiye kayanta a gefe tana cin abinci sai Deejah tagani a
kanta,harda matan gidan guda biyu da ɗakin,wanda su ƴan ɗakin ramma ne.
Irin kallon da tayiwa uwaisu ranar kawota takeyiwa rammah,ta daddake kaman mai
shirin kaiwa farmaki,magana take mai kamada ta birbiri.
"Abinci nahhh abinci naahh kika cinyemin daga dawowarki......dole saikin biyani
abincina ko na cinye namanki....yunwa nakeji"
Karkarwa rammah tafara tareda ajiye kwanon Deejah a gefe,sauran matan kuwa da
sukaga haka da gudu sukayi waje.
Nufar rammah tayi zata sake cizonta,wani ihu tayi tareda ɗaga hannunta sama.
"Tsaya tsaya dan ya rasulullahi kiyimin rai kiyi haƙuri karki sake cizona,bansan
abinci bane,amma zan biyaki idan nayi girki,wlh zan biyaki"
Tsayawa Deejah tayi tana maida numfashi jin abinda rammah ta faɗa.
"Zaki biyani dole saikin biyani,kuma yanzu Ma ban haƙura,kafff kashin abincin ƴaƴan
ki saina cinyeshi yau,yau basuda abinci a gidannan,sannan saina kashe tunkiyarki"
Tana gama faɗan hakan tafita daga ɗakin da gudu,binta rammah tayi a baya itama a
guje musamman ganin ta ɗauki wuƙa a inda ammi ta yanka albasa.
Kewayen awaki ta nufah da gudu rammah tana binta tana ihun taimako,kowa fitowa yayi
daga ƙofarsa,duk da sunsan bazai wuce wata aika aikar Deejah zatayiwa ramma ba.
Tana zuwa gaban tunkiyar batayi wata wata ba ta soka mata wuƙar a wuyanta,jini ne
yafara zuba abinka da dabba da lafiyarta. Faɗuwa tayi a ƙasa tafara shure shure
zata mutu,a lokacin ba shiga uku ba in tara ne ma rammah tashiga,dan hannunta aka
data ɗora haka ta zube wajen kaman itace.
Musbahu ne wanda yashigo daga masallaci jin abinda ake fada yasa ya nufi kewayen
dabbobin,wuƙar hannun Deejah ya fisga wacce take riƙeda itah hannunta yana ɗigar
jini.
Juya tunkiyar yayi gabas yayi mata yankan musulunci.
Saida ya tabbatar komai yayi kafin ya tashi ya tsaya,kife Deejah yayi da mari iyah
ƙarfinsa saida ta kusa hantsilawa.
"Bance miki kada nasake gani kin kashe abu mai rai a gidannan ba,sannan kuma karki
ƙara ɗauke abu ana rabawa ki cinye?"
Riƙe kumatunnata tayi tareda da nuna rammah da yatsa.
"Na kashe mata tunkiyarta meyasa ta cinyemin abincina daga dawowarta,munguwar
matace zata cigaba da cutar da mutane,bazan ƙyaleta ba idan tashiga harkata"
Maganar take muryarta babu alamar nadamar abinda ta aikata a cikinta.
"Khadija ina magana kina mayarmin"
Kallonsa take idonta a tsatstsaye,yana ɗaga ƙafa tayi hanyar waje da gudu.
Tun ranar da ta jiwa yaronnan ciwo bayan ta dawo yakamata yayi ta dukanta,tundaga
ranar inta ganshi take sanja hanya.
"Meyasa ke daga dawowarki kika shiga harkarta?"
"Iyee na'am ya ake so nayine kam,bani na kawota gidannan ba amma ta addabeni ta
takuramin,ta ƙonamin ɗaki,ta kashemin kaza,ta cijeni yanzu kuma ƴar tunkiyar tawa
da kashemin itah,ya akeso nayi toh wlh bari maigidan yadawo sai ya biyani aradu"
Bai sake bi takan rammah ba ya jijjiga kai ya bar wajen. Kai dole ma yasan
abinyi,inaga a makaranta zai sakata,inaga abinnata hadda rashin sanin yanda mutane
suke rayuma.
Toh shikuma mai gidan idan yazo yasan yanda zayyi da inna ramma.

Tunda Musbahu yafita daga kewayen dabbobin,rammah bata tashi daga inda takeba,sai
rusa ihu take tana kallon tunkiyarta,wacce take kwance a inda yayi mata maza wuƙa.
Majina kuwa ta jata babu adadi...........to ku yanzu me zamu cewa inna ramma,ita
tasani koh????

Mu haɗu gobe mutanena a gidan malam goje,zai faracin abincin amarya


Sumaimah.........

Littafi na ɗaya ne dana biyu kaman yanda na sabayi,na ɗaya bati siddan,na biyu kuma
Naira 300 ne dan haka zaka iya biya tun yanzu kafin a shiga kashi na biyu.

3131951977
Auwal Sadiya
First bank

Ko katin mtn ta nan


09035784150

VTU ta nan
2347068390570

Shaida kuma ta nan


09035784150

Ƴan niger ku tuntubi wanann number.


+227 97 21 16 15
----------------------------------------------------

Sadi-sakhan ceh
09035784150
Share please

*SANADIN CACA*

Mallakar SADI-SAKHNA

PROFICIENT WRITER ASSOCIATION


*USERNAMES*
FACEBOOK PAGE:Sadisakhna
WATTPAD:@SAKHNA03
AREWABOOKS:@sadeesakhna
PHONE NO:09035784150
________________________________
*Book 1*
Chp[23]

[Sumaimah a mahangar gani]

Shinkafa da miyah nayi niyyar yi,saboda nayi amfani da naman da goje yasaka aka
kawo,tun safe yaron da Tunga ya hadani dashi yazo yayimin siyayyar duk abinda
nakeso..
Sai wajen shaɗaya kafin na ɗora abincin,wanke wankenmu dan kaɗan ne,tun safe na
wanke komai na kwanukan da muka bata,shara kuwa in na share ƙofar inna shikenan
saita goje.
Bayan na gama shuru nayi ina kallon abincin dana zuba a cikin kulolin,na tafi
tunani naji muryar inna a sama na.
"Wani abune ya faru naga kinyi shuru uhm"
Ashe tana kallon tun ɗazu,so nake da ya fita daga ƙofar tasa saina kai abincin,amma
yaƙi fita gashi azahar tana shirin,banaso najene ya gwaleni ya koroni,korar
dayayimin ranar danazo gidan har yanzu bata bar cikin kaina ba ina tunowa.
"Inna uhm kina ganin zai yarda yaci kuwa? Baice mu dinga yi dashi ba abincin?"
Dariyar dattawa tayi min kafin tace.
"Karki damu Sumaimah Inshaallah zai karba,kuma abincin yayi daɗi sosai da sosai,Ba
kowane zai kauda kai baiciba,musamman ma kinsan maza da son abinci kuwa?? Idan
kinga yafara ci saikiyi masa maganar komawarki islamiyya da kika fadamin kinji,amma
fah kada ki fada sai kinga yana cikin yanayi mai kyau,kin gane koh?"
Ɗaga kai nayi amma kuma saina tuna naga jiya tace zata fadamasa nakoma islamiyyar
meyasa ta sanja ra'ayi.
"Amma inna kince fah zakiyi masa maganar karatunnawa?"
"Uhm uhm da nayi niyyar yimasa maganar,amma inaga kiyi masa maganar da kanki
zaifi,ta hakane zaku samu fahimta da kusanci a tsakaninku,sannan in kina tambayarsa
da kanki hakan zaisaka ya ƙara gane cewa ke ɗin haƙƙinsa ce kuma kina ƙarƙashinsa"
Maganar da tayin ya gamsar dani sosai,yanda take yimin wasu abubuwan har mantawa
nake da itah surukata ce.
Ɗaukar abincin nayi akan tire cikin sanyin jiki na nufi hanyar ƙofar tasa. Tun
dawowar innan bamu tab'a yin abinci dashi ba,saboda baya zama a gidan sam,ko mai
yakeyi oho. Jiyane dawowar sa yasaka yaro yashigo mana da nama kaman ranar farko.
Na buɗe baki zanyi sallama sai kuma naji yana wata magana...
.......Me kake nufi ne wai,jiya fah na dawo yace na fasa fita aikin,kuma yanzu kace
wai na sake dawowa,hakan bazai yiyu ba sam.akwai wani aikin danake so nayi,ba iya
waccanne aikina ba. Idan yin fashin ko satar daɗine shiya je yayi mana,in kuɗinkune
saina dawo muku da kayanku yana nan ban taba ba.......
Sata fashi..nashiga uku dama fashi yake zuwa idan yayi wannan tafiyar...yaushe
yafara fashi?.
"Me kikeyi a tsaye a nan,ko bayan rashin kunyar harda lab'e kika fara yimin"
Saurin tura ƙyauren nayi na shiga ɗakin ina rarraba ido.
A tsakiyar ɗakin na tsugunna tareda ajiye tiren kayan abincin. Da kallo ya bini
yana zaune daga shi sai singlet ruwan toka,da kuma baƙin gajeren wando. Ta gefen
idona na kulada shigar da take jikinsa,hakanne yasa naƙi ɗaga ido na,fatar bakina
rawa take amma kuma na kasa cewa komai.
Matsowa yayi ya dawo bakin katifar yana ƙareni da kallo.
"Ɗago fuskarki ki kalleni"
Bin umarninsa nayi ta hanyar ɗago idanuwannawa,akan ginannen ƙirjinsa na ajiye
idanuwana,ban ƙarisa izuwa fuskarsa ba,magana naji yafarayi,saidai ba irin muryar
danaji yana yiwa mutumin dayake waya dashi bace.
"Me kikaji ina faɗa a waya?"
"Uhm....uhm zancen fashi kuke da sata"
"Dakyau dama na tsani ayimin ƙarya,to kada ki kuskura inna taji wannan zancen"
"Tohh bazata jiba"
Ɗaga kai yayi alamar ya gamsu da abinda nace. Shuru ne ya gibta,ganin baice komai
ba yasa na fara bude kular abincin,a raina ina cewa karka hanani karka ce ka ƙoshi.
Ohh Allah ya amshi Addu'a ta kuwa harna gama zubawa baice komai ba,amma inajin
idanuwansa a kaina. Cokali na saka a kan plate ɗin na miƙa masa. Kar'ba yayi ba
musu yafara garwaya gabansa yana kaiwa baki.
Ruwa na zuba masa a kofin jug ɗin danazo dashi na sake mika masa gabansa,hannunsa
ya kawo zai ɗauka nikuma ban zare hannuna,hannunmu ne ya haɗu dana juna,da sauri na
zare nawa ina sake sunkuyar dakai.
"Akwai magana a bakinki meyasa bazaki furta ba,kina bani mamaki,har yanzu na kasa
gane kanki,lokacin da banyimiki komai ba kina tsorona,da nayi niyyar yimiki kuma
sai kika maida martani"
"Uhm kayi haƙuri a loka......"
"Ahah bance saikin bani dalilinki nayin hakan ba,me yake tafe dake yanzun?"
Dama yana magana haka ta lumana irinna sauran mutane? Tun lokacin dana ke ganinsa a
gari kafin zanen ƙaddarata ya ɗinke da nasa ,nayi zaton idan an zo kusadashi kashe
mutane yake. Tsaida tunanin danake nayi tareda sanar masa buƙata tah.
"Uhm dama inason komawa makarantar islamiyyah ne,amma ta matan aure"
"Tsawon sanda nake cin karo dake a lokacin baya da kayan makaranta nake ganinki
kafin kifara talle,har yanzu bakiyi ya isheki ba?"
Da yayi maganar bansan lokacin dana ɗaga ido na kalleshi ba,dama yasanni yana
kallona.
Kaman yagane abinda nake saƙawa a raina,murmushi yayi amma ba mai tsayi ba yace.
"Ohh a zatonki bana kulada mutane ne idan suka ga zamu haɗa hanya suka juya da
gudu,ina kulada ke duk sanda muka haɗa ido komawa kike da gudu kibi da wata
hanyar,abin yana bani dariya da kuma nishaɗi idan naga mutane suna gudu"
"Babu ɗaɗi da kuma nishaɗi ace kana ɗan adam ƴan adam ƴan uwanka suna
gudunka,alamar maƙiyine a gujeshi,kana kuma alamar masoyine a kusanceshi a duk inda
ya gifta"
Wuuff nasaka hannuna na rufe bakina ina jijjiga kai,Sumaimah kinga ta kanki meya
kaiki fadamasa waɗannan kalaman.
Runtse idona nayi,na ɗanyi wani lokaci,jin bai dakamin tsawa ba ko mari yasa na
buɗe idona,murmushi naga yanayimin....wannan bawan Allah menene yashiga jikinsa.
"Yanzu ma kin sake bani mamaki,kece mutum ta farko data fara faɗamin irin waɗannan
kalaman bayan inna,zuciyata ta kasu kashi biyu a halin yanzu.....ki tattare
kayannan maza ki fitah,batun makarantar kuma zan duba nagani"
Tashi nayi da hanzarina ba bata lokaci na tattare kayan dana shigo na dasu zan
fitah,har nazo bakin ƙofa naji muryarsa,inba nasan muryarsa ba bazan ce bane.
"Abincinki yayi daɗi,nagode"
Ehh juyawa nayi duk da yacemin na tafin,kallonsa nayi ya saka hannayensa akan
kunnuwansa,idanuwansa kuma a runtse kaman yana cikin ciwo,meyasa lokaci ɗaya yakoma
haka saikace bashi ba?
Nidai fitah nayi daga ɗakin zuciyata cikeda mamakin ganin sabbin halayen gojen.

[Goje a mahangar gani]

Ina cikin wayar naji alamar motsin mutum a bakin ƙofah,nasan babu wanda a yanzu
yake zuwa ƙofar tawa sai Sumaimah,dan haka itace a wajen.
Jikina ne yabani cewa taji abinda na faɗa,aikuwa dana tambayeta hakanne,jinta bai
dameni ba,kawai inna ce bana so taji,shiyasa nayi mata gargaɗi.
Lokacin da take zubamin abincin haka kawai na tsinci kaina wajen zuba mata
ido,gashi dai bata ɗaya daga cikin yarana,amma kallonta a tsugunne tana zubamin
abincin saina jini tamkar wani sarki,gashi cikin nutsuwa take zubawa duk da yanda
jikinta yake rawa.
Bayan ta miƙomin loma na ɗiba nasaka a bakina,ba laifi yayi daɗi sosai,ba kaman
wanda ake na siyarwa ba.
Ganin ta zauna tayi shuru tana motsi da baki yasa nagane akwai abinda takeson
tambaya,domin a dan zaman danayi da itah wata ɗaya da satuka na gane hakan.
Islamiyyah takeson komawa itakuma? Toh.....ban wani mamaki ba,dan dama tun sanda
nake ganinta akan hanyar zuwa makaranta muke cin karo.
Bayan mun ɗanyi magana,amsar data bani saina tsinci wani bangare na zuciya ta yayi
na'am da amsar,amma mafi akasarin raina kuma so yake na tsinketa da mari saboda
maganar da tayimin. Karo na farko a rayuwata kenan bayan inna na ƙi amincewa da
muryar da take bani umarni. Sanadiyyar hakan saina farajin ciwon kaina yana
barazanar zuwa da ƙarfi,hakanne yasa nace tattara kayan abincin ta tafi. Harta zo
fitah bakina yasamu faɗamta cewa Nagode....wai mai yake damuna ne,nafi kowa sanin
kaina idan na farantawa wasu ni saina baƙantawa kaina,ko kayan abinci dana kawowa
su inna sai nake ganina kaman baniba.
Farkawa nayi naga duhu yafara ta windown ɗakinnawa,kutt kaddai bacci nayi kai har
magriba ta kusa.
Tashi nayi daga kan katifar na fito,alwala na gurgurza na fice waje.
Masallaci na shiga nayi azahar la'asar da kuma magriba,daga nan na wuce duk inda ta
garamin.
Lokacin dana dawo da daddare na samu Sumaimah ta ajiyemin abincin dare,banciba na
sake fita,saboda ban saba da cin abinci a gidaba,dan nayi full tank a waje..
Da safe soyayyar doyah ta kawomin a ƙaramin kwanon jiya,wannan karon bata nuna
alamar tsoro kaman jiya ba,kayan dana saka na zuba a gefen ɗakin ta tattara tafita
dasu tareda abincin daren data kawo banci ba.
Babu wanda yayiwa kowa a magana a tsakanin nida itah bayan gaisuwar datayimin ta
safe na amsa.
Kai tsaye makarantar garin na tafi ALBAYAN,Babbar makaranta ce sosai,anayin
islamiyyah da kuma boko,sannan ba iya ta yara bace hadda manya. Nasan hakanne
saboda yanda nakejin labarinta,danni bansan wacce waina ake toyawa ba a cikinta.
Makarantar ana faɗan iliminta da kuma tsadarta,amma ni ba wannan ne damuwata ba,ita
kaɗai nasani manya suna zuwa shiyasa na je naji mai yake wakana.
Tun daga shigata makarantar idanuwan mutane suke dawo kaina,banga lafinsu ba wanene
zayyi tsammanin ganin goje a makaranta.
Tun kafin na isa office ɗin shugaban makarantar labari ya isa gareshi,fitowa yayi
bakin office ɗin yana jirana har na ƙariso.
Wuceshi nayi na shiga office ɗin na zauna,biyoni yayi fuskarsa a razane.
"Goje mai kuma yakawoka makarantar mu,wani abu akayi maka wanda ya shafemu?"
Jijjiga kai nayi tareda sosai ƙeyata da makullin mashin ɗina,karewa malaman da suka
shigo office ɗin nayi da kallo,wai sunace wani tawayen nazo yimusu?
Hhhhh harsun bani dariya ma,nuna ma principle ɗin kujera nayi ya zauna.
"Zauna mana shugaban makaranta,niba tawayene ya kawoni makarantar ka ba,koka ganni
da sanda kai?.
Matata nazo sakawa a makarantar nan,ayimin bayanin tsarin naji"
Bashi kaɗai ba ni kaina nayi mamaki dana faɗi abinda yakawonin.
A diririce yafara bani bayanin makarantar,na uniform ɗinsu bangaren islamiyya da
kuma na boko. Dubu goma a shekara islamiyya,boko kuma dubu ishirin.
Damin kuɗi na cire a jakar hannuna bansan nawa bane na ajiyemasa.
"Gashinan kudin makarantar ta harta gama,ku ɗinka mata uniform sannan intazo tayi
muku bayanin ajin da take so tashiga. Inda sanji ku riƙe,in kuma basu isaba ku saka
sorry. Nizan tafi,gobe ku tabbatar komai da take buƙata na karatun tanadeshi,idan
naji labarin ba'a bata wani abuba saina babbake makarantar nan"
"Bakomai bakomai goje zata iya zuwa sai muji inda ta tsayah,komai daya kamata duk
za'ayi mata,inkana so ma har malama za'a ɗauka mai nuna mata yanda zatayi. Batun
ƙudi kuwa sunyi yawa ma a yanda ake buƙata."
"Wannan kuma ku ta shafah,in nayi karo da wani kuskure ko kaɗanne ta ƙaremuku,saina
tashi wajennan dukka"
"Ahh goje ga wannan takardar ka kaimata ta cika,ta nanne zamu san a wanne mataki
take,ta haka ne zamu san wanne abubuwan take buƙata na karatun"
Da bazan karbi takardun ba,nizasu aika dan sun rainani,saikuma dai wata zuciyar
tace na karba ɗin.
Dana fita daga makarantar ba gida na tafiba,wani meeting na tafi wanda zamuyi na
siyasa.
Sai wajen azahar kafin na koma gidan,kicibiss mukayi da itah zata fito daga ɗakina
takaimin abinci.
Har ya wuceni zata tafi na tsaida ita.
"Kee"
"Na'am"
Tafaɗa tareda dawowa tana sunkuyar dakai,takardun na miƙa mata batareda nace komai
ba.
Ganin ta tsaya tana duddubawa yasa nace.
"Takardar makarantar kice,ki duba ki ciccika duk abinda kikaga kina buƙata,nabiya
kuɗin komai harki gama,dan haka inkinje zasu baki gobe"
Ƙiƙƙifta ido naga tanayi,hawayene yake zuba daga idonnata,kaddai bata son wannan
makarantar kai,naji ance kowa so yake ace a itah yake karatu.
Tsugunnawa tayi takama ƙafafuna ta rike.
"Nagode nagode nagode mijina,kayimin abinda bazan taba mantawa ba a
rayuwata,bantaba zaton zaka saurari magana taba bare harkayimin irin wannan
abin,daga yanzu zanyi komai domin faranta maka,wannan alƙawarine daga gareni. Bari
naje na faɗawa inna"
Tashi tayi da gudu tana share hawayen tayi hanyar ƙofar innan dagudu.
Jijjiga kaina nayi tareda ɗaga kafaɗa,wannan lafiyarta ƙalau kuwa??.......

Littafi na ɗaya ne dana biyu kaman yanda na sabayi,na ɗaya bati siddan,na biyu kuma
Naira 300 ne dan haka zaka iya biya tun yanzu kafin a shiga kashi na biyu.

3131951977
Auwal Sadiya
First bank

Ko katin mtn ta nan


09035784150

VTU ta nan
2347068390570

Shaida kuma ta nan


09035784150

Ƴan niger ku tuntubi wanann number.


+227 97 21 16 15
----------------------------------------------------

Sadi-sakhan ceh
09035784150
Share please

*SANADIN CACA*

Mallakar SADI-SAKHNA

PROFICIENT WRITER ASSOCIATION


*USERNAMES*
FACEBOOK PAGE:Sadisakhna
WATTPAD:@SAKHNA03
AREWABOOKS:@sadeesakhna
PHONE NO:09035784150
________________________________
*Book 1*
Chp[24]

[Sumaimah a mahangar gani]

Cikeda murna da tsalle na fada kan inna,tana tsugunne tana alwalar azahar.
"Ahah ahah Sumaimah lafiya mai ya faru?"
"Inna makaranta,inna zan koma makaranta,inna a Albayan ya sakani wai,zan iya cigaba
harda na boko nah inna"
"Mashaallah na tayaki murna Allah yasa kiyi ilimi mai yawa mai amfani,yanzu saki
nutsu ki rubuta komai"
"Yanzu ma kuwa zan cika ai,wayyo daɗi"
Ɗakin innan na faɗa ina tsalle,a yau goje yayimin abinda ko a mafarki bana
kawoshi,saboda nasan bazan samu ba,sai gashina samu,zan koma makaranta,hakanma mai
kyau.
Form din nabi daki daki cikin nutsuwa na cikasu,na islamiyyah ne da kuma na
boko,itah a SS 2 nasaka su sakani,duk da nasan kasada ce amma inason yin
kasadar,tunda ina ji a jikina zan dage nayi karatun bilhakki,islamiyyah kuwa dama
nayi sauƙa dan haka ajin tafsir da sauran litattafai na hukunce hukunce na saka.
Ranar ko baccin kirki da kyar ya daukeni,nayita jiran goje nayi masa godiyah,amma
har nayi bacci bai dawo ba.
Washagari da safe da wuri na tashi na gama komai,indomie na dafa sai kwai
akai,saboda karma nayi mai nauyi ya bata min lokaci,a tsatstsaye naci nada yawa ba
nayi hnayar ɗakin gojen,inna dai banda bina da kallo babu abinda take,in abin yayi
yawa tace uhmm kokuma ta jijjiga kai.
Da sallama ƙatuwa na isa bakin ɗakinnasa,hannuna riƙeda plate nakifah wani akai.
Jin bai amsa ba yasa najuya zan koma,motsin tafiyarsa naji,ina juyowa muka hada ido
dashi,fuskarsa ɗauke da alamar bacci.
Kinshiga uku Sumaimah kaddai tashinsa nayi a bacci kai..
Inda inda nafara ina neman mai zan kama na faɗa,inda sabo na saba ma.
"Uhm uhm dama....kodayake barina koma tun....."
"Shigo"
Haka kawai yacemin tareda komawa ciki,binsa nayi a baya kaina a ƙasa na ajiye plate
ɗin .
Kambu ashe ba riga a jikinsa ma,sai a sannan yake sakawa,kai ya jikinsa fari amma
fuskarsa baƙa....koda yake da wannan uban gashin fuskar wazai ɗorar kamarsa
dama,dan ma narage tsoransa yanzu,amma nasan sauran mutane kam wasu yanzu suka
fara.
Nikaɗai dai nake zantukana har yagama yazo ya zauna,gaisheshi nayi kaman ko yaushe
ya amsa a taƙaice.
"Zan tafi makarantar yanzu?"
"Saikin dawo,duba zif ɗin jakata ki ɗauki ɗari biyar"
To nace tareda da ɗauka kaman yanda buƙata na fita daga gidan cikeda zumuɗi.
Office ɗin shugabar makarantar naje muka gama magana dashi,kaman yanda na nema sun
barni a SS 2 ɗin,wanda nasan dan suna tsoron gojene,amma sun gargaɗeni na dage.
Wata malama ce ta gwadani akan zuwa yamma za'a kawomin kayan makarantar da kuma
litattafai da duk abinda nake buƙata. Nidai da toh nake binsu har suka gama yimin
bayani. Dukka da safene zuwa ɗaya na rana,sai islamiyyah Asabar da lahadi shima
daga safe zuwa sha biyu.
Bayan mungama nayi zaton gida zan dawo,amma sai suka cemin zan iya shiga aji kawai.
Hakan yasa kawai na nufi aji,Allah ya taimakeni ma a farkon shekara suke.
Bayan an tashi tafiyah nake ina jan ƙafah,nagaji tulus abinka da wacce ta daɗe
batayi ba. Duk zumuɗinnawa yakoma ciki,nafara farfaɗowa daga mafarkina yanzu zan
tsunduma zahirin karatu tunda na samu dama.
Lokacin dana isa gida an daɗe dayin azahar,na samu inna tayi abinci,gaji ma ta miƙo
mana awara,dan tunda taga muna abinci intayi ko bazamuci ba saita sakomana,saboda
muma mu saka mata,har wai hirar dare take zuwa ayi ta zance,ni dariya ma take
bani,ko kunya ace mutum bayaji....kai Allah ya kyauta.

Da yamma kuwa kaman yanda shugaban makarantar yafaɗa,ya aikomin kayana uniform da
kuma jaka ɗauke da litattafai,na rubutu da kuma na karatu,harda ƙur'ani izu sittin
aciki..
Nikamma dan daɗi narasa bakin magana,ko ƴaƴan gata albarka,babu abinda yarage sai
karatu kawai..

__***__

"Deejah ki ɗauki ruwannan kiyi wanka kizo ki tafi makaranta,kinsan fah abinda
yayanku ya faɗa"
"Bazan jeba,nace bazanje ɗin ba,ki faɗamasa idan yazo yaga banje ba ya kasheni nace
ya kasheni,littafinma......"
Bata ƙarisa maganar ba ta rabashi gidan biyu fiyattt.
Kallonta ammi take da takaici,komai yasa Musbahu yakeson bata kuɗinsa akan wannan
halittar oho,a zatonsa wai hankali zatayi irin na sauran mutane idan ya kaita
makaranta?
"Deejah kika yaga littafin makarantar?"
"Ehh ɗin na yaga kuma......."
Bata ƙarisa maganar ba sukayi ido huɗu da Musbahu,wanda yake tsaye a bakin shiga
ƙofar tasu,ya saƙala hannunsa a kirjinsa yana kallonta,fuskarsa cikeda bacin rai.
"Ya mukayi dake,me kika cemin jiyah"
"Ehh ni cewa nace zanje makarantar inna je kuma zanyi karatu,idan na ƙiyi a dakani"
"To me yasa daga zuwanki ɗaya jiya kikace bazaki sake zuwa,wato irin duk abinda
zanyi nayi harda yaga littafin koh,ana kije kiyi wanka kina cewa bazakiyi ba"
"Ahah ni bance baxanyi wanka ba,sannann kuma littafin bani na yagaba fatalwar
tunkiyar rammah ce"
"Ohh bayan kin soke tunkiyar ma kaman wata raƙuma bai isheki ba saikin bita kinyi
mata sharri,ki dai faɗi gaskiya abinda yahanaki komawa makarantar,kin fasawa malami
goshi ai dole kice bazaki jeba"
"Ke rammah dagaske ta rotse kan malami,a ina kikaji?"
Ammi ta tambaya tana riƙe haba.
Wata harara Deejah ta watsawa rammah tareda cewa.
"Nasan wadda ta faɗamiki,wato duk da gargaɗin danayi mata bataji ba koh,hmmmm"
Bulala Musbahu ya zara zaiyi kan Deejah,amma kururuwar da uwaisu yakeyi ta tsayar
dashi.
Daga ɗakinsa yafito yana kururuwa,banda ambaton kuɗinsa babu abinda yakeyi.
Kowa tsayawa yayi yana kallonsa a wajen.
"Kuɗina wanene ya ɗebemin kuɗina,wayyo shikenan kun lahantani wane shegenne ya
bankaɗemin ajiya yamin sata waye?"
Haɗa ido sukayi da Deejah wacce take tsaye a bakin banɗaki,saboda gudun da tayi
daga wajen Musbahu.
Gwaliyo tayiwa uwaisu tareda kashe ido,aikuwa nan ya gane mai take nufi.
"Zo shegiyar yarinya zo nan, tunda kika kasheni ai sai ki bar gidannan,ki faɗamin
inda kika kaimin kuɗina"
Kowa yanxu kallo wajen Deejah ya koma,wacce take kallon mutanen wajen idonta a
tsatstsaye kaman nono maza..
"Niba kuɗi na ɗauka ba takardu na ɗauka,jiya fah aka tambayeka a gida za'ayi abinci
kace bakada kuɗi,to ni taya zanga kuɗi a ɗakinka bayan kace bakada kuɗi,takardu na
ɗauka,kuma nayi makamashi dasu"
Tafaɗa hankalinta kwance kaman batasan mai ta aikata ba,bayan kuma tana sane rashin
mutuncine kawai. Dan yanzu ta daina wannan gurnanin,tsiya take shukawa a gidan
cikin hankalinta.
Kama ƙirjin uwaisu yayi numfashinsa yana yin sama sama,kafin Musbahu ya tafi da
sauri ya taroshi har yakai ƙasa..
Ihu da kururuwa mutane gidan suka saka,aka nufi asibiti dashi.
Banda Deejah waccce ta shiga wanka zata tafi makarantar da tace bazata ba.
Ammi ce ta kalleta wacce tazo ɗaukar mayafi zasu tafi asibitin.
"Amma wannan yarinyar bakya cikin mutane inaga,yanzu kiga abinda kika aikata masa
amma bai dameki ba?."
"Ahh to ubana ne dazan damu,kuke wani kukan munafurci naga kuma ba damuwar kukayi
dashi ba,shima kuma ba damuwa daku yayi ba,yanada kuɗin jiya ya kawo ayi tuwo yace
wani bashida kuɗi,kuma yanzu yafito yana faɗuwa wai an ɗauke masa kuɗi,harda za'aji
haushina ma ai na banza ne,kuɗi suna amsa sunansu kuɗi idan za'a kashe ,inku aka
ajiyesu da bunu ne.
Nina tafi makaranta naga yanda zamu ƙare da wancan shima wani uwaisun hmmm,aishima
in bai kiyayeni ba saina figewa wannan ƴar tasa mai suffar agwagi ƙafafu"
Surutun take tana tafiyha harta bar gidan,ita kuma ammi ta tari acaba zuwa
asibitin.
Lokacin da ammi ta isa asibitin har an saka masa ruwa yana kwance,yayi shuru da
alama bacci yakeyi.
Musbahu ne a jingine a jikin bangon ɗakin,sai rammah a gefensa a zaune,magana
yafarayi kaman zautacce..
"Kuɗina kuɗina dana tara,da ƙonamin kuɗina mai kuma ya sauramin tunda na kuɗina"
"Baban ubadu dan Allah kabar zancennan,wai yau kafara rasa kuɗinka ne,naga kusan ko
yaushe kaje caca sai ka rasa kuɗinnaka,har ƴar ka ka rasa abin bai dameka ba,amma
yanzu akan kuɗi kana ta tadawa mutane hankali"
Ammi ce tafaɗa cikeda takaici,dan itama kaman Deejah abinda kuma yafara bata
haushi..
"Dallah rufemin baki,kinsan kuwa kuɗinnan na menene,duk sanda nayi caca tayi kyau
zuwa nake na tara su,hatta kuɗin gonata ma ta hayi tana siyar suna ciki,kuɗinnan su
nake gani nakejin daɗi,saboda yanda sukeda muhimmanci a wajena,kuɗin sadakin
Sumaimah ma suna ciki,harda kuɗaɗenku da in ansiyar dabbobi nake cewa sun
faɗi......"
"Kambuuuu kace har kuɗin tunkiyata ma data kasa narasa su suna wajenka kenan"
"Ke dallah dana ɗauka ma ai ba cinyewa nayi ba ajiyewa nayi,bare kice nayi miki
sata"
Faɗa ne ya kaure tsakanin uwaisu da matannasa,kowa tana faɗin albarkacin bakinsa..
Musbahu bayan ya kallesu na ɗan lokaci ɗauke idonsa yayi yana jijjiga kai,shikamma
inaga barin gidannan zayyi yayi nesa dashi kozai hutah,ace kullum sai wani abu ya
bullo a gidan. A irin wannan rigimar tasa yake ya ɗakko wata hatsabibiyar
yarinya,tausayin halinda take ciki da kuma ganin nauyinta yana kan ubansa shiyasa
ya fara kulada lamuranta,domin ko kaɗan bayaso a kuma yarinya wacce zata maimaita
rayuwa irin ta Sumaimah a gidan,amma kash ba'a ma farashi ba wata ta bullo. Dan da
alama kuɗaɗensu da abubuwansu da uwaisu ya ɗebe ya ajiye na tsawon lokaci sun
faɗa,wanda hakan yana shirin mayar da shi suru suru.
Juyar da kansa yayi bakin ƙofah suka haɗa ido da Sumaimah,sanye take da kayan
uniform na Albayan,yaushe tashiga makaranta..
Hijabinta ya kusa zuwa ƙasa,da sandal da safa a ƙafarta,sai babbar jakar makarantar
data rataya,tayi fari tai kyau kaman ba itah ba..
Shuru kakejin su rammah sunyi,dan suma a tare sukaga Sumaimah tashigo ɗin,babu
wanda zai kalleta yace Itace yarinyar da aka kai gidan miji watanni uku da suka
wuce.
Tayi kyau haskenta yasake fitowa,tunda ta tafi kowa ya manta da babinta saboda
sabon abinda ya kunno musu kai.
A hankali take tafiyah harta isa inda uwaisun yake kwance.
"Baba mai yafaru haka,yanzunnan nadawo daga makaranta na shiga ta gida,anan suke
cewa wai kuna asibiti"
Tausayinta ne yakama Musbahu,inaga bazayyi ƙarya ba idan yace kaff cikin ƴaƴan
gidan babu wanda yakaita tausayin ubannasu,koda yake ita matsayinsa take bashi
cikeda ilimi da kuma sanin darajarsa a wajenta,sabanin sauran yaran gidan da suke
masa kallon ba komai ba,irin yanda iyayensu suka nuna musu. Ƙasa yayi dakai yarasa
ma mai zai ce mata,da alama kunyarta ne yakamashi.
"Uhm uhm bakomai Sumaimah,yakk a gidan naki dai?"
Ɗan murmushi tayi tareda cewa.
"Bakomai baba muna zaune lafiyah,yanda ake zatonsa ma ashe ba haka yakeba,kalli fah
yasakani a makaranta,shine ya kaini makaranta ma yau dazai bi ta wajen,inna ma ta
ɗaukeni tamkar ƴar ta"
"Ahh to to abu yayi kyau Allah ya taimaka,kinga tashi maza ki tafi gidanki,inyaso
wani lokacin sai kizo gidan koh"
"Amma baba mai yasameka aka kawoka asibiti"
"Ke fah dama kin faye magana,to tunda so koke kiji waccar hatsabibiyar yarijyar ce
ta ƙonamin kuɗaɗena,kai wannan ƴa na rasa yanda zanyi da itah,ace ƴaƴan ka basu
takura maka ba sai can wata bare?"
Sumaimah bata tambayi wa yake nufi ba,saboda tagano da Deejah yake.kuɗi ta ciro
kaman dubu Biyar ta ajiye masa a gabansa.
"Gashi baba toh ka riƙe wannan,yace nayi siyayya ne to banyi ba saboda naji kuna
asibiti,sai a siyamaka abinda zai gina jiki. Ammi da inna rammah ni barina wuce toh
saina sake zuwa"
Babu kunya tunkafin ta gama bayanin uwaisu yasaka hannun ya fizge kuɗin tareda
sakawa a cikin rigarsa,babu zancen siyan wani abu kenan.
Ammi ce kawai tayi mata a sauƙa lafiyah,rammah kam ɗauke kanta ma tayi.Fuskarta
ƙarara bata boye baƙincikin da take ciki.
Tashi tayi zata tafi,a nan ta kulada Musbahu wanda yake tsaye,gabaɗaya ma inaga
bata ganshi ba ɗazu.
"Lahh yah Musbahu banganka ba,barka da rana ya mai jiki?"
"Yawwa sannu Sumaimah,akwai maganar danake so muyi dake,in lokacin yazo zan sanar
dake,wata alfarma nakeso kiyimin kinji?"
"To shikenan yaya karka damu Allah ya kaimu lokacin"
Cikin farinciki da murna tabar asibitin zuwa gidanta,dukkan su kowa sai binta da
kallon mamaki yakeyi,kaman ba ita. Wasu sunyi farincikin sauyawarta,wasu kuma babu
yabo ba fallasa,yayinda wasu kuma zuciyarsu take tafarfasa.

Littafi na ɗaya ne dana biyu kaman yanda na sabayi,na ɗaya bati siddan,na biyu kuma
Naira 300 ne dan haka zaka iya biya tun yanzu kafin a shiga kashi na biyu.

3131951977
Auwal Sadiya
First bank

Ko katin mtn ta nan


09035784150

VTU ta nan
2347068390570

Shaida kuma ta nan


09035784150

Ƴan niger ku tuntubi wanann number.


+227 97 21 16 15
----------------------------------------------------
Sadi-sakhan ceh
09035784150
Share please

*SANADIN CACA*

Mallakar SADI-SAKHNA

PROFICIENT WRITER ASSOCIATION

*USERNAMES*
FACEBOOK PAGE:Sadisakhna
WATTPAD:@SAKHNA03
AREWABOOKS:@sadeesakhna
PHONE NO:09035784150
________________________________
*Book 1*
Chp[25]

[Goje a mahangar gani].

A yanzu walwalarta da farincikin da take ciki yafi na lokacin baya.duk da koyaushe


batada lokacin kanta.Kullum tana kan hanyar makaranta,ga kuma aikin gida wanda naga
babu wanda ta tsaya dayi,amma babu alamar nuna sarewa fuskarta,da alama hakan shine
ra'ayinta kuma burinta.
Gobe nake shirin sake komawa ƙungiyar BC sun nemeni wani aiki mai hatsarin
gaske,mutane tarane kacal zasu tafi yin aikin,kuma ina ɗaya daga cikinsu. Haka
kawai saina tsinci kaina ta rashin son barin gidan,bansan meyasa ba.
Yanzunnan shigowata gidan mun gama waya da Don3 sannan a wannan aikinne idan muka
dawo zamu haɗu da Don2 kasancewar har yanzu sunansa kawai mukeji.
Wayace a hannuna ƙarama nokia,wacce zan dunga waya da su inna,duk da wani bangare
na zuciyata yasan danna na dunga magana da Sumaimah ne. Haka kawai yanzu nakejin
bana gajiya da ganin wannan fuskartata idan tana tsorona.
Gidan shuru kakeji da alama wannan gajin itada iyalanta basanan,sun samu gardama da
mijinnata akan zuwansa wajen mata. Aikinsu kenan ai.
Kasancewar anyi isha a daki suke hirar,dan haka nima nan na shiga..
Sumaimah tana kwance akan ƙaramin gadon innan,itakuma tana tsakar gida da carbi a
hannunta.
Karatu take a littafinta ta kunna fitila,wanda hakan yasaka hasken ya haska
fuskarta..
Ban kalleta ba,itama iya sannu tayimin kawai,ƴar hira muka taba da inna kafin na
ciro wayar na miƙa mata..
"Inna zanyi tafiyah irinna wancan karon,dan haka ga wannan ki riƙe saboda ko zamu
dunga gaisawa"
"Ahah ahah kacan matarka ka bani,maza bata gatacan...idan gaisawar ce inka ƙira
saita bani,amma ni ina zan iya wata waya"
Ɗagowa tayi da idonta jin maganar da ake,da tayi niyyar ɗauke kanta,amma ganin na
miƙa mata wayar yasa ta taso ta karba da hannu bibbiyu.
"Nagode"
"Toh inna ni zan tafi ko ya ake ciki duk zan sanar daku"
Fitowa nayi daga ɗakin na nufi nawa,kayan aikin nagama shiryawa a jaka,kana na
saƙalota.
Ina cikin kulle ɗakin naji takun Sumaimah a bayana.
Hannayenta a saƙale suke a bayanta,tanayimin kallon mamak,na gane hakanne saboda
farin watan daya haske wajen.
"Wajen fashinnan zakaje?"
Muryarta tana rawa tayi maganar,haka kawai na tsinci kaina da kasa bata amsar
tambayartata,komai yasa oho.
"Shin dolene sai kaje,kasan fah babu kyau hakan bai dace ba,inda zakaje ka tarwatsa
suma sunada iyalai,ko ya kabamu zai ishemu basai ka ɗebo da yawa ba wanda ba naka
ba"
Matsawa kusada ita nayi na miƙa mata makullin hannuna,har a zuciyata nasan zancenta
gaskiya ne,amma bashine abinda zuciyata takeso ba.
"Ki kulada inna,akwai number Tunga a ciki,ki ƙirashi in kuna son wani abun,aikin
dazanje wannan karon yanada hatsari,dan haka idan ban dawo ba harkika gama
karatunki,to kiyi rayuwarki yadda ya dace tun farko takasance"
Hannuna naji ta riƙe tareda makullin,jijjiga kai take wannan karon ta kasa cewa
komai,shin yaushe kusanci yashiga tsakanina da itah bansani ba..
Zare hannuna nayi tareda yin hanyar waje ina saƙale da zakata. Can ƙasa ƙasa najiyo
ƙaramar muryarta ina shirin fita daga gidan.
"Ka kulada kanka,zamu jiraka harka dawo"
Runtse idona nayi,bantaba jin irin wannan yanayin idan zan bar gidaba sai yau,wanne
irin abune yake shirin faruwa danine. Koma menene kawar dashi nayi na maida
hankalina ga aikin dayake gabana,wannan ne aikina na ƙarshe daga nan zan zama
shugaba a bangarena,zasu bani kayan aiki da komai danake buƙata.
Kaman koyaushe baƙar motar da take ɗaukata ce ta tsayah,ina shiga kuwa taja zuwa
cikin dajin.
Kwananmu uku muna training da shirye shiryen yanda wanann harin zai kasance,tun
daga sannan na gane wannan dabanne da sauran aikin danayi da ƙungiyar.
Sai a kwana na ukun aka taramu domin faɗamana abinda zamu je yi.Kuma yauɗinne zamu
tafi.
Mu tarane kaman yanda suka faɗa a tsakiyar filin.
Don 2 Ne a zauna kan kujera,kaman koyaushe sanye yake da suit baƙaƙe,yafara
manyanta amma kana ganinsa kaga tantiri,ya runa gashin kansa gefe gefe fari,sai
tsakiyar kuma ja.
"Barka da wannan lokaci ya gwarazan jarumanmu,a yau zamu faɗamuku menene abin
harinmu a wannan aikin,sannan in mun gama bayani zaku hau jirgi zuwa babban
sansaninmu na garin abuja.
Munason Sace Bayanan Nuclear da za'a kawo ƙasarnan a ranar 23 ga watannan,wato
nanda sati biyu kenan.Wannan kundin yanada matuƙar muhimmanci,kuma za'a kawoshi
cikin tsaro sosai. Zaku sake samun horo a wajen babban member ɗinmu na can,shine
mai kulada harkar hacking da gano mai ke Iya zuwa ya dawo. Kuma shine zaija ragamar
shirin a can,ku naku aikin shine abin abinda yace.
Ina fatan kun fahimta"
Dukka a tare aka bashi amsa bandani,dan haka kawai bansan meyasa ba yake bani
haushi,kuma nake jinsa kaman na sanshi.
"Wannan aikin yanada hatsarin gaske,wanda ya samu nasarar dawowa za'a bashi maƙudan
kuɗaɗe,sannan a lokacinne zaku haɗu da Don1 kafin kuma shugaban ƙungiyar,wannan
shugabana ne zai faɗamuku mai zakuyi ya haɗaku da shugaban wannan ƙungiyar"
Hmmm dama nasan za'a rina,aikin gamu kashemu zasu turamu,bakomai dama kasada gaba
muka bata ba bayaba,sannan zuciyata bata rayamin tsayawa daga haka tunda na riga na
fara.
Ƙarar sauƙar helicoper muka faraji,hakan yasa muka shirya domin tafiyah.

Layi muka yi zuwa wajen jirage guda biyu wanda suke ta diri,toh satar ma a jirgi
za'a je kenan,kai kaga sata mai aji.
Announcement aka fara bayarwa bayan mun shiga cikin jirgin.
"Daga nan zamu tafi secret domain ne dayake cikin abuja,anan zamu zauna na tsawon
sati guda mu Shirya komai kafin target ɗinmu ya iso"
Yana gama faɗan hakan aka rufe ƙofar jirgin muka tashi sama,belt naja na saka a
kunkumina,abinne yabani mamaki,taya akayi nasan inda belt ɗin yake,sannan na gefena
sai diriricewa suke suna rirriƙe duk inda hannunsu yakai lokacin da jirgin zai
tashi,amma ni banji komai ba,ji nake kaman na saba ma da shiga jirgin,mai yake
faruwa ne?.
Tafiyah muke tayi a saman,har muka iso inda jirgin zai sauƙa.wani gidane daga waje
iya rufune,amma muna shiga naga ashe a can ƙasa aka yi ginin.
Wajen ya ƙawatu matuƙa,idan ba naga lokacin da muka shigo ba,bazan taba yarda cewar
a ƙasa wajen yake ba,gashi tarau tarau duk da hasken da wajen yayi kaman da rana.
Dukkanmu kowa ɗakinsa daban aka bashi da kuma duk wasu abubuwa dazai buƙata,sanann
duk safiya zamu dunga fitah training da yanda zamu tsira idan jamian tsaro sun
taremu. Nidai banajin abinda suke cewa ina sai zuwa gobe,tunda suka nunamin ɗakina
nashiga nayi wanka,wai goje zayyi wankan arziƙi kenan bana sabulu ɗan yanka ba.
Nafaɗa a raina ina murmushi,tsuke fuska nayi tareda ɗan ja da baya a gaban madubin
ina kallon fuskata,wai ba dole ma a dunga gudu idan an ganni,haka Sumaimah take
kallona ashe??.
Kaya Nagani a cikin ƙaramar drawer,bayan nasaka ina fitowa naga dukka sauran suma
irin nawane kayansu.
Bayani aka farayi yanda tsarin sace abun zai kasance,sai koyon harbi da kuma
juriya. Shi mukayi ta koya har ranar 23 ga watan tazo ta.
Tofah abin yazo inji mai tsoron wanka,cikin daren yau zamu kai farmaki babban gidan
tsaron a nan abujan mu ɗauko bayanan wanda yake a wajen da aka killace shi.
Bindigogi aka bamu manyan manya cikeda bullet ɗinsu,kai dolema wannan ƙungiyar
tanada saka hannu wani babba,in ba haka ba taya zasu samu irin waɗannan makaman
haka.
Ta wata ƙofa muka shiga ta sirri wacce tabi ta cikin ƙasa,har muka shiga cikin
ginin a haka.
Nidai abinma kaman film haka naganshi.
Tafiyah muke babu wata matsala a nawa rukunin da nake ja har muka isa ɗakin da
bayanan suke ciki.
An ce mana bayanai ne,amma ni ban yadda da hakan ba,in bayanai meyasa baza'a turo
ta na'urar sadarwa ba. Sannan kuma abin yayi matuƙar bani mamaki,ganin har mukai ga
ɗakin da akwatin yake amma kuma babu kowa a cikin ginin.
Hasalima ƙofar da abun yake a buɗe take.
Wani abokin tafiyarmu ne ya tafi gafa gafa zai ɗauki akwatin,har zan hanashi sai
naji ɗakin yafara wata ƙara,wutar wajen takoma ja mai walwali,shikuma wanda yaje
kusada akwatin dake shoking ya daskararshi..
Ƙarar taku na tahowar jami'an tsaro mukaji,ga ƙofar ta kulle baza'a fitaba saidai a
shigo.
Munanan mutane da yawa cikin kaya na sojoji suka fara shigowa,suna harbi muma
munayi,kafin wani lokaci anyi raga raga da ɗakin,sojojin da mutanen mu sun ji rauni
wasu kuma sun mutu.
Idona ne ya kai kan akwatin,wanda a garin harbi aka jajjage na'urar rezar wajen.
Cikin zafin nama na fizgeshi nayi wani window da gudu,wajen kusan hawa uku ne,ina
faɗawa nafara gudu,naji alamar faɗowar wani ya biyoni,duk da buguwar danayi amma
bna tsayaba na cigaba da gudun.
Munyi ƴar tafiya kafin naji ya bangajeni. Akwatinne ya faɗi gefe muka fara faɗa
nidashi,yanada ƙarfi sosai da alama sojane mai zafin nama.
Saidai nima na nunamasa nawa zafin damtsen,ganin nafara cin galaba akansa yasa
nafara dan sararawa, Hular kansa na yage,saurayine fari,na shagala da kallon
fuskartasa wacce takemin kamada ta wani naji wani zafi ya ziyarci cikina. A hankali
nakai idona wajen,inda ya cokamin wata wuƙa a ciki,hakan bai isheshi ba saida ya
jata yayimin mummunan rauni,dishi nake gani a haka ya samu nasarar cire min nima
hulata,zaro ido kawai naga yayi yana shirin magana,kafin yace wani abun wata mata
sanye da baƙaƙen kaya ta buga masa ƙasan bindiga akansa. Tare ni dashi muka zube a
wajen,na saddakar tawa ta ƙare kawai. Ina jin lokacin da jinina yake fita daga
jikina.
Buɗe idona nayi naganni a cikin wani kogo wanda yayimin kama da wanda nasani,wato
na garinmu.
To waye ya kawoni nan wajen? Nayiwa kaina wannan tambayar.Yunƙurawa nayi zan
tashi,wani azababben raɗaɗi ya jiyarci inda sojan ya soka min wuƙa. Kai sai yanzu
ma na tuna kenan komai ya faru a gaske kenan.
Idona nakai kan cikinnawa wanda aka naɗeminshi da farin bandeji,gefe kuma audugane
wanda akayi ta goge jinin wajen.
Koƙartawa nayi na zauna ina haki na wahala,wata takarda nagani na gefena an naɗeta
an ajiye.
Ɗauka nayi duk da dishi dishin danake gani nafara karantawa.

.....Nasan zakayi mamakin ganin kana abuja amma lokaci guda ka dawo garinku,nice na
kawoka,amma ba lallai sai kasan ni wacece ba,duk da niɗin nasanka......kayi ƙoƙarin
komawa gidanka kayi jinya ka warke,ta hakane zaka samu damar kulada wannan akwatin
da kayi nasarar ɗaukowa,shiɗin abune mai muhimmanci ga ƙasarka da kai kanka a
matsayinka na.........
Wajen bai ƙarisa karantuwa ba ta yage shi,da alama wacce ta rubuta ɗin ta faɗi
matsayina,amma kuma saita sanja shawara ta yage wajen.
Waiwayawa nayi da idon inda akwatin yake.Ban mantaba shine wanda nake shirin saida
raina akansa.
A kwance nake ina tunani,na,rasama mai zanyi.
Cikin dauriyah na miƙe tsaye,hannu nasaka na ɗauki akwatin,amma ko kaɗan na gagara
ƙara ko taku ɗaya daga wanda nayi.
Komawa nayi na zauna,wata dabara ce ta faɗomin. Rigata na fara lalumewa,anan naga
wayata a cikin kayannawa,number Tunga nayi ta ƙira amma a kashe,tun inayi harna
gaji.
Number Sumaimah na ƙira,tana ringing amma ba'a ɗagawa,saida nayi kaman sau uku
kafinnaji ta ɗaga.
Shin meyasa na nemeta a ɗaya daga cikin waɗanda zasu taimakeni lokacin danake neman
taimako? Koma dai menene naji daɗi dana sametan.

Littafi na ɗaya ne dana biyu kaman yanda na sabayi,na ɗaya bati siddan,na biyu kuma
Naira 300 ne dan haka zaka iya biya tun yanzu kafin a shiga kashi na biyu.

3131951977
Auwal Sadiya
First bank

Ko katin mtn ta nan


09035784150

VTU ta nan
2347068390570

Shaida kuma ta nan


09035784150

Ƴan niger ku tuntubi wanann number.


+227 97 21 16 15
----------------------------------------------------

Sadi-sakhan ceh
09035784150
Share please
*SANADIN CACA*

Mallakar SADI-SAKHNA

PROFICIENT WRITER ASSOCIATION

*USERNAMES*
FACEBOOK PAGE:Sadisakhna
WATTPAD:@SAKHNA03
AREWABOOKS:@sadeesakhna
PHONE NO:09035784150
________________________________
*Book 1*
Chp[26]

[Sumaimah a mahangar gani]

A galabice na shigo gidan,na dawo daga makaranta,kai neman ilimi kam akwai wuyah.
Uniform na fara cirewa sai naji wayar da goje tabani tana ƙara,tunda ya tafi bai
taba ƙiraba,iyah Tunga kawai na taba ƙira yakawo mana kananzir.
Ɗauka nayi naga two missed call,goje?? Ni nayi zaton Tunga ne ma ya ƙira.
Tunda ya tafi hadda cewa sati biyu zayyi,abu ana shirin yin wata amma bai dawo,mai
kuma zai ƙira yace. Dama yana raye kalau kenan.
Ɗagawa nayi tareda yin sallama a hankali,yanayin dana ji muryarsa ne yasakani maida
hankali kan abin zai ce,idan ba kunnena ne ya samu matsala ba toh nishi naji yana
yi.
"Hello Sumaimah kin....ajinahh?"
"Ehh ina jinka mai yasameka,wata matsalarce ta faru?"
"Kinga ki tsaya ki saurareni,kinsan wannann dutsen mai kogo na bayan gari?"
"Ehh ....eh nasani"
"Toh kizo ki sameni a wajen,ki tahomin da abinci da kuma kaya,yawwa sannan ki je
chemist zan turo miki sunan wasu magunguna ki tahomin dasu,sannan karki sanar da
inna komai"
Daga haka ya kashe wayar,wani bugawa kirjina yayi,yayinda kaina yafara lissafomin
abubuwa da dama,shin mai ya sameshi yake cikin kogo,shida yayi tafiya..
Kayan na cire a gurguje na nufi inda abincin mu yake. Ɗiba nayi a kula na saka a
kwando da,hijabi na zura na fita daga gidan da sauri..
Akan hanya chemist ɗin yake,magungunan daya faɗamin nasiya,harda auduga,plaster da
kuma bandaji acikin abinda ya turo ɗin, ciwo yaji,shine abinda yafara zuwa kaina
lokacin dana siya abubuwan.
Pure water na siyah a ɗaya shagon,daga nan na nufi inda yayi min kwatance.
Da ɗan tazara wajen da cikin gari,dan haka saida na taka kafin na isa..
Ina shiga wajen na sameshi a kwance akan kayansa,gefensa kuma akwatine da tarin
auduga duk jini a jikinsu,idonsa a rufe yake yana kallon saman kogon,inda bashi
yayi kwatance ba zan iya cewa bashine bane,don babu wannan gashin fuskar dana
sanshi dashi,sannan yayi fari ya rame kaman bashi ba..
Numfashi yake fitarwa hankali ma wahala. Ban lokacin dana isa wajensa ba da
sauri,bayan na ajiye kwandon danazo dashi..
Tsugunnawa nayi a gabansa ina ƙare masa Kallo,fuskata ɗauke da damuwa ƙarara,na
tunanin shin wanne irin mummunan abune yasameshi haka,sannan kuma yaushe?
Buɗe shanyayyun idanuwansa yayi ya ɗora akaina masu kama dana majinyaci.
Nima kallonnasa nake da nawa idanuwan wanda suka cika da ƙwallah,fatar bakina
nakeson na buɗe nayi masa tambaya,amma sai rawa suke sun kasa bani haɗin kai.
Hannunsa ya ɗakko zai kawo wajen fuskata,amma abinka da dama tsoronsa nake,saina
ɗan ja da baya.
Murmushi yayi tareda rufe ido a hankali yakuma buɗewa,dimple ne ya lotsa a gefen
kumatunsa,dama yanada wannan abin a fuskarsa,amma ba wanda yasani saboda gashin
fuskarsa,yanzu daya aske sainaga kaman wani mutum daban aka ajiyemin. Ashe farace
fuskartasa kamar jikinsa,saidai bakinsa yayi duhu bakaman sauran fatar jikinsa
ba,saboda shaye shayen dayake.
"Duk da ina cikin wannan halin amma tsorona kikeji,shin mai zan iya yimiki a
yanayin danake uhm?"
Tari ya fara yana runtse ido,ban san lokacin dana tallafo kansa zuwa jikina,dama
gani Allah yayini banson naga mutum a halin jinya. Bare irin wannan,tsayawa yayi da
tarin tareda saqala hannayensa ya riƙo kunkumina gam,wanda nasan ciwon dayake jine
yasakashi yin hakan,a nanne nima na kulada bandejin dayake cikinsa wanda yayi jajur
dashi da jini.
"Sannu sannu,wayyo please ka tsaya barinaje na ƙira mai chemist ɗinnan,wataƙila
zasu iya taimakawa"
Ƙoƙarin zare jikina nayi domin na tafi,amma sai naji yasake ƙanƙameni sosai..
Magana yafara cikin gajiyayyar murya.
"Ahahh kada ki ƙiramin kowa,banason kowa yasan halinda nake ciki....kin kawomin
abinda na buƙata?"
"Ehh dukka na taho dasu"
"Uhm barina dashi ki gyaramin wajen,jikina ba ƙarfi bazan iya dakai na ba"
"Niiii ban ban....iya ba bazan iya gyara wannan ciwon ba"
"Uhmm zaki iyah mana ko baki iya ba zannunamiki yanda zakiyi,ba wani abune mai wuya
ba,taya zaki ƙira kanki matar goje idan kina tsoro uhmm?"
Nidai kurmiya na koma da zancennasa. Saboda kallonsa nake kaman bashi ba.
Tallafah masa nayi ya jingina da jikin dutsen,jikinsa har rawa yakeyi saboda zafin
ciwo.
A hakan kuma yasaka hannu ya sunce ɗaurin ciwon,wanda matar data kawoshi wajen tayi
masa.
Lokacin da yagama suncewar saida na rufe idona saboda yanda wajen yayi jawur kaman
ɗanyen nama.
"Ohh bazaki iya gani ba,taya kuma zaki iya wankemin idan kika kasa gani?"
"Ya akayi ka samu wannan ciwon haka,a wajen satar ne koh"
Nafaɗa cikeda jin haushin yana satar,koda yake yaudarar kaina nake,zaman danayi
dashine a wannan watannin nafara manta waye shi.
"Uhm a wajenne wani soja ya soka min wuƙa,ina faɗuwa dana bude ido nasamu kaina a
wajennan tareda abinda muka je sata ɗin. Sannan ba sata ce wacce kika sani ba,abune
na sirri da mutanena ma basu sani ba,shiyasa nace miki kada ki faɗawa kowa ina
wajennan ,saidai in yayi yawane ki faɗawa Tunga kinji"
Ɗaga kaina nayi tareda fitowa masa da abubuwan dayace na kawoɗin,naga yanda yake
maganar na fahimci lamarin mai tsaurine.
Kaman yanda yafaɗa shine yake nunamin yanda zanyi har muka gama rufe ciwonnasa,gumi
kuwa ya haɗashi shirkif saboda wahala.
"Gashi sai wahala kakeji,da baka jeba da haka bata faruba"
"Uhm to hakane,amma ni nasamu da sauƙima,tunda abokan aikina kusan duk sun
mutu,wanda sukeda rai ma suna hannun ƴan sanda. Wannan akwatin in zaki tafi gida ki
tafi dashi ki boyemin,zan kaiwa ƙungiya idan na warke"
"Kace tacemaka yanada muhimmanci,amma meyasa zaka kaiwa barayi,bayan kasan hakan
yanada hatsari,dan Allah karka sake komawa wajensu,duk da cewar
kaima........uhm ....amma dai kafisu kasaka hakan a ransu"
"Me kikeson fada kika fasa,nima bana kirki bane koh?"
"Ahah nidai bance ba amma dan Allah karka koma,inna bataso"
Hannunsa yasaka na dama ya ballamin akan goshina,nima sai a sannan nakulada yanda
na zage inata surutu.."
"Ya karatunki,daga gani dawowarki kenan bakici abinci ba..ɗebomin naji ko zan iya
ci"
Ɗan murmushi nayi ina shafa goshinnawa,kafin na ɗebo abincin. Miƙamasa plate ɗin
nayi amma naga ya kafeni da ido yaƙi ƙarba..
Har na fara tunanin ko bayason jallof ɗin taliyar,saikuma naga ya buɗemin baki,wato
so yake na ciyar dashi kenan.
Ɗiba nayi a cokalin cikeda kunya nakai bakinsa,ba kunya kuwa shi ya karba yafara
ci. Shuru wajen yayi sai numfashinmu kawai,baici da yawa ba ya min alamar ya ƙoshi.
"Naƙoshi bani ruwa,sannan ki cinye sauran,dan naga yunwa kikeji"
Ikon Allah tun ɗazu yake cewa yunwa nakeji,yaushe yafara kulada ni haka?.
Maganin dana taho dasu na miƙa masa ya balla,kafin na bashi ruwa ya kora dasu.
Bayan mun gama cin abincin alwala nayi na sallahr la'asar nazo na shimfiɗa
ɗankwalina,yana kallona harna idar da sallahr,Addu'o'i nayi kafin na juyo na
kalleshi..
"Amma tsawon wannne lokaci kayi a kwance"
Ɗaga min kafaɗa yayi tareda cewa.
"Bansani ba,kawai dai abinda nasani shine ranar 23 ga watana march ne aka sokeni da
wuƙa"
Zaro ido nayi tareda rarrafowa kusada shi,kenan satinsa guda a sume?
"Sati guda kenan kayi a kwance,dan yau talatinne ga wata"
"Uhm zai iya yiyuwa,kuma da alama wadda takawoni nan wajen har asibiti suka kawoni"
Yafaɗa yana nunamin hannunsa,inda aka saka masa canular,kaman ma yau aka cireta a
jikinsa,kuma wajen akwai takun sawun takalmin mace,harda robobin lemo da ledar
cakes.
"Amma wacece haka in tana cikin tawagarku meyasa ta ajiye maka akwatinnan,inaga
bataso ka kaiwa kungiyar nan taku"
Dan haka kawai naji banaso ya koma wajensu.
"Hhhhh da alama bakyaso na koma aikina,amma ke ruwanki ne,dan kinga bana iya komai
shiyasa har umarni kike bani ko"
"Ahah ba haka bane kayi haƙuri"
Koƙarin tashi nake shirinyi daga wajen,sai kuma naga ya kamo hannuna gam ya
riƙe,idonsa ya rufe yana jijjiga kan cikin sauri.
"Ciwon kaina wayyo kaina yana shirin tsagewa ahhhh,bansha wiwi ba,kibani wiwi
ɗina......."
Tambayata yake,amma da alama kuma badani yakeba,sambatune kawai na ciwo.
Hannayena na saka a gefe da gefen kannasa na riƙe,Addu'o'i nafara karantowa na
neman sauƙi,hannunsa yasaka yana ƙoƙarin ture hannuna,tareda ƙara sautin ƙarar
dayakeyi. Yayinda nikuma na riƙe gamm na dawo yi ma a fili,kasancewar jikinsa babu
alamar ƙarfi yasa ya kasa ture hannunnawa.
Can bayan kaman wasu mintuna naga yatsaya da jijjiga kan,ina dubawa naga yafara
bacci daga zaunen,gyara shimfiɗin danaga anyi masa da kayansa nayi,tareda kwantar
dashi a wajen.
Tashi nayi na tsaya ina kallonsa,daga yanda yake maganar kaman daman ya san da
ciwon kan kuma ya daɗe yanayi.
Dannima na sha ganinsa a ɗakinsa ya riƙe kai,kenan shiyasa yake shaye shayen. Har
yanzu na gagara fahimtar sa,kowacce rana sainaga wani abu sabo dan gane dashi.
Kayan abincin na ɗauka domin komawa gida,zanje na dawo kada inna inna taka bananan.
Karare na gona na ɗakko nayi ta jerawa saida na rufe wajen tass kafin na tafi.
Ina shiga gidan muka haɗa ido da inna,tun kafin nayi magana ta jefomin tambaya..
"Kekuma daga ina haka kikadawo,ɗazu naji motsinki ina tashikuma na bakyanan"
To anan gizo yake saƙar ,shin mai zan faɗawa inna,gashi yace kada na kuskura
tasani.Wata dabara ce ta faɗomin.
"Umm uhm inna dama wata ƴar ajinmu ce a islamiyya batada lafiyah,kuma ba ƴar
garinnan bace zuwa sukayi,shine to na kai mata abinci.....sannan inaso na zauna
mata kafin ta warke,tunda bakowa wajenta"
"To ikon Allah,dama rashinnaka a garinnan ba daɗi,kin kyauta sosai saki faɗawa shi
mijinnaki a waya"
"Ehh na tura masa message yace ba matsala,yace yana gaisheki ma wajen aikinnasu ne
ba a kiran waya ne"
"To shikenan ba matsala ina amsawa,zan shiga anguwa anyi matar ɗan marka ta haihu"
"To saikin dawo inna a gaisheta"
Daga nan tabar zancen,dan dama ita macece da bata matsamaka sai tasan mai
kake,musamman idan tasan abu kake boye mata.
Kuɗin na ɗauka a cikin wanda Tunga ya kawomana. Kasuwa na tafi na siyo hanta da
kuma alayyahu,dama duk wani abunda nake buƙata.
Farfesunta nayi masa da ɗan romo na juye a kula,saikuma shayi dana haɗa na zuba a
flask.
Wanka nayi lokacin rana ta kusa faɗuwa.
Pillow na ɗauka da sallaya sai butah,a cikin jakar da aka kawomana kayannan na saka
su,saikuma kwandon kayan abincin.
Lokacin dana ɗauki hanyar wajen ba sawun mutane sosai,Allah ya taimakeni dana ɗebi
ƴan kallo an ganni da kaya nayi bayan gari.
Yanda na rufe wajen haka naje na sameshi,saida na ture kararen kafin na shiga.
A kwance yake yanda na tafi na barshi yanata bacci,da alama maganin dayasha akwai
mai saka bacci a ciki.
Ban tsasheshi ba,dana ajiye kayan hannuna wajen na fara gyarawa. Na ɗebe dattin da
wanda suka kawoshi wajen suka zubar,da kuma audugar da sukayi ta goge ciwon
dasu,harda wanda muka cire muma ɗazu.
Shimfiɗa sallayar nayi gefe,kasancewar wajen rairayine,awakin mutanene masu kwana a
jeji suke shiga wajen da daddare,kokuma almajirai idan suka iyo itace su tsaya su
huta.

Littafi na ɗaya ne dana biyu kaman yanda na sabayi,na ɗaya bati siddan,na biyu kuma
Naira 300 ne dan haka zaka iya biya tun yanzu kafin a shiga kashi na biyu.

3131951977
Auwal Sadiya
First bank

Ko katin mtn ta nan


09035784150

VTU ta nan
2347068390570

Shaida kuma ta nan


09035784150

Ƴan niger ku tuntubi wanann number.


+227 97 21 16 15
----------------------------------------------------

Sadi-sakhan ceh
09035784150
Share please

*SANADIN CACA*

Mallakar SADI-SAKHNA

PROFICIENT WRITER ASSOCIATION


*USERNAMES*
FACEBOOK PAGE:Sadisakhna
WATTPAD:@SAKHNA03
AREWABOOKS:@sadeesakhna
PHONE NO:09035784150
________________________________
*Book 1*
Chp[27]

Basan ya tashi ba saida naji maganarsa tukunna.


"Yaushe kika dawo?"
Cikin magagin bacci yake maganar.
"Uhm ban daɗe ba sosai,sannu ya jikinnaka"
"Da sauƙi kawai zance,miƙomin ruwa nasha,bakina bushewa yakeyi akai akai"
Ruwan na ɗauko na bashi,lokaci guda ya zuqe guda biyu,Wannan wanne irin shan ruwane
haka,na faɗa a raina.
"Ga abinci yakamata kaci"
"Mts banajin yunwa, bar abinci nan,ki ƙiramin Tunga kice ya kawomin ajiyata danayi
a jeji"
"Ba abinci bane haka,nayine saboda ina tunanin ko jikinka yana buƙata,sannan a
halinda kake ciki bai kamata ka zauna da yunwa ba"
Ganin bai sake cemin komai bane yasa na jawo kular dana zo da itan,farfesun hantar
na tura masa gabansa,na manta banzo da plate ba..
Matsawa kusada shi nayi ina bashi a baki,daga yanda yake karba ma tabbatar
yanayimasa daɗi sosai,dan saida ya kusa cinyeshi tass.
Kofi na ɗakko bayan yagama na zuba masa shayi shima mai zafi.
"Yaushe kika waɗannan abubuwan haka?"
"Lokacin dana koma gidane,saidai kayi haƙuri na fita zuwa kasuwa da kaina,dama
inason na faɗamaka saikuma na manta."
"Uhm bakomai nagode da kulawarki,bani maganin can nasake sha naga har dare yafara"
Bayan na miƙomasa yasha ruwa na zuba a buta nima nayi alwala nai sallahr
magriba,kaman ɗazu yana kallona har na gama.
Sake zuba wani ruwan nayi nazo inda yake,kallon tambaya yakemin ganin na miƙamasa
hannu yabani nasa hannun.
"Kawo hannunka alwala zanyi maka,yakamata ka rama sallolin da ake binka,tunda ka
ɗan samu sauƙi"
"Taya kike tunanin zan iya sallah a haka?"
"Indai kana cikin hankalinka to zaka iya yin sallah,domin a kowanne yanayi mutum
yake ba'a ɗauke masa sallah,saidai idan baya cikin hankalinsa. Ance idan bazaka iya
a tsaye ba ka jingina,in shima bazayyi ba ka zauna,in ya gagara ka kwanta ka kalli
gabas,in shima bazayyiyu ba toh zaka iya yi a duk yanda ka tsinci kanka.
To haka ma wajen yin alwala,in jikinka bazai ɗauki ruwa ba saikayi taimama da
ƙasa,idan itama bazaka iya da ita ba to saika shafi jikin gini mai tsarki kayi
dashi.
Toh a wannan bayanin kaga kai zaka iya yin alwala kuma kayi sallah a zaune"
Bayan gama bayanin bai ce komai ba,amma ya miƙomin hannayensa na fara yimasa
alwalar. Cikin nutsuwa nake yimasa alwalar har na gama tsaff.
Rigar dana zo da itah na taimaka masa yasaka,yanda bazata shafi ciwon ba,kafin na
juyashi ya kalli gabass,magriba yafarayi wacce ake binsa kafin ya fara da rama
sallahr asuba tun sanda aka jimasa ciwo.
Daki daki yake bin sallahr ina zaune ina kallonsa,daga baya daya gaji sai na koma
ta baynasa ina tallafamasa. Muna daɗe a haka har akayi sallahr isha ya tsaya da
ramakon yayi,ganin yana haki yagaji yasa ya tsaya dayi sai ya huta tukunna.
A bayansa nake ya jingina dani,saiji nayi ya kwanto akan cinyata,kallon fuskata
yakeyi,yayinda nima na sunkuya ina kallonnasa,mun daɗe a haka idonmu a sarƙafe dana
juna,saida naji hannunsa akan fuskata kafin na dawo zahiri..
Magana yafara a cikin wata murya da banyi tunanin yanada itaba.
"A ɗan zamana dake kin taka wata rawa a rayuwata,ko yaushe cikin juyewa kike da
narasa taya zan misaltashi. A lokacin danake son naga kin sake dani saiki ɗankware
jikinki,lokacin danazo yimiki barazana kuma saiki dake,idan nayi laushi kuma sai
zama jaruma,a yau kaɗai kinyimin abinda ban taba tunani ba,kin zamemin hannun a
sanda na rasa nawa,kin zamemin ƙafa da tawa taƙi aiki,kin zauna dani a wannan dokar
dajin da babu kowa a ciki saini kaɗai.
Tun farkon da mahaifinki yabani ke a matsayin fansar kuɗina naga rashin dacewarsa
nayin hakan,shiyasa na nesanta kaina dake,a tunanina hakan zaisa kiyi rayuwarki
yanda kikeso,naƙi shiga rayuwarki saboda nasan nida ke bamu dace ba ko kaɗan,amma
sai naga duk wannan koƙarin danake yatafi a banza,ke koyaushe so kike ki cusa
rayuwarki cikin tawa.
Wannan ƙasa da kan da kike idan kina gabana,da kuma neman izinina a duk wani lamari
na rayuwarki shine yayi babban tasiri wajen karya zuciyata,har tasaka na ajiye
komai na ɗauki nauyinki batareda nasani ba. Saboda tunda nake babu wanda yazo da
kansa yanemi izinina akan abu,saidai na bashi dakaina in kika ɗauke Tunga.
Sannan tun kina zuwa inda nake ina jin kin takuramin,har yazamo idan banganki ba
sai zuciyata tayi ta kewarki. Sumaimah bansan mai kikayimin a rayuwata ba amma dai
shigarki kinyi nasarar share wani a fili a ciki kin mamayeshi yazamo naki. Ciwon
kan dana tashi a rayuwata bansan lokacin dana faraba,bai taba dainawa ba indai ba
shaye shaye nayi ba sai yau,kuma dama yakan tashi ne idan na bijirewa umarnin da
zuciyata tabani,saikashi yau kin karanta min wani abu naji ya tafi batareda nasha
komai ba"
Tunda yafara magana ban ɗauke idona ba daga kan fuskarsa,shin anya kuwa gojen
danasanine yake waɗannan kalaman,meyasa yau ɗaya naga wata nutsuwa a tattare
dashi,babu wannan zazzare idon da kuma cije cijen baki..wannan gashin daya maidashi
dodo duk babu shi. Kar a ji haushina idan nace yayimin kyau fiyeda mutane dayawa a
garinnamu.
Hannuna nasaka akan nasa wanda yake kan fuskata,tareda sakin wani murmushi da
bansan ma'anarsa..
"Duk abinda kake faɗan nayi aikata a rayuwarka banice nabaka wannan
matsayinba,Allah ne dakansa yabaka a matsayinka na mijina,ni kawai umarnin da aka
bani na nayi maka biyayya,kada nayi wani abun batareda saninka ko kuma yardarka
ba,sannan na kyautata maka na kasance sassanyar inuwar dazaka zo ka hutas da
gajiyarka,na kasance tamkar dare wajen rufe sirrinka,sannan na kulada kai da
dukiyarka harma da dani kaina idan baka nan.....domin aljannata tana ƙarƙashin
ƙafarka,sai nayi hakanne Allah zai bani izinin shiga"
A yanda nake kallon idanuwansa lokacin danake faɗomasa wadannan Kalaman,naga
Abubuwa da dama wanda wasu bazan ce mesuke nufi ba. Kawai naga yashiga mamakin,shin
dama ashe yanada irin wannan matsayin a rayuwar wani,kaman nasan mai yakeson faɗa
na cigaba da bayanina.
"Tabbas hakane kanada wannan matsayin a rayuwata tsawon lokacinnan,koda wasu zasu
gujeka suyi nesa dakai. Ni kaiɗin jigona ne,kuma mahaɗin rayuwata,wanda rayuwata ta
riga ta ɗinke da taka tun lokacin da ɗauramin igiyoyin aurenka a kaina,shiyasa duk
abinda zakayi wanda bai dace ba zaifi yimana ciwo nida inna sa'banin sauran mutane"
Hawayen daya zubo acikin idona ne ya sauƙa akan kumatunsa,sai sannan ya ƙifta
ido,da ya tsaya tamkar wanda ya daskare a cikin ƙanƙara.
"Shin dama har haka na shiga rayuwarki,nayi tunanin dan an ɗaura aure ban kulaki ba
bakomai,to idan harda waɗannan haƙƙunan da suke kanki wanda dole saikinyimin kenan
nashiga rayuwarki dayawa,na rabaki da rayuwar da kike hankalinki kwance idan babu
ni a ciki..kinmin abubuwa da dama,dan haka banaso ki cigaba da zama kina amsa sunan
matar mutum kamanni,musamman daya kasance kinada ilimi mai yawa da kuma sanin
yakamata,zalunci ne na ajiyeki a cikin rayuwata...zan sake..........".
Kiff bansan lokacin dana rufe masa baki ba ina jijjiga kai.
"Karka fara faɗin wannan kalmar,dan Allah karka furtata a gareni,da lokacin daka
aka kawoni gidanka ne ka faɗaminsu zanyi farinciki da jinsu,amma a yanzu dana
fahimce ka bana fatan jin wannan kalmar daga gareka,karka faɗesu ka fiddani a cikin
rayuwarka"
"To amma meyasa naga......"
"Saboda na hango wata rawa danake son takawa a rayuwar taka,hmmm bazaka sani bane
amma kanada wani hali da mata zasu zaga mazaje dayawa basu samu mai irinsa ba,duk
da sunaso su samu ɗin. Kai tamkar zinarene a cikin duhun dare,rana bata haskashi na
ballantana a gane wanne irin haske yake ɗauke dashi.....koda babu hasken rana ka
bani dama nazamo fitilar dazata haska shi,ta yanda kaikanka zaka hango irin hasken
da kake ɗauke dashi......dan Allah ka yarda dani,sannan ka bani damar ragamar
kulada rayuwarka,kar nesanta ni daga gareka,ta hakanne zamu gano inda matsalar take
kuma mu gyara.....ni har cikin zuciyata na amince dakai a matsayin mijina,kuma bana
fatan naga ranar da zanyi nadama da ƙiranka da wannan sunan"
Magana nake kawai ina kwararowa abinda yake cikin zuciyata,duk da yanda muryata ke
rawa saboda yanda maganganun suka tabani.
"Tunda nake ban taba yin alaƙa da wata mace ba bayan inna sai ke,a da hakan haushi
yake bani,amma d kaɗan kaɗan nakejin wani abu na mannani da rayuwarki. Yanzu ma
dakikaji na faɗa bawai son raina bane,saidan zanyi hakanne saboda ke,amma tunda
kinji kingani ra'ayinkine zaki zauna tareda ni. Nikuma namiki alƙawarin bazan taba
guje miki ba,kuma zan kyautata miki na faranta miki daidai yanda zan iya,sannan
kaman yanda kika buƙata nabaki jan ragamar dukkan lamurana"
"Naji daɗin maganar ka kuma nagode,nima kuma nayi maka alƙawarin Inshaallah
bazakayi danasanin yarda dani ba"
Shuru ne ya ratsa tsakaninmu,saikuma naga ya jare hannunsa daga fuskata yana riƙe
kai. A yanda na kula kaman irin abinda yayi jiyane,hakanne yasa na ɗauke hannunsa
na mayeshi da nawa.
Addu'o'in danayi jiya na neman sauƙi nafara karanta masa,wanda yawanci sunayen
Allah ne da yayi umarnin a ƙirashi dasu,sai fatiha da kuma su QUL guda uku.
Maimaita masa nashigaba dayi bayan naji yayi shuru ma,a haka har nima bansan
lokacin da baccin ya ɗaukeni ba anan zaune.

___***___

"Me kikace abbanku ya dawo?"


Hajiya Maryam tafaɗa cikeda damuwa tana kallon fatee.
"Ehh mommy yanzunnan ya shigo gidan,naga ya nufi sashensa bai shigo cikin gidaba"
Tana cikin bayanin hajiya maryam tanufi sashennasa tana tafiyar karairaya kaman
wata ƙaramar yarinya.
Ƙwanƙwasawa tayi,jin shuru ba'a amsaba yasa tasaka kai cikin ɗakin.
A tsaye yake a gaban window yana kallon lambun dayake bayan ɗakinnasa,kana ganinsa
kasan faɗawa yayi cikin zurfin tunani.
"Me yasamu wannan babban jarumin naganshi a haka,kaddai kacemin har yanzu baku samu
inda barayin sukeba,kuma sun gudu da akwatin baku kamasu ba?"
Tafada kaman mai jin tausayinsa,amma kanaki kasan ta biyu take zancen.
Zan ajiyar zuciya A.M Aliyu yayi tareda cewa.
"Maryam,waishin yaushe zaki girma ki daina wannan abunne kam iyeee,ƴaƴan ki ma
bazasuyi abinda kikeyi ba,yanda kikeyi haka kikeso ƴaƴan ki suje gidan mijinsu suyi
ne? Ace tsawon sati guda ba nan ina office,duk akan wani abu daya shigemin
duhu,amma daga dawowata babu magana mai daɗi sai ta izgili? Shiyasa fah banshiga
gida ba bare ki ganni,amma saida kika biyoni kina murnar na faɗi koh ?"
"Uhm dagajin yanda kake magana baku kamasu ba da alama,kenan wannan akwatin dayake
ɗauke da bayanai masu hatsari yana hannun 'baya gari"
Juyowa yayi yana kallon hajiyah maryam,wacce take tsaye ta dan goce irin tsayuwar
celebrity ɗinnan.
"Shin wai tukunnama taya kikasan cewar kundin a akwati yake,a tunani na dai bamuyi
wannan zancen dake ba,kuma ko a kafar yaɗa labarai ba'a faɗa ba,taya kika sani?"
Tsareta yayi da ido tareda yimata kallon tuhuma,wanda hakan yasaka jujjuya ido
tareda cewa.
"Ehh dama zaka fara yanzu,dan kasamu ma na kula dakai nazo ina tambayarka shine
zaka faramin wannan kallon rashin yardar,tun batan Ahmad kakemin irin wannan kallon
na rashin fahimta"
"Ohh dama 'bata yayi ba mutuwa yayi ba?"
Gum tayi da idonta tareda nemo abinda zatace.
"Mutuwa nakeso nace,kaima ai kasan mutuwar yayi tunda har gawarsa an kawo maka.
Nida wannan abinda kakemin na ƙin raba sirrinka dani kokuma kana tuhumata ka
daureni mana kawai ka huta iyee. Kaje cibiyar bincike kace zaka ɗaure matarka
dayafiye maka"
Masifah ta cigaba dayi,ta inda take shiga ba tanan take fita,saida tayi mai isarta
ta fice daga ɗakin tareda buga ƙofar.
Runtse ido AM Aliyu yayi tareda ɗora hannunsa a kansa.
Yana jin takun tafiyarta har tayi nisa.
Shin me yayi mata kuma wai itace dayin fushi,shine ya kamata ya ɗau mataki amma duk
sanda yayi yunƙurin yin hakan sai yaji ya kasa.
Gabaɗaya gidan mutane uku ne za'a ce daidai,daga Mammah,saleem sai Noor,su kaɗaine
zaka gansu da sanyin hali. Amma Sameer kam da fatee kana gani kasan ita suka iyo.
Shikuwa Ahmad lokacin dayake nan gwanda kowama dashi,domin ko sashensa a can gefe
yake,bayason ana yimasa katsalandan,saidai kaima bazai maka ba.
Sannan yanada basira da sanin mai yake,komai shine yake zuwa a fari kafin
sauran ,hakanne yasa kullum hankalin hajiyah maryam yana kansa,in za'ayi masa abu
ma ita ke shiga da fita ta hana,shikansa yasan da hakan. Shiyasa ko sashenta baya
taba zuwa sai yakama dole.
Kaman yadda AM Aliyu bai yarda da ita ba hakama Gen Ahmad,don daff da mutuwarsa ya
buɗe wani file akan ta,tunda ta tafi kuma babu wanda yasake bi ta kan zancen har
yau.
Tsohuwar lauyace mai zaman kanta,duk da yanzu bata aiki,amma kuma tasan takan
binciken abinda take son sani sannan kuma da yanda zata gujewa mai son bincikarta.
Tana da son mulki da son ganin ana mata hidima,don ko shi kansa AM Aliyu dayake
shugaban sojoji bai kaita juya sojojin ba,kuma tanada mutanenta a cikinsu,wanda ko
mai tace karsu faɗa babu wanda ya isa ya sakasu magana harda shi kansa uban gayyar.
Wannan abubuwan su suka sa kowa hatta ƴaƴan ta suke shakkarta inta juyo ta kansu
inka cire Ahmad shikaɗai ne baya tsoronta,kuma shine ciwon idon dayake hanata bacci
lokacin dayake raye,yanzu kuwa da baya nan baccinta take sha harda minshari.

Littafi na ɗaya ne dana biyu kaman yanda na sabayi,na ɗaya bati siddan,na biyu kuma
Naira 300 ne dan haka zaka iya biya tun yanzu kafin a shiga kashi na biyu.

3131951977
Auwal Sadiya
First bank

Ko katin mtn ta nan


09035784150

VTU ta nan
2347068390570

Shaida kuma ta nan


09035784150

Ƴan niger ku tuntubi wanann number.


+227 97 21 16 15
----------------------------------------------------

Sadi-sakhan ceh
09035784150
Share please
*SANADIN CACA*

Mallakar SADI-SAKHNA

PROFICIENT WRITER ASSOCIATION

*USERNAMES*
FACEBOOK PAGE:Sadisakhna
WATTPAD:@SAKHNA03
AREWABOOKS:@sadeesakhna
PHONE NO:09035784150
________________________________
*Book 1*
Chp[28]

[Sumaimah a mahangar gani]

Yau kimanin sati guda kenan da zaman goje a bayan garin,kwana uku nayi ina jinyarsa
sosai,dakuma kwana dashi. Dagan nanne ya hanani zama sosai,sai Tunga ne yake kwana
dashi.
A iya satin kawai har yasamu sauƙi yana tashi dakans,kasancewar dama jikine yasan
wahala.
Yau banje wajensa ba,gyaran ƙofar tasa nakeyi,dan jiya da naje yake cemin yau zai
dawo gida.
Inna batasan yana garin ba,ita a zatonta daga can wajen aikin zai dawo,dama kuma
bayason tasan halinda yake ciki.
Kayan ɗakin na fitar dukka wannan tarkacen,iyah katifarsa na bari sai sallaya da
kuma akwatin kayansa,sauran shirgin da baza'ayi amfani dasu ba zubarsu nayi,wasu
kuma nakaisu ɗakin gefen inna..
Wani kuwa nashashi tun safe nake har rana tayi,dana gama na ɗora girki. Yau ba
makarantar safe weekend ne sai islamiyya kaɗai,itakuma banje ba.
Saida na gama abincin rana nayi wanka nayi sallah kafinnasamu na zauna,inna sai
sannu take jeramin.
Kursiyyah ce ta shigo ƙofar tamu hannunta ɗauke da ɗa kwano,wanda nasan awara ce.
Bayanta ajiye kwanon abincinsu wanda muke zuba musu ta ɗauka,dan dama sun saba
yanzu ko magana basayi ɗauka kawai suke....shuru kowa yana ƙofarsa ta ciki na ciki.
Sai bayan la'asar na ɗauko qur'ani kenan zanyi tilawa naji muryar Tunga shida
goje,har yanzu duk sanda naji motsinsa ko kuma muryarsa sai gaba yaɗan buga
ɗinnan,wanda bansan menene dalilin ba. Tun da rana nake jiran dawowar tasa,har na
haƙura tukunna suka shigo.
Ban tashi daga inda nake ba inaji har suka shigo cikin ɗakin innan.
Akan kujerar da take ɗakin ya zauna,yasaka kayansa wanda yatafi dasu baƙaƙe.
Gaisawa suke da inna amma kana ganin kasan yasha wahala a tafiyar da suka iyo
ɗin,yana daurewa ne kada ya nuna rauninsa.
Shi Tunga tun a tsakar gida ya koma,wanda nasan goje yace masa ya tafin.
Ido muka haɗa dashi ya kashemin ido guda ɗaya ,ɗauke idona nayi tareda ajiye
qur'anin nafita daga ɗakin.
Kofarsa na nufah nasake gyara komai,ruwa na kai a jug mai sanyi wanda shine dama
bankai ba kada yayi ɗumi.
Hucin numfashinsa nafara ji a bayana,dan dama najiyo takun sawunsa.
A gadon bayana ya kwantar da kansa tareda saƙalo hannayensa ta cikina,tsayawa nayi
daga tashi tsayen ina sauraran numfashinsa wanda yake fitar dashi kaman mutum yayi
gudu.
"Kinsan nagaji meyasa kika taho kika barni a ɗakin inna,daƙyar fah na iso wajennan"
"Hhhhh sannu toh,a mashin kukazo ne daga can?"
"Uhmm a gashi duk gonakin mutanene a hanyar,sai jijjiga ni Tunga yake tayi a
hanya,wajen ciwo yakemin kaman yanzu nayi raunin"
Jin abinda yafaɗa yasa nafara ƙoƙarin cire hannunsa daga kunkumina,amma kuma sai ya
sake riƙeni kaman zai maidani ciki.
"Kace wajen yana ciwo,yakamata a duba kar ko ya buɗe,sannan ka haɗa gumi yakamata
kayi wanka kaci abinci,saika sake shan maganin"
Cikin nuna damuwa nake maganar,ai yayi ƙoƙari ma da nice da wannan ciwo bazan iya
tashi ba.
Tashi yayi daga bayannawa ya dawo kan katifa ya zauna,ɗakin yake ƙarewa kallo baki
buɗe.
"Wow dama ɗakinnan yanada girma kaman haka,ban taba saniba saboda shirginsa,gaskiya
kinsha aiki sosai na gyarashi"
Ƴar dariya nayi tareda matsawa na cire masa canvas ɗin ƙafarsa.
"Tohh yanzu abinci zaka faraci kokuma wanka zakayi?"
"Uhm bari naci abincin,dan yunwa nake ji sosai,sannan inason shan magani,saboda
tafiyar danayi wajen yana min ciwo sosai"
Yaƙarisa maganar harda lumshe ido yana maida numfashi. Ganin yanda yake bansan
lokacin dana kai hannuna ba na bude maballin rigar,wajen da ciwon yake nake
kallo,hatta fatar cikinsa ma tayi ja,saidai bayyi jini ba alama yafara kamewa
kenan.
"Uhm take it easy mana madam,sauri kike har haka ne?"
Yanayin magana na kulada yanda na ɗora hannayena akan cikinsa,saurin janyewa nayi
tareda matsawa baya. Me yake damuna ne haka,yaushe na fara ɗaukar taba jikinsa ba
komai bane ba.
Dariya yakeyimin tareda ƙarisa cire rigar gabaɗaya ya ajiye a gefe.
"Uhm nagode da kulawarki,hakan yana yimin daɗi idan naga kin damuwa da halinda nake
ciki,sannan karki damu bazan ɗauki komai ba dan kin taba jikina,ya hallata a
garekine ba shiyasa kika taba ba uhm?"
Ohh kunya ce takamani naji kaman na nutse a ƙasa,maza fa daman sun iya zarar zance.
"Yawwa yanzu naji kayi turanci dama ka iya ne?"
Nayimasa tambayar dan ya manta da waccar maganar,kaman hakan kuwa yayi
tasiri,dannaga ya tafi tunani.
"Turanci kikaji nayi,uhm zai iya yiyuwa,dan wani lokacin mutane kan faɗa cewar
inayi,ko karanta rubutu danake kawai gani nayi ina rubutawa,amma ban tuno
makarantar danayi ba kuma"
"Taya ya hakan zai kasance toh?"
"Uhm ta haka mana,zubamin abincin naci inason shan maganinnan"
Zancenne yaƙare a haka na zuba masa abincin kaman yanda ya buƙata.
Har yashiga wanka ya fito ina zaune a ɗakin,dan cewa yayi kada na tafi na
jirashi,daga shi sai gajeran wando ya shigo yana goge kansa da,wani ƙaramin ƙyalle.
Ɗauke kaina nayi,amma sai naji ya zauna a kusadani har muna gogar juna...ohh wannan
sabon hali na goje na kasa gane kansa sam.
Mai yasaka na miƙo masa yafara shafawa,shuru mukayi dagani harshi babu wanda yace
komai.
Tashi nayi zan tafi ya riƙo hannuna,
"Ina kuma zakije,ni kaɗai zaki tafi ki bari a ɗakin?"
"Uhn zan ɗora girkin dare,Sannan ba kace bacci zakayi ba?"
"Oh na tuna,to ki dunga zuwa kina leƙowa akai akai harna tashi"
"Hhhh to shikenan yanzu na tafi?"
Ɗaga kai yayi kaman baya so,wai dama wannan bawan Allah haka yake ne,kokuma yanzu
ya koyi waɗannan abubuwan..
Bayan na fito inna tayi mamakin daɗewata a wajen gojen,amma batace komai ba,nima
kuma banyi maganar ba.
Ina cikin jajjaga kayan miya naga ya fito daga ɗakinnasa ya fita,ƙananan kayane a
jikinsa yana tafiya normal ba wannan bubbuɗawar. Ko ciwonne yasakashi oho..
Tsayawa nayi daga abinda nake na zubawa bayansa ido yana tafiyar,saida yaje saitin
zaure ya juyo muka haɗa ido.
Kunya ce ta rufeni ganin yakamani ina kallonsa,da hannu yayi min alama
nazo,fuskarsa ɗaukeda murmushi.
Zatona wani abu zaicemin,sai kawai ji nayi ya sumbaci goshina,tareda ɗallamin
yatsarsa kuma a wajen duk lokaci guda.
Shafa wajen nayi tareda turo baki.
"Meyasa dana juyo kika ɗauke idonki kaman wacce nakamaki kina laifi?"
"Dama zaka iya fita ne?"
"Silly girl na kula wani lokacin idan bakyason bani amsa saiki yimin tambaya koh"
Hannu yakawo zai sakeyimin ɗall amma wannan karon na koma gefe ina dariyah,shima
murmushi yayi tareda cewa.
"Zanje wajen su dunga ne karsuga shuru bayan sunsan nadawo"
"Banda bawa mutanen gari tsoro"
Nafaɗa ina komawa cikin gidan da sauri,yanda nasan bazai dawo ya kamani ba.

__***__

"Wayyo Allah nah"


Wani yaro yasaka kuka ana cikin karatu a aji. Malaminne ya tsaya da karatu tareda
juyowa yana kallon yaran ajin,wanda yayi kukan ya kalla tareda tambayarsa mai
yafaru.
"Kai tashi,miye kake yiwa mutane kuka a aji?"
"Malam Deejah ce ta sokamin wani abu a wuyana"
Tun kafin malamin yayi magana tayi caraff tace.
"Malam bacci yakeyi a aji kana karatu"
Jijjiga kai yayi tareda riƙe kai,ya akeso yayine da wannan tantiriyar yarinya,duk
ajin yarane masu shekaru biyar zuwa bakwai,amma ita shekararta kusan sha uku,dukka
tafi yaran aji girma. Shi ba abin yace akaita aji sa'anninta ba babu abinda ta
iya,in yayi kokarin cewar a koreta kuma abokinsa Musbahu ne ya roƙeshi akan ya
barta a ajin.
"Zo nan kizo ki tsaya a gaban aji"
Yafaɗa a zuciye,tahowa tayi tana kallon ƙasa kaman wata ta Allah.
"Karanta min Kul'azubi rabbin nass naji,tunda shi bacci yakeyi ke ai idonki biyu
ina"
Wuri wuri tafara da ido alamar bata ma san mai yakecewa ba,sai wuss wsusss takeyi
kawai ta bakinta.
Bulalar hannunsa ya ɗaga ya zambaɗa mata a gadon baya,sake zura mata yayi,aikuwa
take ta kwarara ihu.
Ƴan ajinne suka sheqe da dariyah ganin yanda take tsalle tana dadare.
"Malam aradu ya isheka,dan kaga abokaina basa biyoni cikin wannan makarantar taku
ne ina ko,wlh zaka fito daga ciki ai saina ƙona ka kurmus mungu kawai,ku kuma ni
kukeyiwa dariya koh,idan na dawo gobe sai nayi muku shegen duka"
Tana gama faɗan hakan ta fita da gudu daga ajin.
Hanyar gidnasu tanufah tana ihu,duk inda ta shige sai an kalleta,amma ko a
jikinta..
Tana yankowa kwanar gidan turuss tayi da suka haɗa ido da Musbahu a zaune a ƙofar
gidan.
Raragefe tafara zata shige gidan taji muryarsa.
"Zo nan wato da girmanki kika zagaye anguwa kina kuka kaman mahaukaciya koh?"
Dawowa tayi gabansa ta zauna a ƙasa,har sannan bata daina kukan ba,wanda yasan na
iskanci ne bakomai ba.
"Menene me aka miki,iyanzu ba'a tashi daga makaranta ba,meyasa kika taho"
"Haka kawai wannan abokinnaka mai gemun bunsuru sai yayi ta dukana ban masa komai
ba,ai aradu dan yaga abokaina basa bina cikin makarantar ne shiyasa yakemin abinda
ya dama,da duk saina ƙone makarantar naga tsiya"
Shuru Musbahu yayi yana nazarin maganar tata,tunda yake da ita bata taba maganar
wasu abokanta ba sai yanzu.
"su waye abokanan naki?"
"Uhm uhm kona fadamaka baka sansu ba,sannan sunce kada na faɗawa kowa waye
su.....nidai bazan koma makarantar nan ba"
"Zaki koma mana khadija,makaranta ai yanzu kika fara,saidai in kinaso nayi fushi
dake na daina saya miki shayin safe toh,idan nasiyo abuna da daddare ma na daina
baki"
Zaro ido tayi,da alama batason aikata abinda yace ɗin.
"Zan dunga zuwa toh,amma wlh ni na tsani wajennan banasonsa,nafison wannan ta
safen,saidai ita daɗewa ake ba'a dawo gida ba. Kuma ma in gaskiya ne naga ƴan gidan
basa zuwa makaranta,kowa in yace bazaije ba barishi ake saini za'a takurawa"
Kan gari ya gari take maganar tana kuka kaman ance sai ta faɗa dole.
"Yau bakiyi wanka ba ko"
"Uhm taya ka gane baka gidan,nasan ma faɗamaka akayi banyi ba,gidannan akwai ƴan
baƙin ciki buhu"
Dariya Musbahu yayi jin tambayar tata lokaci guda.ba wai sanin yayi ba,kawai dai
yasan idan ya tambaya zaigane tayi ko batayi ba
"Tun bakiyi wanka ba yau babu abin daɗi,kuma kika gudo daga makaranta,tashi ki
shiga gida."
"Nashiga uku ka bari yanzu zan shiga gida nayi wankan,makaranta kuma bazan sake
gudowa ba,amma kacewa abokinnan naka ya daina dukana toh"
Tana gama faɗan hakan tashige gidan da gudu. Dariya Musbahu ya dungayi ganin wauta
irinta Deejah. Haka kawai yake tausayinta,yarinyar tana buƙatar tallafi na gyaran
rayuwarta,wanda in ba'a taimaka mataba zata tashi kaman gara.
Allah ya gani yayi niyyar inganta rayuwarta daidai ƙarfinsa,gashi kuma wani satin
yake shirin tafiya interview na shiga soja,dama ya daɗe yana son tafiyar,sai yanzu
yasamu nasara.
Ga kuma wani abu daya gano a wajen Deejah,aljanun da take tareda su ba ajikinta
suke ba,zaman ta a jeji ita kaɗai da rashin kula yasa suka zama makusanta fiyeda
mutane ƴan uwanta,shiyasa mutane ke ganinta kaman itmaa ba mutum bace.
Dan haka Maganin dayake tunani bazayyi wuyar yi ba,muddin tana shiga cikin mutane
tana alaƙa dasu akai akai,sannan tafara yin karatu musamman na addini akwai alamar
zasu iya barinta.
Wanda yasan babu mai iya yimasa wannan aikin sai Sumaimah,indai tana tareda itah
zata iya taimakonta,amma ta yaya.
Tana gidan mijinta yaushe zai ɗora mata wani nauyi da bai shafeta ba,duk da yaji
ana labarin rayuwar gidan ba kaman daba,shikansa mijinnata yanzu yanada nutsuwa
sosai,wanda shima yaga hakan da idonsa a tattare da itah lokacin dataje asibiti.
Ganin abun kaman bazai yiyu ba kawai barin zance yayi a ransa.

Littafi na ɗaya ne dana biyu kaman yanda na sabayi,na ɗaya bati siddan,na biyu kuma
Naira 300 ne dan haka zaka iya biya tun yanzu kafin a shiga kashi na biyu.

3131951977
Auwal Sadiya
First bank

Ko katin mtn ta nan


09035784150

VTU ta nan
2347068390570
Shaida kuma ta nan
09035784150

Ƴan niger ku tuntubi wanann number.


+227 97 21 16 15
----------------------------------------------------

Sadi-sakhan ceh
09035784150
Share please

*SANADIN CACA*

Mallakar SADI-SAKHNA

PROFICIENT WRITER ASSOCIATION

*USERNAMES*
FACEBOOK PAGE:Sadisakhna
WATTPAD:@SAKHNA03
AREWABOOKS:@sadeesakhna
PHONE NO:09035784150
________________________________
*Book 1*
Chp[29]

[Sumaimah a mahangar gani]

Tun lokacin da Goje ya fita har dare yafara kafin ya dawo,ina kwance akan gadona na
ɗakin inna najiyo muryarsa yana ƙirana.
Shuru na ɗanyi saida inna tace
"Sumaimah ba ƙiranki yake bane?"
"Uhmm eh"
Kaina a sunkuye naje bakin kofar ɗakin,saidai ban ganshi ba da alama ya yi ƙofarsa.
Dan haka hijabina na saka akan doguwar rigar jikina na nufi ƙofar tasa.
Ɗakin a bude yake amma baya ciki,da alama yana bandaki,dan haka zama nayi akan
katifa ina jiransa.
Ganin yaɗan daɗe yasa nayi tunanin inaga wanka yakeyi,hakanne kuwa dan shigowa yayi
dagashi sai gajeran wando.
Bai min magana ba ya fara shafa mai,nima bance masa komai ba ina nan zaune. Sai
bayan yagama kafin yazo inda nake ya zauna,kallona yake kaman mai nazari yakasa
cewa komai.
Duk da cewar babu wani wadataccen haske iya na wayarsa ne daya kunna amma ina ganin
fuskarsa.
"Meyasa baki bude wannan abunba da kikaga ina wanka?"
Saida yayi magana na kulada ledar da take tsakar ɗakin,sakkowa nayi na buɗe,tsirene
a cikin yaki albasa.
"Lahh ban gani bane shiyasa"
"Uhm toki ɗibama inna kema kuma in zaki ji sai......."
"Wai anya kuwa inna zataji yanzu,dan yanzu muka gama cin abinci,nima kuma gaskiya
ba lallai ba,amma barina tafi dashi koh?"
Nafada inason barin ɗakin,danna kula babu wani abu dayake buƙata,kawai ƙirana
yayi,sannan yasamu sauƙi sosai bare yace da wani abun zan taimaka masa.
"Ahah tunda kun ƙoshi shikenan ajiyeshi kawai sai kuci da safe"
Na ajiyeshi,ba tafiya zanyi ba sai na tafi dashi kawai ai.
"Uhm naga nima tafiya zanyi to...."
Dariya yayi min tareda cewa.
"Ki tafi inaaa,aikin dawo ɗakin mijinki kekam,daga yau ban yadda ki dunga kwana a
ɗakin inna ba,nan ne ɗakinki"
Dumm gabana ya buga,ban taba tunanin hakan nan kusa ba.
Hannuna ya zawo ya zaunar dani a gefensa,wanda hakan yasakani ajiye ledar da take
hannunnawa. Kallona yake cikeda sigar damuwa da neman taimako wanda bansan na
menene ba.
Hannayennawa yahaɗa dukka biyun a cikinnasa,tareda tattaro dukkan wani sauran
nutsuwarsa,nima ganin hakan yasa na kafeshi da ido.
"Sumaimah nine na koreki da ɗakinnan a zuwanki na farko,a yau kuma na buɗe baki ina
rokon daki zauna a cikinsa,ko kaɗan bawai tilastaki zanyi ki zauna dani ba,illah
iyaka ina son hakan. Kiyi haƙuri da abubuwan dasuka faru a baya waɗanda nayi
miki,bazan ce ki manta dasu ba,amma please kada ki ƙullaceni akansu. Dan Allah ki
zauna dani ƙarƙashin inuwa ɗaya,idan kin amince dani kaman yadda kika faɗa,ki bani
damar shiga a rayuwarki a yau ɗin,idan kinga kuma abin yayi miki sauri ki faɗamin
zan barki kiyi nazari akai"
Bayan yagama maganar shuru yayi domin yaji mai zance,ganin nayi shuru yasa ya murza
hannaye na.
Ajiyar zuciya na saki tareda cewa.
"Ba....bansan mai zance ba takamaimai akan wannan maganar,abinda ya faru da baya ya
riga ya wuce wanda dama hakan ake fata a manta dashi. Batun nadawo kwana ɗakinnan
kuma idan hakan ka buƙata to dole shi zanyi,saboda gidanka ne kuma ikonka ne,inda
kaga dama ka sakani matuƙar bawai cutarwace ta shigaba dole anan zan zauna.
Sannan kana alaƙar aure kuma haƙƙinka ne daman,kaine da baka biɗa ba tunda. Zan iya
hanaka idan da a bayane baka ciyardani ba baka tufatar dani ba. Amma a yanzu idan
nace baka ɗaya daga cikinsu nayi ƙarya,dan kayimin wanda ban tsammata bama. Dan
haka ka buƙaci samun nutsuwa dani na hanaka saboda wai kayimin ba daidai ba a baya
bai tasoba"
"Hmmm naji daɗin bayananki,sannan ina jin daɗi a duk lokacin dakika faɗomin
matsayin da nake dashi a wajenki,amma a yanzu ra'ayinki na buƙata ba wai matsayina
ba,na yanke shawarar son fara rayuwa dake,sannan banason batun musgunawa ko cutarwa
yashigo ciki. Shin kina ji a ranki nayi cancantar da zaki iya miƙamin amanar
kanki?"
Wannan tambaya ta taba zuciyata sosai,ni wacece da bazan amince ba. Zare hannuna
nayi daga cikin nasa tareda saqalasu ta bayan wuyansa,kuka na fara na
farinciki,ganin lokaci guda kaman almara Allah ya karkato da hankalinsa gareni,ya
kasance namiji mai nutsuwa da ban taba tunani zai zama,idan wani yace a lokacin
baya zan kasance a tsakanin kafaɗun goje to zan iya rantsewa ƙarya yake. Amma yanzu
sai nake ganinsa kamar yafi sauran mazan garin ma sauƙin kai.
Hannunsa naji yasaka yana bubbuga bayana,mun dan ja lokaci a haka kafin nazare
hannayennawa,a yanzu kuma ina kan cinyarsa a zaune.
Naso kafin na bashi kaina kona shirya yin mu'amala ta aure dashi sai yaƙara nutsuwa
da kuma sanin addini sosai,amma tunda ya buƙata ɗin zan amince masa,wataƙila hakan
yaƙara tasiri wajen gyaruwar tasa.
Ina cikin tunanin naji bakinsa akan nawa,bansan lokacin daya iso kusa har haka ba.
Kwantarni yayi akan katifar a hankali,tareda ƙoƙarin maidani cikin sahun jerin
matan aure masu albarka. Lokacin danaji mai afkuwa tana shirin afkuwa saurin buɗe
bakina nayi tareda karanto Addu'ar da ma'aiki muhammad (SAW)ya umarcemu dayi,dan
nasan gogan koda ya iyata ma bata ita yake ba a lokacin,abune dama da bai dameshi
ba yanzu ake ƙoƙarin ganar dashi.
Nasha wahala ba kaɗan ba a wajensa,duk da cewar yayi iya ƙoƙarinsa wajen ganin bai
min ta ƙarfi ba,amma halitta ta da tasa ba ɗaya bace.
Bayan komai ya lafah shuru naji yayi lokacin daya gangara ɗaya barin katifar,zato
na idonsa biyu,saida naji minsharinsa kafin na jijjiga kai,wato a wannan yanayin
najasar shi bacci yayi abinsa.
Tashi nayi da ƙyar ina cije baki na ɗaura zanina,jikina banda tsami babu abinda
yakeyi,abinka da ban saba wannan dambarwar ba.
Randarsa na leƙa naga akwai ruwa a ciki,godiya nayi ga Allah kafin na ɗiba na
nashiga banɗakinsa domin tsaftace jikina.
Lokacin dana fito har baccinsa yafara nisa,ruwan dayake hannuna na yarfa masa,nayi
sa'a kuwa ya juyo yana kallona.
"Ka tashi ka tsaftace jikinka,bai kamata ka kwanta da najasa ba,ina ka iya wankan
tsarki ko"
Tashi yayi ya zauna yana kallona,ba fuskata yake kallo ba,dan haka sai na bi inda
yakalla,kan kirjina idonsa yake,kasancewar iya zaninne kawai jikina..
Hannuna na saka a wayance na tare saboda kunyar data kamani..
"Uhm badai wannan wankan bane da ake wanke bangare bangare na jiki,na iya shi
mana,na kanyi innayi mafarkin wata......wanann kam maza dayawa ai sunayinsa..
Meyasa kike kare jikinki,bayan yanzu naga......."
"Am na bar maka ruwa a banɗaki,wataƙila zai isheka"
Da sauri nayi maganar ina nuna masa ƙofah,dariya yayi tareda dan jan hancina,dan ya
kula so nake yabar zancen..
Kafin ya dawo kayana mayar tareda yaye zanin kan gadon naɗauko wani na saka,duk da
yanda jikina yake min magiyar zai kwanta.
Ina kwanciya naji alamar shigowarsa ɗakin,yi nayi kaman bacci nake saboda in yayi
magana ma bansan mai zance ba..
Ina jinsa ya hawo kan katifar tareda jawoni jikinsa,daga ƙarshema ya ɗora kaina
akan kafaɗarsa.
"Saida safe matata,nagode sosai da kyautarki"
Yafaɗa a hankali tareda sumbatar goshina.
Zanyi ƙarya idan nace hakan bayyimin daɗi ba.

Dasafe dana buɗe ido ni kaɗai nagani a ɗakin,tashi nayi zaune ina ƙarewa ɗakin
kallo. Hannu nasaka a inda goje ya kwanta,wajen ya dan lotsa saboda nauyinsa.
Murmushi nayi ina shafa wajen,yayinda ƙwaƙwalwata tafara tariyomin abinda ya faru
jiyah..
Zabura nayi zan tashi amma naji ƙafafuna kaman lilo saboda rashin ƙarfi,haka na
manta dasu cikin dauriya na fito daga ɗakin,kaman zanyi kuka na nufi ƙofar inna.
Wayyo ni ƴasu mai zancewa inna,daga cewa jeki ana ƙiranki kawai sai kwana,nasan
kuma tana kallona zata san mai yafaru,wayyo Allah ka taimakeni.
Daga bakin ƙofar na rakabe ina kallonta,a zaune take tana saqa tukarta,gefenta kuma
rediyo tana jin labarai,kana kallon yanayin zaka san rana tayi sosai,meyasa goje
bai tasheni ba to.
Kaina ya sunkuye nashiga ƙofar,ko kaɗan naƙi bada ƙofah mu haɗa ido da inna..
Zama nayi a gabanta tareda gaisheta cikin wata munafukar murya,wadda nasan saita
nutsu tajini.
Amsawa tayi cikin fara'ah tareda tashi ta nufi ɗakin da muke ajiyar kayan abinci.
Kwanuka da ɗauko dakuma ledar tsiren jiyah,kenan gojene ya kawo mata ita da safe?
"Ga nan abinci kici"
"Uhm inna ke kikayi abin karyawar?"
"Ehh mana nice nayi,tun da sassafe goje dayazo gaisheni yace nayi abincin karyawa
bakyajin daɗi,yaran gaji ma korarsu yayi daga gidan sassafe,wai sai sun tafi
makaranta kada su dameki,nasan lokacin ko mai gadi ma bai buɗe makarantar ba. Gaji
haka tayi ta faɗa daya fita har tayi shuru"
Wayyo goje bazai gasheni ba,saikace wata ƴar sarki,wato da kansa ma yazo yafaɗawa
inna abinda yafaru,ninan nake wata haukata....kai maza kunyarsu da sauƙi.
Daukar kwanon abincin nayi daga gaban inna nashige ɗaki da gudu.
Ina shiga nasamu ta shiryamin kayana a cikin jakata tsaff.
"Inna yanaga kin shiryamin kaya koh....."
"Gojene yace na shiryamiki kayanki ki koma ƙofarsa,daga yau bazaki sake kwana a
wajen ba,kinga kuwa mai abu zai karbe kayarsa ai dole na tattaramiki kayanki,duk da
banason zaman ni kaɗai ɗin,saina ƙira su kursiyyah kwana"
Ohh jinayi kaman ƙasa ta buɗe na shige,wai dama haka yakene ko yanzu yazama haka.

.....bayan wata biyu.....


Abubuwa da dama sun faru,ciki harda sabuwar rayuwar data ɗinkeni da goje,mukayinta
cikin farinciki da mutunta juna.Na koma ɗakinsa da zama,wanda yanzu yazama
ɗakinmu,zama na dashi na gane ɗabi'unsa na sauƙin kai da kuma soyayyar dayake
nunamin babu kama hannun yaro.
Makaranta ma shine yake kaini kullum ya dawo dani. Yanzu nasan lalurar dayake ɗauke
da itah harda aljanu,na gano hakanne tun bayan bamu daɗe dafara zama tare ba sai
naga yafara sauyamin,wani lokacin ko kwana bayayi a gida.
Hakan ya dameni sosai da sosai,gashi duk yanda zanyi dashi bazai bani amsa ba.
Hakan yasa na samu Tunga na tambayeshi,baicemin komai ba kawai sai rakani bukkar da
goje ya haɗa a jeji dayayi..
Ranar har kuka nayi daga halinda yake ciki a bukkar,harma da labarin halin dayake
ciki duk ya faɗamin komai. Da ashe shine abinda zai faɗamin duk ranar dana
tambayeshi.. Nida Tunga daƙyar muka lallameshi yafito daga wajen,anan nabawa Tunga
shawarar ya ƙona bukkar,da dafarko yaji tsoro amma nace masa ya aikata bakomai..
Nikuma tundaga wannan lokacin nafara nema masa magunguna na islamic batareda
saninsa ba,ko turarene na maganin saina sakashi da sunan turaren ɗakine,tun
yanacemin bayaso yana sakashi ciwon kai har ya fara sabawa.
Ruwan shankuwa dama anan nake saka masa tofin da ake na ganyen magarya na aljanu.
Sannan na dage da kunna karatun ƙur'ani ko yawan karantawa a koda yaushe.
Yanzu ya daina yin wannan fushin da kuma shaye shayen,amma wani lokacin ko tafiya
yake sai ya tsaya kaman ya daskare,sai daga baya kuma sai ya cigaba da tafiyah,ko
zance yake sai ya tsaya kaman mai son tuno abin. Tsoro ne yafara shigata da wannan
sabon halayen,wanda hakan yasa nasake dagewa na yimasa maganin a boye,yanzu har da
daddare idan yana kwance saina ina tofa masa Addu'o'i,amma maimakon naga sanji
saima gaba gaba dayakeyi.
Duk kuma wannan abun da akeyi babu wanda yasani dagani sai Tunga,saboda baya shiga
cikin mutane sosai. Soyayyarmu da mu'amalarmu bata sanja ba ko kaɗan,dan ko yana
waje yaji ciwon kai da sauri yake dawowa wajena,nikuma sai nake amfanj da wannan
wajen bashi maganin batareda yasani ba.
Yauma a zaune yake akan kujerar daya saka a ɗakinnamu,ruwan Addu'ar dana karbo a
wajen wani mai magani nabashi,cemasa nayi na ciwon kansa ne,dan haka bayyi musi ba
ya karba. Bayan ya shanye miƙomin kofin yayi na ajiye.
"Sumaimah inason yin tafiyah zuwa gwagwalada yau,amma ba kwana zanyi ba"
Innalillahi badai waɗancan mutanen bane da mukasamu wata biyu bayyi zancensu ba.
Aikuwa sune dai.
"Sun gano ina raye har sun nemi naje meeting ɗin dazasuyi yau ɗin,bai kamata na
boye tamkar matsoraci ba,inason na tunakresu na kuma faɗamusu cewar na fita daga
ƙunyarsu"
Ajiyar zuciya nasaki na jin daɗi ganin ya yarda zai fita daga shirginsu,dan dama
sunyi magana da wani dan auguwar kan zai fara safarar shinkafa dashi,nayi farinciki
sosai danaji yadaina dabanci zai fara sana'a irinta sauran kamilallun mutane.
"Eh to hakan yayi,amma dai bazaka je da wannan jakar ba ko?"
"Uhmm kekam yadameki da jakar nan,waya sani ma ko kinfi damuwa da itah kanni"
Yafaɗa yana sauya fuska,zama nayi akan cinyarsa tareda kama kumatunsa ina murmushi.
"Ni na isa,kawai dai ina tunanin danshi zasu nemeka ne,sannan indai har za'a dawo
dakai garinku ace ka kulada ita,to tanada matuƙar muhimmanci"
"Uhm hakana kam bazan je da itah,idan kuma naga sunsan tana wajena to zan san yanda
zanyi"
"Inaso na faɗamaka ma yau nakeson zuwa gida,rabona da zuwa tun lokacin danaje baba
yana asibiti"
"To shikenan kije,dama nima bana nan,za'a bar inna ita kaɗai yaukenan"
"Eh kam,amma da kaɗau Tunga ku tafi mana tare,kaga kowani abune ma biyu yafi ɗaya
ko a wajen ƙirge"
Da bai yarda da zancennawa ba,amma a hankali nashawo hankalinsa ya yarda zasu tafi
su biyun a mashin ɗinsa. Kasancewar bamuda nisa da can ɗin.
Sai bayan ya shirya yafita daga gidan kafin nima na shirya... Tunda ya fita nakejin
faɗuwar gaba wacce bansan ta mecece ba.
"Allah dai yasa alkhairi ne"
Nafaɗa a raina.

Littafi na ɗaya ne dana biyu kaman yanda na sabayi,na ɗaya bati siddan,na biyu kuma
Naira 300 ne dan haka zaka iya biya tun yanzu kafin a shiga kashi na biyu.

3131951977
Auwal Sadiya
First bank

Ko katin mtn ta nan


09035784150

VTU ta nan
2347068390570

Shaida kuma ta nan


09035784150

Ƴan niger ku tuntubi wanann number.


+227 97 21 16 15
----------------------------------------------------

Sadi-sakhan ceh
09035784150
Share please

*SANADIN CACA*

Mallakar SADI-SAKHNA

PROFICIENT WRITER ASSOCIATION

*USERNAMES*
FACEBOOK PAGE:Sadisakhna
WATTPAD:@SAKHNA03
AREWABOOKS:@sadeesakhna
PHONE NO:09035784150
________________________________
*Book 1*
Chp[30]

Goje baya nan,dan haka da ƙafata na taka zuwa gidan,kasancewar ba wani nisa ne
dashi sosai ba.
Lace ne a jikina mai kyau a jikina wanda goje yayimin,sai hijabi dana saka da
takalmi,naƙara fari da ƙiba ainihin siffah ta ta jin daɗi ta bayyana,ko makaho ya
shafani yasan na sanja fiyeda da..
Sallama nayi daga shigata gidan,kasancewar ƙofarmu na dan ciki saida na gaisheda
matan dake wajen tukunna.
Suma kallona suke da mamakin sanjawar tawa.
Wucesu nayi zuwa ƙofar tamu,ammi tana zaune da tiren gyaran shinkafa a gabanta,faɗi
in faɗa suke da rammah wacce take daga cikin ɗakinta.
"Haka kawai dankin rainani kinga bana magana,lokacin da aka kawo Sumaimah nina
ɗauketa,wannan kuma har an baki kice wajena zata dawo? To naji da nawa tarin gayyar
mana,ba kayanta dazan ɗauka,kuna nan dake da itah mutu ka raba,indai kin auren
ubanta. Yo ubanta mana tunda ya riga ya lakato ai dole ya tanɗe"
Sallama nayi ganin abinnasu ba ƙarewa zayyi a lokacin ba.
Ammi ce tafarayin shuru tareda ɗagowa ta kalleni,murmushin ƙarfin hali nayi mata
kana na zauna a wata ƙaramar kujera a gefenta.
"Lahh Sumaimah kece a gidan"
"Ammi na sameku lafiya ya gida?"
"Uhm gida kam gashinan mana,kekam ai kinji daɗinki,muna jin labarin goje ai a gari
yazama tamkar ba shiba"
Uhm kawai nace,daga zuwa sai zancen daɗi kawai,koda yake haka gidannamu suke,basuda
aiki sai zancen ayi auren yarinya ta huta,a ga mai take sakawa kokuma mai take
ci,sannan ya kuɗin mijinta.
Wata maganar da rammah tayine ta katseni daga tunanin.
"Ahh lallai kam,tayi bulbul da ita ga zahiri nan ma harda shigar ciki,da alama
shine yasaka ta kyan bawai zallan jin dadin bane yanda ake tunani"
Wani takaici ne ya cikani amma haka na shanye,wai basuda abin faɗa sai wannan
ne,ita kam inna rammah ko gaisawa bamuyi ba da itah,tafara zancen da bai shafeta
ba.
"Ammi ina baba kuwa,ko ya fita?"
"Wai ya fita,tun safe ya tafi akan magana gonarsa rabin,ya siyar da ɗayan ai kuɗin
ya bata,shine har kika samemu a asibiti wancan karon,to zancen ya tafi yau ma..
Shiga ɗaki ki cire hijabin mana,sannu da zuwa ya innar gojen?"
"Tana nan ƙalau"
Hira muka dan fara tabawa,wanda yawanci na abubuwan da suka faru bana nanne,muna
tsaka da haka najiyo kukan yarinya tundaga bakin shigowa gidan,saikuma muryar
Musbahu yana magana kaman mai faɗa.
Butt suka shigo a ƙofar yana riƙe da hannayenta,sai dadare take tana jijjiga kai.
"Kayi min rai yaya Musbahu wlh bazan sake fasawa kowanne yaro goshi ba daga
yau,Allah da gaske nake"
Ihu take kan gari ya gari kowa na jiyota a gidan,abinda yabani mamaki babu wanda ya
kulada sha'anin,har inna ma batace komai ba sai cigaba da tayi da aikinta. Hakanne
yasa na gane cewar Deejah ce yar baba uwaisu daya samo a caca,wacce nake jin
labarin ta..
Bulalar hannunsa ya zuba mata a gadon baya,ta kuwa sake ƙara saurin kukannata,ganin
bazan iya jurewa ba yasa na tafi da sauri na karbeta,lallai itama wannan da sakarci
take,ta kusana girman jiki amma take abin yara haka.
Haƙuri na fara bashi tareda janyeta daga hannunsa,har sannna bai kulada ni ba sai
dukanta yake.
"Kayi haƙuri yaya Musbahu duka baya magani ko kaɗan,kada ka jimata ciwo a garin
gyara"
Sakin hannunta yayi ta zube a wajen tana burburwa. Shikuma sai numfashi yake sakewa
kaman wanda yayi faɗa da bijimi.
"Hmmm ƙyaleni Sumaimah na koya mata hankali,bakisan abinda tayi bane shiyasa,ɗan
shugaban makarantar fah ta rotsewa kai,kuma a hakan bai isheta ba za'ayi mata
hukunci ta zazzagi malaman da sunyi jikanu da itah,shine yanzu suka ƙirani kan naje
na tafi da itah sun koreta a makarantar. Wannan fah itace makaranta ta uku dana
sauya mata,banida buri illah naga tayi hankali,amma ita da alama ba hakanne a ranta
ba,a na tausayinta bata tausayin kanta"
Yana nunata yake maganar,kana gani kasan ransa ya baci sosai. Maida idona nayi
kanta,tana sunkuye tana rira kaman wata ƴar bori.
"Kayi haƙuri yaya Musbahu komai da sannu zai wuce kaman bai faru ba Inshaallah"
"Hmm Allah yasa,sannun ki dazuwa ya gidan?"
"Lafiya kalau nake"
"Barina je na dawo,yawwa inaso muyi magana dake amma barina sauya kaya tukunna"
To nace masa daga nan yafita daga ƙofar,komawa nayi wajen zamana na zauna ina
kallon Deejah wacce ta dasa aikin kuka a tsakar gidan,kayan makarantar tata sunyi
butu butu dasu. A yanayin girmanta bai kamata a ace tana haka ba. Su ammi har akayi
aka gama babu wanda yayi ko tari a cikinsu,da alama sun saba ganin hakan ba yau ne
farau ba.
Wata kazace tazo zata wuce,aikuwa takai mata cafka kaman wata kuliyah,saurin
tsallakewa tayi ta gudu domin ta tsira da ranta.
Wata mata ce daga cikin matan gidan tayi magana.
"Ahah dakata kada ki huce akan kazata bataji ba bata gani ba,inkuwa kika kasheta
saina faɗawa wanda ya dakekin ya ƙara miki"
"Yiiii Ki faɗa ɗin mana,ina ɗan ki zaizo kwanciya da daddare koh,wlh saina sanja
masa kamanni,ƴar matsiyata kawai"
Zaro ido nayi ina kallon yarinyar,wai dama haka take ashe,babu wanda tabari a gidan
da jarabarta,gaba ɗaya ta zame musu ƙarfan ƙafa. Shikam uwaisu yanzu ko hanyar
gidan cacar bayayi,gani yake kaman za'a ƙara bashi wata Deejah. Wancan satin
ɗakinsa ta shiga zata yankashi d wuƙa a hannunta,wai taji labarin bai kawo kuɗin
cefane ba kuma yunwa take ji. Tunda bazai ciyarsu ba toh bashida amfani. Tun daga
ranar kullum sai ya iyo cefane yakawo gidan,ko yana dashi ko shida shi,dan daga
taga ba abinci zata fita neman sa a garin,kowa ma yasan hakan.
Shiyasa ba shiri ya maida hankali kan sana'arsa,gashi sai taga Musbahu baya nan
takeyi,ba wanda kuma ya isa faɗamasa in ya dawo saboda yana tsoron ta huce akansa.
Nidai na daɗe a nan zaune ina kallon ikon Allah.
"Khadija ki tashi a ƙasannan haka,babu kyau mace ta dunga zama a ƙasa,Sannan kinga
kayanki duk sun baci da datti kaman ba babbar yarinya ba,ko so kike yara su rainaki
kai?"
Cikin sigar rarrashi da jan hankali nayi maganar,yanda zai ɗau hankalinta. Aikuwa
nayi nasara,dan tayi shuru dayin kukan,amma bata daina tofah yawu a gaban hijabin
ba.
"Kinga shi wanda aka dukaki akansa yana can yayi shuru kuma bai bata kayansa
ba,idan ya ganki cewa zayyi ashe ma ba ƙarfine da itaba,tunda ni nayi shuru ita
kuwa tana kuka,zaice ma yafiki ƙarfi,hakane?"
"Ahah wlh nafishi ƙarfi,niba sa'ar sa bace"
"Yawwa to kin gani,kuma inkina faɗa da maza darajarki da mata zata zube,ko so kike
duk inda kika wuce a dunga cewa ga wannan wacce take faɗa da mazan"
"Na daina toh"
Tashi tayi daga ƙasan tafara kakkaɗe kayanta,a dole ita kar a ce tayi datti,hakan
da tayi ba ƙaramin dariya yabani ba,batada girman kai kaman goje,a haka ne mutum
zai gansu sunada wuyar sha'ani,amma idan mutum ya zauna dasu a hankali zai gano
sauƙin kansu.
Gyaran murya Musbahu yayi ,ashe yana wajen lokacin da nake magana da Deejah,har ta
tashi daga wajen ta nufi ɗakinsu..
"Ban taba ganin tayi abu cikin ruwan sanyi batareda duka ba sai yau,da alama magana
zata iya yin amfani a kanta kenan"
"Hhhh yaya Musbahu kenan,shin akwai wanda magana bata tasiri akan sa ne,har zaki ma
ai yana jin magana wani lokacin"
"Abinda ya faru har yasake tunamin abinda nake son faɗa, wani satin zan tafi
training na aikin sojoji,shine nakeson barmiki kulada Deejah a hannunki,bawai zata
zauna a wajenki bane,illah dai koda sama sama ne ki dunga bincikar ya take,sannan
ki ɗan ja ta a jiki tasan abubuwa a matsayinta na ƴa mace,yanda zata kula da kanta"
Dallla dalla yakemin maganar ina saurarensa,haƙiƙa ya burgeni sosai,kuma nayi na'am
da wannan taimakon dayake shirin yi,harni ma yasakani a ciki,mai zai hana na
taimaketa kuwa,indai abinda zan iyane.
"Ba damuwa yah Musbahu karka damu,Inshaallah zanyi iya kokarina,kai kuma Allah
yabaka sa'a ya tsareka daga mungun abu da mungun nufi"
"Ameen ya Allah nagode sosai"
Muna cikin hirar ne naji wayata tayi ringing,ɗaukowa nayi nasan bazai wuce goje
ba,ko ya faɗamin sun isa..
Da murmushi na na ɗaga wayar,saidai abinda naji a ɗaya bnagarenne yasa yanayin
fuskata ya sanja nan take,jikina ya tsaya da aiki na wani lokaci,iyah ƙwaƙwalwata
ce kawai take aiki sai jinin dayake bugawa a cikin zuciyata kaɗan kaɗan.
Sakin wayar nayi ta faɗi a saka yayinda fatar bakina tafara rawa ina rarraba idona
akan su ammi da yah Musbahu.
"Ya....yahh yah Musbahu mmmi.....mijinah ya Musbahu mijina kukaini wajensa yanzu na
roƙeku"
Ganin nafara maganganun da bansan mai nake cewa ba ne yasakashi ɗaukar wayar dan
yaji mai naji..
"Hello hello Sumaimah kina jina,muna general hospital anan gwagwaladan sun shiga
dashi emergency,saboda kansa ya bugu sosai"
"Ba ita bace yayanta ne Musbahu,Tunga bai kamata ka fada mata,wannan maganar
ba,yanzu dai karka damu gamunan zuwa garin,yanzunnan zan kawota"
Yana kashe wayar ya fita waje da sauri,jan lilon ƙafata nayi dasauri na bishi
wajen,saboda kada ya tafi ya barni,dan ji nake idan bangnashi ba bazan iya sukuni
ba.
Ina fita naganshi yana tada mashin ɗinsa,ban tsaya tambayarsa ba kawai na ɗale.
Gidana muka tafi domin sanarwa inna abinda yake faruwa,a Ƙofar gida ya tsaya nikuma
nashiga ciki domin sanarwa mata.
Tana zaune da tukarta a gabanta daga na faɗo gidan ko sallama babu,kaman banice
mukayi sallama da itaba na tafi gida ɗazu..
"Hasbunallahu Sumaimah lafiya na ganki haka kaman an jefo ki?"
"Inna goje yayi hatsari inna kizo muje da sauri mu ganshi"
"Innalillahi wai inna ilaihi raji'un yanzun ke daga ina kike?"
"Uhn tare muke da Musbahu a mashin ɗin sa zai kaini. Inna karki damu ki shirya
barina je inyaso saiki taho"
Ina faɗamata hakan nafita daga gidan batareda na jirata ba,saboda bana cikin
hankalina ko kaɗan.
Tafiya muke a mashinɗin amma gani nake kaman baya sauri.
Munsha iska kam saboda tafiyar da ɗan nisa sosai,amma ko kaɗan bata wannan nake
ba,burina na isa naga mai yake faruwa dashi..
Kai tsaye babban asibitin muka wuce,bamusha wahala ba tunda munsan inda aka kwantar
dasu,wato a emergency..
Muna shiga ward ɗin wajen bada suna muka nufa,bakina har rawa yake wajen fadamata
sunan wanda aka kwantar.
Muna cewa goje suka gane,dan sunan da Tunga ya shigar kenan.
"Am sorry madam patient ɗinku yana dakin tiyata basu fito ba tukunna,amma ku shiga
ɗakin can akwai wanda aka kawosu tare"
Bin hanyar data nuna mukayi ,ina gaba Musbahu yana bina a baya,ɗakin mukashi anan
nayi arba da Tunga a kwance an naɗe ƙafarsa da bandeji..
Cikin sauri na isa bakin gadonnasa,cikeda zumuɗin jin amsar tambayata,duk kuwa
yanayin Tunga ma bamai daɗi bane,amma daga gani zai iya magana.
"Tunda mai yafaru,ya akayi kukai hatsari,meya sameshi,yaji ciwo sosai,zai tashi
ko........"
Yah Musbahu ne ya dafa kafaɗa saboda ya tsayar dani daga tambayoyina marasa adadi.
"Ki kwantar da hankalinki Inshaallah zai samu lafiya"
Ya Musbahu yafaɗa cikin tattausar murya.
Muryar Tunga naji wanda dama ita nakeson ji yanzu,saboda amsoshina.
"Nima wlh Sumaimah bansan mai ya faru ba,kawai muna cikin tafiya yana
tuƙawa,shigowarmu garin kenan kawai sai gani nayi yasake kan mashinɗin kaman wanda
ya suma,kafin na ɗagoshi har mota ta hau kanmu,kasancewar shi baya cikin hayyacinsa
shiyasa buguwar tayi masa mummunan rauni akai. Shine mukazo a asibitinnan,amma
batun sauƙi kam saidai a wajen Allah"
Ban gama jin maganar Tunga ba naji wata nurse ta shigo.
"Am wacece mrs goje"
Ɗagowa nayi tareda kallonta,itace wacce ta nuna mana ɗakin Tunga.
"Am sorry to say,amma likita yace kuyi shirin tafiyah babban asibiti a abuja,domin
yasamu ciwo sosai a kansa,ko motsi bayayi har yanzu. Ki kwantar da hankalinki fah
zai samu sauƙi"
Hmmm zancen kwantar da hankali takemin a wannan yanayin..
A bakin gadon Tunga na zauna ina yaƙi da numfashi na dayake cikowa.
Ina cikin wannan yanayin inna ta iso,itama dataji abinda yake faruwa ba ƙaramin
kiɗima tayi ba.
Ƙarar tura gado naji irin na aikin tiyata,hakan yasa na tashi tsaye ina kallon masu
turowar,mutumin dana rabu dashi ɗazu muna zance,shi ake turomin akan gado kaman
gawa.......

Littafi na ɗaya ne dana biyu kaman yanda na sabayi,na ɗaya bati siddan,na biyu kuma
Naira 300 ne dan haka zaka iya biya tun yanzu kafin a shiga kashi na biyu.

3131951977
Auwal Sadiya
First bank

Ko katin mtn ta nan


09035784150

VTU ta nan
2347068390570

Shaida kuma ta nan


09035784150

Ƴan niger ku tuntubi wanann number.


+227 97 21 16 15
----------------------------------------------------

Sadi-sakhan ceh
09035784150
Share please

*SANADIN CACA*

Mallakar SADI-SAKHNA

PROFICIENT WRITER ASSOCIATION

*USERNAMES*
FACEBOOK PAGE:Sadisakhna
WATTPAD:@SAKHNA03
AREWABOOKS:@sadeesakhna
PHONE NO:09035784150
________________________________
*Book 1*
Chp[31]
Nice nafara takawa zuwa inda gadon yake,yana kwance an nannaɗe kansa da bandeji da
kuma ƙafarsa ta hagun,ganin fuskar tasa nayi kaman mai bacci,amma nasan ba haka
bane,a sume yake da babu dama nayi ƙiransa ya amsamin.
Hawayene yake jirarowa a cikin idona,na ɗan samu lokaci a hakan kafin inna ta
janyeni suka wuce dashi zuwa motar asibitin..
Bayan an sakashi a ciki nice na shiga sai inna,sun turamu asibitin abuja,bayan mun
saka hannu a takardar yarda da hakan.
TH suka turamu inda za'ayi masa aikin akannnasa,biyan kuɗi kuma yana garemu kenan.
Tafiya muke a cikin motar asibitin,idona yana kan goje wanda yake kwance kaman
gawa,ban san wanne lokaci muka ɗauka muna tafiya ba,domin ba wannan ne a
rainaba,sai jin nafito naji kawai.
Fuskata tayi shabe shabe da hawaye,da suka turashi neurology department ɗin ji nayi
kaman nabishi mu shiga tare,amma nasan bazasu barni ba.
Waje muka samu muka zauna,a duk cikin mu ukun babu wanda yake cewa komai.
Shikam yah Musbahu tunda yaji cewar abuja zamu taho bai biyomu ba,sai ya koma
faɗawa sauran yan gidanmu. Tunga ma a halinda yake ciki bazai iya biyomu ba,saboda
jikinsa bai hutaba tukunna,saidai yace zai taho gobe da kuɗin aikin,wanda nasan a
cikin wannan jakar kuɗin gojen zai ɗauka.
Kaina na kwantar a jikin inna,duniyar tayimin zafi na rasama abinyi,banda bugawa
babu abinda zuciyata takeyi,kowanne daƙiƙa tunani nake shin zasuyi nasarar yimasa
aikin kokuma ahah.
"Kiyi haƙuri ki saka tawakkali aranki Sumaimah Inshaallah zai tashi kaman bayyi
ba,abin kam zai taba miki zuciya,musamman yanda kuka shaƙu dashi a wannan lokacin"
Abinka da wanda ya ciko an rarrasheshi,kuka na rushe mata dashi tareda
ƙanƙameta,itama ganin hakan yasa ta juyo tana bubbuga bayana.
A hakan a wajen muka kasance har goshin magriba,in lokacin sallah tayi muyi musake
dawowa mu zauna,Addu'a kuwa nayi har bansan abinda nake faɗa ba.ina cikin yin
Addu'o'i bayan na idar da sallahr magriba naga sun buɗe ƙofar wajen tiyatar sun
fito dashi,da gudu na tashi har ina tuntube na nufesu,dakatar dani sukayi kafin
nakai ga inda yake,wata nurse ce ta tsayar dani,tareda yimin alamar nayi haƙuri
ba'ason hayaniya kusada shi.
Ɗaga mata kai nayi ina binsu kaman raƙumi da akala har zuwa ɗakin da za'a kwantar
dashi ɗin.
Kana ganin yanda suke kasan a cikin nutsuwa suke saboda tsaro,nidai nida inna kallo
kawai muke binsu dashi har suka gama.
"Yawwa kece matarsa koh,munyi nasarar janye jinin daya shiga cikin kansa,amma zai
ɗau ɗan lokaci kafin ya tashi,kafin sannan muna buƙatarki a office,mama kekuma zaki
iya zama a wajensa kafin ta dawo,amma fah banda yin motsi mai sauti sosai.
Toh inna ta ɗaga musu kai tareda zama akan kujera a ɗakin,yayinda nikuma na bisu
office ɗin..
Yawanci dai bayanai sukayi tayimin na abinda yafaru,naji daɗi sosai da suka ce
aikin yayi kyau zai tashi babu wata matsala. Murmushi nakeyi har haƙorana suna
fitowa da sukace zai tashi nan da kwana uku..
"Yawwa sai biyan kuɗin aiki a ƙa'ida saikun biya a fara aiki,munyi muku ne saboda
asibitine suka turoku,amma ku tabbatar kun biya xuwa gobe"
"Inshaallah zamu biya doctor mun gode sosai da sosai"
Tashi nayi da murnata zan rafi,sai naji yayi magana ƙasa ƙasa..
"Nikuwa ina nasan wani mai irin fuskar wannan mutumin?"
"Ehh doctor kace me?"
"Ahah bakomai zaki iya tafiya wani hasashe kawai nayi"
Ban kawo komai a raina ba nakoma wajen inna,inaga ba dani yake bama.
Nida ita muka kwana a ɗakin gojen,duk da ma ba motsi yakeba ballantana ya buƙaci
wani abun.
Washagari da safe Tunga suka taho shida Musbahu,sun taho mana da kaya wanda zamu
buƙata a zaman.
Sannan a lokaci kaɗan suka gama cuku cukun biyan kuɗin aikin,daɗin abu dana miji
kenan.
Rayuwar asibitin muka kama gabagaɗi ba kama hannun yaro,a kwana uku dukka munyi su
ne ba gajiya,da tunanin goje zai tashi ya buɗi ido kaman koyaushe yacigaba da
hidimar sa,saidai me.....anyi kwana huɗu daren na biyar yana shirin shiga ko motsi
bayyi ba,wannan abu ya saremin gwiwa fiyeda yanda mai tunani zai tuna. Tun ina kuka
a gaban inna ganin tana shiga damuwa yasa nake shiga banɗaki nayi naƙoshi.
Likitoci abu kaɗan su shigo su dubashi,in sun gama gwaje gwajensu saisu ce mana
lafiyarsa ƙalau yanzu,ko yaushe zai iya tashi,tun ina yarda dasu yanzu na gane
ƙarya suke tunda bai tashin ba..
Jiya naje gida na dawo,damma munyi hutun makaranta,yau kuma inna ce ta tafi gidan
gobe zata dawo,sannan tare zasu taho da kawunta daya keso yazo yaga jikin gojen.
Maganganu take bani na ban baki,tareda ƙarfin gwiwar cewar zai tashi,itama yanzu
jinta kawai nake tareda cewa toh.
"Ni zan tafi Sumaimah dan Allah kada ki sakashi a gaba kin wannan kukan da daddare
ki ƙiyin bacci,shima kin san bazai so ganinki cikin damuwa ba"
"Shikenan inna saikin dawo"
Ban amsa mata yin kukan ba,saboda nasan konace bazanyi ba sai nayi ne"
Bayan ta tafi banɗaki na shiga na ɗauro alwala,karatun kur'ani nayi na tsawon
lokaci kafin bacci ya kwasheni,saida naji muryar wata nurse kafin na farka. Sister
Fauziyya ce mai zuwa duba goje,a satin da mukayi a wajen har munyi sabo da itah.
"Ahhh baccine haka kikeyi,ko kin kishingiɗa ne bayan kinyi magriba,dan gashi har
tara ta kusa"
Zaro ido nayi tareda miƙewa ina kallon gaban wayata,tara saura na dare,nida na
kwanta tun huɗu da wani abu.
Wannan wanne irin bacci ne nake haka kaman marar lafiyah,cikeda mamaki nashiga
banɗaki na sake dauro wata alwalar domin yin sallolin.
Kallonsa nake nayi tagumi,ciwon dayake jikinsa har sun fara warkewa saboda yana
samun kulawa,amma shikam yaƙi tashi har yanzu,na daɗe idona biyu har cikin dare.

___***___

A hankali ya buɗe idonsa ya daidai hasken yanda zai iya ɗauka,kallon farin cilin
yake da tunanin mai kuma ya kawoshi nan?.
Tashi yayi ya zauna yana kallon ɗakin,asibitine mai ya sameshi aka kawoshi
asibiti,koda yake inaga lokacin da motarsa tafaɗinnan yaji ciwo shiyasa suka kawo
shi asibiti.
To amma ina mommah take da Madeena ko hajiya maryam batazo ba yasan su zasu zo.
Gefensa ya leƙa inda wata mace ke kwance ta kifa kanta da gadon tana bacci. Da
alama ƴar aikice,ya faɗa a ransa yana yatsine fuska,amma waye zai kawo yar aiki
harta zo kusada shi haka..
Tafiya yake a hankali har ya fita daga ɗakin,kasancewar yasan asibitin shiyasa
baisha wahalar zuwa bakin titi ba,da sasafene kuwa taxi sai wucewa suke. Wani ya
tsayar tareda yimasa kwatancen inda zai kaishi. a cikin motar kallon jikinsa yake
tayi ganin yanda yayi baƙi fatarsa tayi tauri,ko yana tsaka da mission iya
kaci,haushi abinda yabashi,hakan yasa ya yiwa mai taxi ɗin magana.
"Am malam please ko zan iya ganin wayarka yanzunnan"
"Ranka ya dade wlh ba caji"
"Mts kaga kaini security headquater daga nan"
To yace masa tareda karya akalar motarsa,bayan ajiyeshi shuru yayi saboda bashida
kuɗi,ganin haka yasa mai taxi ɗin cemasa ya barshi kawai,tunda wajen ma ba nisa.
Kai tsaye cikin wajen yashiga office ɗin Sadeeq abokinsa,shi anan yake aiki.
Baizo wajen aikin ba,amma dayayi bayani ƴan wajen sun barshi ya shiga.
Yana nan zaune akan kujera yaji alamar buɗe kofar,yana ɗaga Kai sukayi ido biyu da
Sadeeq,wanda yayi saurin jefar da wayarsa tareda cewa.
"Gen Ahmad Aliyu Hamma"
Cikin rawar murya yana nunashi.
"Kai Sadeeq wai lafiyarka kuwa,ko kaima kaga yanda jikina ya koma kai?"
"Dagaske kaine AA Hamma a gabana wai,duk tsawon shekarunnan a ina kake toh"
Yafaɗa yana zare idanuwa kaman yaga aljani,duk da sanyin safiya amma gumi yake
zubawa.
"Shekaru wanne iri?"
Sadeeq bai bashi amsaba sai nuna masa calander da yayi,wannnan karon Ahmad ne
yashiga razanin,saurin riƙe kai yayi tareda saka wata ƙara ta wahala.
"Sadeeq mai yake damun kaina ne,tunda na tashi nake jin kaman zai tsage"
Yana gama faɗin hakan ya kwanta a kan kujerar kaman ya suma.
Ganin hakanne yasa Sadeeq ɗaga waya ya ƙiran Abban su Ahmad ɗin,saboda ya sanar
dashi abinda yake faruwa..

__***__

Tun wayewar safiyar Sumaimah take neman goje a asibitin bayan ta tashi amma shuru
bata ganshi ba,har rana tayi inna tazo itada ƙaninta,abin yabawa kowa mamaki sosai.
"Inna banga mijina ba ya bata inna,wasu sun ɗaukemin shi bai tashi na ganshi
ba,shin wanene yake shirin rabani da mijina innaa... Inna kice su dawomin dashi,ban
taba cewa ina sonshi ba,ina so na nuna masa soyayya innaaaaaaa ahhhhh"
Tunda safen Sumaimah take jin wani abu yana hawanta,amma bata san menene har zuwa
yanzu daya ci ƙarfin ta faɗi..
Abu goma da ishirin,ga batan goje ga kuma faɗuwar Sumaimah,cikin asibitin aka
maidata da gaggawa,kowa a zatonsa rashin ganin gojenne yasakata yin haka,amma ana
gwadata aka gano tanada shigar ciki na wata uku,ga kuma jininta ya hau saboda
tension ɗin data sha a kwanakinnan.
Dan haka asibitin suka Kwantarta ta samu hutu tukunna..
"Mairo wai yaronnan anya kuwa ba hankalinsa ya dawo ba shiyasa ya tafi,dama ina
kince baisan komai nasa ba sanda kuka tsinceshi,hatta sunansa baya tunawa?"
Kawu ya faɗa ƙanin inna mairo,zatayi magana kenan sukaji muryar Sumaimah a bayansu.
"Inna shin mai kunnuwana suka jiyo kina cewa,dama bake kika haifi goje ba,to su
waye suka haifeshi,daga ina yake? Shin menene asalinsa,danginsa da kuma sunansa ma.
Inna dan Allah ki faɗamin,inna gudan jininsa ne a yanzu a cikin cikina,nayi saton
na sanshi kuma na fara fahimtarsa,ashe ba haka bane,taya zayyimin irin wannan nisan
a lokacin da mukeda buƙatarsa haka?"
Zubewa Sumaimah tayi a wajen tareda rushewa da wani zazzafan kuka.....

Toh fah Jama'u anan fa littafi na ɗaya zai dasa ayah,tunda malam goje kam ya koma
ga rayuwarsa ta ainihi,da alama bai san wani shafi ma da aka rubuta Sumaimah a
cikinsa ba a rayuwarsa ballantana ya duba..........

Nagode nagode nagode da kuka biyo a sannu a cikin wannan littafi na SANADIN CACA
Book 1 .......masu buƙatar son jin cigaban labari inda wasan zai fara sai su antayo
min 300 na zuba a asusuna nasha mai mu cigaba da tafiyah,inda zaguji amsar waɗannan
tambayoyin.

#shin dama ashe goje shine Ahmad?.

#waye sanadin shigarsa rayuwa a matsayin goje?

#wacece Madeena da Ahmad ya ambata lokacin daya farfaɗo?

#Wa kuke zargi da yimasa wannan tuggu?

#Ina labarin akwatin da aka bawa goje,Ahmad baisan dashi ba?,sannnan waye shugaba
na biyu dana ɗaya na kungiyar BC?

#Allah sarki Sumaimah shin ya zatayi,wacce ƙaddara ce zata sake haɗata da,wannan
miji nata wanda bai san da ita ba sam?.
#Irin waɗannan buhuhhunan cakwakiyah dana tafka anya ni SADI-SAKHNA zan iya warware
su kuwa?

#domin jin zan iya ko bazan iya ba miƙomin 300 da fari tukunna tanan
3131951977
Auwal sadiya
First bank
😊😊😊

Ko kuma ku tuntubeni tanan 0903578415

SADI-SAKHNA ce dai wacce kuka sani mai GIDAN GANDU da kuma BAƘAR AYAH ,wanda
yasansu yasan tsarina......

Muhaɗe a littafi na biyu,ni nayi nan da ikon rabbis samawati,Allah ya yafemana


abinda mukayi ba daidai ba.

Bye.........

You might also like